HAUSA NOVEL

Rabo Ajali Episode 1 – 15

◆◆ RABO AJALI ◆◆ 5.
A unguwar “zoo road” dake cikin garin
“kano” ta dabo tumbin giwa nan zan ďan tsakuro
muku tarihin gidajen makota ukun, Alhaji Basheer
Balarabe dan asalin k’asar Cameroon ne, sana’ar
Gwal ita ta shigo dashi kasar nigeria tun yana saro kaďan2 yana siyarwa har Allah ya sanya wa abin
albarka ya koma sarinsu da yawa yana shigowa
dasu yana siyarwa, a duk cikar kasuwar gwal dake
cikin garin kano babu wani wanda yakai Alhj
Basheer kawo ingantattun gwalagwalan da babu
mixed a cikinsu, wannan dalilin ne yasa duk wanda ya tashi siyan gwal to fa a gurinshi zai siya
dan shagunanshi sun fi karfin goma a cikin
kasuwar, Alhj Basheer ya auri matarshi ta farko
kuma yar uwarshi Zeenatu, auran zumunci akayi
musu wanda ganin girma da kuma karamcin rik’on
da iyayen zeenatu sukayi mishi yasa ya yarda da auren amma badan yanaso ba, shekararsu uku da
aure suna zaman lafiya saboda irin biyayyar da
take mishi, a cikin wannan shekarun ne ya dakko
ta suka dawo Nigeria da zama kwata2 sai dai suje
cameroon hutu, a shekararsu ta biyar da aure ne
hankalinsu yayi matukar tashi saboda rashin haihuwa, babu ma kamar alhj basheer da yake
ganin madarar kuďi babu maciyansu sai dai yan
uwa da makota, ya kosa matuka yaga yana da
ya’ya barin ma ďa namiji dan wani lokaci har
mafarkin gashi nan an haifa mishi ďa kuma namiji
yakeyi, a wannan yan lokutan ne ya fara tunanin k’aro aure duk da a lokacin ba mazauni bane
saboda bai fi yayi sati a nigeria ba sauran kwanakin
duk a kasar waje yake yinsu yana turo kaya, Wata
ranar asabar ya baro airport cikin tsananin jin
yunwar da ta bashi mamaki, nan ya tsinci kanshi da
tsayawa a wani restaurant dake Jabi dan bazai iya matsawa ko’ina ba tare da yaci abinci ba, cikin
karairaya wata farar ingarmar budurwa ta matso
kusa dashi tace alhj me kake bukata, cikin ruďewar
ganin jar fata gata a cike gaba da baya ko’ina sai
rawa yakeyi a jikinta yace anytn special yanmata
dan yunwa nakeji sosai, ta ďan tsuguno kadan tace an gama ranka ya dade, tayi gaba jikinta na girgiza
alhj basheer ya bita da ido baki sake yana kallonta
har ta bace ma ganinshi, ajiyar zuciya mai karfi yayi
sannan ya gyara zamanshi dan ba karamin tafiya
da imanin shi tayi ba, cikin yan dak’ik’u ta dawo
dauke da plate din fried rice da pepper chicken sai peprsoup din kayan ciki a gefe da drinks, alhj
basheer da bai cika cin abincin restaurant ba sai
gashi ya tsinci kanshi da cin abincin nan sosai,
takardar bill ta kawo mishi yabi kirjinta da ya cika
kamar zai faso cikin rigarta da kallo yace yanmata
duk wadannan kudin ni zan biya, tayi walll da ido tace alhj yayi kaďan ko, yayi wata kasaitacciyar
dariya yasa hannu a aljihu ya ciro rafar dari biyar
yace ya daiyi yawa ni kinga abinda zan iya biya
nan, tayi murmushi tasa hannu ta karba haďe
tsugunawa, tace to an gode yallabai, tayi gaba ya
bita da kallo yana lasar baki kamar tsohon maye, tashi yayi bayan ya gama goge bakinshi da tissue
yana sakace ya yafito wani yaron da yaji an kirashi
da John, da sauri yaron yazo ya tsuguna yace alhj
any problm, alhj basheer ya ďagoshi yace no
young man ina bukatar taimakon ka ne,, john cikin
mamaki yace taimakon me alhj, alhj basheer ya jashi waje yace wannan yarinyar da take kawo
