Rabo Ajali Episode 1 – 15

RABO AJALI 4 ◆◆ By Sulaiman Bomboy Tana fitowa
tayi tafiya kadan ta fada gidansu
jabeer,
gaisawa tayi da Ado mai gadi, yace yar lelen jabeer
kwana
biyu kinyi wuyar gani, tace wallhy baba ado mun kusa fara jarabawa ne,
yace au too to Allah ya bada sa’a, tace Ameen ta
wuce ciki
idonta kan motar jabeer tasan tabbas yana ciki,
kai tsaye ta wuce dakin Ummi ta murda ta shiga
hade da sallama, amsa sallamar yayi haďe da ďago kanshi suka
haďa ido,
kallonshi ta tsaya yi idonta cike da kwalla shi kuwa
murmushi yake mata yana mai jin dadin ganinta,
girgiza kanta tayi ta wuce kitchen inda taji
buruntun ummi, ummi na ganinta ta fadada fara’arta tace Afee yan
matana,
Afiya ta tsuguna ta gaisheta, ummi ta amsa haďe da
ďagota tace kin gujeni kwana biyu ko ďan girki kin
daina zuwa tayani, afee ta sunne kanta tace wallhy
ummi jarabawa zamu fara yanzu bana fita amma ay nazo
ran
Saturday bakya nan,
ummi tace eh kwarai naje daura, ya hajja, afiya tace
tana gida ita ta aikoni wai gashi a kaima anty
Asiyah, ummi ta karbi maganin tace Allah sarki kice mata
an gode
sosai kinji,
afiya ta gyaďa kanta sannan tace bari in tayaki
wanke wanken, ummi tace aiko nagode kamar
kinsan na gaji, ga
dayyaba har yanzu bata dawo ba, Afee ta fara
wanke2 tace
ummi Amirah fa, ummi ta wanke hannunta tace
tana can kaduna gidan Asiyah har yanzu bata
dawo ba, Afeeyah tace Allah ya dawo da ita lafiya, ummi tace
Ameen
yar albarka ta fita ta tarar da jabeer zaune yana
latsa waya
tace au ashe baka fita ba, yace walhy ummi nagaji
ne sosai, tace ay da gajiya ni bari in ďan kwanta kafin la’asar,
yace to ummi Allah huta gajiya tace Ameen ta wuce
ciki,,
saida ya tabbatar ummi ta kwanta sannan ya mike
ya shiga kitchen ďin,
tana tsaye tana goge kwanukan da ta wanke tana mita tana
girgiza kai,
dariya ta bashi a zuciyarshi yace yau ya shiga uku
da masifarta,
karasawa kusa da ita yayi ya dauki plates din da ta
goge zai jera tayi saurin rikesu tace malam ka ajiye ni ban
sa ka
ba, yace ay nasan baki sani ba tayaki kawai zanyi,
tace to
banaso ko dole ne,
yayi murmushi yace dole ne mana in ban tayaki aiki ba wa
zan taya,
tayi tsaki tace wacce ka samu a cikin sati biyu nidai
ka fita
kawai, da nasan ma zan sameka a gida da ban
shigo ba, yayi dariya haďe da rike kafadunta yace
makaryaciya dan
ki ganni ne ma kika yarda aka aiko ki, tace God
forbid, in ganka inyi maka me, yace kiji
daďi mana
in kuma bakiji dadin ganina ba kalli cikin idona ki faďa min,
ta ďago a tsiwace zatayi masifa suka haďa ido tayi
saurin sauke kanta saboda wani abu da ta gani a
cikin
kwayar
idonshi, yayi murmushi yace nasan kinyi missing ďina,
cikin muryar shagwaba tace ni banyi missn dinka
ba, yace um um fa karki sani in tafi gurin da bazaki
kara
ganina ba,
muryarta ta fara rawa tace me ya rage kuma tunda har ka
iya yin sati biyu baka neme ni ba, ya dago kanta ya
kalli idonta da hawaye ya fara zuba a cikinsu yace
bake
kikace
in tafi ba, ta dunkule hannunta ta buga a kirjinshi da karfi
tace to ba
wasa nakeyi ba, shine ka daina bari in ganka baka
ma
damu da halin da zan shiga ba kasan ko kwana
ďaya ne in ban ganka ba banajin daďi ni nasan yanzu ka
daina sona
tunda har ka iya yin sati biyu baka ganni ba kuma
ka zauna
la-fiya ta karasa fadi cikin kuka mai tsanani,
kwantar da kanta yayi kan kirjinshi dake bugawa da sauri
yace am so sorry Afee nah kece bakya ji in na miki
magana, tace wallhy na daina kaje ma ka tambayi
hajja Allah
ko sun
tsokaneni bana tanka musu, jabeer yace to yi shuru na yadda ki daina kuka
kinji,
ta gyada kanta tace promise me bazaka kara yin
bacci baka
ganni ba,
yace I promise baby in dai da rai da lafiya bazan kara ba
kinji, tayi murmushi tace Allah ya kara maka
tsawon rai da kuma lafiya in dinga ganinka har
karshen
rayuwata,
ya ja kumatunta yana murmushi yace Ameen my queen,
tayi dariyar jindadi suka cigaba da kife kwanukan
suna hira har suka gama,
a parlor suka zauna yake tambayarta karatun
jarabawa,
tace tanayi sosai saidai maths ke dan bata wahala, yace
baki da matsala zamu dinga yi kullum kafin ku fara
exams
tashi ki rakani gidansu Affan,
ta turo baki tace nidai bazan shiga ba,
ya harareta yace yau sai kinzo munje kin gaisheshi rabonki
da shiga gidan tun kafin ya fara ciwo saboda haka
yau sai
kin shiga, ta marairaice tace ni fa ba ruwana in
