Rabo Ajali Episode 1 – 15

Posted by Aisha Yau Kurah on 09:25 PM, 20-Mar-16
Under: RABO AJALI
[10:14AM, 18/03/2016] .: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣4⃣
By
Aysha Ya’u Kurah Ciki ta juya tana tafiya da kyar, ga bakin ciki ga
kullewar
mara,
a gado ta kwanta tana kuka sosai kamar wacce
akayi ma
mutuwa, sai da tayi kuka ma’ishi sannan tayi shuru da
tunanin itama
fa cikin gareta kuma chummy ta bata assurance din
namiji
zata haifa,
yanzu kawai abinda ya rage mata shine tasan yadda zatayi
ta kashe jaririn nan tun kafin ya girma yasan
kanshi, da
wannan tunanin zuciyarta tayi wasai ta mike ta
shiga
wanka.. Kwanan zeenatu huďu da haihuwa kullum da
daddare alhj
basheer na makale a ďakinsu, duk wanda ya
ganshi a
kwanakin yasan farin ciki ne cike da zuciyarshi,
haka mai jego na samun kulawa daga gurin makotanta da
kanwar
kakarsu Yadikko da tazo daga cameroon,
a ranar da suka cika kwana shida da yamma sunyi
wanka
ita da baby yadikko ta debo rushi tasa garin “habbatis
sauda” a ciki tana sa hannunta a hayakin in ya dau
zafi
saita daura a kan cibiya da marar jaririn tana
karanto
adduoi tana tofa mishi, juyawa oyiza tayi da sauri da ta
tunkaro dakin da wasu magungunan tsafinta
wanda
chummy tace in har ta shafi babyn da maganin a
hannunta
to tabbas jininshi zai kafe ya mutu, jin hayakin tayi kamar zai tafi da ranta, ta shiga daki
da
sauri ta datso kofa tana haki haďe da kakarin amai,
ta dade
sosai a haka kafin wani irin murdaddan ciwon
mara ya dawo da ita daga duniyar azabar shakar hayakin
habbatis
sauda,
ciwon da oyiza taji ne yasata sakin ihu tana karawa
kamar
zararriya, babu wanda yajita dan su yadikko suna can suna
hira dasu hajja da suka shigo a lokacin sunata
preparation
din suna washe gari,
sai da ta galabaita sosai tana ihu tana faďin “ohh
my lord” “chummy wr are u,”
Ma’u ce ta fara jin ihun saboda zagayawa baya da
tayi dan
kwaso shanyar baby, da sauri ta zagayo ta faďa
musu suka
mike sukayi dakinta suka murďa sunata bugawa yaki
buduwa saboda tasa key,
kiran alhj basheer zeenatu tayi lokacin har oyiza ta
suma
saboda azaba,
cikin yan dakiku ya baro inda yake ya dawo gida ya dauko
spare key ya bude dakinta,
kwance cikin jini suka sameta, da sauri suka karasa
suka
kamata suka sata a mota sai asibiti,
dakin theater aka wuce da oyiza, cikin gaggawa likitoci
suka shiga ceton ransu ita da babyn,
cikin nasara suka samu fitowa da baby mai kyan
gaske
gata katuwa dan da sukayi wghn dinta ta kai
6.2kg, doctor yayi ma oyiza “PS” nurses suka shirya baby suka
fito ma
alhj basheer da ita, cikin murna ya karbeta yana
kallonta
yana mata addua,
ita kuwa oyiza sai can cikin dare ta farfado tana ihun kuka
dakyar,,,,
wata nurse ce a gefenta da yadikko suka matso
suka riketa
suna fadin sannu,
ta kwanta lamoo tana shafa cikinta dakyar tace na haihu
ne, yadikko ta daga mata kai tace eh kin haihu, tayi
murmushin da bata san ya fito ba saboda azabar
ciwo tace
ina yaron yake, yadikko ta fito da babyn cikin
gadon jarirai tace gata nan, oyiza cikin rashin fahimta ta gwalo
dasassun
idanuwanta tace gashi nan ko gata nan,
yadikko tace gata nan dai inaga bakiji da kyau
bane,
oyiza ta waigo a hankali ta kalli babyn ta juyar da kanta
tana kuka sosai tace “why chummy” why? Meyasa
zan haifi
mace, kin manta alkawarin da kikayi min,
meyasa zeenatu zata haifi namiji ni mace,
meyasa zanyita haihuwar mata, magana oyiza takeyi cikin
zaucewa tama manta da wata yadikko a kusa da
ita, saida
tayi kuka sosai nurse tazo tayi mata allura sannan
ta samu
bacci, Yadikko komawa tayi ta zauna tana kallon oyiza
tana
mamakin furucinta, tabbas sai sun mike tsaye akan
zeenatu
da ďanta saboda wannan furucin na oyiza ba
karamin ďaga hankalin yadikko yayi ba, ‘”CHUMMY” kalmar da ta
dinga
maimaitawa kenan a ranta, wacece kuma chummy?
