ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ﻭﺍﻟﺼﻼﺓ ﻭﺍﻟﺴﻼﻡ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺍﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﻭﺳﻠﻢ . ….. Affan… Affan… Affan.. sau uku saurayin dake tsaye a kanshi ya kira sunanshi amma ko waiwayowa baiyi ba bare ya amsa,, hankalinshi na kan ruwan dake malale cikin wani katon ramin kiwon kifin dake cikin gidansu yana kallon yadda suke wuntsil wuntsil ciki yana girgiza kanshi da jikinshi hakoranshi waje yana dariya da karfi, duk wanda ya ganshi yasan hankali sam bai isheshi ba, dafashi saurayin yayi hade da zama gefenshi ya watsa ma kifin abincinsu nan take suka kara hautsinewa suna yawo cikin ruwan gwanin ban sha’awa, ihuu Affan yasa yana kaďa kanshi yana kokarin kai hannunshi cikin ramin kuma yana nokesu alamar tsoro, saurayin yayi murmushi ya kara watsa abincin,,, affan ya cikwikwiyeshi cikin murna yana fadin yeeehhh Jabeer kara zuba musu yunwa suke ji dama, jabeer ya shafa fuskarshi cikin tausayin halin da amininshi yake ciki yace affan lokacin sallah yayi muje muyi sallah mu dawo sai in cigaba da basu abincin, affan ya no’ke wuyanshi kamar karamin yaro yace um um ba yanzu zanyi sallah ba mummy tace ko da yaushe nayi sallah dai2 ne saboda ni ba a rubuta min zunubi, Jabeer da idonshi ya fara canza kala dan ya riga ya saba da jin hakan a bakin affan kullum in yayi mishi maganar sallah, cikin dabara yace waya fada maka ba a rubuta maka zunubi Affan, to bari kaji kasan wutar nan da ake kunnawa mai zafin nan? Affan cikin firgici yace eh na santa wanda ake dafa min indomie mai zafi ko, jabeer yace of course ita ay kasan tafi indomie zafi ma ko, affan ya gyada kanshi, jabeer yace to wutar da Allah ke kona waďanda basa sallah tafi wannan zafi sau “dubu malala gashin tinkiya” affan ya mike a firgice idonshi zuru2 yace tafi wutar dake dafa ruwan toilet heater ma wanda yake kona ni in zanyi wanka, jabeer yace sosai ma ay wannan ruwan kamar ruwan sanyi ne akan wutar Allah, affan ya fara ja baya yace karya kakeyi sai naje na tambayi mummy, jabeer ya mike da sauri dan yasan yana zuwa ya tambayi mummy to fa bazata taba bari yayi sallah ba, da sauri ya rike hannunshi yace affan ni ke karya, ya fizge hannunshi yace eh mana kaine kake karya ya juya ya ruga cikin gida da gudu jabeer na kiranshi yayi banza dashi, dafe kai jabeer yayi cikin damuwa sai da yafi minti 5 tsaye sannan ya wuce ya tafi masallaci,,,, Jabeer ďinne ya fada maka haka, affan ya gyada kanshi yana daďa kwanciya jikinta alamun tsoro yakeji kar wuta ta kona shi, mummy tace rabu dashi makaryaci ne na fada maka ka daina kulashi kullum burinshi ya tirsasa maka yin abinda da bakayi niyya ba kuma ko a musulunce babu takura a addini, rabu dashi kaji affan din daddy tashi kaje kaci abinci kayi wasanka kaji, ya daga kanshi ya mike yana tsalle har ya karasa gurin cin abinci yana kiran sunan Hansa’u mai aikinsu tazo ta zuba mishi abinci, murmushi mummy tayi hade da ajiyar zuciya, Salma babar diyarta ta ajiye laptop dinta tace mummy wannan tsinannan jabir din so kawai yake ya ruguza miki plan dinki, kullum shi kenan maganar sallah sai kace wani sallau, mummy tayi dariyar mugunta ta kalli gurin da affan ke cin abinci duk yayi kaca2 da gurin amma ko digo bai diga a rigarshi ba saboda tsananin tsaftarshi, tace barni dashi ummu, jabeer yana wuce gona da iri tabbas zan san duk yadda zanyi in rabasu da affan in ba haka ba wata rana zai sa kwaba ta tayi ruwa, Fareedah tace wallhy I so much hate him sai ya dinga wani ďadďaga kai kamar kadangare shi a dole ga kyakykyawa mtsww taja tsaki, mummy tace ku barni dashi dani yake magana in yasan wata ay bai san wata ba….. posted by sulaiman bomboy Wannan yayi kuwa? RABO AJALI ◆◆ 2 by Sulaiman Bomboy Da gudu ta shigo gida ta tarar da jarababbiyar kishiyar uwarta a tsakar gida tana fiffita, sannu da gida kawai tace bata jira amsa ba ta wuce ďakin kakarta Hajja Giďe, fadawa dakin tayi babu ko sallama ta cire skul Bag ďinta tayi wurgi da ita a kan gado sam bata kula da mutum a kan gadon ba ta fita da sauri ta shiga toilet, Hajja ta idar da sallah tayi tsaki tace wannan yarinya saidai Allah ya shirya yi hakuri jabeer, ya mike zaune yana murmushi yace zata sani ay bari ta dawo, hajja tace ay kai baka iya yi mata faďa sai dai kullum kace zata sani kullum kai ke kara sangarta ta, kafin yayi magana ta shigo ta ďane kan cinyar hajja tace hajjanah” sannu da gida, hajja ta tureta tace dalla ni sauka karki karya ni, sai a sannan idonta yakai kan jabeer dake kallonta baya ko kiftawa, da sauri ta mike tana murmushin jindadi ta zauna kusa dashi kamar zata shige jikinshi tace dama kana cikin dakin nan, ta shagwabe fuska tace shine kana kallon hajja tana tureni ko kayi mata magana kalli fa hannu na saura kaďan taji min ciwo, Hajja tace Allah ya kiyaye dai banji miki ciwon ba ko, ta turo baki tace kinso kiji min mana inaga ma dan kinsan yaya jabeer na nan ne shiyasa baki ji min ciwon ba, hajja ta kwashe da dariya tace to yau dai sharrin kaďan ne ko Allah nagode maka ma yana cikin dakin da yana zuwa nasan ce mishi zakiyi yau da kyar na barki da rai, jabeer ya kwashe da dariya, ta kwabe baki ta fashe da kukan shagwabe harda buga kai a gado, jabeer yace subhallahi me kuma akayi miki, hajja ta mike tace tabarar fa, ni bari kaga in fita dan in ina dakin nan zane yarinya zanyi, cikin kuka tace kaji ko wallhy bulala takemin kullum yauma dan ta ganka ne, jabeer ya haďe rai yace gaskiya hajja zamu kai kararki can kotun karshe a yanke miki hukunci, hajja tayi dariya tace mu fara shariar daga yau ma in dai akan AFEEYAH ne, afiyah ta dago kai ta harareta, jabeer yayi murmushi ya ciro hndky dinshi yana share mata hawaye, yace so sorry babynah, ya dago fuskarta ya kalli cikin idonta yace baki san kin girma da kuka ba, ta kara marairaicewa kamar karamar yarinya tace to baka ganin abinda takemin, yace to nace kiyi hakuri kinji, ki daina yarda suna saki kuka kinaso a dinga ce miki ruwa2, ta noke wuyanta tace ah’ah, yace to sai kin zama mai hakuri kin daina yawan kuka kinji, tace tam zan daina, yace yauwa wifey nah,, ya dakko ledar gefenshi ya fito dasu biscuits da chocolates, rungumeshi tayi cikin murna ta mishi peck a kumatu tace I love u so much hubbynah, wani abu yaji yana mishi yawo cikin kwanyarshi, a hankali cikin rashin kuzari yace more than u do babynah,, ta sakeshi tana dariya, nan suka cigaba da hirah cikin jindadi tana shan chocolates, sai da aka kira la’asar sannan ya fito zai tafi, rakoshi ta fito yi bayan yayi sallama da hajja, a dai2 kofar dakin inna suwaiba kausar ke zaune tana ganinsu ta shiga wakar habaici tana fadin Allah wadai da halin yan iska sai a shige daki afi karfin awa wai da sunan ana hira, ran Afiya ya baci matuka jabeer ya lura da hakan ya rike hannunta gam ta fisge, tace da uban wa kike , kausar ta mike tace da ubanki nake kinji na kira sunanki, in ba tsarguwa kikayi ba meye na jin haushi shegiya marar kunyar banza, Afeeya ta kuma hassala tayi kanta da sauri jabeer ya riketa da iya karfinshi ya jata da kyar suka fita, kukan bakin ciki ta fashe mishi dashi tana ta tirje hannunta, murmushi yayi dan yasan in bata tsaya ta mayar da martani ba bazata taba hucewa ba, hakuri ya shiga bata amma ko kalma daya bata iya rikewa ba saboda zuciyarta cike take da bakin ciki gani take idan basuyi fada da kausar ba yau sai tayi ciwo mai tsanani, matsowa sosai yayi kusa da ita yace haba afee nah, ba nace kiyi hakuri ba, kinaso inyi fushi ne, ta turo baki tana kuka tace ko zaka fashe yau bazanyi hakuri ba, ya hade rai yace to ni kuma in bakiyi hakuri ba mun bata garin ma zan bari gaba daya, cikin dakewar zuciya tace ka tafi gaba da birnin sin ma dan wallhy bazan hakura ba, sakin hannunta yayi yace ni ko? Ta juya mishi baya tace eh ďin, yace to shikenan bye yasa kai ya fita, ko ajikinta a lokacin saboda zuciyarta na azalzalarta taje gurin kausar……. 11 hours ago Sulaiman Bomboy [7:00am 08/11/2016] .: ◆◆ RABO AJALI 3 By Sulaiman Bomboy Tana shiga ta tarar da kausar na buga k’ullun alale, sam kausar bata kula da shigowarta ba sai saukar wata sanda taji akanta da karfi, zafin ya gigita ta sosai tasa ihun da ya fito da inna suwaiba da hajja daga ďaki, cikin rudewa inna suwaiba ta kama kausar tace kausar meya faru, kausar ta kasa magana sai kuka takeyi hannunta rike da gurin jini na fita, hajja ta kwace sandar hannun Afiya tace yanzu ke saboda tsabar mugunta wannan murďaďďiyar sandar kika buga mata, Afiya ta turo baki tace hajja fa baki san abinda tayi min bane shiyasa, inna suwaiba cikin fushi ta saki kausar tace uban me ta miki, Afiya ta murguďa baki tace gata nan ki tambayeta, inna suwaiba tace lallai yau za’a haifi ďa mara ido a gidannan wallhy, Afiya tace a haďa harda mara hanci ma a haifa, hajja ta bige bakinta tace ke wai wace irin yarinya ce da baki jin maganar kowa, Afiya tace to wai hajja ita baki tambayeta me tace mana ba, ce mana fa tayi yan iska, inna suwaiba tace ay kunfi karfin ya’yan iska saidai na guguwa, wallhy yau saina miki shegen duka a gidan nan sai na tabbatar wannan tsinannan bakin naki yayi laushi, Afiya tace Allahn da halicci baki na shi kadai zai iya sashi yayi laushi ba wata ca— hajja ta toshe mata baki tace na shiga uku ni Giďe, yanzu ke Afiya bazan miki magana kiji ba, inna suwaiba tace hajja ki wuce daki ki barni da yarinyar nan wallhy yau sai na mata lahani a gidannan, Hajja tace kiyi hakuri suwai— karki bani hakuri ki cuceni hajja kullum mu kenan a cuce mu a taushe mu, to wallahi bazan dauka ba, ji yadda jini ke zuba a kan kausar ay dan tasan kuna daure mata gindi ne ke da malam shiyasa take abinda takeso, in ba ta raina mutane ba ay kausar ba sa’arta bace, hajja tace kiyi hakuri dai nace suwaiba, Afiya ta harari hajja tace wai hajja hakuri kike basu ni baki bani hakuri ba sai su da babu abin ma da nayi musu, inna suwaiba ta hassala sosai tayi kan Afiya ta cakumota, hajja ta riketa tace wallhy suwaiba karki taba min marainiyar Allahn nan, wallhy kika kuskura kika sata kuka sai ranki yayi matukar baci, inna suwaiba tace ay ko sai dai ya baci ta kaima Afiya duka ta goce tana kicikicin kwacewa, kausar dake jin kanta kamar dutse ta mike tazo ta bayan Afiya ta kai mata duka, Afiya tayi kukan kura ta kwace jikinta a gurin inna suwaiba ta haye kan kausar inna suwaiba na jibgarta ita kuma tana jibgar kausar, hajja na gefe tana kuka ita sam bata ma ga dukan da afiya kema kausar ba ita dai tafi jin dukan da akema Afiya, dakyar da taimakon shigowar malam faďan ya rabu kowa na maida numfashi, kausar bayan inna taje ta boye tana kuka sosai saboda taji jiki, Malam Atiku cikin bacin rai yake ma inna faďa itama cikin fushi take mayar mishi, yace yanzu in banda ke babbar kwabo ce meye na shiga faďan yara, wai ke in an barki ga mai ýa ko, kin gama zubar da mutuncinki a idon karamar yarinya, inna cikin fushi tace faďa min mai mutunci a idon wannan shegiyar yarinyar, hajja ta fashe da kuka tace wallhy ba shegiya bace, Danbaba ni na gaji da zaman gidan nan kullum sai sun tsokani yarinyar nan ita kuma Allah bai ďiga mata hakuri a ranta ba gara muyi nesa dasu su zauna su kadai a gidan, malam Atiku yace babu inda zaku hajja, baku da inda yafi nan, zan dauki tsatstsauran mataki akan wannan alamarin, inna suwaiba tayi tsaki ta hararesu tace ka daďe baka ďau mataki ba, wannan