Rabo Ajali Episode 1 – 15

11 hours ago Sulaiman Bomboy [7:00am 08/11/2016] .: ◆◆ RABO AJALI 3
By Sulaiman Bomboy
Tana shiga ta tarar da kausar na buga k’ullun alale,
sam
kausar bata kula da shigowarta ba sai saukar wata
sanda taji akanta da karfi, zafin ya gigita ta sosai tasa ihun
da ya
fito da inna suwaiba da hajja daga ďaki,
cikin rudewa inna suwaiba ta kama kausar tace
kausar
meya faru, kausar ta kasa magana sai kuka takeyi hannunta
rike da gurin jini na fita,
hajja ta kwace sandar hannun Afiya tace yanzu ke
saboda
tsabar mugunta wannan murďaďďiyar sandar kika
buga mata,
Afiya ta turo baki tace hajja fa baki san abinda tayi
min
bane shiyasa,
inna suwaiba cikin fushi ta saki kausar tace uban
me ta miki, Afiya ta murguďa baki tace gata nan ki
tambayeta,
inna suwaiba tace lallai yau za’a haifi ďa mara ido a
gidannan wallhy,
Afiya tace a haďa harda mara hanci ma a haifa,
hajja ta bige bakinta tace ke wai wace irin yarinya ce da
baki jin maganar kowa,
Afiya tace to wai hajja ita baki tambayeta me tace
mana ba,
ce mana fa tayi yan iska, inna suwaiba tace ay kunfi
karfin ya’yan iska saidai na guguwa, wallhy yau saina
miki shegen
duka a gidan nan sai na tabbatar wannan
tsinannan bakin
naki yayi laushi,
Afiya tace Allahn da halicci baki na shi kadai zai iya sashi
yayi laushi ba wata ca— hajja ta toshe mata baki
tace na
shiga uku ni Giďe, yanzu ke Afiya bazan miki
magana kiji
ba, inna suwaiba tace hajja ki wuce daki ki barni da yarinyar nan wallhy yau sai na mata lahani a
gidannan,
Hajja tace kiyi hakuri suwai— karki bani hakuri ki
cuceni
hajja kullum mu kenan a cuce mu a taushe mu, to
wallahi bazan dauka ba,
ji yadda jini ke zuba a kan kausar ay dan tasan
kuna daure
mata gindi ne ke da malam shiyasa take abinda
takeso, in
ba ta raina mutane ba ay kausar ba sa’arta bace, hajja tace kiyi hakuri dai nace suwaiba, Afiya ta
harari hajja
tace wai hajja hakuri kike basu ni baki bani hakuri
ba sai su
da babu abin ma da nayi musu,
inna suwaiba ta hassala sosai tayi kan Afiya ta cakumota,
hajja ta riketa tace wallhy suwaiba karki taba min
marainiyar Allahn nan,
wallhy kika kuskura kika sata kuka sai ranki yayi
matukar
baci, inna suwaiba tace ay ko sai dai ya baci ta kaima
Afiya duka
ta goce tana kicikicin kwacewa,
kausar dake jin kanta kamar dutse ta mike tazo ta
bayan
Afiya ta kai mata duka, Afiya tayi kukan kura ta kwace
jikinta a gurin inna suwaiba ta haye kan kausar
inna
suwaiba na jibgarta ita kuma tana jibgar kausar,
hajja na
gefe tana kuka ita sam bata ma ga dukan da afiya kema
kausar ba ita dai tafi jin dukan da akema Afiya,
dakyar da taimakon shigowar malam faďan ya
rabu kowa
na maida numfashi, kausar bayan inna taje ta boye
tana kuka sosai saboda taji jiki, Malam Atiku cikin bacin
rai yake
ma inna faďa itama cikin fushi take mayar mishi,
yace yanzu in banda ke babbar kwabo ce meye na
shiga
faďan yara, wai ke in an barki ga mai ýa ko, kin gama zubar
da mutuncinki a idon karamar yarinya, inna cikin
fushi tace
faďa min mai mutunci a idon wannan shegiyar
yarinyar,
hajja ta fashe da kuka tace wallhy ba shegiya bace, Danbaba ni na gaji da zaman gidan nan kullum sai
sun
tsokani yarinyar nan ita kuma Allah bai ďiga mata
hakuri a
ranta ba gara muyi nesa dasu su zauna su kadai a
gidan, malam Atiku yace babu inda zaku hajja, baku da
inda yafi
nan, zan dauki tsatstsauran mataki akan wannan
alamarin,
inna suwaiba tayi tsaki ta hararesu tace ka daďe
baka ďau mataki ba, wannan yarinyar wata rana saita dauko
muku na
barin gari, ta kama hannun kausar suka wuce ciki
tana
masifa zuciyarta na ķuna saboda Afiya, ta rasa
dalilin da yasa ta kasa samun nasara akan Afiya,
zama tayi bakin gado idonta yayi jajur dan ba
karamin caza
mata kwakwalwa Afiya keyi ba,
Can kuma dakin hajja fada sosai suke ma Afiya
akan rashin hakuri, malam atiku yace ni wallhy na rasa inda
yarinyar
nan tayi gadon wannan halin hajja ko kadan bata
da hakuri
komai aka mata tace saita rama kuma rayuwa
bazata taba tafiya haka ba,