abinci nake son sanin sunanta, john yayi dariya
yace OYIZA kake nufi, alhj basheer yace ban sani ba
wata fara kakkaura, yace yes itace alhj sunanta
“Safiya” Oyiza ake ce mata ita y’ar mai restaurant
din nan ce, bata cika zuwa nan ba sai in tazo daga lagos kuma I think gobe ma zata koma saboda tafi
1wk anan gurin, ya fara waige2 ya ďan rage murya
cikin gulma yace amma fa alhj bat— maganarshi ta
katse sakamakon kiranshi da yaji madam dinshi
nayi, da sauri yace alhj bari in tafi sai anjima ya ruga
ciki da gudu, alhj basheer a zuciyarshi yace ko bata dame ya ke so ya fada mishi oho? ya ďaga
kafadarshi kawai ya dawo ciki dan yayi magana da
mahaifiyar oyiza, Guri na musamman maman oyiza
ta bawa alhj basheer ya zauna tana yashe hakori
cikin murna dan taga gurin ďana tarko, cikin
girmamawa suka gaisa, saida shuru ya đan ratsa na kusan 2mins sannan alhj basheer ya fara magana
yace madam naga yarinya a gurinki ne kuma inaso,
wallhy da aure nake sonta ba yaudararku zanyi ba,
ni in kin amince ma a cikin sati biyu a gama komai
na maganar aure, maman oyiza tayi ajiyar zuciya
cikin gurbatacciyar hausarta tana girgiza kai tace anya kuwa gaskiya bazan iya ba bahaushe oyiza
ba, kaiii bazan iya ba alhj hausawa basu cika rik’e
mata ba, yayi murmushi yace wasu dai madam ai ba
duka aka taru aka zama daya ba, tace ummm haka
ne amma gaskiya— alhj basheer ya katseta yace
madam na barki kije kiyi tunani, zan dawo nan da 2days sai inji abin da kika yanke ya ajiye mata
wasu kudin a gabanta sannan ya tashi ya tafi….

◆◆ RABO AJALI ◆◆ 6⃣
By sulaiman bomboy
Jujjuya kuďin maman oyiza takeyi cikin fargaba dan ita a
tunaninta harka kawai zaiyi da ďiyarta su tatsi kudi su bar
banza,
sai kuma gashi da aure yazo musu, ita kuwa sam bazata
iya aurawa ďiyarta bahaushe ba tafi son kabilarta kuma dan
garinsu wato OKENE, mikewa tayi ta shiga wani ďan lungu
da oyiza ke yawan zama kullum in tazo abuja, waya takeyi
tana dariya cikin murnar da uwarta ta kasa gane daga inda
murnar ta samo asali,
zama tayi kusa da ita tana mata magana, oyiza tayi saurin
katse wayar da takeyi ta kalli mamanta,
maman oyiza ta dafa ta tace sofy mun shiga cikin matsala,
oyiza ta haďe rai tace matsalar me mum, maman oyiza ta
share gumin da ya tsatstsafo mata ta labarta ma oyiza duk
yadda sukayi da alhj basheer, cikin damuwa tace ni bansan
me yasa kika fito har kika kai mishi abinci ba, ke da ko ruwa
bakya kai ma customers in kina gurin nan,
oyiza tayi dariyar farin ciki a zuciyarta tace thank uu
“Chummy lord” ta kalli mamanta tace mum wannan shine
matsala? ay wannan is a blessn to us,
kinsan irin dukiyar da yake dashi ne,
kuma kinsan abun dadin bai taba haihuwa ba,
maman oyiza ta saki baki tace a ina kika san bai taba
haihuwa ba,
gaban oyiza ya fadi amma ta dake tace john ne ya fada
min, mamanta tace koma dai menene ni bana son auren
bahaushe, oyiza ta dafa mamanta tace mum karki fara
wannan maganar ma saboda bazai yiwu ba, kawai in yazo
kice mishi eh mun shirya yazo ayi maganar aure,
maman oyiza cikin bacin rai tace kina hauka ne,
oyiza cikin fushi tace yess am mad in dai akan kuďi ne,
kuma duk wanda ya nemi shiga tsakanina da samun kuďi
ko waye wil fc d consequences,..