tambayar da yadikko tayi ta ma kanta kenan ta
kasa samo
amsa daga karshe ta mike ta shiga tayi alwala ta fara
nafilar nemawa jikokinta tsari daga sharrin
makiya…
Ranar suna jariri yaci suna AFFAN, anyi taron suna
na gani
na fada mutane sunzo sosai tayasu murna, faďin farin cikin
da duka su biyun suke ciki bata lokaci ne domin
bazai taba
misaltuwa ba, oyiza kuwa tana can cikin bakin ciki
dan
tunda ta farka anyi anyi ta bawa baby nono taki, kuka
kawai takeyi tana tufka da warwara, maimakon
isharar da
Allah ya nuna mata yasa ta saduda tasan babu
wani mai yi
sai shi taki ta gane, sam batayi gv up ba sai ma wani karin
mugunta da zuciyarta ta naďo, babu abinda yafi
daga mata
hankali sai cewa da doctor yayi mahaifarta bazata
kara rike
kwai ba saboda ta samu gagarumar matsala, a wannan lokcin likitoci sunga bori saboda tsine
musu
kawai takeyi tana zaginsu, dakyar alhj basheer ya
lallabata
da kalamai masu kwantar da hankali,,,
Kwananta hudu a asibiti aka sallameta ta dawo gida da
muggan kudirai a cikin ranta, a zuciyarta tace
wannan
karan ita zata zama shaidaniyar kanta dan taga
yanzu aikin
chummy baya tafiya mata yadda ya kamata, haka ta cigaba da jinyar jikinta da kula da yarta
wacce taci
suna FAREEDAH,
oyiza kullum idonta na kan side din zeenatu taga
ko sun bar
Affan shi kaďai amma bata samun wannan damar saboda
yadda yadikko ke manne dashi a ko dayaushe,
sai da yadikko tayi wata biyu a gidan tana kula da
zeenatu,
tun ana saura sati ďaya ta tafi kullum dare bata
aikin da ya wuce yi ma zeenatu faďa akan ta kula da kanta da
ďanta
da kuma adduoi,
zeenatu saidai tayi dariya dan abin na yadikko ya
zame
mata kamar waka tunda kullum sai anyi maimaicinshi..
