HAUSA NOVEL

Rabo Ajali Episode 1 – 15

[8:38PM, 16/03/2016] .: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣1⃣ By
Aysha Ya’u Kurah
Tun daga ranar suwaiba ta samu gurin zuwa su zauna
suyita hira suna shewa suna kulle kullensu dan ta
kuntatawa zeenatu, anan suwaiba ke yini In ba
ranar
girkinta bane,
ko kallon zeenatu ta daina yi, saboda ita a ganinta tayi kawa
wacce zata ci arziki da ita kamar yadda ma’u ke ci
da
zeenatu,
(bata san bomb ta samu a madadin kawa ba)..
Watansu uku da aure oyiza bata fara nuna komai na halin
tsafinta ba,
sai dai abinda ke bawa alhj basheer mamaki game
da ita
shine rashin sallarta, ko ya matsa mata tayi sallah to
fa zata san yadda tayi ta zille dan baza tayi ba,
gurin zeenatu kuwa mugun kyankyamin cin
abincin oyiza
takeyi saboda sam bata yarda da musuluncinta ba,
ko sun
haďu a dinning ana cin abinci sai tace ita yanxu abinci mai
nauyi bata mata cikinta yakeyi,,
a cikin wannan lokacin ne oyiza ta fara laulayi mai
zafin
gaske,
komai bata iya ci, haka ta tsani kamshin gidan gaba ďaya,
tunda alhj basheer yasan ciki ne makale jikin oyiza
shikenan duk wani kula da soyayya ta duniya ya
ďauka ya
daura mata,
babu dama zeenatu tayi abu in oyiza tace bata son kamshin
shi to fa shikenan zai hauta da faďa sosai kamar
tababbe,
suwaiba ce ke shigowa ta kula da ita suyita yada
habaici
dan zeenatu taji haushi, duk da zeenatu na jin haushin abin
amma sai ta danne ta dinga tambayar oyiza ko
akwai abin
da takeso, ko kallonta oyiza batayi bare ta bata
amsa,
abubuwa suka hadu sukayi ma zeenatu yawa, gashi sam
mijinta ya juya akalarshi gurin kula da oyiza a
cewarshi,
gurin Ma’u da amaryar da Alhj bara’u yayi kadai
zeenatu ke
samun sauki, Kayan baby babu wanda alhj basheer bai siyo ba a
nan
nigeria da waje, kuma duk kayan maza ya siya dan
a
scaninng an tabbatar mishi namiji ne, itama
chummy ta tabbatar mata namiji zata haifa, gaba daya oyiza ta
gama
wasa wukarta dan ta gama hada plan din yadda
zata
mallake gidan da duk wasu kadarori na alhj
basheer, Cikin oyiza ya kusa wata tara alhj basheer ya
ďauketa suka
tafi india acewarshi zasu fi samun kula ita da
babynshi,
tafiyarsu ita tasa zeenatu tasamu sauki take bacci
da adduointa cikin kwanciyar hankali, da rana su ma’u
da
Abida amaryar Alhj bara’u su shigo su ďebe mata
kewa da
bata shawarwari duk da Abida itama ba isashshen
lafiya gareta ba saboda cikin dake makale jikinta na wata
hudu,
A daren ranar talata ta idar da sallar tana shirin
kwanciya
taji ringing din waya, daukar wayar tayi taga alhj
basheer ta dauka cikin mamaki dan rabonshi da ya kirata har
ta manta,
sallama ta mishi ya amsa murya babu walwala tace
ya mai
jiki, yace da sauki ta sauka lafiya,
zeenatu ta washe baki tace Allah ya raya ya kuma bata
lafiya, me muka samu,
kukan da oyiza ke yi ya hana shi bata amsa, kuka
takeyi
sosai tana fadin ya za’ayi ace ya’ mace ta haifa,
tsawa ya daka mata yace to ubanwa kike tunanin ya canza
miki, ko wannan din ke kika bawa kanki,
ki rufe min baki kar ranki ya baci,
zeenatu ta kashe wayar da sauri ta hau gado ta
dukunkune
(nidai bansan me ke ranta ba a wannan lokacin, farin ciki ne
ko kuma tausayin oyiza,, masu kishiya su bamu
amsa
plss..)..
