Rabo Ajali Episode 1 – 15

◆◆ RABO AJALI ◆◆ 9..
BY SULEIMAN BOMBOY
Cikin satin aka ďaura auren alhj basheer da Safiya
oyiza a
okene, shiri na musamman chummy tayi ma oyiza
ta
haďata da special kayan tsafi a cewarta su zasu
taimaketa
ta zauna lafiya saboda wannan matar tashi mai
yawan
addu’a,
Washe garin daurin auren ne ya dauki matarshi
da
kawayenta biyu suka kamo hanyar kano,
tunaninshi ďaya
shine yadda zai fara tinkarar zeenatu da maganar
ya auri
oyiza saboda sam duk wainar da ake toyawa bata
sani ba,
ita dai taga ana ta aikin gyaran part din gefenta
sama da
kasa amma sam bata kawo aure yayi a ranta ba,
sai gurin
bakwai suka shigo garin kano, kallon garin oyiza
da esther
keyi har suka kawo kofar dankareran gidan alhj
basheer
dake zoo road,
a kofar gidan alhj bara’u ya hango su tsaye shi
da malam
atiku suna hira, ganin motarshi yasa suka mike
suka karaso
gurinshi da saurinsu, ya leko ta cikin glass cikin
fara’a suka
gaisa, yace ga amarya fa ku gaisa,
alhj bara’u yayi dariya yace wace amaryar kuma,
alhj
basheer yace amaryata da aka ďaura min aure da
ita jiya,
malam atiku yace shine ko labari ranka ya daďe
to Allah ya
sanya alkhairi sannu amarya,
oyiza ta gyara gyalenta tace yauwa, alhj bara’u
ma yayi
mishi addu’a suka ja suka tsaya shi kuma ya
danna kai
cikin gida kirjinshi na duka sosai, parking yayi
suka fito
duka su ukun suna mika gasu ďirka2, sannu alhj
basheer
yace musu sannan ya fara tafiya suna binshi a
baya,
yana buďe kofar main parlon yayi arba da zeenatu
cikin
kyakykyawar shigar material dinkin stone work
fatar nan
tata sai kyalli takeyi ga wani kamshi da sanyin
dadi ko’ina a
cikin parlon, da sauri ta karaso tana mishi sannu
da zuwa,,
gabanta ya faďi sosai da ta hango su oyiza
amma sai ta
kara fadada fara’arta tana musu sannu da zuwa,
karasawa
sukayi cikin parlon suna yabawa da kyau da
tsarin parlon
ga kuma kula da yake samu ta musamman,
zeenatu ta nuna musu guri suka zauna ta wuce
kitchen cike
da tambayoyi a zuciyarta, kayan shaye2 ta kawo
musu da
snacks tanata yake,
ta kalli alhj basheer da ya dafe kanshi tace
yallabai gajiyar
ne, tashi muje ciki kayi wanka,
oyiza cikin kishi ta watso ma zeenatu harara,
alhj basheer yace zauna zeena akwai maganar da
nakeso
muyi dake,
ta nemi guri kusa dashi ta zauna,
a hankali ya fara magana yace sai kuma kika
ganni da baki,
tayi murmushi tace eh,,
yace dafatan zaki fahimceni zeenah, kinsan komai
nufi ne
na Allah kuma matar mutum duk inda take sai ya
aureta,
ya nuna oyiza yace wannan matata ce jiya aka
ďaura min
aure da ita bawai dan inci mutuncinki ko kuma
dan bana
sonki ba, “a’a” wannan auren ki ďaukeshi
kaddararre ne
daga Allah kuma babu mamaki safiyya na tafe da
alkhairai
masu yawa cikin gidan nan,
zeenatu da tayi mutuwar zaune tayi maza ta
saita kanta ta
kirkiri murmushi tace kaii barka Allah ya sanya
alkhairi nayi
maka murnar samun karuwa,
ay aure cigaba ne yallabai Allah ubangiji ya
bayyana
alkhairan dake cikin wannan auren kuma
alkhairan ya
wanzu a tsakaninmu,
yace ameen yar albarka zeenatu nagode sosai da
kika
fahimceni,
tace ba komai yallabai bana jayayya da abin da
Allah ya
kaddara Allah ya bamu zaman lafiya,
yace ameen, nan yayi introducn zeenah a gurin
oyiza da irin
muhimmacin da take dashi a gurinshi,
oyiza ranta ya baci da irin praisn zeenah da
yakeyi a
gabanta da kawayenta,
bayan ya gama maganganun da zaiyi yace ma
oyiza su
tashi ya nuna mata part dinta, suka mike kamar
samudawa
