HAUSA NOVEL

Rabo Ajali Episode 1 – 15

ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ﻭﺍﻟﺼﻼﺓ ﻭﺍﻟﺴﻼﻡ ﻋﻠﻰ
ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺍﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﻭﺳﻠﻢ . …..
Affan… Affan… Affan..
sau uku saurayin dake tsaye a kanshi ya kira sunanshi
amma ko waiwayowa baiyi ba bare ya amsa,, hankalinshi
na kan ruwan dake malale cikin wani katon ramin kiwon
kifin dake cikin gidansu yana kallon yadda suke wuntsil
wuntsil ciki yana girgiza kanshi da jikinshi hakoranshi waje
yana dariya da karfi,
duk wanda ya ganshi yasan hankali sam bai isheshi ba,
dafashi saurayin yayi hade da zama gefenshi ya watsa ma
kifin abincinsu nan take suka kara hautsinewa suna yawo
cikin ruwan gwanin ban sha’awa, ihuu Affan yasa yana
kaďa kanshi yana kokarin kai hannunshi cikin ramin kuma
yana nokesu alamar tsoro, saurayin yayi murmushi ya kara
watsa abincin,,, affan ya cikwikwiyeshi cikin murna yana
fadin yeeehhh Jabeer kara zuba musu yunwa suke ji dama,
jabeer ya shafa fuskarshi cikin tausayin halin da amininshi
yake ciki yace affan lokacin sallah yayi muje muyi sallah
mu dawo sai in cigaba da basu abincin,
affan ya no’ke wuyanshi kamar karamin yaro yace um um
ba yanzu zanyi sallah ba mummy tace ko da yaushe nayi
sallah dai2 ne saboda ni ba a rubuta min zunubi, Jabeer da
idonshi ya fara canza kala dan ya riga ya saba da jin hakan
a bakin affan kullum in yayi mishi maganar sallah,
cikin dabara yace waya fada maka ba a rubuta maka zunubi
Affan,
to bari kaji kasan wutar nan da ake kunnawa mai zafin nan?
Affan cikin firgici yace eh na santa wanda ake dafa min
indomie mai zafi ko,
jabeer yace of course ita ay kasan tafi indomie zafi ma ko,
affan ya gyada kanshi, jabeer yace to wutar da Allah ke
kona waďanda basa sallah tafi wannan zafi sau “dubu
malala gashin tinkiya”
affan ya mike a firgice idonshi zuru2 yace tafi wutar dake
dafa ruwan toilet heater ma wanda yake kona ni in zanyi
wanka,
jabeer yace sosai ma ay wannan ruwan kamar ruwan sanyi
ne akan wutar Allah,
affan ya fara ja baya yace karya kakeyi sai naje na tambayi
mummy,
jabeer ya mike da sauri dan yasan yana zuwa ya tambayi
mummy to fa bazata taba bari yayi sallah ba,
da sauri ya rike hannunshi yace affan ni ke karya,
ya fizge hannunshi yace eh mana kaine kake karya ya juya
ya ruga cikin gida da gudu jabeer na kiranshi yayi banza
dashi,
dafe kai jabeer yayi cikin damuwa sai da yafi minti 5 tsaye
sannan ya wuce ya tafi masallaci,,,,
Jabeer ďinne ya fada maka haka,
affan ya gyada kanshi yana daďa kwanciya jikinta alamun
tsoro yakeji kar wuta ta kona shi,
mummy tace rabu dashi makaryaci ne na fada maka ka
daina kulashi kullum burinshi ya tirsasa maka yin abinda da
bakayi niyya ba kuma ko a musulunce babu takura a addini,
rabu dashi kaji affan din daddy tashi kaje kaci abinci kayi
wasanka kaji,
ya daga kanshi ya mike yana tsalle har ya karasa gurin cin
abinci yana kiran sunan Hansa’u mai aikinsu tazo ta zuba
mishi abinci,
murmushi mummy tayi hade da ajiyar zuciya,
Salma babar diyarta ta ajiye laptop dinta tace mummy
wannan tsinannan jabir din so kawai yake ya ruguza miki
plan dinki, kullum shi kenan maganar sallah sai kace wani
sallau,
mummy tayi dariyar mugunta ta kalli gurin da affan ke cin
abinci duk yayi kaca2 da gurin amma ko digo bai diga a
rigarshi ba saboda tsananin tsaftarshi,
tace barni dashi ummu, jabeer yana wuce gona da iri
tabbas zan san duk yadda zanyi in rabasu da affan in ba
haka ba wata rana zai sa kwaba ta tayi ruwa,
Fareedah tace wallhy I so much hate him sai ya dinga wani
ďadďaga kai kamar kadangare shi a dole ga kyakykyawa
mtsww taja tsaki,
mummy tace ku barni dashi dani yake magana in yasan
wata ay bai san wata ba…..
posted by
sulaiman bomboy
Wannan yayi kuwa?

