Noor Albi

NOOR ALBI 47

Mamuhgee 47_*
Parking motocinsu sukai a harabar gidan,

A Abdoul ne yafara fitowa motar dayake ciki zaune a gaba sai Ruky a sit din baya,

Motar da Turakin suke ciki ya nufa da niyar bude Masa sai gashi ya bude da kansa tareda zuro qafafunsa Dake sanye da black Camilo Italian leather loafers ya fito motar.

Hannu ya miqa Mata ahankali ta Kama zuciyarta na bugawa ta fito motar sanyeda Ash turkish abaya da light Ash gyale akanta nade.

Handbag dinta ma qarama ce sosai sbd yanzu batason masu girma suna damunta,

Ahankali ta zare hannunta daga nasa Bayan fitowarta motar sbd tasan yanzu Kuma ita dashi sai kallo daga nesa tunda suna gida daya da mum Na’ima gakuma Anne.

Kai tsaye Sashen Annen Suka nufa Ruky da A Abdoul tuni sukai gaba da Suitcases dinta zuwa bangaren Annen,

Ahankali jiki a matuqar sanyaye take tafiya gashi kamarma yanzu tafi ganin girman cikin nata,

Dan Haka duk tabi ta sake shiga halin firgici da damuwa…

Suna gap da Isa su shige babbar kofar dazata sadasu da babban palon bangaren Annen motar Ms Na’ima ta sako Kai harabar gidan ita ke tuqawa da kanta Haj Zinat na gefenta zaune
Kowaccensu cikin Shiga ta alfarmar manyan Mata Kuma matan masu abin duniya…

Motacin Turakin da aka daukosa daga airport dake sarari a pake ta kalla kalla batareda idonta yakai Kan gabansuba hanyar Sashen Annen
Tana kokarin parking tace”

TURAKI ya dawo kenan¿Amma dazu da mukai waya baicemun yau zai dawo din ba,
Zinat shiyasa nake fada Miki Turaki ya……

Haj Zinat da tun shigowarsu idonta ya sauka kansu Laylan dake kokarin Isa kofar bangaren Anne
Batareda ta dauke idontaba akansu cikin zallan mamaki da shakkar abin datake gani a idonta tace”

Na’ima Kamar fa mace Mai ciki ce tareda turakin gasu can zasu shige gurin Anne……

Baammmmm…..wata irin qara Mai qarfi ta tashi na buga motar gabansu da Na’ima tayi ba shiri sbd zancen Zinat…

Ware idonta tayi a bangaren daidai sun sunshige lokaci daya atare….

Bata kashe motarba barewa tsayawar ta bude kofa tana kokarin fita Zinat cikin tashin hankali biyu da biyu ta riqota tana cewa”

Tsayar da motar ki kashe tukuna kafin ki kashemu da sauran kwananmu a gaba..

Tsayar da motar tayi Amma Bata tsaya kashewaba ta fito
Tana cewa”

Zinat wlh itace ya kawo gidan,
Anne ta sane kenan,
Aikuwa yau za’ayi budaddiyar wasika kowa ya dauki sakamonsa….

Gaba tayi har tana tuntube saura kiris ta kife,
Haj Zinat da sauri ta fito tabiyo bayanta batareda itama ta tsaya kashe motarba sbd Ganin ko ganin gabanta Na’iman batayi,

Tasan Sarai Yau mahaukaciyar hauka zata buga idan tayi Ido biyu da Matar Nan,
Yau Babu maganar aro hauka koina original tata din zata buga abarta,

Itakuma bazata yarda ba Na’iman tayi abinda zaisa agane lalurarta gwara ta bita ta danneta duk da itama dazata samu damar idonta idon Matar data rigasu daukan cikin Turaki da hannunta zata halakar da cikin kafin ita Daga baya sayi lokacinta.

Anne ce zaune a Palo tana Amsa wayar Sa’adah cikin kwanciyar hankali nutsuwa,

Palon sai qamshin Turaren wutar YERWA INCENSE yake tashi tareda sanyin Ac da hayaqin Oud Dake fita ahankali daga qatuwar humidifier Dake can gurin hanyar kofar shigowa palon.

Shigowar A Abdoul da ruky Dake janye da set din akwatinan Louis Vuitton guda hudu yasata kallonsu da mamaki akan fuskarta,

Ruky data gefe tana gaidata cikin tsananin girmamawa ta kalla kafin ta kalli A Abdoul din shima tace”

Abdoul-Hameed baqi mukayi ne da Kaya Hakan?

Fara gaidata yayi cikin girmamawa da sakewar Dake tsakaninta dashi yace”

Ms Laylah ce ta dawo..

Da sabon mamaki Mai girma ta Kuma kallonsa murmushi na sauka Kan fuskarta tace”

Laylah Kuma?
Zuwan bazata ba sanarwa….