yarinyar wata rana saita dauko muku na barin gari, ta kama hannun kausar suka wuce ciki tana masifa zuciyarta na ķuna saboda Afiya, ta rasa dalilin da yasa ta kasa samun nasara akan Afiya, zama tayi bakin gado idonta yayi jajur dan ba karamin caza mata kwakwalwa Afiya keyi ba, Can kuma dakin hajja fada sosai suke ma Afiya akan rashin hakuri, malam atiku yace ni wallhy na rasa inda yarinyar nan tayi gadon wannan halin hajja ko kadan bata da hakuri komai aka mata tace saita rama kuma rayuwa bazata taba tafiya haka ba, Allah na tuba kayi hakurin ma ya ka kare a wannan zamanin bare kuma bakayi ba, hajja tace ay ni yanzu inaga nawa ido tsakanina da Afiya dan gani sukeyi kamar goyon bayanta nakeyi ni take ďaura ma bakin jini dan kawai taga banason abinda zai bata mata rai shiyasa takeson a dinga ci min mutunci, Afiya ta fashe da kuka tace dan Allah hajja kuyi hakuri in shaa Allahu ko duka na zasuyi bazan kara tanka musu ba, hajja tayi tsaki tace ke ďin ce zaki faďi magana in yarda, malam atiku yace hajja muyi mata addua babu mamaki bazata kara ba, Afiya tace Allah abba bazan kara ba, hajja tace to Allah yasa da gaske kikeyi, duk suka ce ameen, nan suka cigaba da yi mata nasiha akan rayuwar duniya cikin dabara suke mata nuni da illar rashin hakuri, Afiya jinsu kawai takeyi dan ita bataga rashin hakurin da aketa ikirarin tana dashi ba ita dai tasan ko manzon Allah s.a.w yace in aka bata maka ka rama dai2 yadda akayi maka, to ita kuwa akan me zata yarda tanaji tana gani a taka ta, bazai yiwu ba,, har suka gama nasiharsu Afiya tana gyada kai kamar taji abinda suka ce sai gab da magriba malam atiku ya fita suma suka tashi suka je yin alwala… Tun daren ranar take zuba idon ganin jabeer shiru har kofar gida ta fito ta tsaya tana kallon kofar gidansu ko zata ga fitowarshi amma ko giftawarshi bata gani, kullum ta dawo skull sai ta tambayi hajja ko yazo, in hajja tace bai zo ba nan zata fara sababi tace hajja kawai ki fadamin ko kin fita yazo baki nan ko kuma kina baccinki bakisan yazo ba, hajja saidai tayi tsaki tayi banza da ita ta cigaba da abin da takeyi, Afiya ta damu sosai da rashin ganin jabeer ji takeyi kamar ta mutu saboda rashin ganinshi haka kawai zata zauna taki cin abinci tayi ta kuka hajja bata ko kallonta bare ta rarrasheta.. Yauma kamar kullum a cikin sati biyun da tayi bata ga jabeer ba tana zaune ta haďa kai da gwiwa tana rero kuka hajja ta ajiye mata abinci a kusa da ita ta zauna gefenta ta kira sunanta, bata dago ta kalleta ba ta cigaba da kukan da takeyi, hajja tace to shikenan tunda bazaki saurareni ba dama jabeer ne,,, ta ďago kanta da sauri tace me ya sameshi hajja, hajja tace yana nan cikin koshin lafiya baki ga yadda yayi kyau ba, dazu kina makaranta yazo yace in faďa miki yana gaisheki in ya samu lokaci nan da wata daya bayan kin gama jarabawa zai zo ku gaisa, idonta ya ciko da kwalla tace hajja wata daya? Hajja tace eh mana, ba yace kince ya tafi gaba da birnin sin ba, to ba wasa nake mishi ba afiya ta faďi haďe da fashewa da kuka, hajja tace ay ko shi da gaske ya ďauka, Afiya ta maida kanta cikin gwiwoyinta cikin kuka tace shikenan kar ma yazo din dama nasan so kawai yakeyi ya kasheni, hajja ta gimtse dariyarta tace kull kar na kara ji, duk laifinki ne meyasa in yayi miki magana bakya ji, Afiya tace to ba nace na daina ba kema shaidace yau sati biyu kenan banyi fada da kowa a gidan nan ba kuma suna tsokanata meyasa baki faďa mishi haka ba, da wani abun nayi da yana zuwa zaki fada mishi amma saboda nayi abun kirki shine kika ki fada mishi, Hajja dariya taci karfinta sosai ta mike ta fita tana dariya ita kaďai, Afiya ranta ya kara baci ta kwanta tanata kuka harda sheshsheka tana tausayin kanta dan tasan in bata ga jabeer ba nan da kwana biyu to tabbas zata iya mutuwa,,, muryar hajja taji tana kwalawa Mahmud kanin kausar kira, ya taho da gudu yana buga ball yace hajja gani, tace Gidan Alh Bara’u zan aikeka, Afiya ta mike zubur ta dakko hijab dinta ta fito tace zanje hajja, hajja ta kalleta tace da wannan kumburarren idon zaki shigar musu gida, Afiya tace eh dashi zan shiga ni dai ki fada min sakon, hajja tace to ay sai kije ki shiga din mu gani zonan mamu kaji ta miko mishi kullin magani tace kace a aikawa Asiyah nayi mata bayanin amfaninsu, ya karba yace to hajja, bin bayanshi Afiya tayi ta hađe rai tace bani, jikinshi na rawa ya mika mata hajja tace Afiya karki fita gidannan haka ko uniform baki cire ba, bata saurari hajja ba ta fita dan so kawai takeyi yau ko ta halin k’ak’a taga jabeer…. RABO AJALI 4 ◆◆ By Sulaiman Bomboy Tana fitowa tayi tafiya kadan ta fada gidansu jabeer, gaisawa tayi da Ado mai gadi, yace yar lelen jabeer kwana biyu kinyi wuyar gani, tace wallhy baba ado mun kusa fara jarabawa ne, yace au too to Allah ya bada sa’a, tace Ameen ta wuce ciki idonta kan motar jabeer tasan tabbas yana ciki, kai tsaye ta wuce dakin Ummi ta murda ta shiga hade da sallama, amsa sallamar yayi haďe da ďago kanshi suka haďa ido, kallonshi ta tsaya yi idonta cike da kwalla shi kuwa murmushi yake mata yana mai jin dadin ganinta, girgiza kanta tayi ta wuce kitchen inda taji buruntun ummi, ummi na ganinta ta fadada fara’arta tace Afee yan matana, Afiya ta tsuguna ta gaisheta, ummi ta amsa haďe da ďagota tace kin gujeni kwana biyu ko ďan girki kin daina zuwa tayani, afee ta sunne kanta tace wallhy ummi jarabawa zamu fara yanzu bana fita amma ay nazo ran Saturday bakya nan, ummi tace eh kwarai naje daura, ya hajja, afiya tace tana gida ita ta aikoni wai gashi a kaima anty Asiyah, ummi ta karbi maganin tace Allah sarki kice mata an gode sosai kinji, afiya ta gyaďa kanta sannan tace bari in tayaki wanke wanken, ummi tace aiko nagode kamar kinsan na gaji, ga dayyaba har yanzu bata dawo ba, Afee ta fara wanke2 tace ummi Amirah fa, ummi ta wanke hannunta tace tana can kaduna gidan Asiyah har yanzu bata dawo ba, Afeeyah tace Allah ya dawo da ita lafiya, ummi tace Ameen yar albarka ta fita ta tarar da jabeer zaune yana latsa waya tace au ashe baka fita ba, yace walhy ummi nagaji ne sosai, tace ay da gajiya ni bari in ďan kwanta kafin la’asar, yace to ummi Allah huta gajiya tace Ameen ta wuce ciki,, saida ya tabbatar ummi ta kwanta sannan ya mike ya shiga kitchen ďin, tana tsaye tana goge kwanukan da ta wanke tana mita tana girgiza kai, dariya ta bashi a zuciyarshi yace yau ya shiga uku da masifarta, karasawa kusa da ita yayi ya dauki plates din da ta goge zai jera tayi saurin rikesu tace malam ka ajiye ni ban sa ka ba, yace ay nasan baki sani ba tayaki kawai zanyi, tace to banaso ko dole ne, yayi murmushi yace dole ne mana in ban tayaki aiki ba wa zan taya, tayi tsaki tace wacce ka samu a cikin sati biyu nidai ka fita kawai, da nasan ma zan sameka a gida da ban shigo ba, yayi dariya haďe da rike kafadunta yace makaryaciya dan ki ganni ne ma kika yarda aka aiko ki, tace God forbid, in ganka inyi maka me, yace kiji daďi mana in kuma bakiji dadin ganina ba kalli cikin idona ki faďa min, ta ďago a tsiwace zatayi masifa suka haďa ido tayi saurin sauke kanta saboda wani abu da ta gani a cikin kwayar idonshi, yayi murmushi yace nasan kinyi missing ďina, cikin muryar shagwaba tace ni banyi missn dinka ba, yace um um fa karki sani in tafi gurin da bazaki kara ganina ba, muryarta ta fara rawa tace me ya rage kuma tunda har ka iya yin sati biyu baka neme ni ba, ya dago kanta ya kalli idonta da hawaye ya fara zuba a cikinsu yace bake kikace in tafi ba, ta dunkule hannunta ta buga a kirjinshi da karfi tace to ba wasa nakeyi ba, shine ka daina bari in ganka baka ma damu da halin da zan shiga ba kasan ko kwana ďaya ne in ban ganka ba banajin daďi ni nasan yanzu ka daina sona tunda har ka iya yin sati biyu baka ganni ba kuma ka zauna la-fiya ta karasa fadi cikin kuka mai tsanani, kwantar da kanta yayi kan kirjinshi dake bugawa da sauri yace am so sorry Afee nah kece bakya ji in na miki magana, tace wallhy na daina kaje ma ka tambayi hajja Allah ko sun tsokaneni bana tanka musu, jabeer yace to yi shuru na yadda ki daina kuka kinji, ta gyada kanta tace promise me bazaka kara yin bacci baka ganni ba, yace I promise baby in dai da rai da lafiya bazan kara ba kinji, tayi murmushi tace Allah ya kara maka tsawon rai da kuma lafiya in dinga ganinka har karshen rayuwata, ya ja kumatunta yana murmushi yace Ameen my queen, tayi dariyar jindadi suka cigaba da kife kwanukan suna hira har suka gama, a parlor suka zauna yake tambayarta karatun jarabawa, tace tanayi sosai saidai maths ke dan bata wahala, yace baki da matsala zamu dinga yi kullum kafin ku fara exams tashi ki rakani gidansu Affan, ta turo baki tace nidai bazan shiga ba, ya harareta yace yau sai kinzo munje kin gaisheshi rabonki da shiga gidan tun kafin ya fara ciwo saboda haka yau sai kin shiga, ta marairaice tace ni fa ba ruwana in wadannan masu kama da iyamuran sukayi min wllhy ramawa zanyi saidai kace bani da hakuri, ya murďe bakinta har saida tayi kara yace suwaye masu kama da inyamurai, tace oho ni nasan sunansu ne, yayi dariya yace bazaki taba canzawa ba afee sai dai addu’a, tace wallhy zan canza amma fa baza a dakeni a hanani kuka ba, yace to naji tashi muje bazamu daďe ba, tace too ta mike suka fita suka shiga gidan Alhj Basheer,, Yana zaune as usual a gurin kifaye yayi kasake yana kallonsu kamar me nazarin wani abu, jabeer ya dafashi ya juyo a firgice ganin jabeer yasa shi washe hakori sosai yana kaďa kanshi cikin murna, jabeer yace Affan abokin jabeer kuma abokin kifi, Affan yayi dariya cikin maganar dolaye yace jiya baka zo ba inata kallon can kofar mota har dare baka zo ba, jabeer yace kayi hakuri na danyi wata tafiya ne, Afiya dake tsaye fuskarta dauke da tausayin halin da affan ke ciki tace ina wuni, ya ďago kanshi dake rawa yana washe hakori yana kallonta baya ko kiftawa, duk maganar da jabeer ke mishi bai kalleshi ba idonshi na kan Afeeya kanshi yaki tsayawa guri daya, jabeer ya kalli afeeya da ta rabe tana jin tsoron kallon da Affan ke mata yayi murmushi yace affan baka gane Afeeyah ba, affan ya girgiza kanshi ya runtse idonshi kamar yana son tuno wani abu can ya bude idonshi yace na ganeta amma na manta a wani cartoon na taba ganinta, jabeer ya kwashe da dariya haka shima affan suka dinga dariya tare saida jabeer yayi shuru sannan affan ma yayi, jabeer ya kalli afeeya da ta cika tayi fam ya maza ya mike yace Affan ka jamin bala’i, affan ya mike shima ya matso kusa da afiya sosai kamar zai shige jikinta yasa hannu ya shafi fuskarta wani irin laushi yaji haďe da sanyi mai fisgar zuciya ya maza ya cire hannunshi yana tsalle yace bari inje in fada ma mummy yau na taba fuskar cartoon, jabeer ya janyoshi yace karka kara ce mata cartoon, Affan ya bata fuska yace to mecece in ba cartoon ba kalli fa idonta kato irin nasu, kuma ka taba fuskarta kaji, jabeer yace idonka ne ya ga cartoon wannan Afeeya ta ce, ka tuna ta, Afeeya mai kyuiya mai kukan banza ya faďi yana mata kallon tsokana,,, affan ya kara rufe idonshi ya bude yace mai kuka irin na mage, Afiya tayi tsaki cikin fushi ta fara tafiya, affan yace jabeer kace ma cartoon ta dawo dama bani da barbie din wasa, jabeer yabi bayan afeeya yana cema affan jeka kace ma mummy ta siyo maka wannan barbie din tawa ce, Affan ya bata rai yace sai na fadama daddy in ya dawo ince kaki bani barbie, jabeer bai kulashi ba shidai