Salma ta kalli mahaifiyarta tace mummy kika ce
wannan
nawa wannan na affan ko,
oyiza tace a’a wannan ne naki, ki kula fa sosai, ta
gyaďa kanta ta fita da gudu fareeda na binta a baya,
Affan zaune suna bin karatun lptp din yara na
“alifun ba’un”
shi da jabeer lokacin shekararsu biyu da rabi shi da
fareeda
ita kuma salma ta kusa 6, dafashi salma tayi yayi saurin
ďago kanshi, a razane ya matsa dan mugun
tsoronta yake ji
saboda dukkan da take mishi,
zama tayi kusa dashi ta kara duba ice cream din
dan ta tabbatar da wanda mummy tace na affan din ne,
mika
mishi tayi tana murmushi tace gashi inji mummy,
farida cikin gwaranci tace “wanshan ne naci,”
salma ta
harareta tace wannan ne, farida ta dage akan dayan ne
saboda tafi salma wayau, kuka ta fashe dashi da
taga
alamar salma bazata bashi wanda mummyn tace ta
bashi
ba, da sauri zeenatu ta fito tace lafiya me aka miki
farida,
salma tace ice cream mummy ta bani in kawo ma
affan
kuma wannan ne nashi wai ita dole sai dai in bashi
Nawa, farida cikin kuka tace “wanshan ne mummy ta
kaya mici
sugar” kuma “cha kiji” ,
gaban zeenatu ya faďi sosai tace to duk bari in raba
muku
gardama ke salma je ki kara tambayota wanne ne na affan
din,
da gudu suka fita suka bar zeenatu cikin jimamin
maganar
farida,
innalillahi kadai take fada tana kara rokon Allah ya tsare
mata ďanta da a kullum sai an kawo mishi harin
kisa tun
yana karaminshi,
shafa kansu tayi shi da jabeer tace ma jabeer tashi
kuje gidan Antie Ma’u kafin umminka ta dawo kaji,
ya gyada mata kai ya kama hannun affan dan yafi
affan
wayau, har sun fita ta tuna da kar su hadu da su
salma ta
bashi ice cream din yasha, binsu tayi da sauri tace ku dawo bari Gaje ta dawo
daga
kasuwa sai ta kaiku kunji, ta kamo hannunsu suka
shigo
ciki dai2 lokacin su salma suka dawo da ice cream
daya suka ce gashi wannan ne nashi,
zeenatu ta amsa tace to kuce ya gode sosai, salma
tace
mummy tace yasha a gaban mu sai mu tafi, zeenatu
tace to
an gama yaran kirki bari in raba musu shi da jabeer,
ta mike ta shiga kitchen, Allah ya taimaketa akwai
nashi na
jiya a fridge, daukowa tayi ta raba musu shi da
jabeer ta fito
ta mika musu tace gashi maza ku sha ku tafi gidan anty
ma’u wanda bai shanye ba a gida zai zauna, suka
karba
suka fara rige rigen sha,
salma da farida suka fita da gudu tun kafin su kai
ďaki suke rige rigen faďin mummy yasha,
suna karasawa ta toshe bakinsu tace ku rufemin
baki ku
wuce ku bani guri, suka wuce ciki suka dau nasu
suna sha,
zama oyiza tayi cikin farin ciki dan tasan yau babu makawa
aikinta yaci tunda har sun tabbatar mata yasha,,
har bayan isha tana kasa kunne taji ihu, amma
shuru takeji
hankalinta ya fara tashi,,
karfe 9 lokacin taji dawowar alhj basheer ta mike ta fito ita
da yaranta,
zaune ta taddashi affan na kan ruwan cikinshi suna
hira
suna kyalkyace dariya kamar da sa’anshi yakeyi,
wani abu ne ya tokare mata wuya wanda ta kasa controlling
dinshi har ya kaita ga jan razanannan tsaki, taja
hannun
farida dake kokarin zuwa gurin babanta tace dalla
wuce
kuje ďaki, an faďa muku ta taku yakeyi, ai ku muna ya’ya ne
a gidan nan amma ba ya’ya ba,
alhj basheer ya dago da sauri yace haba safiya,
me yasa kike faďin haka, da affan da su salma duk
daya ne
agurina, da karfi tace biyu ne, karka kara cewa ďaya ne, ka
riga ka
nuna musu tun yanzu basu da wata daraja a
idonka saboda
sun zo a ya’ya mata,
nan ta shiga masifa kamar zata tsaga gidan, bakin ciki ne
dankare a zuciyarta saboda yadda in tayi abu akan
affan
baya kamashi,
alhj basheer bai kalleta ba ya kara rungume affan
da ya tsorata ya mike ya wuce ciki ya barta anan tana
bala’i……
Mrs tijjani shattima….