Satinsu biyu a india suka dawo gida cikin koshin
lafiya,, tun acan ya raďa mata sunan mahaifiyar oyiza wato
Salamatu (ummu Salma) tunda suka dawo makota
ke
shigowa yi mata barka, suwaiba sai tausarta takeyi
akan
gara ita tana haihuwa ba juya bace, wannan kalaman na suwaiba suna matukar sosa
ran
zeenatu su ke sata kuka a kullum dare da rana tana
rokon
Allah akan ya bata farin cikin rayuwa itama,
dan haihuwa farin cikin rayuwa ne, in ka haihu ka wuce
bakin cikin duniya da lahira,
ya Allah ka azurta wadanda basu haihu ba da ya’ya
masu
albarka cikin gaggawarka bata shaidan ba,
wadanda suke dashi kuma Allah ka shiryar mana kuma ka
tayamu raino ameen thumma ameen…..
Mrs tijjani shattima….
[8:57PM, 16/03/2016] .: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣2⃣ By
Aysha Ya’u Kurah
Shekarar ummu salma uku, in ka ganta sak uwarta gata
katuwa kamar renon agric, tana matukar samun
kulawa
gurin mahaifinta dan ba kananan kudi yake kashe
mata ba,
a wadannan shekarun banda karfin imani da salatin annabi
da tuni zuciyar zeenatu ta buga saboda ko kallo
kwakwkwara tayi ma ummu salma to fah zata
fashe da
kuka ta dinga nunata, shi kuwa alhaji basheer
babu bincike babu komai zai hauta masifa wani lokaci harda
gorin
haihuwa,
zeenatu sam ta kasa gane kan mijinta saboda
kullum
alamuranshi kara tabarbarewa sukeyi sam babu sauki a
tare dashi game da ita dan ko hanyar dakinta baya
bi, ta ma
manta rabon da su kebe tare a matsayin mata da
miji,
Oyiza kuwa yanzu burinta ta samu ciki amma kafin ta samu
sai ta shirya tsaff saboda wannan karan bazata
taba yin
sakacin haihuwar ya mace ba, sai kace ita zata
bawa kanta
haihuwar,, ( kaii Rashin ilimin addini shine babbar cuta a
rayuwar dan
adam)
A cikin kwanakin kullum dare suna gurin meeting
duk dan
saboda ta samu haihuwar ďa namiji, chummy ce ta kalleta
bayan ta gama duk abinda zatayi na tsafi, tace oyee
zaki
haifi ďa namiji amma sai kin bamu jinin yaro karami
namiji
kar ya wuce 2yrs, oyiza ta dafe kanta tana tunanin inda zata samu ďa
namiji,
chummy tace ki kokarta oyee wannan bazai miki
wahala ba
in kikayi la’akari da yanzu iyaye na sakin yan 1 nd
half year a titi da sunan wasa,, sweet kadai zaki bawa yaro
shikenan,,,
kije ki kawo zuwa jibi sai muyi aiki mu gama cikin
satin
nan..