hakuri kawai yake bawa afeeya, suna kaiwa gate zasu fita shima affan yasa kafa zai bisu yaji wani irin tsawa mai firgitarwa sannan gabanshi yaga kamar namun daji suna so su biyoshi, a sittin ya ruga ciki yana ihu yana kiran sunan mummy, jabeer sam bai lura da yanayinshi ba ya ďauka shirmenshi ne dan baya taba wuce kofar mai gadi yauma yayi mamakin da ya biyosu har gate saboda barbie,, Har cikin gida ya rakata yana rarrashinta da kyar ta sauka da alwashin ta gama shiga gidan Alhj basheer har ta koma ga Allah dama sam jininta bai haďu da flowers din kofar gidan ba ma bare a kai ga mutanen cikinshi gara ma daddy da shi affan din suna gaisawa in jabeer ya kaita gidan, ta saki ajiyar zuciya tace yaya jabeer haka Yaya affan ya dawo rabona da ganinshi tun ina js3, Amma wai wane irin ciwo ne wannan, hajja dake gefensu tace au ke yau kin shiga kin ganshi,, ay a unguwar nan babu wanda ake bari yaje dubashi ko meye dalili oho, jabeer yace hmm babu wani dalili hajja kawai dai matar gidan ce bata yarda a ganshi ni ma dan ta rasa yadda zatayi dani ne shiyasa ta barni,, ga daddy ba mazauni ba dan sai yafi wata bayanan, hajja tace to Allah dai—- sai bakinta ya sar’ke kamar a datseshi da gum… wannan itace babbar jarabawar da Allah ya daurawa AFFAN ta hanyar kishiyar uwa babu wani mahaluki a doron kasa da zai iya yi mishi addu’ar samun sauki, jabeer shi ne kadai yake iya ganinshi har yayi yunkurin sanyashi a hanya amma saboda karfin iko da lokacin da Allah ya ara ma mummy, daga affan ya fara jin maganar jabeer kamar kiftawar walkiya sai ya mance abinda yace ya bijire mishi, duk yadda taso rabasu ta kasa saboda amintar su mai karfi ce wacce zaiyi wuya kasamu labarinta a kasar hausa, Bari in baku takaitaccen tarihin gidaje ukun… ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 5. A unguwar “zoo road” dake cikin garin “kano” ta dabo tumbin giwa nan zan ďan tsakuro muku tarihin gidajen makota ukun, Alhaji Basheer Balarabe dan asalin k’asar Cameroon ne, sana’ar Gwal ita ta shigo dashi kasar nigeria tun yana saro kaďan2 yana siyarwa har Allah ya sanya wa abin albarka ya koma sarinsu da yawa yana shigowa dasu yana siyarwa, a duk cikar kasuwar gwal dake cikin garin kano babu wani wanda yakai Alhj Basheer kawo ingantattun gwalagwalan da babu mixed a cikinsu, wannan dalilin ne yasa duk wanda ya tashi siyan gwal to fa a gurinshi zai siya dan shagunanshi sun fi karfin goma a cikin kasuwar, Alhj Basheer ya auri matarshi ta farko kuma yar uwarshi Zeenatu, auran zumunci akayi musu wanda ganin girma da kuma karamcin rik’on da iyayen zeenatu sukayi mishi yasa ya yarda da auren amma badan yanaso ba, shekararsu uku da aure suna zaman lafiya saboda irin biyayyar da take mishi, a cikin wannan shekarun ne ya dakko ta suka dawo Nigeria da zama kwata2 sai dai suje cameroon hutu, a shekararsu ta biyar da aure ne hankalinsu yayi matukar tashi saboda rashin haihuwa, babu ma kamar alhj basheer da yake ganin madarar kuďi babu maciyansu sai dai yan uwa da makota, ya kosa matuka yaga yana da ya’ya barin ma ďa namiji dan wani lokaci har mafarkin gashi nan an haifa mishi ďa kuma namiji yakeyi, a wannan yan lokutan ne ya fara tunanin k’aro aure duk da a lokacin ba mazauni bane saboda bai fi yayi sati a nigeria ba sauran kwanakin duk a kasar waje yake yinsu yana turo kaya, Wata ranar asabar ya baro airport cikin tsananin jin yunwar da ta bashi mamaki, nan ya tsinci kanshi da tsayawa a wani restaurant dake Jabi dan bazai iya matsawa ko’ina ba tare da yaci abinci ba, cikin karairaya wata farar ingarmar budurwa ta matso kusa dashi tace alhj me kake bukata, cikin ruďewar ganin jar fata gata a cike gaba da baya ko’ina sai rawa yakeyi a jikinta yace anytn special yanmata dan yunwa nakeji sosai, ta ďan tsuguno kadan tace an gama ranka ya dade, tayi gaba jikinta na girgiza alhj basheer ya bita da ido baki sake yana kallonta har ta bace ma ganinshi, ajiyar zuciya mai karfi yayi sannan ya gyara zamanshi dan ba karamin tafiya da imanin shi tayi ba, cikin yan dak’ik’u ta dawo dauke da plate din fried rice da pepper chicken sai peprsoup din kayan ciki a gefe da drinks, alhj basheer da bai cika cin abincin restaurant ba sai gashi ya tsinci kanshi da cin abincin nan sosai, takardar bill ta kawo mishi yabi kirjinta da ya cika kamar zai faso cikin rigarta da kallo yace yanmata duk wadannan kudin ni zan biya, tayi walll da ido tace alhj yayi kaďan ko, yayi wata kasaitacciyar dariya yasa hannu a aljihu ya ciro rafar dari biyar yace ya daiyi yawa ni kinga abinda zan iya biya nan, tayi murmushi tasa hannu ta karba haďe tsugunawa, tace to an gode yallabai, tayi gaba ya bita da kallo yana lasar baki kamar tsohon maye, tashi yayi bayan ya gama goge bakinshi da tissue yana sakace ya yafito wani yaron da yaji an kirashi da John, da sauri yaron yazo ya tsuguna yace alhj any problm, alhj basheer ya ďagoshi yace no young man ina bukatar taimakon ka ne,, john cikin mamaki yace taimakon me alhj, alhj basheer ya jashi waje yace wannan yarinyar da take kawo abinci nake son sanin sunanta, john yayi dariya yace OYIZA kake nufi, alhj basheer yace ban sani ba wata fara kakkaura, yace yes itace alhj sunanta “Safiya” Oyiza ake ce mata ita y’ar mai restaurant din nan ce, bata cika zuwa nan ba sai in tazo daga lagos kuma I think gobe ma zata koma saboda tafi 1wk anan gurin, ya fara waige2 ya ďan rage murya cikin gulma yace amma fa alhj bat— maganarshi ta katse sakamakon kiranshi da yaji madam dinshi nayi, da sauri yace alhj bari in tafi sai anjima ya ruga ciki da gudu, alhj basheer a zuciyarshi yace ko bata dame ya ke so ya fada mishi oho? ya ďaga kafadarshi kawai ya dawo ciki dan yayi magana da mahaifiyar oyiza, Guri na musamman maman oyiza ta bawa alhj basheer ya zauna tana yashe hakori cikin murna dan taga gurin ďana tarko, cikin girmamawa suka gaisa, saida shuru ya đan ratsa na kusan 2mins sannan alhj basheer ya fara magana yace madam naga yarinya a gurinki ne kuma inaso, wallhy da aure nake sonta ba yaudararku zanyi ba, ni in kin amince ma a cikin sati biyu a gama komai na maganar aure, maman oyiza tayi ajiyar zuciya cikin gurbatacciyar hausarta tana girgiza kai tace anya kuwa gaskiya bazan iya ba bahaushe oyiza ba, kaiii bazan iya ba alhj hausawa basu cika rik’e mata ba, yayi murmushi yace wasu dai madam ai ba duka aka taru aka zama daya ba, tace ummm haka ne amma gaskiya— alhj basheer ya katseta yace madam na barki kije kiyi tunani, zan dawo nan da 2days sai inji abin da kika yanke ya ajiye mata wasu kudin a gabanta sannan ya tashi ya tafi…. ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 6⃣ By sulaiman bomboy Jujjuya kuďin maman oyiza takeyi cikin fargaba dan ita a tunaninta harka kawai zaiyi da ďiyarta su tatsi kudi su bar banza, sai kuma gashi da aure yazo musu, ita kuwa sam bazata iya aurawa ďiyarta bahaushe ba tafi son kabilarta kuma dan garinsu wato OKENE, mikewa tayi ta shiga wani ďan lungu da oyiza ke yawan zama kullum in tazo abuja, waya takeyi tana dariya cikin murnar da uwarta ta kasa gane daga inda murnar ta samo asali, zama tayi kusa da ita tana mata magana, oyiza tayi saurin katse wayar da takeyi ta kalli mamanta, maman oyiza ta dafa ta tace sofy mun shiga cikin matsala, oyiza ta haďe rai tace matsalar me mum, maman oyiza ta share gumin da ya tsatstsafo mata ta labarta ma oyiza duk yadda sukayi da alhj basheer, cikin damuwa tace ni bansan me yasa kika fito har kika kai mishi abinci ba, ke da ko ruwa bakya kai ma customers in kina gurin nan, oyiza tayi dariyar farin ciki a zuciyarta tace thank uu “Chummy lord” ta kalli mamanta tace mum wannan shine matsala? ay wannan is a blessn to us, kinsan irin dukiyar da yake dashi ne, kuma kinsan abun dadin bai taba haihuwa ba, maman oyiza ta saki baki tace a ina kika san bai taba haihuwa ba, gaban oyiza ya fadi amma ta dake tace john ne ya fada min, mamanta tace koma dai menene ni bana son auren bahaushe, oyiza ta dafa mamanta tace mum karki fara wannan maganar ma saboda bazai yiwu ba, kawai in yazo kice mishi eh mun shirya yazo ayi maganar aure, maman oyiza cikin bacin rai tace kina hauka ne, oyiza cikin fushi tace yess am mad in dai akan kuďi ne, kuma duk wanda ya nemi shiga tsakanina da samun kuďi ko waye wil fc d consequences,.. Maman oyiza ta mike tace to zanga yadda za’ayi ki aureshi tunda ke baki da hankali kina zuwa 1yr ya koroki in dai bahaushe ne ki ma cire a ranki dan I swear bazan bari ya shigo ko gate din restaurant dinnan ba bare yazo jin wani feedbk ta wuce tana masifa, Idon oyiza yayi jawur nan da nan fuskarta ma ta rikiďa ta zama jawur gunin ban tsoro, ta mike kamar walkiya ta wuce motarta taja tayi gida, wani jan akwati ta bude ta dakko wani farin kyalle da wata jar baby kamar sassakar laka, wani kirari tayi mai karfi da ya girgiza gidan da take ciki, cikin second uku wata mace ta bayyana a gabanta cikin jajayen kaya, “fitsarin tsoro na saki ganin halittar wannan matar jikina take ya fara rawa idona ya ciko da kwalla a zuciyata nace duk “Badiyya” ce ta sani wannan bin diddigin gashi na kawo kaina inda zan halaka” dakewa nayi na fara karanto adduoin neman tsari, nan na samu kwarin gwiwar kai kunnena da idona gurin abun da sukeyi, oyiza na hango tayi ma matar da naji ta kira da “Chummy lord” sujjada (wa’iyazubillah) chummy tasa ma oyiza wani nannaďaďďen farin yadi a kanta tace “u are safe wit me by ur side”, oyiza ta ďago kanta zuciyarta a dake tace I found him my lord, amma mum naso ta kawo min matsala, chummy tayi dariya mai karfi tace ur mum ko kuma gvn mum, kin manta u sacrifice her sannan kika samu alhj basheer yasan inda kike, cikin faduwar gaba oyiza tayi kasa da kanta tace I love my mum my lord, chummy tace I knws dat amma in har kinason jin dadi dole ki katse numfashin mahaifiyarki, kuma bari in fada miki kina shiga gidanshi zaki samu ciki so u will be d apple of d house saboda u bring air to d family, , mum dinki ta fara tsufa so let her go ke kuma ki fara rayuwarki mai daďi, haka tayita convincn dinta har ta gamsu ta fitar da uwarta a ranta tayi alkawarin yau da dare zata bada uwarta saboda komai ya tafi mata daidai, sun kusa awa suna tattaunawa kafin Chummy ta bace, oyiza ta mayar da komai na tsafinta ta fito ta shiga kitchen dan tayi ma innocent mum dinta girki, tsayawa tayi a kitchen ta kasa komai tana tunano rayuwar da tayi da mahaifiyarta da irin wahalar da mahaifiyarta tasha akanta da karatunta, tayi tsaki a zuciyarta tace kuďi yafi min komai ciki harda ke mum, am so srry mum u have to go, ina son sunana ya shiga jerin mata masu arzikin duniya, girki ta farayi duk da jikinta a mace yake amma ta dake saboda zuciyarta ta daďe da kangarewa da shan jinin bil adama, Oyiza ta shiga cikin kungiyar asiri ne tun shekararta ta farko a jamiar lagos, wata kawarta esther Babajo ita tasata lokacin tana shan wahalar rashin kuďi da abinci saboda mahaifiyarta bata da kuđi, sannan kuma sun shiga ne dan su dinga samun first class result a set dinsu, haka kuwa yake faruwa dasu dan su biyun nan saida ya zamana babu wanda yake iya bugesu, kuma kuďi ma babu macen da zata nuna musu shanawa a cikin skull, duk irin gulmarsu da akeyi babu wanda ko wacce ta isa tazo gabansu tayi saboda tsabar tsoronsu da ake ji, jini kuwa su kansu basu san adadin na mutanen da suka sha ba, oyiza ta hadu da alhj basheer ne a airport lokacin