[10:24AM, 18/03/2016] .: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣5⃣
By
Aysha Ya’u Kurah Haka rayuwa ta cigaba da tafiya a gidan alhj
basheer,
kullum da sabon makirci da muguntar da oyiza ke
fitowa
dashi na tsafi da kuma na magunguna amma
dayake rayuwarmu da mutuwarmu tana gurin rabbil izzati
babu
abinda ya faru da zeenatu da affan duk da wani
lokacin in
tayi tana cin nasara saboda ance tsafi gaskiyar
maishi sai dai duk tsafin mutum in har ka dogara da Allah to
ko ya
kamaka na ďan lokaci ne zai sake ka,
a yan shekarun da suka wuce oyiza ta kara karfi
cikin
kungiyar asiri dan yanzu haka tana cikin kungiyoyi masu
karfin gaske guda hudu, zeenatu kuwa addua
takeyi ba dare
ba rana akan Allah ya kare su ita ďanta ya ďaurasu
akan
makiyansu… Affan da jabeer zaune ďakin hajja suna cin
danwake,
jabeer ya kalli affan yace kaii yau banga su anty
salma a
skool ba, affan ya juyar da kanshi yace ohoo musu
wai dan daddy yace shi zai kaini zana C.E exams su su jira
driver
shine sukayi fushi mummynsu tace bazasu ba,
Hajja dake gefe tana saka suwaitar kulu tace ca
nakeyi
ajinku daya da farida kenan bata rubuta jarabawar ba,
jabeer yayi dariyar shakiyanci yace dondi kenan
hajja, ay
anyi mata repeating yanzu p4 take,
Affan yace p4 din ma da ya aka bari ta kai,
ni ay ban taba ganin wacce brain dinta baya ďaukar karatu
irin farida ba cewar jabeer,
Affan yace tabb ay wallhy gara farida a haka, dan
anty
salma knws nottn banda mugunta,
ma’u ta ďeko dakin hajja da tsohon cikinta da kullum suke
adduar Allah yasa zaunanne ne tace ashe baku
wuce gida
ba, na ďauka ma kun tsufa a gida,
jabeer yace eh “Mama” sunan da yake kiranta dashi
kenan saboda a gurinta ya girma bacci kadai ke maidashi
gida”,
yanzu zamu tafi muna nan muna cin ďanwaken
tsohuwa,
Ma’u ta juya tace ai ya kamata kuje gida ku faďa
musu kun gama jarabawar sai kuma a ďan fita yawo tunda ba
mata
bane ku,
suka rufe kwanon danwaken suka mike sukayi
sallama da
hajja da ma’u,, sun kusa da kofar fita kausar yar suwaiba
tana rarrafe a tsakar gida tsirara ta mike ta rike
wani abu
tana dabo ta fetso kashi saura kaďan ya taba
wandon
Affan, da gudu suka fita jabeer na mishi dariya harda rike
ciki
yana tayashi dubawa ko ya taba wandonshi,
dakyar ya
karasa gida yana masifa ya wuce bayi saida yayi
wanka ya canza kaya sannan ya fito ya shiga ďakin
mahaifiyarshi,
zaune ya sameta tana waya ya zauna kusa da ita,
sai da ta
gama wayar ta juyo ta kalleshi tana murmushi tace
daga ina haka,
yace gidan maman jabeer, tace ya jarabawar kun
gama ko,
yace mun gama umma sai dai ayi mana adduar
samun
nasara, tace addua kullum yinta akeyi Affan, saidai a ďaura,
ni dai
ina kara jaddada maka ka rike ibada da karatun
qur’ani da
tsoron Allah wadannan abubuwan in ka rikesu sun
isheka duniya da lahira,
yace in shaa Allah umma, Allah ya kara mana karfin
imani,
tace ameen,
ya mike zai fita kenan Asiya ta shigo da sauri,
tace ina wuni umma, zeenatu tace lfy lau dan asy, ya na
ganki haka,
tace ummi ce tace in zo in fada miki anty ma’u ta
haihu
yanzun nan tana can gidan ma,
da sauri zeenatu ta mike cike da murna tace me muka
samu, asiya tace nima ban sani ba,
ta dauko hijab ďinta suka fita da sauri a ranta tana
adduar
Allah yasa zaunanne ne abin da ta haifa,
tun kafin su shiga ciki kukan yarinyar ke musu kuwwa cikin
kunne,
kuka takeyi irin na jarirai da iya karfinta wata nurse
a
unguwar tana gyarata,
Affan a kofar gida ya tsaya dan yana tsoron ya shiga ya
kara arba da kausar dan bai sani ba ko wannan
karan a
jikinshi zatayi kashin,
A cikin gida kuwa murna sukeyi lokacin an gama
kimtsasu anyi ma mai jego allura tana kwance tana hutawa,
duk makota anata shigowa tayata murna banda
suwaiba da
tace meye na barka a gurin gawa, mudai je zuwa
nan da
anjima itama zata bi layin yan uwanta su cike su bakwai,
karaf wannan furucin na suwaiba ya shiga kunnen
jabeer,
hararta yayi ya mikama mamanshi babyn suka fita
shida
Asiya, a kofar gida suka hadu da affan suka wuce gidansu..