Shigowar Laylan ne yasa ta dakata da maganarta tana zuba Mata dukkanin idonta da hankalinta saidai har lokacin murmushin fuskarta Bai gusheba saima fadada da yayi
Harma batasan ta zubawa cikin Laylan idoba.

Kunya Mai tsananin girma ta Sanya idanuwan Laylan cikowa da hawaye tana Sunkuyar da Kai qasa a sanyaye take takowa..

Halima ce data fito kitchen tagansu
Aikuwa bakinta yakasa rufuwa da sauri ta ja kayan tana cewa Ruky ta biyota da sauran kayan
Suka nufi dakin Laylan tun na farko dake guri daya Dana Sa’adah
take halima tasa Ruky din ta Kama aiki suka hau gyaran dakin dukda yananan da komai na tsari da buqata acikinsa.

Sir Turakin kuwa qarasowa yayi zai gaida Annen ya wuce nasa bangaren,

Ita Kuma a silale ta nufa inda Annen take zaune tana kokarin Nemo muryarta data maqale a maqoshinta zata gaidata Ms Na’ima ta shigo palon Kai tsaye ta sallamar da kwata kwata batamasan Yaya ta fito abakintaba..

Yana ganin Na’ima ya dakata daga inda yake tsaye Bai qarasa gurin Annenba ya tsaya kallonta fuska a kame hankalinsa kwance.

Anne kuwa tashi daga zaunen datake tayi Tana qarasawa gaban Laylan Kai tsaye tace”

Wuce ciki kifara hutawa tukuna.

Duk yanda take tunanin tashin hankalin fuskantar mum dinta abin ya wuce hakan a zuciyarta sbd daukewa numfashinta yayi Jin muryar mum din daga bayanta,

Yanda zuciyarta ke harbawane yasa takasa juyowa ta tsaya cak a inda take tareda rufe idanuwanta hawayen dasuke ciki suka gangaro har sai dataji saukan muryan Anne datace ta wuce ciki.

Daga kafa tayi zata wuce batareda ta juyoba har lokacin,
Cikin tsananin bacin Rai Mai girma daya sake rufe Ran Ms Na’ima tace”

Laylah? Tsaya agurin,
Yaushe Kika dawo?
Meyasa Baki fadamun ba?
Wacece kuka dawo da ita tareda Turaki??

Cak Laylan ta tsaya agurin cikeda mamaki da fargaban yanda mum din tagane itace zuciyarta na karyewa da abubuwa da dama,

Har cikin ranta tasan Bata kyautawa riqon da Mum tayi Mataba,

Ta wani bangaren ta yarda da tabbas taci Amanar mum sbd koma yayane tayi Mata riqon ‘ya ba irin Wanda ta taso acikinsaba Amma ace itace take dauke da cikin mijin Mum.,

Da wane idon zata kallo mum data kamu da tsananin son Turakinta Mai tsananin datake Jin rabata dashi shine mafi Munin illar da zaaiwa rayuwarta….

Cikin fushi Ms Na’ima ta tinkari Laylan idonta rufe da bacin ran wadda suke boyewa da Turaki yazo da ita tana cewa”

Magana nake Miki amsa Zaki juyo kibani Raina abace yake
karki dora wani laifi akan wannan na zuwan da kikai batareda kin sanar dani b……

Hannunta Turaki ya riqo akaro na farko tun shigowarsu gidan daya bude Baki Yana kallon cikin idonta Kai tsaye murya a kame yace”

Ki nutsu banason hayaniya Anan,

Wuce,koma kije bangarenki….

Qwace hannunta tayi da qarfi tana kallon Anne idonta jajir tace”

Anne gwara ayi komai a gabanki tunda da alama kinsan komai,
Turaki Wlh nasan yanada wata macen daban bayan Ni da waccar dayar,

Najima da Dani Dan Haka gwara a fadamun meyasa za’a rufeni akan wani auren daya Kuma…..

Just shut up Na’ima,
Ki fita kibar Nan nace…

Gurin Laylah takuma nufa gadan gadan tana cewa”

Wallahi bazan fita ba sai nayi magana da Laylah kokuma tabiyoni muje ai dama nice mum dinta,
Nice nake riqonta,
Ta wuce muje da kaina zanyi magana da ita.

Kallonta Anne tayi cikin kulawa kafin tayi mgn
Baice komaiba ya Kama hannun Na’iman ya juya da ita
yana ganin Haj Zinat bayansu ya sakar Mata ita Kai tsaye yace”

Jata ku tafi.

Kama hannun Na’ima Zinat tayi dukkanin wutarta na daukewa da zallan mamaki da firgici harma da tashin hankali dan kuwa kallon tsaf dataiwa Laylah daga bayanta sbd a hangi ciki a jikinta wallahi…..

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button