sun dawo daga Italy ita da esther, tunda ta daura idonta akanshi da suka sakko daga jirgi taji sonshi mai tsanani ya kamata, tun a airport suke bin bayan motar da ta daukeshi har zuwa hotel din da zai kwana kafin safiya ya wuce kano, Saida suka bari ya shiga ciki sannan suka samu drivern da ya daukoshi suka tambayeshi sunanshi, da kyar da kuma kuďi da suka bashi ya sanar dasu sunanshi da kuma garin da yake, godiya sukayi mishi sannan suka wuce, tun daga ranar Chummy ta fara mata aiki akanshi, nan ta gano irin kudin da yake dashi da kuma wanda zaiyi nan gaba, ta kuma gano matsalar da yake ciki na rashin haihuwa , jin yunwarshi da tsayuwa a restaurant dinsu 4d first tym duk aikinsu ne.. dariya oyiza tayi bayan ta gama tunano wadannan abubuwan sannan ta sauke abincin da ta daura ta kwashe ta haďa juice ta jere su akan dining ta zauna zaman jiran mamanta dan suyi hirar karshe…. Allahu akbar,,, tabbas mun tsinci kanmu a zamanin da kuďi suka fi wadanda suka kawo mu duniya daraja, kuďi sunfi ďan da ka tsuguna ka haifa saboda a cikin 100% 85% zasu iya bada komai nasu dan su samu kuďi dattin duniya,,, tabbas a wannan zamanin da muke ciki masu karancin imani da tawakkali zasu iya aikata komai saboda kudi, Ya Allah ka tsarkake mana zuciyarmu da ta yan uwa musulmi baki ďaya, Allah ka azurta mu da baye bayenka kayi mana rowar talaucin da zai kaimu ya baro mu,, ameen thumma ameen…. [7:00am 11/11/2016] ◆◆ RABO AJALI ◆◆7 By Sulaiman Bomboy Daren ranar bayan sun gama hirah da mamanta ta nuna mata ta hakura da maganar alhj basheer, mum ta yi murna sosai dajin hakan daga bakin oyiza, sai gurin sha ďaya taga mum na hamma ta dafata tace mum bacci kike ji, mum tace eh bacci sosai nakeji bari inje in kwanta, oyiza ta mike tace bari in kara gyara miki ďaki saboda kiji dadin bacci da kyau, mum tayi murmushin jin dadin ganin yadda yarta ke tarairayarta, dakinta oyiza ta wuce ta yaye shimfiďar zanin gadon tasanya mata wani fari kall a kasa sannan ta ďaura nata akai, idonta yayi ja lokacin da ta dauko wata kwalbar farin magani zata yayyafa a gadon, sai da ta ďan zubar da hawaye sannan ta yayyafa maganin ta fita taje ta taso mum da ta fara bacci, har ďaki ta rakata ta rufo kofar ta koma ďakinta tayi tagumi tana jiran dare ya raba ta tafi gurin meeting, ,, 2:45am Tsugune suke gaban “CHUMMY LORD” cikin jajayen kaya su kusan goma sha biyar maza da mata masu neman arziki da mulki, jini ne a kwarya wani bakin mutum ya ďauko ya mika ma wacce take gaba ta sha ta mika ma sauran duk suka sha sannan suka ajiye kwaryar, wani irin kirari haďe da ihu “chummy” tayi akan wani farin kyalle sai ga wasu yara yanmata basu wuce shekara 14 ba sun bayyana a gabanta cikin night gown, yara ne farare kyawawa masu kama da juna da ganinsu yan biyu ne, a firgice yaran suka fara waige2 suna kankame junansu, chummy tayi dariya sosai tace Alhaji Sambo aikinka yayi kyau lallai ka tabbatar kana son cin wannan kujerar, da sauri yaran suka fara kallon mutanen gurin ko zasu ga wanda aka kira da sunan mahaifinsu, jikinsu ya kara rawa lokacin da idonsu ya sauka akan babansu mai kaunarsu dare da rana wanda a wannan daren kafin su kwanta bacci saida yayi yawo dasu cikin garin abuja da kewayenta ya kashe musu makudan kudi na ban mamaki, cikin rawar murya suka ce PA–PA, alhj sambo ya sunkuyar da kanshi kasa, daya daga cikinsu tayi karfin halin zuwa gabanshi ta dafashi dan gani takeyi kamar mafarki takeyi, jin da gaske shi ďinne yasa ta rusa ihu ta kalli yar uwarta tace “Fanne” ba mafarki nakeyi ba wallhy papa ne, meyasa zaka mana haka, yanzu ashe neman duniya zai iya saka ka bayar da ya’yanka na cikinka, papa sanda zaka bada damu bakayi tunanin bazaka kara ganin mu ba, cikin fushi dayar tace “Fanna” meye a ciki dan ya bada mu an kashe, kika san iya adadin mutanen da ya kashe saboda neman duniyarshi, kukan me kikeyi? Saboda bazaki kara shakar iskar duniya ba kome? Inda zamu tafi nan zai zo yau ko gobe ko jibi in kwananshi ya kare shima, gara ma su kashemu da zama karkashin zalunci da cin kudin haram da na kawunan mutane, wani mugun mari aka dauketa dashi ta waiga ta kalli bakin mutumin zuciyarta ta kara zafi tace ba mari nake bukata ba kashemu zakayi mu huta, “chummy” tayi dariyar kusan minti uku sannan tace ai dama kun mutu ruhinku ne anan, in naso zan iya barin ruhinku yayita yawo shi kadai a duniya gangar jikinku kuma tana rami, Fanna tace ki so din, fanne tayi saurin cewa dan Allah dan annabi ku maida mu gurin mammi ta waiga ta kalli mahaifinta tace papa kaji tsoron Allah, Oyiza cikin Fushi tace chummy lord yaran nan na bata mana lokaci gashi har asuba ta gabato ga kuma mum can daure gara ayi mata abinda za’ayi in wuce gida, Fanne ta waigo ta kalleta a hankali tace mum? U mean mum dinki kika bayar saboda— wannan karan chummy ce da kanta ta kai mata duka a baki, chummy tace bazan kashe yaranka yanzu ba alhj sambo dey wl be under my control, zan watsasu duniya saboda naga za’a dama dasu, fanne tace karya kikeyi jininmu ne yafi karfin ki,,, chummy tayi murmushi tana girgiza kai,, Alhj sambo cikin tsoro yace my lord ina tsoron kar suyi min illa, chummy tace babu kai babu su saboda zaku binne gangar jikinsu a grave so ka kwantar da hankalinka, yayi ajiyar zuciya yana kallon hararar da fanne take musu shi da oyiza,,, dafa kansu chummy tayi da wata sanda mai kyalli nan da nan suka bace,, Mum din oyiza kuwa kuka ta dingayi ganin ďiyarta ce ta bada ita, gaba daya magana ma kasa fita tayi a bakinta sai girgiza kai kawai takeyi tana tunano rayuwar da tayi da yarta, cikin minti goma aka gama da maman oyiza suka gama shaye shayensu sannan kowa ya bace, ,, Kuka oyiza takeyi a bakin gadon da mum ke kwance tana ihu makotan da ta aika mai gadinsu ya faďa musu suna kanta suna bata hakuri, ta kira can kauyensu ta fada musu suma suka dinga ihu suka shirya suka kamo hanyar abuja, Guraren karfe biyu akayi mata sutura da kyar dan yan uwanta sunce saidai su kaita can okene a binneta ita kuma oyiza ta kafe saidai a binneta anan saboda tsoron kar asirinta ya tonu dan tasan kakarta na ganinta zata san abin da ya kasheta dan itama mayyar kanta ce, saida malamai sukayi ma yanuwanta nasiha sannan suka yarda akayi mata sutura aka kaita gidanta na gaskiya… Washe gari ta kira john a waya tace yaje ya buďe shago in alhj basheer yazo ya kawoshi gidansu, haka kuwa akayi yaje ya bude shago amma har dare babu alhj basheer, washe gari ma haka, oyiza hankalinta in yayi dubu ya tashi tana ta kai kawo saboda rashin zuwan alhj basheer gashi har an kusa sati daya, a daren ranar ta bayyana gaban chummy da matsalolinta, chummy ta gama incantation dinta tana girgiza kai tace yana karkashin kulawar matarshi, ta nuna mata wata kwarya, bakar mace ta gani a ciki sanye da hijab tsaye gefen gadon mijinta dake bacci tana sallar dare in ta idar sai tayi adduoi ta tofeshi dashi sannan ta mike ta kara tada kabbara, chummy tace kin gani da idonki ko? Oyiza ta haďe rai tace na gani amma ay ni babu ruwana da wannan, mum na bayar saboda haka so kisan duk yadda zakiyi, chummy tayi dariya tace dadina dake wutar ciki, trust me Oyee cikin satin nan za’a daura miki aure da alhj basheer, cikin farin ciki oyiza tace yanzu naji magana….. ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 8⃣ By SULAIMAN BOMBOY Alhaji basheer tsugune yana gyara canvas din kafarshi cikin shigar blue nd white track suit, mikewa yayi bayan ya gama ya kalli matarshi zeenatu dake gyaran gadon da ya tashi yace to ni na fita training, tace to a dawo lafiya yallabai, yace Allah yasa sannan yasa kai ya fita, Zagaye ya dinga yi yana jogging cikin farin ciki saboda yadda sanyin safiyya ke kaďashi, yayi zagaye na tara yana yi yana hutawa, a zagaye na goma ne ya hango wani shima jogging din yakeyi dai2 gurin wata katuwar kwata kafarshi ta gurďe ya tafi zai faďa alhj basheer yayi saurin rikoshi yana fadin subhanallah sannu, mutumin ya ďago yana gyara kafarshi yace yauwa nagode sosai gaskiya ka taimake ni, alhj basheer yayi murmushi yace mu gode ma Allah, mutumin ya mika ma alhj basheer hannu yace sunana Bara’u ina nan zoo road, “BB close” opp gidan alhj Basheer Balarabe, Alhj basheer yayi dariya yace ni kuma sunana Basheer Balarabe (BB) nima ina zaune a zoo rd BB close cikin gidan Alhj Basheer balarabe, Alhj Bara’u yayi dariya sosai yace ikon Allah alhj basheer, kaga yadda Allah ke abunshi ko, . alhj basheer yayi dariya yace kai gaskiya bamu fitar da hakkin makobtaka in ba haka ba ga gida ga gida ace bamu san juna ba,, Alhj bara’u yace ko 1week banyi da tarewa ba kuma nasa ayi min magana da duk makota na kai kaďai ne Allah baiyi zamu hadu ba saboda ance min baka gari, alhj basheer yace kwarai kuwa ban daďe da dawowa ba, to ya unguwar tamu da fatan dai baka samun matsala, Alhj bara’u yace walhy babu matsala unguwar cike take da mutanen kwarai naji dadin kasancewata cikin ku, Alhj basheer yayi murmushi suka fara tafiya yace to ya iyalin fa, Alhj bara’u yace tukunna dai har ansa rana jiranta nakeyi ta karasa skull zuwa nan da 3monts sai ayi in shaa Allah, Alhj basheer yace Allah ya nuna mana kai kadai ne a cikin gidan kenan, alhj bara’u yace eh ni kadai ne amma weekends a daura nakeyi saboda rashin iyali, alhj basheer yace hakan yayi Allah ya taimaka yace ameen har suka karaso gida suna hira cikin kankanin lokaci suka saba da juna, a dai2 kofar gida sukayi sallama kowa ya shiga gida, kanshi tsaye yake tafiya cikin gidanshi yana amsa gaisuwar masu musu hidima, yazo gab da shiga parlo yaji wata muguwar faďuwar gaba, juyawa kanshi ya fara yi sosai ya dafeshi ya karasa parlon dakyar ya zauna kan kujera, zeenatu na can kitchen bata san halin da mijinta yake ciki ba, runtse idonshi yayi siffar Oyiza ta dinga mishi yawo a cikin kwakwalwar kanshi, buďe idonshi yayi da sauri da ya tuno da oyiza gaba daya yaji wani abu ya tokare mishi kahon zuciyarshi, ga wutar son ganinta da ta ruru a zuciyarshi kamar wacce aka iza da petur, mikewa yayi da sauri ya shiga bayi yayi wanka sharp2 ya fito ya shirya da gaggawa ya feshe jikinshi da turare ya debi kudi a sv dinshi na gida masu yawan gaske sannan ya wuce kitchen ya sami zeenatu, Cikin rashin fahimta tace tafiya weekend kaiko ina zaka, yace abuja zeena alheri ne yake kirana, tayi murmushi tace to Allah ya kawo mana alkhairin tare, yace ameen yar matata sai na dawo, tace to Allah ya tsare ya kuma kiyaye hanya, yace ameen ya fita da sauri, biyoshi tayi da gudu tace na manta ban fada maka ba, dan Allah zan shiga gidan Malam atiku gurin Ma’u tayi min kitso, yace to adawo lafiya tayi miki mai kyau fa, tace karka ji komai in dai kitson ma’u ne, yayi murmushi ya fita ya tafi… Da kyar ya gane restaurant din, yana isa ya fito cikin farin ciki,, tsayawa yayi turus saboda ganin gurin da yayi a rufe, jingina jikin motarshi yayi ya rasa me ke mishi daďi yanzu wa zai fara tambaya inda take anan gurin, ya kusa 30mins kafin ya shiga motarshi da niyyar tafiya, kamar daga sama ya hango john yana bude gurin, fitowa yayi da sauri kamar wanda akayi ma albishir da gidan aljanna, karasawa yayi yana kiran yaron, john ya juyo rai a bace saboda yadda yaji ana kiranshi ganin alhj basheer yasa john jindadi ya fito da gudu ya tsuguna a gabanshi ya gaishe shi, alhj basheer ya amsa suka shiga ciki, ya kalli john yace ina madam dinku, john ya raunana fuska yace madam is no more alhj tun ranar da kazo washe gari ta mutu, alhj basheer ya girgiza kanshi cikin tausayin oyiza yace Allah ya jikanta to ina yarta oyiza, john yace tana gida dama tace idan kazo in kaika can gida, alhj basheer yaji dadi sosai a ranshi dan a tunaninshi kafin mahaifiyarta ta rasu tayi mata bayanin komai, tashi yayi suka fito shi da john suka shiga mota suka wuce gidansu oyiza… Bayan ya gama yi mata gaisuwa yana rarrashinta saboda kukan munafurcin da take yi ita a dole tayi rashin uwa, tausayinta sosai ne ya ratsashi ya tambayeta ko mahaifiyarta tayi mata bayaninshi, tayi kasa da murya tace eh a daren ranar ta fada min komai kuma tace in ka dawo zata yarda ka aureni, ta fashe da kuka tace ashe bazata ga auren ba, alhj basheer zuciyarshi ta kara narkewa yace kin yarda to zaki aureni, tayi kasa da kanta tace ko banaso zan yarda tunda shine last will din mahaifiyata, alhj basheer yace haka ne naji dadi sosai da kuka amince dani, yanzu ina son cikin satin nan a gama magnar komai muyi aure in tafi dake, wani daďi ya ratsata tace to ba matsala bari in turo maka kanin babana kuyi magana, mikewa tayi ta shiga ciki ta turo mishi kanin babanta da wan mamanta, Kudin da alhj basheer ya wankesu dashi da kuma nuna yanason ya auri oyiza saboda yana tausayinta shi kadai yasa suka yarda da auren suka sa rana ya biya sadaki da komai, sannan ya tafi cikin farin ciki, A daren ranar ya fita da oyiza yawo ya siyo mata duk wani abu da mace zata bukata na aure,, sun daďe tare har suka saba sosai kafin su rabu, Tana shiga gida ta dinga tsalle tana murna nan ta shirya ta wuce gurin chummy yin godiya…. ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 9.. BY SULEIMAN BOMBOY Cikin satin aka ďaura auren alhj basheer da Safiya oyiza a okene, shiri na musamman chummy tayi ma oyiza ta haďata da special kayan tsafi a cewarta su zasu taimaketa ta zauna lafiya saboda wannan matar tashi mai yawan addu’a, Washe garin daurin auren ne ya dauki matarshi da kawayenta biyu suka kamo hanyar kano, tunaninshi ďaya shine yadda zai fara tinkarar zeenatu da maganar ya auri oyiza saboda sam duk wainar da ake toyawa bata sani ba, ita dai taga ana ta aikin gyaran part din gefenta sama da kasa amma sam bata kawo aure yayi a ranta ba, sai gurin bakwai suka shigo garin kano, kallon garin oyiza da esther keyi har suka kawo kofar dankareran gidan alhj basheer dake zoo road, a kofar gidan alhj bara’u ya hango su tsaye shi da malam atiku suna hira, ganin motarshi yasa suka mike suka karaso gurinshi da saurinsu, ya leko ta cikin glass cikin fara’a suka gaisa, yace ga amarya fa ku gaisa, alhj bara’u yayi dariya yace wace amaryar kuma, alhj basheer yace amaryata da aka ďaura min aure da ita jiya, malam atiku yace shine ko labari ranka ya daďe to Allah ya sanya alkhairi sannu amarya, oyiza ta gyara gyalenta tace yauwa, alhj bara’u ma yayi mishi addu’a suka ja suka tsaya shi kuma ya danna kai cikin gida kirjinshi na duka sosai, parking yayi suka fito duka su ukun suna mika gasu ďirka2, sannu alhj basheer yace musu sannan ya fara tafiya suna binshi a baya, yana buďe kofar main parlon yayi arba da zeenatu cikin kyakykyawar shigar material dinkin stone work fatar nan tata sai kyalli takeyi ga wani kamshi da sanyin dadi ko’ina a cikin parlon, da sauri ta karaso tana mishi sannu da zuwa,, gabanta ya faďi sosai da ta hango su oyiza amma sai ta kara fadada fara’arta tana musu sannu da zuwa, karasawa sukayi cikin parlon suna yabawa da kyau da tsarin parlon ga kuma kula da yake samu ta musamman, zeenatu ta nuna musu guri suka zauna ta wuce kitchen cike da tambayoyi a zuciyarta, kayan shaye2 ta kawo musu da snacks tanata yake, ta kalli alhj basheer da ya dafe kanshi tace yallabai gajiyar ne, tashi muje ciki kayi wanka, oyiza cikin kishi ta watso ma zeenatu harara, alhj basheer yace zauna zeena akwai maganar da nakeso muyi dake, ta nemi guri kusa dashi ta zauna, a hankali ya fara magana yace sai kuma kika ganni da baki, tayi murmushi tace eh,, yace dafatan zaki fahimceni zeenah, kinsan komai nufi ne na Allah kuma matar mutum duk inda take sai ya aureta, ya nuna oyiza yace wannan matata ce jiya aka ďaura min aure da ita bawai dan inci mutuncinki ko kuma dan bana sonki ba, “a’a” wannan auren ki ďaukeshi kaddararre ne daga Allah kuma babu mamaki safiyya na tafe da alkhairai masu yawa cikin gidan nan, zeenatu da tayi mutuwar zaune tayi maza ta saita kanta ta kirkiri murmushi tace kaii barka Allah ya sanya alkhairi nayi maka murnar samun karuwa, ay aure cigaba ne yallabai Allah ubangiji ya bayyana alkhairan dake cikin wannan auren kuma alkhairan ya wanzu a tsakaninmu, yace ameen yar albarka zeenatu nagode sosai da kika fahimceni, tace ba komai yallabai bana jayayya da abin da Allah ya kaddara Allah ya bamu zaman lafiya, yace ameen, nan yayi introducn zeenah a gurin oyiza da irin muhimmacin da take dashi a gurinshi, oyiza ranta ya baci da irin praisn zeenah da yakeyi a gabanta da kawayenta, bayan ya gama maganganun da zaiyi yace ma oyiza su tashi ya nuna mata part dinta, suka mike kamar samudawa suka rataya jakunkunansu suka wuce, zeenah da kiris ya rage ta fashi da kuka ta danne kishinta ta shiga kitchen ta hado musu abinci ta kai musu dakinsu ta fito tayi nata dakin ta rufeshi da key ta faďa gado tanata rusa kuka, Can dakin oyiza kuwa bin ko’ina sukeyi ita da kawayenta suna tsalle suna murna ganin irin dukiyar da alhj basheer ya zuba a ciki, zama sukayi a kan gado esther tace oyee baby sai kinyi da gaske da wannan matar dan da ganinta ta iya munafurci, evelyn tace green snake kenan, gata very pretty, gaskiya akan matar nan na kara yarda black is beauty kuma suna kama da bash, oyiza tayi tsaki tace trust mee mana ai matar nan sai mai aikina ta fita daraja bari dai in haihu, kunsan bata haihuwa kuma na riga na gano abinda alhj yafi so a rayuwarshi kenan haihuwa, ta shafa cikinta tace baby boy zan haifa maka alhj a lokacin ne zan nuna karfin ikona a gidanka,, duk suka kwashe da dariya evelyn tace shegiya a ina kika san baby boy zaki haifa, oyiza tace bansani ba amma dat’s wat I want kuma zan samu kinsan ni duk abinda nake so sai na samu, suka kara kwashewa da dariya suka cigaba da hira har dare ya raba sannan sukayi bacci oyiza batai maganar sallar magrib da isha ba, wa ma yasani ko tayi na safe da rana ohooo…… RABO AJALI ◆◆10 BY SULEIMAN BOMBOY Kwanan su Esther biyu a kano suna yawon bude ido tare da alhj basheer, , ba kananan kuďi ya kashe musu ba a yan kwanakin da sukayi har suka tafi, ita kuwa zeenatu bata ko bi ta kansu tsakaninta dasu gaisuwa sai kuma in ta gama girki ta kai musu, a ranar da suka tafi da daddare ya tarasu a parlor ya kara musu nasiha haďe da janyo hankalinsu akan su zauna lafiya da juna dan shi ba mazauni bane, sun daďe zaune a parlon har zeenatu ta gaji da irin hirar karuwancin da oyiza ke mishi ta tashi tayi musu sai da safe ta wuce ďaki, kamar jiran zeenatu oyiza takeyi ta matso sosai ta shige jikin alhj basheer ta soma rikirkitashi da abubuwan karuwan mata wadanda suka daďe suna damawa a duniya, cikin rashin kuzari ya kashe komai na parlon suka wuce side dinshi.. Bacci ne ya kaurace a idon zeenatu sakamakon tunawa da tayi yau mijinta babu makawa zai kasance da wata mace ba ita ba, tashi tayi tana kuka ta shiga bayi ta dauro alwala ta hau yin sallah tana rokon Allah ya cire mata duk wata damuwar da tayi mata kawanya a cikin zuciyarta, ba ita ta samu rintsawa ba saida tayi sallar asuba sannan wani nauyayyen bacci yayi gaba da ita… Karfe 9 ta tashi zuciyarta wasai ta ma manta akwai wata bil adama a cikin gidan, bayi ta shiga tayi wanka tayi alwalar walha ta fito tayi sallah ta shirya cikin orange Nouvo riga da skirt, kitchen ta nufa ta hada musu break ta jere kan dinning ta zauna ta karya sannan ta koma parlor ta zauna tana kallo,, sai gurin 11 suka fito cikin kananan kaya dukkansu, zeenatu ta kau da kanta da sauri tace ina kwana, ya zauna kusa da ita yace lafiya lau uwargidana an tashi lafiya, tayi murmushi tace lfy lau, ta kalli oyiza da ta zauna tana gyara gashin kanta tace amarya kin tashi lfy, oyiza tace lfy lau, zeenatu tace ga break can kan dinning, alhj basheer ya mike yace kamar kinsan yunwa nakeji ya kalli oyiza dake yatsina fuska yace zo muje mu karya, oyiza ta mike tana kaďa jiki ta isa dinning ta zauna suka karya, zeenatu ďaki ta koma saboda yadda oyiza ke ta ciyar da mijinta a gabanta duk da yana ďan kakkaucewa alamar yana jin kunyar zeenatun shiyasa ta basu guri dan su sakata su wala.. Tana idar da sallar azahar ta nufi kitchen dan yin girkin lunch, oyiza na zaune a parlor ta bararraje tana kallo tana shan fruits tana dariya, sannu zeenatu tace mata oyiza tace yauwa sannu ta mayar da idonta kan TV tana gunguni a zuciyarta dan ita bata son shishshigi, kitchen ta wuce ta fara haďa musu abinci taji sallama, amsawa tayi haďe da fitowa dan ta gane masu sallamar, tace sannunku da zuwa hajja, Ta nuna musu guri suka zauna, Ma’u da Suwaiba suka kalli oyiza da ko kallonsu batayi ba suka ce ina wuni, ta kallesu a wulakance dan taga alamun talauci a tare dasu tace lfy, Ma’u ta kauda kanta da sauri tana mamaki a cikin ranta, zeenatu tace hajja ya gida, hajja tace lafy lau yar nan, ina mai gidan mun shigo yi mishi Allah sanya alkhairi ne, zeenatu tace Allah sarki tunda suka fita da alhj bara’u bai shigo ba, ga amaryar nan ay, hajja ta jinjina kai tace Allah sarki Allah dai ya baku zaman lafiya, duk suka amsa da ameen banda oyiza da surutunsu ya soma cika mata kunne dan tana kallon series din “No greater love ne”, hira sukeyi yayin da suwaiba ke sako oyiza cikin hirar dan tana shigowa tasa ma ranta tayi kawar da zasu dinga kuntatawa Ma’u da zeenatu, cikin kosawa oyiza ta saki tsaki mai karfi tace wallhy kun cika min kunne, da zaki jasu kuje side dinki kuyi ta surutunku da yafi miki, zeenatu tayi murmushi tace kiyi hakuri amarya hajja ku tashi muje ciki, hajja da ma’u suka mike, hajja ta kalli suwaiba da bata da niyyar tashi tace ke suwai baza ki tashi ba, suwaiba ta maida kanta kan TV tace film din ne ya dau dadi hajja, kuje ku fito sai mu tafi, hajja tace ikon Allah, nasan in za’a shakeki suwaiba baki san me suke fadi ba, suwaiba tace yo hajja amma dai idona yana gani kuma zan iya gane komai ko, hajja zatayi magana ma’u tace dan Allah hajja ki barta muje, suka wuce cikin mamakin suwaiba, , suna shiga suwaiba ta matso kusa da oyiza tace amarya sannu, oyiza ta harareta tace yauwa, ta fara waige2, tace shawara ce zan baki akan wannan munafukar kishiyar taki, in har zaki daukeni yar uwa kuma kawa to wallhy gidannan sai ya zama naki ke kadai, oyiza tayi mata kallon rainin wayau tace ke kuma asuwa, suwaiba ta kara dakewa tace ni kishiyar kawarta ce, munafukai ne sosai, komai nasu a kasa2 suke yinshi dan ace sunada hakuri shiyasa har yanzu Allah bai basu haihuwa ba dukkansu, oyiza ta dan fara gamsuwa da suwaiba tace kishiyarki ma bata haihu ba, suwaiba tayi murmushi tace WABI takeyi, ranar da ta haifa ranar suke mutuwa yanxu haka tayi biyar kenan, tsabar mugun halinsu yasa Allah bai basu ba, gashi sun asirce mazajenmu kema sai kinyi da gaske, oyiza ta jinjina kanta zatayi magana hajja ta fito tana cewa to sai anjima zeenatu Allah ya baku zaman lafiya, suwaiba ta mike a hankali tace ma oyiza zan shigo zuwa anjima kinji, ma’u tayi ma oyiza sallama suka wuce