Maman oyiza ta mike tace to zanga yadda za’ayi ki aureshi
tunda ke baki da hankali kina zuwa 1yr ya koroki in dai
bahaushe ne ki ma cire a ranki dan I swear bazan bari ya
shigo ko gate din restaurant dinnan ba bare yazo jin wani
feedbk ta wuce tana masifa,
Idon oyiza yayi jawur nan da nan fuskarta ma ta rikiďa ta
zama jawur gunin ban tsoro, ta mike kamar walkiya ta wuce
motarta taja tayi gida,
wani jan akwati ta bude ta dakko wani farin kyalle da wata
jar baby kamar sassakar laka,
wani kirari tayi mai karfi da ya girgiza gidan da take ciki,
cikin second uku wata mace ta bayyana a gabanta cikin
jajayen kaya,
“fitsarin tsoro na saki ganin halittar wannan matar jikina
take ya fara rawa idona ya ciko da kwalla a zuciyata nace
duk “Badiyya” ce ta sani wannan bin diddigin gashi na kawo
kaina inda zan halaka” dakewa nayi na fara karanto adduoin
neman tsari, nan na samu kwarin gwiwar kai kunnena da
idona gurin abun da sukeyi, oyiza na hango tayi ma matar
da naji ta kira da “Chummy lord” sujjada (wa’iyazubillah)
chummy tasa ma oyiza wani nannaďaďďen farin yadi a
kanta tace “u are safe wit me by ur side”,
oyiza ta ďago kanta zuciyarta a dake tace I found him my
lord, amma mum naso ta kawo min matsala, chummy tayi
dariya mai karfi tace ur mum ko kuma gvn mum,
kin manta u sacrifice her sannan kika samu alhj basheer
yasan inda kike,
cikin faduwar gaba oyiza tayi kasa da kanta tace I love my
mum my lord,
chummy tace I knws dat amma in har kinason jin dadi dole
ki katse numfashin mahaifiyarki, kuma bari in fada miki
kina shiga gidanshi zaki samu ciki so u will be d apple of d
house saboda u bring air to d family, ,
mum dinki ta fara tsufa so let her go ke kuma ki fara
rayuwarki mai daďi,
haka tayita convincn dinta har ta gamsu ta fitar da uwarta a
ranta tayi alkawarin yau da dare zata bada uwarta saboda
komai ya tafi mata daidai,
sun kusa awa suna tattaunawa kafin Chummy ta bace,
oyiza ta mayar da komai na tsafinta ta fito ta shiga kitchen
dan tayi ma innocent mum dinta girki, tsayawa tayi a
kitchen ta kasa komai tana tunano rayuwar da tayi da
mahaifiyarta da irin wahalar da mahaifiyarta tasha akanta
da karatunta, tayi tsaki a zuciyarta tace kuďi yafi min komai
ciki harda ke mum,
am so srry mum u have to go,
ina son sunana ya shiga jerin mata masu arzikin duniya,
girki ta farayi duk da jikinta a mace yake amma ta dake
saboda zuciyarta ta daďe da kangarewa da shan jinin bil
adama,
Oyiza ta shiga cikin kungiyar asiri ne tun shekararta ta farko
a jamiar lagos,
wata kawarta esther Babajo ita tasata lokacin tana shan
wahalar rashin kuďi da abinci saboda mahaifiyarta bata da
kuđi, sannan kuma sun shiga ne dan su dinga samun first
class result a set dinsu,
haka kuwa yake faruwa dasu dan su biyun nan saida ya
zamana babu wanda yake iya bugesu, kuma kuďi ma babu
macen da zata nuna musu shanawa a cikin skull, duk irin
gulmarsu da akeyi babu wanda ko wacce ta isa tazo
gabansu tayi saboda tsabar tsoronsu da ake ji,
jini kuwa su kansu basu san adadin na mutanen da suka
sha ba,
oyiza ta hadu da alhj basheer ne a airport lokacin sun dawo
daga Italy ita da esther, tunda ta daura idonta akanshi da
suka sakko daga jirgi taji sonshi mai tsanani ya kamata,
tun a airport suke bin bayan motar da ta daukeshi har zuwa
hotel din da zai kwana kafin safiya ya wuce kano,
Saida suka bari ya shiga ciki sannan suka samu drivern da
ya daukoshi suka tambayeshi sunanshi, da kyar da kuma
kuďi da suka bashi ya sanar dasu sunanshi da kuma garin
da yake, godiya sukayi mishi sannan suka wuce,
tun daga ranar Chummy ta fara mata aiki akanshi, nan ta
gano irin kudin da yake dashi da kuma wanda zaiyi nan
gaba, ta kuma gano matsalar da yake ciki na rashin
haihuwa ,
jin yunwarshi da tsayuwa a restaurant dinsu 4d first tym
duk aikinsu ne..
dariya oyiza tayi bayan ta gama tunano wadannan
abubuwan sannan ta sauke abincin da ta daura ta kwashe
ta haďa juice ta jere su akan dining ta zauna zaman jiran
mamanta dan suyi hirar karshe….
Allahu akbar,,,
tabbas mun tsinci kanmu a zamanin da kuďi suka fi
wadanda suka kawo mu duniya daraja,
kuďi sunfi ďan da ka tsuguna ka haifa saboda a cikin 100%
85% zasu iya bada komai nasu dan su samu kuďi dattin
duniya,,,
tabbas a wannan zamanin da muke ciki masu karancin
imani da tawakkali zasu iya aikata komai saboda kudi,
Ya Allah ka tsarkake mana zuciyarmu da ta yan uwa
musulmi baki ďaya,
Allah ka azurta mu da baye bayenka kayi mana rowar
talaucin da zai kaimu ya baro mu,, ameen thumma
ameen….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button