Munafurci dodo ne tabbas mai shi ya kan ci,, Oyiza ce zaune a tsakar gida tana kallon salma na
wasa
cikin motarta da a kiyasi zata kai 350k dan har
petur ana
zuba mata ta fita yawo da ita cikin unguwa,
suwaiba ce ta shigo rike da Abulbait tana ma ummu wasa,
zama tayi a kasa kusa da kafar oyiza ta fara mata
kirari,
nan da nan oyiza ta saki fuska suna hira tana bin
Abulbait
da kallo, oyiza ta kalli suwaiba tace wai ni ko yanzu abul ya
kai
shekara uku, suwaiba tayi dariya tace wane uku,
shekararshi 1 da wata takwas,
oyiza ta haďiye miyau ta shafa kanshi tace naga
yayi saurin girma ne, suwaiba cike da murnar an yabi ďanta
tace a
hakan, ay ko ni ganinshi nakeyi a motse kamar
fara, oyiza
tace aiko ya girma wallhy bari in bashi sweet kema
akwai wata yar kyautar da zan miki, suwaiba cikin murna
ta mike
tana godiya ta bi bayan oyiza jiki na rawa,
dubu ashirin oyiza ta bata tace ta kara jari sannan
ta bare
sweet ta bawa Abulbait tace shanye kar ka bawa kowa kaji,
bakin suwaiba ya kasa rufuwa tanata godiya
kamar wacce
akayi ma kyautar aljanna,
oyiza tace haba ba komai ay zaman tare ya wuce
komai nima kin min abinda ya fi wannan,
har gate ta raka suwaiba tana kallon Abulbait saida
ya
shanye tass sannan ta juya gida,
Suwaiba da rawa ta shiga gida tanata ďaga kuďin
sama tana nunawa ma’u dake ma Asiya yar Abida kitso,
rawa
takeyi tana habaici wai wata saidai bauta amma
bata
samun kudi, kullum aikinta renon yayan da ba nata
ba daga a bata ragowar abinci sai a bata na batarwa,
Ma’u ko kallonta batayi ba ta karasa ma asiya kitso
tayi
mata wanka ta bata abinci ta goyata kafin mamanta
ta
dawo daga gurin aiki,,, Tun bayan isha’i Abulbait ke kakarin amai kamar
zai
amayar da yayan hanjinshi,
jike jike suwaiba ke tayi mishi tana bashi amma ina
amai
yaki tsayawa, kudin da oyiza ta bata ta kalla a zuciyarta tace
nasan yanzu
in nace zan kaishi asibiti zan kashe fin dubu biyu, ta
maxa
ta mayar dasu tace inaa a gida zaka zauna bari in
jiķa maka tazargade dan da gani aman hakori ne,
tashi tayi tana bincika tazargade bata gani ba, ta
duba ko
ina na dakin amma bata ganshi ba kuma tasan tana
dashi
ko dazu ta ganshi, mikewa tayi ta fita da gudu ta shiga gurin hajja dan
bata
rabo dashi, hajja ta dubo ta mika mata tace Allah ya
bashi
lafiya, tace ameen ta fita da gudu,
tana shiga ďaki ta tarar da gawarshi bakinshi duk ya baci
da jini,
wani irin ihu ta saki tana jijjigashi tana kiran
sunanshi, da
gudu hajja da ma’u suka shigo cikin dakin, ganin
Abulbait ya daga musu hankali hajja ta daukeshi tana
dubashi ko da
sauran numfashi, girgiza kanta tayi tace saidai kiyi
hakuri
suwaiba Allah ya karbi abinshi, ta kara sa ihu tana
kuka tana birgima kamar tababbiya, dakyar aka
lallasheta tayi
shuru akayi mishi wanka aka suturceshi malam
atiku ya
daukeshi ya kaishi dakinshi yayi kwanan keso
acan… Aiki sosai chummy takeyi ma oyiza akan ta samu
cikin ďa
namiji,
tace mata ta nesanci alhj basheer har tsawon
kwana uku, a
ranar na hudun ne zata bata magani sai tasa ya kusance ta,
haka kuwa akayi oyiza ta kauracewa shimfidar alhj
basheer
gashi mabukaci gashi kuma ta hanashi kusantar
zeenatu,
abin na damunshi amma haka ya daure dan kar ya bata
mata rai..