wadannan
masu kama da iyamuran sukayi min wllhy ramawa zanyi
saidai kace bani da hakuri, ya murďe bakinta har
saida tayi kara yace suwaye
masu
kama da inyamurai,
tace oho ni nasan sunansu ne, yayi dariya yace bazaki taba canzawa ba afee sai
dai addu’a, tace wallhy zan canza amma fa baza a
dakeni a
hanani kuka ba,
yace to naji tashi muje bazamu daďe ba, tace too ta
mike suka fita suka shiga gidan Alhj Basheer,, Yana
zaune as usual a gurin kifaye yayi kasake
yana
kallonsu kamar me nazarin wani abu,
jabeer ya dafashi ya juyo a firgice ganin jabeer yasa
shi washe hakori sosai yana kaďa kanshi cikin murna,
jabeer yace Affan abokin jabeer kuma abokin kifi,
Affan yayi dariya cikin maganar dolaye yace jiya
baka zo
ba inata kallon can kofar mota har dare baka zo ba,
jabeer yace kayi hakuri na danyi wata tafiya ne, Afiya
dake tsaye fuskarta dauke da tausayin halin
da affan
ke ciki tace ina wuni, ya ďago kanshi dake rawa
yana
washe hakori yana kallonta baya ko kiftawa, duk maganar da jabeer ke mishi bai kalleshi ba idonshi
na kan
Afeeya
kanshi yaki tsayawa guri daya,
jabeer ya kalli afeeya da ta rabe tana jin tsoron
kallon da Affan ke mata yayi murmushi yace affan baka gane
Afeeyah ba, affan ya girgiza kanshi ya runtse
idonshi kamar
yana son tuno wani abu can ya bude idonshi yace
na
ganeta amma na manta a wani cartoon na taba ganinta, jabeer ya kwashe da dariya haka shima
affan suka
dinga
dariya tare saida jabeer yayi shuru sannan affan ma
yayi,
jabeer ya kalli afeeya da ta cika tayi fam ya maza ya mike yace Affan ka jamin bala’i,
affan ya mike shima ya matso kusa da afiya sosai
kamar
zai shige jikinta yasa hannu ya shafi fuskarta wani
irin
laushi yaji haďe da sanyi mai fisgar zuciya ya maza ya cire
hannunshi yana tsalle yace bari inje in fada ma
mummy
yau na taba fuskar cartoon, jabeer ya janyoshi yace
karka
kara ce mata cartoon, Affan ya bata fuska yace to mecece in ba cartoon
ba kalli fa
idonta kato irin nasu, kuma ka taba fuskarta kaji,
jabeer yace idonka ne ya ga cartoon wannan
Afeeya ta ce,
ka tuna ta, Afeeya mai kyuiya mai kukan banza ya faďi yana
mata kallon tsokana,,,
affan ya kara rufe idonshi ya bude yace mai kuka
irin na
mage, Afiya tayi tsaki cikin fushi ta fara tafiya, affan
yace jabeer kace ma cartoon ta dawo dama bani da barbie din
wasa,
jabeer yabi bayan afeeya yana cema affan jeka
kace ma
mummy ta siyo maka wannan barbie din tawa ce,
Affan ya bata rai yace sai na fadama daddy in ya dawo ince
kaki bani barbie,
jabeer bai kulashi ba shidai hakuri kawai yake
bawa afeeya,
suna kaiwa gate zasu fita shima affan yasa kafa zai
bisu yaji wani irin tsawa mai firgitarwa sannan gabanshi
yaga
kamar namun daji suna so su biyoshi,
a sittin ya ruga ciki yana ihu yana kiran sunan
mummy, jabeer sam bai lura da yanayinshi ba ya
ďauka shirmenshi
ne dan baya taba wuce kofar mai gadi yauma yayi
mamakin
da ya biyosu har gate saboda barbie,,
Har cikin gida ya rakata yana rarrashinta da kyar ta
sauka da alwashin ta
gama shiga gidan Alhj basheer har ta koma ga
Allah dama
sam jininta bai haďu da flowers din kofar gidan ba
ma bare a kai ga mutanen cikinshi gara ma daddy
da shi affan din
suna gaisawa in jabeer ya kaita gidan, ta saki ajiyar
zuciya
tace yaya jabeer haka Yaya affan ya dawo rabona
da ganinshi tun ina js3,
Amma wai wane irin ciwo ne wannan, hajja dake gefensu tace au ke yau kin shiga kin
ganshi,, ay
a unguwar nan babu wanda ake bari yaje dubashi
ko meye dalili oho,
jabeer yace hmm babu wani dalili hajja kawai dai
matar gidan ce bata yarda a ganshi ni ma dan ta rasa
yadda
zatayi dani ne shiyasa ta barni,, ga daddy ba
mazauni ba
dan sai yafi wata bayanan,
hajja tace to Allah dai—- sai bakinta ya sar’ke kamar a
datseshi da gum…
wannan itace babbar jarabawar da Allah ya
daurawa AFFAN
ta hanyar kishiyar uwa babu wani mahaluki a
doron kasa da zai iya yi mishi addu’ar samun sauki,
jabeer shi ne kadai yake iya ganinshi har yayi
yunkurin sanyashi a hanya amma saboda karfin
iko da
lokacin da
Allah ya ara ma mummy, daga affan ya fara jin maganar
jabeer kamar kiftawar walkiya sai ya mance abinda
yace ya bijire mishi,
duk yadda taso rabasu ta kasa saboda amintar su
mai karfi
ce wacce zaiyi wuya kasamu labarinta a kasar hausa,
Bari in baku takaitaccen tarihin gidaje ukun…