zeenatu ta rakasu har gate sannan ta koma kitchen dan karasa girkin da ta ďaura…. [8:38PM, 16/03/2016] .: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣1⃣ By Aysha Ya’u Kurah Tun daga ranar suwaiba ta samu gurin zuwa su zauna suyita hira suna shewa suna kulle kullensu dan ta kuntatawa zeenatu, anan suwaiba ke yini In ba ranar girkinta bane, ko kallon zeenatu ta daina yi, saboda ita a ganinta tayi kawa wacce zata ci arziki da ita kamar yadda ma’u ke ci da zeenatu, (bata san bomb ta samu a madadin kawa ba).. Watansu uku da aure oyiza bata fara nuna komai na halin tsafinta ba, sai dai abinda ke bawa alhj basheer mamaki game da ita shine rashin sallarta, ko ya matsa mata tayi sallah to fa zata san yadda tayi ta zille dan baza tayi ba, gurin zeenatu kuwa mugun kyankyamin cin abincin oyiza takeyi saboda sam bata yarda da musuluncinta ba, ko sun haďu a dinning ana cin abinci sai tace ita yanxu abinci mai nauyi bata mata cikinta yakeyi,, a cikin wannan lokacin ne oyiza ta fara laulayi mai zafin gaske, komai bata iya ci, haka ta tsani kamshin gidan gaba ďaya, tunda alhj basheer yasan ciki ne makale jikin oyiza shikenan duk wani kula da soyayya ta duniya ya ďauka ya daura mata, babu dama zeenatu tayi abu in oyiza tace bata son kamshin shi to fa shikenan zai hauta da faďa sosai kamar tababbe, suwaiba ce ke shigowa ta kula da ita suyita yada habaici dan zeenatu taji haushi, duk da zeenatu na jin haushin abin amma sai ta danne ta dinga tambayar oyiza ko akwai abin da takeso, ko kallonta oyiza batayi bare ta bata amsa, abubuwa suka hadu sukayi ma zeenatu yawa, gashi sam mijinta ya juya akalarshi gurin kula da oyiza a cewarshi, gurin Ma’u da amaryar da Alhj bara’u yayi kadai zeenatu ke samun sauki, Kayan baby babu wanda alhj basheer bai siyo ba a nan nigeria da waje, kuma duk kayan maza ya siya dan a scaninng an tabbatar mishi namiji ne, itama chummy ta tabbatar mata namiji zata haifa, gaba daya oyiza ta gama wasa wukarta dan ta gama hada plan din yadda zata mallake gidan da duk wasu kadarori na alhj basheer, Cikin oyiza ya kusa wata tara alhj basheer ya ďauketa suka tafi india acewarshi zasu fi samun kula ita da babynshi, tafiyarsu ita tasa zeenatu tasamu sauki take bacci da adduointa cikin kwanciyar hankali, da rana su ma’u da Abida amaryar Alhj bara’u su shigo su ďebe mata kewa da bata shawarwari duk da Abida itama ba isashshen lafiya gareta ba saboda cikin dake makale jikinta na wata hudu, A daren ranar talata ta idar da sallar tana shirin kwanciya taji ringing din waya, daukar wayar tayi taga alhj basheer ta dauka cikin mamaki dan rabonshi da ya kirata har ta manta, sallama ta mishi ya amsa murya babu walwala tace ya mai jiki, yace da sauki ta sauka lafiya, zeenatu ta washe baki tace Allah ya raya ya kuma bata lafiya, me muka samu, kukan da oyiza ke yi ya hana shi bata amsa, kuka takeyi sosai tana fadin ya za’ayi ace ya’ mace ta haifa, tsawa ya daka mata yace to ubanwa kike tunanin ya canza miki, ko wannan din ke kika bawa kanki, ki rufe min baki kar ranki ya baci, zeenatu ta kashe wayar da sauri ta hau gado ta dukunkune (nidai bansan me ke ranta ba a wannan lokacin, farin ciki ne ko kuma tausayin oyiza,, masu kishiya su bamu amsa plss..).. Satinsu biyu a india suka dawo gida cikin koshin lafiya,, tun acan ya raďa mata sunan mahaifiyar oyiza wato Salamatu (ummu Salma) tunda suka dawo makota ke shigowa yi mata barka, suwaiba sai tausarta takeyi akan gara ita tana haihuwa ba juya bace, wannan kalaman na suwaiba suna matukar sosa ran zeenatu su ke sata kuka a kullum dare da rana tana rokon Allah akan ya bata farin cikin rayuwa itama, dan haihuwa farin cikin rayuwa ne, in ka haihu ka wuce bakin cikin duniya da lahira, ya Allah ka azurta wadanda basu haihu ba da ya’ya masu albarka cikin gaggawarka bata shaidan ba, wadanda suke dashi kuma Allah ka shiryar mana kuma ka tayamu raino ameen thumma ameen….. Mrs tijjani shattima…. [8:57PM, 16/03/2016] .: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣2⃣ By Aysha Ya’u Kurah Shekarar ummu salma uku, in ka ganta sak uwarta gata katuwa kamar renon agric, tana matukar samun kulawa gurin mahaifinta dan ba kananan kudi yake kashe mata ba, a wadannan shekarun banda karfin imani da salatin annabi da tuni zuciyar zeenatu ta buga saboda ko kallo kwakwkwara tayi ma ummu salma to fah zata fashe da kuka ta dinga nunata, shi kuwa alhaji basheer babu bincike babu komai zai hauta masifa wani lokaci harda gorin haihuwa, zeenatu sam ta kasa gane kan mijinta saboda kullum alamuranshi kara tabarbarewa sukeyi sam babu sauki a tare dashi game da ita dan ko hanyar dakinta baya bi, ta ma manta rabon da su kebe tare a matsayin mata da miji, Oyiza kuwa yanzu burinta ta samu ciki amma kafin ta samu sai ta shirya tsaff saboda wannan karan bazata taba yin sakacin haihuwar ya mace ba, sai kace ita zata bawa kanta haihuwar,, ( kaii Rashin ilimin addini shine babbar cuta a rayuwar dan adam) A cikin kwanakin kullum dare suna gurin meeting duk dan saboda ta samu haihuwar ďa namiji, chummy ce ta kalleta bayan ta gama duk abinda zatayi na tsafi, tace oyee zaki haifi ďa namiji amma sai kin bamu jinin yaro karami namiji kar ya wuce 2yrs, oyiza ta dafe kanta tana tunanin inda zata samu ďa namiji, chummy tace ki kokarta oyee wannan bazai miki wahala ba in kikayi la’akari da yanzu iyaye na sakin yan 1 nd half year a titi da sunan wasa,, sweet kadai zaki bawa yaro shikenan,,, kije ki kawo zuwa jibi sai muyi aiki mu gama cikin satin nan.. Munafurci dodo ne tabbas mai shi ya kan ci,, Oyiza ce zaune a tsakar gida tana kallon salma na wasa cikin motarta da a kiyasi zata kai 350k dan har petur ana zuba mata ta fita yawo da ita cikin unguwa, suwaiba ce ta shigo rike da Abulbait tana ma ummu wasa, zama tayi a kasa kusa da kafar oyiza ta fara mata kirari, nan da nan oyiza ta saki fuska suna hira tana bin Abulbait da kallo, oyiza ta kalli suwaiba tace wai ni ko yanzu abul ya kai shekara uku, suwaiba tayi dariya tace wane uku, shekararshi 1 da wata takwas, oyiza ta haďiye miyau ta shafa kanshi tace naga yayi saurin girma ne, suwaiba cike da murnar an yabi ďanta tace a hakan, ay ko ni ganinshi nakeyi a motse kamar fara, oyiza tace aiko ya girma wallhy bari in bashi sweet kema akwai wata yar kyautar da zan miki, suwaiba cikin murna ta mike tana godiya ta bi bayan oyiza jiki na rawa, dubu ashirin oyiza ta bata tace ta kara jari sannan ta bare sweet ta bawa Abulbait tace shanye kar ka bawa kowa kaji, bakin suwaiba ya kasa rufuwa tanata godiya kamar wacce akayi ma kyautar aljanna, oyiza tace haba ba komai ay zaman tare ya wuce komai nima kin min abinda ya fi wannan, har gate ta raka suwaiba tana kallon Abulbait saida ya shanye tass sannan ta juya gida, Suwaiba da rawa ta shiga gida tanata ďaga kuďin sama tana nunawa ma’u dake ma Asiya yar Abida kitso, rawa takeyi tana habaici wai wata saidai bauta amma bata samun kudi, kullum aikinta renon yayan da ba nata ba daga a bata ragowar abinci sai a bata na batarwa, Ma’u ko kallonta batayi ba ta karasa ma asiya kitso tayi mata wanka ta bata abinci ta goyata kafin mamanta ta dawo daga gurin aiki,,, Tun bayan isha’i Abulbait ke kakarin amai kamar zai amayar da yayan hanjinshi, jike jike suwaiba ke tayi mishi tana bashi amma ina amai yaki tsayawa, kudin da oyiza ta bata ta kalla a zuciyarta tace nasan yanzu in nace zan kaishi asibiti zan kashe fin dubu biyu, ta maxa ta mayar dasu tace inaa a gida zaka zauna bari in jiķa maka tazargade dan da gani aman hakori ne, tashi tayi tana bincika tazargade bata gani ba, ta duba ko ina na dakin amma bata ganshi ba kuma tasan tana dashi ko dazu ta ganshi, mikewa tayi ta fita da gudu ta shiga gurin hajja dan bata rabo dashi, hajja ta dubo ta mika mata tace Allah ya bashi lafiya, tace ameen ta fita da gudu, tana shiga ďaki ta tarar da gawarshi bakinshi duk ya baci da jini, wani irin ihu ta saki tana jijjigashi tana kiran sunanshi, da gudu hajja da ma’u suka shigo cikin dakin, ganin Abulbait ya daga musu hankali hajja ta daukeshi tana dubashi ko da sauran numfashi, girgiza kanta tayi tace saidai kiyi hakuri suwaiba Allah ya karbi abinshi, ta kara sa ihu tana kuka tana birgima kamar tababbiya, dakyar aka lallasheta tayi shuru akayi mishi wanka aka suturceshi malam atiku ya daukeshi ya kaishi dakinshi yayi kwanan keso acan… Aiki sosai chummy takeyi ma oyiza akan ta samu cikin ďa namiji, tace mata ta nesanci alhj basheer har tsawon kwana uku, a ranar na hudun ne zata bata magani sai tasa ya kusance ta, haka kuwa akayi oyiza ta kauracewa shimfidar alhj basheer gashi mabukaci gashi kuma ta hanashi kusantar zeenatu, abin na damunshi amma haka ya daure dan kar ya bata mata rai.. Suna zaune a kofar gidanshi shi da alhj bara’u suna hirar rayuwa, alhj bara’u ya tuno da wani tsumi a motarshi ya shiga ya dakko ya mikawa alhj basheer daya, alhj basheer yace na menene wannan, alhj bara’u yayi dariya yace goggo ta aikomin shi daga daura maganin basir ne, alhj basheer ya fara sha yace lallai wannan irin bauri haka da basu sa zuma ba dakyar zai shawu, sai gurin sha ďaya suka rabu kowa ya shiga gidanshi, a parlor ya tarar da oyiza cikin wata matsiyaciyar shiga mai tada sha’awa, karasowa yayi kusa da ita ya zauna, matsawa tayi sosai tace meye haka kuma, idonshi yayi ja yace ki taimakeni safiyya, , tayi tsaki ta mike tace in taimakeka akan me, nifa banason jaraba na fada maka kayi min hakuri na tsawon 3dys jibi ne fa , ni banason gajen hakuri walhy, ta wuce ciki ya bita da sauri tayi maza tasa keyy ta datse dakin,, ya koma ya zauna cikin tashin hankali, mararshi yaji tana murďa mishi sosai ya rasa yadda zaiyi sai juyi yakeyi, kamar an mintsileshi ya mike rike da mararshi ya wuce dakin zeenatu, tana zaune tana addua tana kai kukanta gurin Allah ya murda kofar ya shigo, waigowa tayi ta kalleshi ta mike da sauri saboda yadda taga idonshi yayi ja, karasawa tayi kusa dashi cikin damuwa ta rikeshi tace lafy me ya sameka, kankameta yayi yana fitar da wani wahalallen numfashi yace ki taimakeni zeenatu, dan Allah ki taimakeni in sauke nauyin da rataya a wuyana akanki saboda ina cikin mawuyacin hali, ta rikeshi sosai itama tace babu taimako tsakanin mata da miji, duk lokacin da kake bukatata a shirye nake in amsa kiranka, ya sauke ajiyar zuciya yace Allah ya miki albarka zeenatu, nan suka shiga faranta ran junansu, tabbas zuciyarshi tayi missing zeenatu ta ko wane bangare amma ya rasa meye ya tokare wani shashi nata har baya iya kyautata mata, Alhj basheer ya ji dadin wannan daren saboda yayi gamsuwar da ya dade baiyi ba, ga zeenatu ma haka abin yake domin ganin daren tayi kamar duk yafi sauran darurruka amma ta dangantashi da missing din mijinta da tayi, sai da yayi wanka a dakinta yana sa mata albarka sannan ya fita cikin tsananin ciwon kan da yarasa dalilinshi, a daren ranar Alhj basheer da zazzabi mai zafi ya kwana saukinta ma ya sauke wani nauyin, sai kawai yaji da na zazzabin….. Mrs tijjani shattima…. [9:13PM, 16/03/2016] .: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣3⃣ By Aysha Ya’u Kurah Satin Alhj basheer daya yana zazzabi har saida yasha allurai, zeenatu ke kula dashi dan oyiza na fushi dashi tun da ta ganshi ya fito daga dakin zeenatu a ranar, Ga kuma maganin da chummy ta bata ya wuce ka’idar amfaninshi saboda ciwon da yakeyi, a ranar da taga alamun yaji