Allah na tuba kayi hakurin ma ya ka kare a wannan
zamanin
bare kuma bakayi ba, hajja tace ay ni yanzu inaga
nawa ido
tsakanina da Afiya dan gani sukeyi kamar goyon bayanta
nakeyi ni take ďaura ma bakin jini dan kawai taga
banason
abinda zai bata mata rai shiyasa takeson a dinga ci
min
mutunci, Afiya ta fashe da kuka tace dan Allah hajja kuyi
hakuri in
shaa Allahu ko duka na zasuyi bazan kara tanka
musu ba,
hajja tayi tsaki tace ke ďin ce zaki faďi magana in
yarda, malam atiku yace hajja muyi mata addua babu
mamaki
bazata kara ba,
Afiya tace Allah abba bazan kara ba,
hajja tace to Allah yasa da gaske kikeyi, duk suka
ce ameen, nan suka cigaba da yi mata nasiha akan
rayuwar
duniya cikin dabara suke mata nuni da illar rashin
hakuri,
Afiya jinsu kawai takeyi dan ita bataga rashin
hakurin da aketa ikirarin tana dashi ba ita dai tasan ko manzon
Allah
s.a.w yace in aka bata maka ka rama dai2 yadda
akayi
maka, to ita kuwa akan me zata yarda tanaji tana
gani a taka ta, bazai yiwu ba,, har suka gama nasiharsu
Afiya tana
gyada kai kamar taji abinda suka ce sai gab da
magriba
malam atiku ya fita suma suka tashi suka je yin
alwala… Tun daren ranar take zuba idon ganin jabeer shiru
har kofar
gida ta fito ta tsaya tana kallon kofar gidansu ko
zata ga
fitowarshi amma ko giftawarshi bata gani,
kullum ta dawo skull sai ta tambayi hajja ko yazo, in hajja
tace bai zo ba nan zata fara sababi tace hajja kawai
ki
fadamin ko kin fita yazo baki nan ko kuma kina
baccinki
bakisan yazo ba, hajja saidai tayi tsaki tayi banza da ita ta cigaba da
abin da
takeyi,
Afiya ta damu sosai da rashin ganin jabeer ji takeyi
kamar
ta mutu saboda rashin ganinshi haka kawai zata zauna taki
cin abinci tayi ta kuka hajja bata ko kallonta bare ta
rarrasheta..
Yauma kamar kullum a cikin sati biyun da tayi bata
ga
jabeer ba tana zaune ta haďa kai da gwiwa tana rero kuka
hajja ta ajiye mata abinci a kusa da ita ta zauna
gefenta ta
kira sunanta, bata dago ta kalleta ba ta cigaba da
kukan da
takeyi, hajja tace to shikenan tunda bazaki saurareni ba
dama jabeer ne,,, ta ďago kanta da sauri tace me ya
sameshi hajja,
hajja tace yana nan cikin koshin lafiya baki ga
yadda yayi
kyau ba, dazu kina makaranta yazo yace in faďa miki yana
gaisheki in ya samu lokaci nan da wata daya bayan
kin
gama jarabawa zai zo ku gaisa,
idonta ya ciko da kwalla tace hajja wata daya? Hajja
tace eh mana, ba yace kince ya tafi gaba da birnin sin
ba,
to ba wasa nake mishi ba afiya ta faďi haďe da
fashewa da
kuka, hajja tace ay ko shi da gaske ya ďauka,
Afiya ta maida kanta cikin gwiwoyinta cikin kuka tace
shikenan kar ma yazo din dama nasan so kawai
yakeyi ya
kasheni,
hajja ta gimtse dariyarta tace kull kar na kara ji, duk
laifinki ne meyasa in yayi miki magana bakya ji,
Afiya tace to ba nace na daina ba kema shaidace
yau sati
biyu kenan banyi fada da kowa a gidan nan ba
kuma suna
tsokanata meyasa baki faďa mishi haka ba, da wani abun
nayi da yana zuwa zaki fada mishi amma saboda
nayi abun
kirki shine kika ki fada mishi,
Hajja dariya taci karfinta sosai ta mike ta fita tana
dariya ita kaďai, Afiya ranta ya kara baci ta kwanta tanata kuka
harda
sheshsheka tana tausayin kanta dan tasan in bata
ga jabeer
ba nan da kwana biyu to tabbas zata iya mutuwa,,,
muryar hajja taji tana kwalawa Mahmud kanin kausar kira,
ya taho da gudu yana buga ball yace hajja gani,
tace Gidan
Alh Bara’u zan aikeka,
Afiya ta mike zubur ta dakko hijab dinta ta fito tace
zanje hajja, hajja ta kalleta tace da wannan kumburarren
idon
zaki shigar musu gida,
Afiya tace eh dashi zan shiga ni dai ki fada min
sakon,
hajja tace to ay sai kije ki shiga din mu gani zonan mamu
kaji ta miko mishi kullin magani tace kace a aikawa
Asiyah
nayi mata bayanin amfaninsu,
ya karba yace to hajja, bin bayanshi Afiya tayi ta
hađe rai tace bani, jikinshi na rawa ya mika mata hajja tace
Afiya
karki fita gidannan haka ko uniform baki cire ba,
bata
saurari hajja ba ta fita dan so kawai takeyi yau ko ta
halin k’ak’a taga jabeer….