Suna zaune a kofar gidanshi shi da alhj bara’u suna
hirar
rayuwa, alhj bara’u ya tuno da wani tsumi a
motarshi ya shiga ya dakko ya mikawa alhj basheer daya, alhj
basheer
yace na menene wannan, alhj bara’u yayi dariya
yace
goggo ta aikomin shi daga daura maganin basir ne,
alhj basheer ya fara sha yace lallai wannan irin bauri haka
da basu sa zuma ba dakyar zai shawu,
sai gurin sha ďaya suka rabu kowa ya shiga
gidanshi,
a parlor ya tarar da oyiza cikin wata matsiyaciyar
shiga mai tada sha’awa, karasowa yayi kusa da ita ya zauna,
matsawa tayi sosai tace meye haka kuma, idonshi
yayi ja
yace ki taimakeni safiyya,
, tayi tsaki ta mike tace in taimakeka akan me, nifa
banason jaraba na fada maka kayi min hakuri na tsawon
3dys jibi ne
fa
, ni banason gajen hakuri walhy, ta wuce ciki ya
bita da
sauri tayi maza tasa keyy ta datse dakin,, ya koma ya zauna cikin tashin hankali,
mararshi yaji tana murďa mishi sosai ya rasa yadda
zaiyi
sai juyi yakeyi,
kamar an mintsileshi ya mike rike da mararshi ya
wuce dakin zeenatu, tana zaune tana addua tana kai
kukanta
gurin Allah ya murda kofar ya shigo,
waigowa tayi ta kalleshi ta mike da sauri saboda
yadda taga
idonshi yayi ja, karasawa tayi kusa dashi cikin damuwa ta
rikeshi tace lafy me ya sameka,
kankameta yayi yana fitar da wani wahalallen
numfashi
yace ki taimakeni zeenatu, dan Allah ki taimakeni in
sauke nauyin da rataya a wuyana akanki saboda ina cikin
mawuyacin hali,
ta rikeshi sosai itama tace babu taimako tsakanin
mata da
miji, duk lokacin da kake bukatata a shirye nake in
amsa kiranka,
ya sauke ajiyar zuciya yace Allah ya miki albarka
zeenatu,
nan suka shiga faranta ran junansu,
tabbas zuciyarshi tayi missing zeenatu ta ko wane
bangare amma ya rasa meye ya tokare wani shashi nata har
baya
iya kyautata mata,
Alhj basheer ya ji dadin wannan daren saboda yayi
gamsuwar da ya dade baiyi ba,
ga zeenatu ma haka abin yake domin ganin daren tayi
kamar duk yafi sauran darurruka amma ta
dangantashi da
missing din mijinta da tayi,
sai da yayi wanka a dakinta yana sa mata albarka
sannan ya fita cikin tsananin ciwon kan da yarasa dalilinshi,
a daren ranar Alhj basheer da zazzabi mai zafi ya
kwana
saukinta ma ya sauke wani nauyin, sai kawai yaji
da na
zazzabin….. Mrs tijjani shattima….
[9:13PM, 16/03/2016] .: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣3⃣ By
Aysha Ya’u Kurah
Satin Alhj basheer daya yana zazzabi har saida
yasha
allurai, zeenatu ke kula dashi dan oyiza na fushi dashi tun
da ta ganshi ya fito daga dakin zeenatu a ranar,
Ga kuma maganin da chummy ta bata ya wuce
ka’idar
amfaninshi saboda ciwon da yakeyi,
a ranar da taga alamun yaji sauki ne ta fara neman hanyar
da zatayi amfani da maganin har ya kusanceta,
haka kuwa akayi sai da tasan duk yadda tayi da
kissa da
yaudara har ya kusanceta,,
oyiza ta kasance cikin farin ciki a wannan dare dan gani
take ma har ta haifi ďan komai ya dawo under her…
4mnts ltr
Zeenatu ce zaune suna hirah da Abida dake da
tsohon ciki,
Abida ta kalli zeenatu tace matar nan fa ni ban gane miki
ba, tun wata biyu da suka wuce kika wani canza
kikayi
fresh, yanzu kuma gaba daya kin cika famm sai
kace me
ciki, zeenatu ta shafa cikinta tace sai kace yin cikin
wasan yara
ne, ko sign fa ban taba ji ba,
Abida tace ji ki da wata magana, akwai cikin da
haka yake