sauki ne ta fara neman hanyar da zatayi amfani da maganin har ya kusanceta, haka kuwa akayi sai da tasan duk yadda tayi da kissa da yaudara har ya kusanceta,, oyiza ta kasance cikin farin ciki a wannan dare dan gani take ma har ta haifi ďan komai ya dawo under her… 4mnts ltr Zeenatu ce zaune suna hirah da Abida dake da tsohon ciki, Abida ta kalli zeenatu tace matar nan fa ni ban gane miki ba, tun wata biyu da suka wuce kika wani canza kikayi fresh, yanzu kuma gaba daya kin cika famm sai kace me ciki, zeenatu ta shafa cikinta tace sai kace yin cikin wasan yara ne, ko sign fa ban taba ji ba, Abida tace ji ki da wata magana, akwai cikin da haka yake ba’a taba ganeshi sai in ya fito da kanshi kuma wallhy alamu sun nuna cikin nan ya dan dade a jikinki, zeenatu tayi dariya sosai tace to doctr Abida naji bayaninki, dama ana jini in ana da ciki, Abida tace nawa akayi kedai ina zuwa, gida ta shiga ta dauko ragowar “pt strip” din da tayi amfani dashi farkon cikinta sannan ta dawo ta bata kwalba tace taje tayi fitsari, zeenatu ta mike tana dariya tace Abida kenan wahala kawai zaki bawa kanki, Abida tace tunda ba ke zaki wahala ba meye na compln, ta yi dariya hade da shiga bayi tayi fitsari ta fito ta mika mata kwalbar, Wani irin ihun murna Abida tayi da taga postive, ta kalli zeenatu tace wallhy nayi tunanin hakan, wayyo dadi kasheni, zeenatu a ruďe ta shafa cikinta tace kina nufin ciki gareni, u mean akwai halitta mai rai a cikina, Abida tace sosai ma kuwa in baki yarda ki shirya gobe kafin na tafi karbar hutun haihuwa muje asibiti, zeenatu idonta ya ciko da kwallar farin ciki tace Abida bansan irin farin cikin da zanyi ba in har wannan maganar taki ta tabbata, Allah ka tabbatar da wannan maganar kasa Abida ta faďi a bakin mala’iku, Abida tace ameen zeenah, tashi zeenah tayi ta shige ďaki ta cire rigarta tana kallon kanta a mudubi, kirjinta ne kadai ya ciko amma mararta a shafe take, maida rigarta tayi tana adduar Allah ya tabbatar da wannan abun,, Washe gari tun asuba ta gama shiri dama bata rintsa ba tana ta addua, karfe takwass dai2 ta fito suka wuce dan mai gidan baya gari sunyi tafiya shi da oyiza mai laulayi wai batasan warin gidan da nigeriar gaba ďaya, (samun guri), AKTH suka nufa, basu wani sha wahala ba saboda akwai kawar Abida a asibitin, test din jini akayi mata aka tabbatar da tana da ciki, scanning ppr aka bata suka je tayi scanning inda ya nuna makalallen ciki na wata hudu, ‘”HAMDAN KASIRAN DAYYIBAN MUBARAKAN FIHI,”” abinda zeenatu ke fadi kenan hade da kuka, saida suka gama komai a asibitin Abida ta maidata gida cike da murna ta tsaya tayi wa su Ma’u albishir sannan ta wuce aiki, Hajja da ma’u a lokacin suka shigo taya ta murna, har ta ďaga waya zata kira alhj basheer ta fada mishi sai wata zuciyar ta haneta, haka gida ma so takeyi ta musu surprise, Kula sosai take bawa cikinta da ya kai wata biyar har ta fara zuwa awo alhj basheer da oyiza basu dawo ba, gidan Abida take zama suyi hirarsu lokacin ta haifi ďanta namiji mai suna JABEER, Cikin zeenatu na wata bakwai su oyiza suka dawo itama da nata cikin watanshi bakwai, fitowa tayi cikin hijab tana musu sannu da zuwa, alhj basheer ne kadai ya amsa babu yabo babu fallasa, ta kalli salma tace ummu ya hanya, salma tayi banza da ita suka wuce daki ita da mamanta, saida alhj basheer yayi wanka ya huta sannan ya fito cin abinci, zeenatu ce tayi serving dinshi tana mishi hira yana amsawa jefi2, bayan ya gama cin abincin ne ta fara mishi magana cikin hikima, tace ranka ya dade kudi nakeso, ya yatsuna fuska yace me zakiyi da kudi, ta sunkuyar da kanta kasa tace siyayya nakeso inyi ma kyautar da Allah ya bani, cikin rashin fahimta yace ban gane ba, ta daga hijab din jikinta ta dauko hannunshi ta ďaura kan cikinta tace Allah ya azurtani da ciki har na tsawon wata bakwai, “karaf a kunnen oyiza da ta fito cin abinci,” fuskar alhj basheer ta kasa boye farin cikin da yake ciki a wannan lokacin, janyota yayi ya zaunar da ita kan jikinshi sam bai kula da oyiza ba, ya kalleta yana shafa cikin da ya dan taso yace da gaske zeenah, ta gyada mishi kai, yayi murmushin jindadi ji yakeyi kamar wannan ce haihuwar da zaiyi ta fari, yace Allah ya fito min da abinda ke cikin nan kuma yasa namiji— ta maza ta toshe mishi baki tace namiji da mace duk Allah ke hallitarsu, muyi fatan samun masu albarka shine kawai yallabai, yaji wani nutsuwa ta ratsashi yace hakane Allah ya bamu masu albarka, “mtswwwwwww” sukaji an ja tsaki mai karfi suka waiga suka ga oyiza tayi gaba tana huci kamar zakanya, kau da kanshi yayi ya cigaba da kallon cikin zeenatu yace gobe ta shirya suje siyayya da asibiti a kara duba lafiyarta, sun dade suna hira cikin jin dadi ya ma manta da wata oyiza a rayuwarshi… Oyiza kuwa tana shiga ďaki ta maida salma ďakinta, ta hau kan buzun tsafinta sai gata ta bayyana gaban “chummy” idonta jawur take fada ma chummy halin da take ciki, chummy tayi iya yinta da duk wasu siddabarun da zatayi tace oyee wannan cikin bazai zube ba, cikin jikinta na tare da kariyar adduoi sosai sai dai ki bari in ta haifeshi sai kisan abun yi, cikin tashin hankali tace “my lord” to idan ta haifi namiji fa, chummy tace sai kinso ya rayu in ya fito duniya, oyiza hankalinta ya ďan kwanta tayi sallama da chummy ta bace ta nufi gida…. Ciwo takeji sosai amma hakan bai hanata ci gaba da aikinta da tasbihi a bakinta ba, wani irin Murďawa mararta tayi ta tsuguna da sauri tana faďin “YA HAYYU YA KAYYUMU BI RAHMATIKHA ASTAGITHU ASLIHLI SHA’ANI KULLAHU WALA TAKILNI ILA NAFSEE ĎARFATU AYNUN” da dai taga abun kamar gaba yakeyi ta mike tayi hanyar parlo tana maimaita adduoi a bakinta, oyiza na zaune tana cin abinci zeenatu ta shigo da kyar, tace dan Allah safiya ki taimak— ta kasa karasawa saboda wani irin nishi mai karfi da yazo mata, oyiza tayi tsaki ta juya tana adduar Allah yasa ki mutu ke da ďan cikinki, zeenatu kuka sosai takeyi ga wani ruwa dake bin kafarta, sallamar Abida taji nan taji kamar an sauke mata zafin wani bangaran, da sauri Abida ta karaso ta ajiye jabeer tace haba zeenatu ay da sai ki kirani a waya, zeenatu ta runtse bakinta ta rike hannun Abida dake kiran Ma’u a waya, da sauri ma’u ta shigo suka kamata, Abida ta kalli oyiza tace dadin abin nakuda Allah bai ďauke wa uban kowa ba, kowacce yar iska zata dandani nata in lokaci yazo, oyiza ta harzuka matuka ta mike tana bala’i suka fita sukayi banza da ita, drivrn gidan ya karaso da sauri suka wuce asibiti, Suna shiga Allah ya taimaketa batayi wata doguwar nakuda ba ta haifo ďanta namiji kyakykyawa mai kama da iyayenshi, likitoci suka shirya baby suka kimtsa mamanshi suka kwashe mata jini suka turota dakin hutu, murna a gurin su ma’u ba’a cewa komai, Abida ta kira Alhj basheer tayi mishi albishir, murnar da yayi a lokacin ba mai faďuwa bace, saida yaje gida ya shirya sannan ya fito zai tafi asibitin, oyiza ta fito rike da kugu tace ina zaka je, ya fadada fara’arshi yace hospital zeenatu ta haihu, oyiza ta kauda kanta tace Allah ya raya, yace ameen, har yayi gaba, ta tuna ta kwala mishi kira ya tsaya tace me ta haifa, yace baby boy, wani irin murdawa mararta tayi cikin ruďewa tace namiji kenan ta haifa,, yace eh mana, ya shiga mota cikin farin ciki ya wuce ya barta tsaye kamar an dasata hawaye masu zafi suna kwaranya a idonta…. Posted by Aisha Yau Kurah on 09:25 PM, 20-Mar-16 Under: RABO AJALI [10:14AM, 18/03/2016] .: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣4⃣ By Aysha Ya’u Kurah Ciki ta juya tana tafiya da kyar, ga bakin ciki ga kullewar mara, a gado ta kwanta tana kuka sosai kamar wacce akayi ma mutuwa, sai da tayi kuka ma’ishi sannan tayi shuru da tunanin itama fa cikin gareta kuma chummy ta bata assurance din namiji zata haifa, yanzu kawai abinda ya rage mata shine tasan yadda zatayi ta kashe jaririn nan tun kafin ya girma yasan kanshi, da wannan tunanin zuciyarta tayi wasai ta mike ta shiga wanka.. Kwanan zeenatu huďu da haihuwa kullum da daddare alhj basheer na makale a ďakinsu, duk wanda ya ganshi a kwanakin yasan farin ciki ne cike da zuciyarshi, haka mai jego na samun kulawa daga gurin makotanta da kanwar kakarsu Yadikko da tazo daga cameroon, a ranar da suka cika kwana shida da yamma sunyi wanka ita da baby yadikko ta debo rushi tasa garin “habbatis sauda” a ciki tana sa hannunta a hayakin in ya dau zafi saita daura a kan cibiya da marar jaririn tana karanto adduoi tana tofa mishi, juyawa oyiza tayi da sauri da ta tunkaro dakin da wasu magungunan tsafinta wanda chummy tace in har ta shafi babyn da maganin a hannunta to tabbas jininshi zai kafe ya mutu, jin hayakin tayi kamar zai tafi da ranta, ta shiga daki da sauri ta datso kofa tana haki haďe da kakarin amai, ta dade sosai a haka kafin wani irin murdaddan ciwon mara ya dawo da ita daga duniyar azabar shakar hayakin habbatis sauda, ciwon da oyiza taji ne yasata sakin ihu tana karawa kamar zararriya, babu wanda yajita dan su yadikko suna can suna hira dasu hajja da suka shigo a lokacin sunata preparation din suna washe gari, sai da ta galabaita sosai tana ihu tana faďin “ohh my lord” “chummy wr are u,” Ma’u ce ta fara jin ihun saboda zagayawa baya da tayi dan kwaso shanyar baby, da sauri ta zagayo ta faďa musu suka mike sukayi dakinta suka murďa sunata bugawa yaki buduwa saboda tasa key, kiran alhj basheer zeenatu tayi lokacin har oyiza ta suma saboda azaba, cikin yan dakiku ya baro inda yake ya dawo gida ya dauko spare key ya bude dakinta, kwance cikin jini suka sameta, da sauri suka karasa suka kamata suka sata a mota sai asibiti, dakin theater aka wuce da oyiza, cikin gaggawa likitoci suka shiga ceton ransu ita da babyn, cikin nasara suka samu fitowa da baby mai kyan gaske gata katuwa dan da sukayi wghn dinta ta kai 6.2kg, doctor yayi ma oyiza “PS” nurses suka shirya baby suka fito ma alhj basheer da ita, cikin murna ya karbeta yana kallonta yana mata addua, ita kuwa oyiza sai can cikin dare ta farfado tana ihun kuka dakyar,,,, wata nurse ce a gefenta da yadikko suka matso suka riketa suna fadin sannu, ta kwanta lamoo tana shafa cikinta dakyar tace na haihu ne, yadikko ta daga mata kai tace eh kin haihu, tayi murmushin da bata san ya fito ba saboda azabar ciwo tace ina yaron yake, yadikko ta fito da babyn cikin gadon jarirai tace gata nan, oyiza cikin rashin fahimta ta gwalo dasassun idanuwanta tace gashi nan ko gata nan, yadikko tace gata nan dai inaga bakiji da kyau bane, oyiza ta waigo a hankali ta kalli babyn ta juyar da kanta tana kuka sosai tace “why chummy” why? Meyasa zan haifi mace, kin manta alkawarin da kikayi min, meyasa zeenatu zata haifi namiji ni mace, meyasa zanyita haihuwar mata, magana oyiza takeyi cikin zaucewa tama manta da wata yadikko a kusa da ita, saida tayi kuka sosai nurse tazo tayi mata allura sannan ta samu bacci, Yadikko komawa tayi ta zauna tana kallon oyiza tana mamakin furucinta, tabbas sai sun mike tsaye akan zeenatu da ďanta saboda wannan furucin na oyiza ba karamin ďaga hankalin yadikko yayi ba, ‘”CHUMMY” kalmar da ta dinga maimaitawa kenan a ranta, wacece kuma chummy? tambayar da yadikko tayi ta ma kanta kenan ta kasa samo amsa daga karshe ta mike ta shiga tayi alwala ta fara nafilar nemawa jikokinta tsari daga sharrin makiya… Ranar suna jariri yaci suna AFFAN, anyi taron suna na gani na fada mutane sunzo sosai tayasu murna, faďin farin