suka rataya jakunkunansu suka wuce,
zeenah da kiris ya rage ta fashi da kuka ta danne
kishinta ta
shiga kitchen ta hado musu abinci ta kai musu
dakinsu ta
fito tayi nata dakin ta rufeshi da key ta faďa gado
tanata
rusa kuka,
Can dakin oyiza kuwa bin ko’ina sukeyi ita da
kawayenta
suna tsalle suna murna ganin irin dukiyar da alhj
basheer ya
zuba a ciki, zama sukayi a kan gado esther tace
oyee baby
sai kinyi da gaske da wannan matar dan da
ganinta ta iya
munafurci, evelyn tace green snake kenan, gata
very pretty,
gaskiya akan matar nan na kara yarda black is
beauty
kuma suna kama da bash,
oyiza tayi tsaki tace trust mee mana ai matar
nan sai mai
aikina ta fita daraja bari dai in haihu, kunsan bata
haihuwa
kuma na riga na gano abinda alhj yafi so a
rayuwarshi
kenan haihuwa,
ta shafa cikinta tace baby boy zan haifa maka
alhj a lokacin
ne zan nuna karfin ikona a gidanka,,
duk suka kwashe da dariya evelyn tace shegiya a
ina kika
san baby boy zaki haifa, oyiza tace bansani ba
amma dat’s
wat I want kuma zan samu kinsan ni duk abinda
nake so sai
na samu, suka kara kwashewa da dariya suka
cigaba da
hira har dare ya raba sannan sukayi bacci oyiza
batai
maganar sallar magrib da isha ba,
wa ma yasani ko tayi na safe da rana ohooo……
RABO AJALI ◆◆10
BY SULEIMAN BOMBOY
Kwanan su Esther biyu a kano suna yawon bude
ido tare da
alhj basheer,
, ba kananan kuďi ya kashe musu ba a yan
kwanakin da
sukayi har suka tafi,
ita kuwa zeenatu bata ko bi ta kansu tsakaninta
dasu
gaisuwa sai kuma in ta gama girki ta kai musu,
a ranar da suka tafi da daddare ya tarasu a
parlor ya kara
musu nasiha haďe da janyo hankalinsu akan su
zauna
lafiya da juna dan shi ba mazauni bane,
sun daďe zaune a parlon har zeenatu ta gaji da
irin hirar
karuwancin da oyiza ke mishi ta tashi tayi musu
sai da safe
ta wuce ďaki,
kamar jiran zeenatu oyiza takeyi ta matso sosai
ta shige
jikin alhj basheer ta soma rikirkitashi da
abubuwan karuwan
mata wadanda suka daďe suna damawa a duniya,
cikin rashin kuzari ya kashe komai na parlon suka
wuce side
dinshi..
Bacci ne ya kaurace a idon zeenatu sakamakon
tunawa da
tayi yau mijinta babu makawa zai kasance da
wata mace
ba ita ba, tashi tayi tana kuka ta shiga bayi ta
dauro alwala
ta hau yin sallah tana rokon Allah ya cire mata
duk wata
damuwar da tayi mata kawanya a cikin zuciyarta,
ba ita ta
samu rintsawa ba saida tayi sallar asuba sannan
wani
nauyayyen bacci yayi gaba da ita…
Karfe 9 ta tashi zuciyarta wasai ta ma manta
akwai wata
bil adama a cikin gidan, bayi ta shiga tayi wanka
tayi
alwalar walha ta fito tayi sallah ta shirya cikin
orange Nouvo
riga da skirt,
kitchen ta nufa ta hada musu break ta jere kan
dinning ta
zauna ta karya sannan ta koma parlor ta zauna
tana kallo,,
sai gurin 11 suka fito cikin kananan kaya
dukkansu,
zeenatu ta kau da kanta da sauri tace ina kwana,
ya zauna
kusa da ita yace lafiya lau uwargidana an tashi
lafiya, tayi
murmushi tace lfy lau, ta kalli oyiza da ta zauna
tana gyara
gashin kanta tace amarya kin tashi lfy,
oyiza tace lfy lau, zeenatu tace ga break can kan
dinning,
alhj basheer ya mike yace kamar kinsan yunwa
nakeji ya
kalli oyiza dake yatsina fuska yace zo muje mu
karya, oyiza
ta mike tana kaďa jiki ta isa dinning ta zauna
suka karya,
zeenatu ďaki ta koma saboda yadda oyiza ke ta
ciyar da
mijinta a gabanta duk da yana ďan kakkaucewa
alamar
yana jin kunyar zeenatun shiyasa ta basu guri
dan su
sakata su wala..