ba’a taba ganeshi sai in ya fito da kanshi kuma wallhy
alamu sun nuna cikin nan ya dan dade a jikinki,
zeenatu tayi
dariya sosai tace to doctr Abida naji bayaninki,
dama ana
jini in ana da ciki, Abida tace nawa akayi kedai ina zuwa, gida ta
shiga ta
dauko ragowar “pt strip” din da tayi amfani dashi
farkon
cikinta sannan ta dawo ta bata kwalba tace taje tayi
fitsari, zeenatu ta mike tana dariya tace Abida kenan
wahala kawai
zaki bawa kanki,
Abida tace tunda ba ke zaki wahala ba meye na
compln, ta
yi dariya hade da shiga bayi tayi fitsari ta fito ta mika mata
kwalbar,
Wani irin ihun murna Abida tayi da taga postive, ta
kalli
zeenatu tace wallhy nayi tunanin hakan, wayyo
dadi kasheni, zeenatu a ruďe ta shafa cikinta tace kina
nufin ciki
gareni, u mean akwai halitta mai rai a cikina,
Abida tace sosai ma kuwa in baki yarda ki shirya
gobe kafin
na tafi karbar hutun haihuwa muje asibiti, zeenatu idonta ya
ciko da kwallar farin ciki tace Abida bansan irin
farin cikin
da zanyi ba in har wannan maganar taki ta tabbata,
Allah ka tabbatar da wannan maganar kasa Abida
ta faďi a bakin mala’iku,
Abida tace ameen zeenah,
tashi zeenah tayi ta shige ďaki ta cire rigarta tana
kallon
kanta a mudubi, kirjinta ne kadai ya ciko amma
mararta a shafe take, maida rigarta tayi tana adduar Allah ya
tabbatar
da wannan abun,,
Washe gari tun asuba ta gama shiri dama bata
rintsa ba
tana ta addua, karfe takwass dai2 ta fito suka wuce dan mai gidan
baya
gari sunyi tafiya shi da oyiza mai laulayi wai batasan
warin
gidan da nigeriar gaba ďaya, (samun guri),
AKTH suka nufa, basu wani sha wahala ba saboda akwai
kawar Abida a asibitin,
test din jini akayi mata aka tabbatar da tana da ciki,
scanning ppr aka bata suka je tayi scanning inda ya
nuna
makalallen ciki na wata hudu, ‘”HAMDAN KASIRAN DAYYIBAN MUBARAKAN FIHI,”” abinda zeenatu ke
fadi
kenan hade da kuka, saida suka gama komai a
asibitin
Abida ta maidata gida cike da murna ta tsaya tayi
wa su Ma’u albishir sannan ta wuce aiki,
Hajja da ma’u a lokacin suka shigo taya ta murna,
har ta ďaga waya zata kira alhj basheer ta fada
mishi sai
wata zuciyar ta haneta, haka gida ma so takeyi ta
musu surprise,
Kula sosai take bawa cikinta da ya kai wata biyar
har ta
fara zuwa awo alhj basheer da oyiza basu dawo ba,
gidan
Abida take zama suyi hirarsu lokacin ta haifi ďanta namiji
mai suna JABEER,
Cikin zeenatu na wata bakwai su oyiza suka dawo
itama da
nata cikin watanshi bakwai, fitowa tayi cikin hijab
tana musu sannu da zuwa,
alhj basheer ne kadai ya amsa babu yabo babu
fallasa, ta
kalli salma tace ummu ya hanya,
salma tayi banza da ita suka wuce daki ita da
mamanta, saida alhj basheer yayi wanka ya huta sannan ya
fito cin
abinci, zeenatu ce tayi serving dinshi tana mishi hira
yana
amsawa jefi2, bayan ya gama cin abincin ne ta fara
mishi magana cikin hikima,
tace ranka ya dade kudi nakeso,
ya yatsuna fuska yace me zakiyi da kudi, ta
sunkuyar da
kanta kasa tace siyayya nakeso inyi ma kyautar da
Allah ya bani,
cikin rashin fahimta yace ban gane ba, ta daga hijab
din
jikinta ta dauko hannunshi ta ďaura kan cikinta
tace Allah ya
azurtani da ciki har na tsawon wata bakwai, “karaf a kunnen oyiza da ta fito cin abinci,”
fuskar alhj basheer ta kasa boye farin cikin da yake
ciki a
wannan lokacin, janyota yayi ya zaunar da ita kan
jikinshi