Anyi suna dai2 na masu rufin asiri,
mai jego ta samu kaya da kudi masu yawan gaske
haka
mahaifinta ya samu kudi sosai haihuwar tazo mishi
da goshi, jaririya taci sunan Hajja “Hajara” Abida tace a
dinga
kiranta da “AFEEYAH”, suwaiba kuwa bakin ciki
kamar zai
kasheta da taga har kwana bakwai jinjira na raye
ga kaya da kudi da uwarta ta samu kamar za’a bude shago
dasu,
sam ta kasa boye bakin cikinta har saida sukayi
fada da
Abida ta gaggaya mata bakaken maganganun da
yasata shigewa ďaki ba shiri dan Abida ba kanwar lasa
bace
itama…
Tun daga lokacin kullum sai suwaiba ta kasa
kunne ko
zataji kururwar mutuwar jinjinra amma shuru takeji ga
jinjira har ta wuce wata bakwai kullum cikin koshin
lafiya,
Afeeya ta taso cikin kulawar mahaifiyarta da
kakarta hajja,
yarinyar duk wanda ya ganta sai yayi sha’awarta saboda
kullum a tsaftace take kan nan nata baya rabo da
kitso da
ribbons saboda tana da yalwar gashi, gata yar
lutuya
goyonta gunin ban sha’awa, saidai fa akwai azabar kuka da
masifaffen kwuiya, banda mamarta da hajja babu
wanda
take yarda ya ďauketa a duniya sai jabeer, shima
dan tana
ganinshi kullum a dakinsu kuma yana fita da ita yawo,
sam bata yarda da affan dan ko ya miko hannu zai
ďauketa
in ta soma tsala ihu bata taba yin shuru har sai taga
baya
gurin, wannan dalilin yasa kullum ya shiga gidan sai yasan
yadda akayi yasa ta kuka ta hanyar daukanta ta
karfin
tsiya,,
Afeeya na da shekara biyu jabeer yasa babanshi
yasata a makarantar da suke zuwa lokacin suna js2, dakyar
ma’u ta
yarda dan gani takeyi kamar wata hidimar ta ďaura
musu,
tare suke zuwa makaranta in sun dawo ya wuce
gidansu da ita sai can yamma yake mayar da ita gida, duk wani
kuďin
break da ake bawa jabeer akan afeeya yake
karewa,
gata sosai takesha gurin yan samarin biyu duk da
har lokacin bata cika yarda da affan ba,
salma da farida ba karamin tsanarta sukayi ba, in
suna
cikin mota ta kallesu sai su sakar mata harara,
turo baki takeyi a tsiwace irin na yara itama ta rama
sai tayi lamoo a jikin jabeer ta runtse idonta dan kar su
daketa,
haka a skul ko takata yaro yayi bai sani ba ko yafi
karfinta
sai ta bishi ta rama in ya daketa taje ta faďa ma
jabeer, in kuma tafi karfinshi to ta samu nama dan sam
bazata raga
mishi ba….
Mrs tijjani shattima….