Tana idar da sallar azahar ta nufi kitchen dan yin
girkin
lunch, oyiza na zaune a parlor ta bararraje tana
kallo tana
shan fruits tana dariya,
sannu zeenatu tace mata oyiza tace yauwa sannu
ta mayar
da idonta kan TV tana gunguni a zuciyarta dan ita
bata son
shishshigi,
kitchen ta wuce ta fara haďa musu abinci taji
sallama,
amsawa tayi haďe da fitowa dan ta gane masu
sallamar,
tace sannunku da zuwa hajja, Ta nuna musu guri
suka
zauna, Ma’u da Suwaiba suka kalli oyiza da ko
kallonsu
batayi ba suka ce ina wuni, ta kallesu a
wulakance dan taga
alamun talauci a tare dasu tace lfy,
Ma’u ta kauda kanta da sauri tana mamaki a
cikin ranta,
zeenatu tace hajja ya gida, hajja tace lafy lau yar
nan, ina
mai gidan mun shigo yi mishi Allah sanya alkhairi
ne,
zeenatu tace Allah sarki tunda suka fita da alhj
bara’u bai
shigo ba,
ga amaryar nan ay, hajja ta jinjina kai tace Allah
sarki Allah
dai ya baku zaman lafiya, duk suka amsa da
ameen banda
oyiza da surutunsu ya soma cika mata kunne dan
tana
kallon series din “No greater love ne”, hira sukeyi
yayin da
suwaiba ke sako oyiza cikin hirar dan tana
shigowa tasa ma
ranta tayi kawar da zasu dinga kuntatawa Ma’u
da zeenatu,
cikin kosawa oyiza ta saki tsaki mai karfi tace
wallhy kun
cika min kunne, da zaki jasu kuje side dinki kuyi
ta
surutunku da yafi miki,
zeenatu tayi murmushi tace kiyi hakuri amarya
hajja ku
tashi muje ciki, hajja da ma’u suka mike, hajja ta
kalli
suwaiba da bata da niyyar tashi tace ke suwai
baza ki tashi
ba,
suwaiba ta maida kanta kan TV tace film din ne
ya dau dadi
hajja, kuje ku fito sai mu tafi, hajja tace ikon
Allah,
nasan in za’a shakeki suwaiba baki san me suke
fadi ba,
suwaiba tace yo hajja amma dai idona yana gani
kuma zan
iya gane komai ko,
hajja zatayi magana ma’u tace dan Allah hajja ki
barta
muje, suka wuce cikin mamakin suwaiba, , suna
shiga
suwaiba ta matso kusa da oyiza tace amarya
sannu, oyiza
ta harareta tace yauwa,
ta fara waige2, tace shawara ce zan baki akan
wannan
munafukar kishiyar taki, in har zaki daukeni yar
uwa kuma
kawa to wallhy gidannan sai ya zama naki ke
kadai,
oyiza tayi mata kallon rainin wayau tace ke kuma
asuwa,
suwaiba ta kara dakewa tace ni kishiyar kawarta
ce,
munafukai ne sosai, komai nasu a kasa2 suke
yinshi dan
ace sunada hakuri shiyasa har yanzu Allah bai
basu
haihuwa ba dukkansu,
oyiza ta dan fara gamsuwa da suwaiba tace
kishiyarki ma
bata haihu ba,
suwaiba tayi murmushi tace WABI takeyi, ranar
da ta haifa
ranar suke mutuwa yanxu haka tayi biyar kenan,
tsabar
mugun halinsu yasa Allah bai basu ba, gashi sun
asirce
mazajenmu kema sai kinyi da gaske, oyiza ta
jinjina kanta
zatayi magana hajja ta fito tana cewa to sai
anjima zeenatu
Allah ya baku zaman lafiya, suwaiba ta mike a
hankali tace
ma oyiza zan shigo zuwa anjima kinji, ma’u tayi
ma oyiza
sallama suka wuce zeenatu ta rakasu har gate
sannan ta
koma kitchen dan karasa girkin da ta ďaura….