sam bai kula da oyiza ba, ya kalleta yana shafa cikin da ya
dan taso yace da gaske zeenah,
ta gyada mishi kai, yayi murmushin jindadi ji yakeyi
kamar
wannan ce haihuwar da zaiyi ta fari, yace Allah ya
fito min da abinda ke cikin nan kuma yasa namiji— ta maza
ta toshe
mishi baki tace namiji da mace duk Allah ke
hallitarsu,
muyi fatan samun masu albarka shine kawai
yallabai, yaji wani nutsuwa ta ratsashi yace hakane Allah ya
bamu
masu albarka, “mtswwwwwww” sukaji an ja tsaki
mai karfi
suka waiga suka ga oyiza tayi gaba tana huci
kamar zakanya,
kau da kanshi yayi ya cigaba da kallon cikin
zeenatu yace
gobe ta shirya suje siyayya da asibiti a kara duba
lafiyarta,
sun dade suna hira cikin jin dadi ya ma manta da wata
oyiza a rayuwarshi…
Oyiza kuwa tana shiga ďaki ta maida salma ďakinta,
ta hau
kan buzun tsafinta sai gata ta bayyana gaban
“chummy” idonta jawur take fada ma chummy halin da take
ciki,
chummy tayi iya yinta da duk wasu siddabarun da
zatayi
tace oyee wannan cikin bazai zube ba, cikin jikinta
na tare da kariyar adduoi sosai sai dai ki bari in ta haifeshi
sai
kisan abun yi,
cikin tashin hankali tace “my lord” to idan ta haifi
namiji fa,
chummy tace sai kinso ya rayu in ya fito duniya, oyiza hankalinta ya ďan kwanta tayi sallama da
chummy ta
bace ta nufi gida….
Ciwo takeji sosai amma hakan bai hanata ci gaba
da
aikinta da tasbihi a bakinta ba, wani irin Murďawa mararta tayi ta tsuguna da sauri
tana
faďin “YA HAYYU YA KAYYUMU BI RAHMATIKHA
ASTAGITHU ASLIHLI SHA’ANI KULLAHU WALA
TAKILNI ILA
NAFSEE ĎARFATU AYNUN” da dai taga abun kamar gaba
yakeyi ta mike tayi hanyar parlo tana maimaita
adduoi a
bakinta,
oyiza na zaune tana cin abinci zeenatu ta shigo da
kyar, tace dan Allah safiya ki taimak— ta kasa karasawa
saboda
wani irin nishi mai karfi da yazo mata,
oyiza tayi tsaki ta juya tana adduar Allah yasa ki
mutu ke da
ďan cikinki, zeenatu kuka sosai takeyi ga wani ruwa dake bin
kafarta,
sallamar Abida taji nan taji kamar an sauke mata
zafin wani
bangaran, da sauri Abida ta karaso ta ajiye jabeer
tace haba zeenatu ay da sai ki kirani a waya, zeenatu ta
runtse
bakinta ta rike hannun Abida dake kiran Ma’u a
waya,
da sauri ma’u ta shigo suka kamata,
Abida ta kalli oyiza tace dadin abin nakuda Allah bai ďauke
wa uban kowa ba, kowacce yar iska zata dandani
nata in
lokaci yazo,
oyiza ta harzuka matuka ta mike tana bala’i suka
fita sukayi banza da ita, drivrn gidan ya karaso da sauri suka
wuce
asibiti,
Suna shiga Allah ya taimaketa batayi wata doguwar
nakuda
ba ta haifo ďanta namiji kyakykyawa mai kama da iyayenshi,
likitoci suka shirya baby suka kimtsa mamanshi
suka
kwashe mata jini suka turota dakin hutu, murna a
gurin su
ma’u ba’a cewa komai, Abida ta kira Alhj basheer tayi mishi
albishir,
murnar da yayi a lokacin ba mai faďuwa bace, saida
yaje
gida ya shirya sannan ya fito zai tafi asibitin, oyiza ta
fito rike da kugu tace ina zaka je, ya fadada fara’arshi
yace
hospital zeenatu ta haihu,
oyiza ta kauda kanta tace Allah ya raya, yace
ameen, har
yayi gaba, ta tuna ta kwala mishi kira ya tsaya tace me ta
haifa, yace baby boy,
wani irin murdawa mararta tayi cikin ruďewa tace
namiji
kenan ta haifa,, yace eh mana,
ya shiga mota cikin farin ciki ya wuce ya barta tsaye kamar
an dasata hawaye masu zafi suna kwaranya a
idonta….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button