RABO AJALI ◆◆ 2 by Sulaiman Bomboy
Da gudu ta shigo gida ta tarar da jarababbiyar
kishiyar
uwarta a tsakar gida tana fiffita,
sannu da gida kawai tace bata jira amsa ba ta wuce
ďakin kakarta Hajja Giďe,
fadawa dakin tayi babu ko sallama ta cire skul Bag
ďinta
tayi wurgi da ita a kan gado sam bata kula da
mutum a kan
gadon ba ta fita da sauri ta shiga toilet, Hajja ta idar da sallah tayi tsaki tace wannan yarinya
saidai
Allah ya shirya yi hakuri jabeer, ya mike zaune yana
murmushi yace zata sani ay bari ta dawo, hajja tace
ay kai
baka iya yi mata faďa sai dai kullum kace zata sani kullum
kai ke kara sangarta ta,
kafin yayi magana ta shigo ta ďane kan cinyar hajja
tace
hajjanah” sannu da gida,
hajja ta tureta tace dalla ni sauka karki karya ni, sai a sannan idonta yakai kan jabeer dake kallonta
baya ko
kiftawa, da sauri ta mike tana murmushin jindadi ta
zauna
kusa dashi kamar zata shige jikinshi tace dama
kana cikin dakin nan,
ta shagwabe fuska tace shine kana kallon hajja
tana tureni
ko kayi mata magana kalli fa hannu na saura
kaďan taji min
ciwo, Hajja tace Allah ya kiyaye dai banji miki ciwon ba
ko, ta turo
baki tace kinso kiji min mana inaga ma dan kinsan
yaya
jabeer na nan ne shiyasa baki ji min ciwon ba,
hajja ta kwashe da dariya tace to yau dai sharrin kaďan ne
ko Allah nagode maka ma yana cikin dakin da
yana zuwa
nasan ce mishi zakiyi yau da kyar na barki da rai,
jabeer ya kwashe da dariya,
ta kwabe baki ta fashe da kukan shagwabe harda buga kai
a gado,
jabeer yace subhallahi me kuma akayi miki, hajja ta
mike
tace tabarar fa,
ni bari kaga in fita dan in ina dakin nan zane yarinya zanyi,
cikin kuka tace kaji ko wallhy bulala takemin
kullum yauma
dan ta ganka ne,
jabeer ya haďe rai yace gaskiya hajja zamu kai
kararki can kotun karshe a yanke miki hukunci,
hajja tayi dariya tace mu fara shariar daga yau ma in
dai
akan AFEEYAH ne,
afiyah ta dago kai ta harareta,
jabeer yayi murmushi ya ciro hndky dinshi yana share mata
hawaye, yace so sorry babynah, ya dago fuskarta
ya kalli
cikin idonta yace baki san kin girma da kuka ba, ta
kara
marairaicewa kamar karamar yarinya tace to baka ganin
abinda takemin, yace to nace kiyi hakuri kinji, ki
daina yarda
suna saki kuka kinaso a dinga ce miki ruwa2,
ta noke wuyanta tace ah’ah, yace to sai kin zama
mai hakuri kin daina yawan kuka kinji,
tace tam zan daina, yace yauwa wifey nah,, ya
dakko ledar
gefenshi ya fito dasu biscuits da chocolates,
rungumeshi
tayi cikin murna ta mishi peck a kumatu tace I love u so
much hubbynah, wani abu yaji yana mishi yawo
cikin
kwanyarshi,
a hankali cikin rashin kuzari yace more than u do
babynah,, ta sakeshi tana dariya, nan suka cigaba da hirah
cikin
jindadi tana shan chocolates,
sai da aka kira la’asar sannan ya fito zai tafi, rakoshi
ta fito
yi bayan yayi sallama da hajja, a dai2 kofar dakin inna
suwaiba kausar ke zaune tana ganinsu ta shiga
wakar
habaici tana fadin Allah wadai da halin yan iska sai
a shige
daki afi karfin awa wai da sunan ana hira, ran Afiya ya baci matuka jabeer ya lura da hakan ya
rike
hannunta gam ta fisge, tace da uban wa kike ,
kausar ta
mike tace da ubanki nake kinji na kira sunanki, in
ba tsarguwa kikayi ba meye na jin haushi shegiya
marar
kunyar banza,
Afeeya ta kuma hassala tayi kanta da sauri jabeer
ya riketa
da iya karfinshi ya jata da kyar suka fita, kukan bakin ciki ta fashe mishi dashi tana ta tirje
hannunta,
murmushi yayi dan yasan in bata tsaya ta mayar da
martani ba bazata taba hucewa ba,
hakuri ya shiga bata amma ko kalma daya bata iya
rikewa ba saboda zuciyarta cike take da bakin ciki gani
take idan
basuyi fada da kausar ba yau sai tayi ciwo mai
tsanani,
matsowa sosai yayi kusa da ita yace haba afee nah,
ba nace kiyi hakuri ba, kinaso inyi fushi ne, ta turo
baki tana
kuka tace ko zaka fashe yau bazanyi hakuri ba,
ya hade rai yace to ni kuma in bakiyi hakuri ba mun
bata
garin ma zan bari gaba daya, cikin dakewar zuciya tace ka
tafi gaba da birnin sin ma dan wallhy bazan hakura
ba,
sakin hannunta yayi yace ni ko? Ta juya mishi baya
tace eh
ďin, yace to shikenan bye yasa kai ya fita,
ko ajikinta a lokacin saboda zuciyarta na azalzalarta
taje
gurin kausar…….

1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button