cikin da duka su biyun suke ciki bata lokaci ne domin bazai taba misaltuwa ba, oyiza kuwa tana can cikin bakin ciki dan tunda ta farka anyi anyi ta bawa baby nono taki, kuka kawai takeyi tana tufka da warwara, maimakon isharar da Allah ya nuna mata yasa ta saduda tasan babu wani mai yi sai shi taki ta gane, sam batayi gv up ba sai ma wani karin mugunta da zuciyarta ta naďo, babu abinda yafi daga mata hankali sai cewa da doctor yayi mahaifarta bazata kara rike kwai ba saboda ta samu gagarumar matsala, a wannan lokcin likitoci sunga bori saboda tsine musu kawai takeyi tana zaginsu, dakyar alhj basheer ya lallabata da kalamai masu kwantar da hankali,,, Kwananta hudu a asibiti aka sallameta ta dawo gida da muggan kudirai a cikin ranta, a zuciyarta tace wannan karan ita zata zama shaidaniyar kanta dan taga yanzu aikin chummy baya tafiya mata yadda ya kamata, haka ta cigaba da jinyar jikinta da kula da yarta wacce taci suna FAREEDAH, oyiza kullum idonta na kan side din zeenatu taga ko sun bar Affan shi kaďai amma bata samun wannan damar saboda yadda yadikko ke manne dashi a ko dayaushe, sai da yadikko tayi wata biyu a gidan tana kula da zeenatu, tun ana saura sati ďaya ta tafi kullum dare bata aikin da ya wuce yi ma zeenatu faďa akan ta kula da kanta da ďanta da kuma adduoi, zeenatu saidai tayi dariya dan abin na yadikko ya zame mata kamar waka tunda kullum sai anyi maimaicinshi.. Salma ta kalli mahaifiyarta tace mummy kika ce wannan nawa wannan na affan ko, oyiza tace a’a wannan ne naki, ki kula fa sosai, ta gyaďa kanta ta fita da gudu fareeda na binta a baya, Affan zaune suna bin karatun lptp din yara na “alifun ba’un” shi da jabeer lokacin shekararsu biyu da rabi shi da fareeda ita kuma salma ta kusa 6, dafashi salma tayi yayi saurin ďago kanshi, a razane ya matsa dan mugun tsoronta yake ji saboda dukkan da take mishi, zama tayi kusa dashi ta kara duba ice cream din dan ta tabbatar da wanda mummy tace na affan din ne, mika mishi tayi tana murmushi tace gashi inji mummy, farida cikin gwaranci tace “wanshan ne naci,” salma ta harareta tace wannan ne, farida ta dage akan dayan ne saboda tafi salma wayau, kuka ta fashe dashi da taga alamar salma bazata bashi wanda mummyn tace ta bashi ba, da sauri zeenatu ta fito tace lafiya me aka miki farida, salma tace ice cream mummy ta bani in kawo ma affan kuma wannan ne nashi wai ita dole sai dai in bashi Nawa, farida cikin kuka tace “wanshan ne mummy ta kaya mici sugar” kuma “cha kiji” , gaban zeenatu ya faďi sosai tace to duk bari in raba muku gardama ke salma je ki kara tambayota wanne ne na affan din, da gudu suka fita suka bar zeenatu cikin jimamin maganar farida, innalillahi kadai take fada tana kara rokon Allah ya tsare mata ďanta da a kullum sai an kawo mishi harin kisa tun yana karaminshi, shafa kansu tayi shi da jabeer tace ma jabeer tashi kuje gidan Antie Ma’u kafin umminka ta dawo kaji, ya gyada mata kai ya kama hannun affan dan yafi affan wayau, har sun fita ta tuna da kar su hadu da su salma ta bashi ice cream din yasha, binsu tayi da sauri tace ku dawo bari Gaje ta dawo daga kasuwa sai ta kaiku kunji, ta kamo hannunsu suka shigo ciki dai2 lokacin su salma suka dawo da ice cream daya suka ce gashi wannan ne nashi, zeenatu ta amsa tace to kuce ya gode sosai, salma tace mummy tace yasha a gaban mu sai mu tafi, zeenatu tace to an gama yaran kirki bari in raba musu shi da jabeer, ta mike ta shiga kitchen, Allah ya taimaketa akwai nashi na jiya a fridge, daukowa tayi ta raba musu shi da jabeer ta fito ta mika musu tace gashi maza ku sha ku tafi gidan anty ma’u wanda bai shanye ba a gida zai zauna, suka karba suka fara rige rigen sha, salma da farida suka fita da gudu tun kafin su kai ďaki suke rige rigen faďin mummy yasha, suna karasawa ta toshe bakinsu tace ku rufemin baki ku wuce ku bani guri, suka wuce ciki suka dau nasu suna sha, zama oyiza tayi cikin farin ciki dan tasan yau babu makawa aikinta yaci tunda har sun tabbatar mata yasha,, har bayan isha tana kasa kunne taji ihu, amma shuru takeji hankalinta ya fara tashi,, karfe 9 lokacin taji dawowar alhj basheer ta mike ta fito ita da yaranta, zaune ta taddashi affan na kan ruwan cikinshi suna hira suna kyalkyace dariya kamar da sa’anshi yakeyi, wani abu ne ya tokare mata wuya wanda ta kasa controlling dinshi har ya kaita ga jan razanannan tsaki, taja hannun farida dake kokarin zuwa gurin babanta tace dalla wuce kuje ďaki, an faďa muku ta taku yakeyi, ai ku muna ya’ya ne a gidan nan amma ba ya’ya ba, alhj basheer ya dago da sauri yace haba safiya, me yasa kike faďin haka, da affan da su salma duk daya ne agurina, da karfi tace biyu ne, karka kara cewa ďaya ne, ka riga ka nuna musu tun yanzu basu da wata daraja a idonka saboda sun zo a ya’ya mata, nan ta shiga masifa kamar zata tsaga gidan, bakin ciki ne dankare a zuciyarta saboda yadda in tayi abu akan affan baya kamashi, alhj basheer bai kalleta ba ya kara rungume affan da ya tsorata ya mike ya wuce ciki ya barta anan tana bala’i…… Mrs tijjani shattima…. [10:24AM, 18/03/2016] .: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣5⃣ By Aysha Ya’u Kurah Haka rayuwa ta cigaba da tafiya a gidan alhj basheer, kullum da sabon makirci da muguntar da oyiza ke fitowa dashi na tsafi da kuma na magunguna amma dayake rayuwarmu da mutuwarmu tana gurin rabbil izzati babu abinda ya faru da zeenatu da affan duk da wani lokacin in tayi tana cin nasara saboda ance tsafi gaskiyar maishi sai dai duk tsafin mutum in har ka dogara da Allah to ko ya kamaka na ďan lokaci ne zai sake ka, a yan shekarun da suka wuce oyiza ta kara karfi cikin kungiyar asiri dan yanzu haka tana cikin kungiyoyi masu karfin gaske guda hudu, zeenatu kuwa addua takeyi ba dare ba rana akan Allah ya kare su ita ďanta ya ďaurasu akan makiyansu… Affan da jabeer zaune ďakin hajja suna cin danwake, jabeer ya kalli affan yace kaii yau banga su anty salma a skool ba, affan ya juyar da kanshi yace ohoo musu wai dan daddy yace shi zai kaini zana C.E exams su su jira driver shine sukayi fushi mummynsu tace bazasu ba, Hajja dake gefe tana saka suwaitar kulu tace ca nakeyi ajinku daya da farida kenan bata rubuta jarabawar ba, jabeer yayi dariyar shakiyanci yace dondi kenan hajja, ay anyi mata repeating yanzu p4 take, Affan yace p4 din ma da ya aka bari ta kai, ni ay ban taba ganin wacce brain dinta baya ďaukar karatu irin farida ba cewar jabeer, Affan yace tabb ay wallhy gara farida a haka, dan anty salma knws nottn banda mugunta, ma’u ta ďeko dakin hajja da tsohon cikinta da kullum suke adduar Allah yasa zaunanne ne tace ashe baku wuce gida ba, na ďauka ma kun tsufa a gida, jabeer yace eh “Mama” sunan da yake kiranta dashi kenan saboda a gurinta ya girma bacci kadai ke maidashi gida”, yanzu zamu tafi muna nan muna cin ďanwaken tsohuwa, Ma’u ta juya tace ai ya kamata kuje gida ku faďa musu kun gama jarabawar sai kuma a ďan fita yawo tunda ba mata bane ku, suka rufe kwanon danwaken suka mike sukayi sallama da hajja da ma’u,, sun kusa da kofar fita kausar yar suwaiba tana rarrafe a tsakar gida tsirara ta mike ta rike wani abu tana dabo ta fetso kashi saura kaďan ya taba wandon Affan, da gudu suka fita jabeer na mishi dariya harda rike ciki yana tayashi dubawa ko ya taba wandonshi, dakyar ya karasa gida yana masifa ya wuce bayi saida yayi wanka ya canza kaya sannan ya fito ya shiga ďakin mahaifiyarshi, zaune ya sameta tana waya ya zauna kusa da ita, sai da ta gama wayar ta juyo ta kalleshi tana murmushi tace daga ina haka, yace gidan maman jabeer, tace ya jarabawar kun gama ko, yace mun gama umma sai dai ayi mana adduar samun nasara, tace addua kullum yinta akeyi Affan, saidai a ďaura, ni dai ina kara jaddada maka ka rike ibada da karatun qur’ani da tsoron Allah wadannan abubuwan in ka rikesu sun isheka duniya da lahira, yace in shaa Allah umma, Allah ya kara mana karfin imani, tace ameen, ya mike zai fita kenan Asiya ta shigo da sauri, tace ina wuni umma, zeenatu tace lfy lau dan asy, ya na ganki haka, tace ummi ce tace in zo in fada miki anty ma’u ta haihu yanzun nan tana can gidan ma, da sauri zeenatu ta mike cike da murna tace me muka samu, asiya tace nima ban sani ba, ta dauko hijab ďinta suka fita da sauri a ranta tana adduar Allah yasa zaunanne ne abin da ta haifa, tun kafin su shiga ciki kukan yarinyar ke musu kuwwa cikin kunne, kuka takeyi irin na jarirai da iya karfinta wata nurse a unguwar tana gyarata, Affan a kofar gida ya tsaya dan yana tsoron ya shiga ya kara arba da kausar dan bai sani ba ko wannan karan a jikinshi zatayi kashin, A cikin gida kuwa murna sukeyi lokacin an gama kimtsasu anyi ma mai jego allura tana kwance tana hutawa, duk makota anata shigowa tayata murna banda suwaiba da tace meye na barka a gurin gawa, mudai je zuwa nan da anjima itama zata bi layin yan uwanta su cike su bakwai, karaf wannan furucin na suwaiba ya shiga kunnen jabeer, hararta yayi ya mikama mamanshi babyn suka fita shida Asiya, a kofar gida suka hadu da affan suka wuce gidansu.. Anyi suna dai2 na masu rufin asiri, mai jego ta samu kaya da kudi masu yawan gaske haka mahaifinta ya samu kudi sosai haihuwar tazo mishi da goshi, jaririya taci sunan Hajja “Hajara” Abida tace a dinga kiranta da “AFEEYAH”, suwaiba kuwa bakin ciki kamar zai kasheta da taga har kwana bakwai jinjira na raye ga kaya da kudi da uwarta ta samu kamar za’a bude shago dasu, sam ta kasa boye bakin cikinta har saida sukayi fada da Abida ta gaggaya mata bakaken maganganun da yasata shigewa ďaki ba shiri dan Abida ba kanwar lasa bace itama… Tun daga lokacin kullum sai suwaiba ta kasa kunne ko zataji kururwar mutuwar jinjinra amma shuru takeji ga jinjira har ta wuce wata bakwai kullum cikin koshin lafiya, Afeeya ta taso cikin kulawar mahaifiyarta da kakarta hajja, yarinyar duk wanda ya ganta sai yayi sha’awarta saboda kullum a tsaftace take kan nan nata baya rabo da kitso da ribbons saboda tana da yalwar gashi, gata yar lutuya goyonta gunin ban sha’awa, saidai fa akwai azabar kuka da masifaffen kwuiya, banda mamarta da hajja babu wanda take yarda ya ďauketa a duniya sai jabeer, shima dan tana ganinshi kullum a dakinsu kuma yana fita da ita yawo, sam bata yarda da affan dan ko ya miko hannu zai ďauketa in ta soma tsala ihu bata taba yin shuru har sai taga baya gurin, wannan dalilin yasa kullum ya shiga gidan sai yasan yadda akayi yasa ta kuka ta hanyar daukanta ta karfin tsiya,, Afeeya na da shekara biyu jabeer yasa babanshi yasata a makarantar da suke zuwa lokacin suna js2, dakyar ma’u ta yarda dan gani takeyi kamar wata hidimar ta ďaura musu, tare suke zuwa makaranta in sun dawo ya wuce gidansu da ita sai can yamma yake mayar da ita gida, duk wani kuďin break da ake bawa jabeer akan afeeya yake karewa, gata sosai takesha gurin yan samarin biyu duk da har lokacin bata cika yarda da affan ba, salma da farida ba karamin tsanarta sukayi ba, in suna cikin mota ta kallesu sai su sakar mata harara, turo baki takeyi a tsiwace irin na yara itama ta rama sai tayi lamoo a jikin jabeer ta runtse idonta dan kar su daketa, haka a skul ko takata yaro yayi bai sani ba ko yafi karfinta sai ta bishi ta rama in ya daketa taje ta faďa ma jabeer, in kuma tafi karfinshi to ta samu nama dan sam bazata raga mishi ba…. Mrs tijjani shattima…. To be Continued………. Post navigation [ad_2]