FITAR RANANOVELS

RANA DAYA BOOOK 2 CHAPTER 17

RANA DAYA BOOOK 2 COMPLETE HAUSA NOVEL | BY HALIMA ABDALLAHI K/ MASHIBY HALIMA ABDALLAHI K/ MASHI

Amna tace “Ina zuwa”

Aliya ta juya ta fice.

Tsaki kawai Amna taja banda Hajiya ce babu abinda zaisa taje wani dakin wata daga cikin su,dan kawai ta nunamana cewa tafison yar’uwarsu ne kowaye Nafisa tafi Oho…..

Aliya na fita dakin Salma ta nufa ta sameta a jingine tayi jajjage.

Tace “to gasu Hajiyar Shatima can kije ki gaidasu Maman Shatima ne,Salma ta danyi rau rau da ido cike da tsoro,tace “Aunty tsoro nikeji”

“Tsoron wa.?”

Salma tace Hajiya wallahi,Aliya ta”sai kace wata mayya,ta haifa maki miji gashi nan yanata kashe maki uban kudi amma kice wai kinajin tsoron ta”.

Salma tace “ba haka bane Aunty,ta taba man fada kuma ni ina tsoron fadanta.

Aliya tayi murmushin mugunta a ranta tace yanzu ma wani fadan zan sake ja maki,ta dubi Salma tace to wuce kije ki gaisheta,” Salma tace to bari in canza kaya in cire na makarantar nan.

“Ta ya mutsa fuska jin cewa Salma zata samu canza kaya,inta cire kayan nan ai shikenan zata rage mata sauki ma har ta samu tseguntawa Hajiya irin kudin da ke kashewa Salma wadda abin ke damunta Kullum, Salma ta dauki dan mayafin jallabiyar ta tayafa tunda daga kanta babu dan kwali ta fito cikin fargaba ta nufi shashen Nafisa.

Aliya ta shiga dakin ta dama ranar itace da Shatima kuma ta shirya mashi farfesun kaza yana wuta batama gama ba,sannan tayi dafadukan cos-cos da hanta,nan ta jerowa su Hajiya a katon tire ta shigo dakin Nafisa ta samu Salma tana rabe rabe a gefe ta kasa karasawa ciki,harda tsawar ta tace “muje mana kin wani rabe gefe guda.”

Hajiya tace”wacece?” Aliya cikin sigar son tura kiyayyar Salma ga surukar tasu tace “Salma ce uwar shanshanci”.

Hajiya ta gimtse fuska harma da Amna da Maman Nafisa da suke zaune, Salma ta tsugunna a gabansu kana kallon ta kasan a firgice take,Aliya ta dire tiren a gabansu nan kamshi ya daki cikin su,ta kalli Hameeda “kawo filet da cukula mana kisa”.

Salma cikin raunin murya tace sannunku da zuwa Hajiya,Mama ne kadai ta amsa “yauwa sannu Yarinyar nan”.

Ta kalli Nafisa wacce ke zaune saman kujera tace sannu Aunty ya jikin? Itama fuskar ta a daure tace “jiki da sauki” ta yunkura zata mike Hajiya tace koma ki zauna”

Salma ta zaro ido tare da zama cikin tsananin faduwar gaba,ta tuno alwashin da Hajiya tayi sai tazo har kaduna tasa ankoreta,hawaye suka soma zubo mata…

Muryar Hajiya ne ya katseta daga tunanin da takeyi “iyayen kine sukazo daga Zaria suka saki makaranta?”. Cikin in inah Salma tace a’ah.

Aliya tace “Ina sukaga halin sata a makaranta sunaji da abinda zasuci” Salma ta kalli Aliya a tunanin ta wannan maganar ta Aliya kamar tayine domin kareta a gurin Hajiya sai kawai taji Hajiya tace

“Badai shi Shatima ne yasata ba?”

Nafisa ta tabe baki “shiyasa ta mana Hajiya makaranta me shegen tsada”

Aliya tace “tsada ai ba kadan ba ma tsadar,kusan dubu dari harda doriya”

Amna ta kalli Aliya domin jin bakon lamari ita bata shiga harkar kowa batasan ma me akeyi a gidan ba.

Hajiy tace “Eyyeh!”

Aliya tace “to ai kudin shiga makarantar nan dubu saba’in da biyar ne banda kudin motar dawowar ta da Kullum sai ya bada dari biyar ga kudin namanta da komai da yake badawa dubu daya,”Aliya takai karshen maganar tanajin dadin tasamu abinda takeso.

Hajiya ta kalli Salma cike da tsana tace hakane kudin makarantar dubu saba’in da biyar?

Salma cikin rawar jiki tace “yanzu sun cike tamanin”.

Hajiya ta mike da sauri tana fadin “lallai kam sun cike tamanin wato ke yakeyiwa aiki kenan kullum rana ta Allah dubu daya da dari biyar a wata nawa zai kama? Jama’a kuyi mani lissafi?

Da sauri Amna tace dubu arba’in da biyar kenan zai kama duk wata”

Nafisa tace “Kan uba!! Muna zaune?”

Hajiya tace “to aikoni dana haifeshi idan ya yi man haka nasan ya kai daa”

Maman Nafisa tace “to shime yakaishi wannan batan basira? Wai rokon Allah da goge”

Hajiya ta soma kiran layinshi ya daga tace “Ina gidanka Allah yasa ka kusa tashi” yace “insha Allahu nan da awa daya zan dawo” tace “saika iso” keda wayene? “Nida Mamanku ne Mustapha ne ya kawomu”.

Salma wacce sautin kukanta ya fara fitowa tace “don Allah Hajiya kuyi hakuri…..”jifar da Hajiya tayi matane da karamin filon kan kujera ya hanata karasa maganar ta.

Hajiya tacigaba da cewa “banason jin komai daga gareki Yar gidan masu asiri kawai,ai tundaga lokacin da yaron nan ya zoman tamkar zaiyi hauka akan wannan kazamiyar Yarinyar nasan aikin asirine.

Ta kalli Maman su Nafisa ki tunafa be taba kwanciya a asibiti akan wata ba sai silar wannan Yarinyar dan nace bazai aureta ba ranar ya tashi a sankare idanuwa a kakkafe mukai asibiti”

Duk matan nan suka kalli Salma cikin mamaki musamman ma Amna wadda take da matukar tsoron asiri.

Nafisa tace “wai dama ciwon nan nashi yanada nasaba da itane?”

Hajiya tace “inkinje gaba ma saiki fada daga nan abinda nayi mashi ya yi yawa kawai sai nasa ayiman tambaya wajen malamai can ne suka fadaman wai uwar tane tasa akayi masa asiri da sunan Shatima kuma an hada da naman bakar akuya da yawun bakinta da ruwan hawayenta aka bashi yaci,daf da bikin nan fa har gida sai da ya siya masu da sauri Salma ta dago tana fadin “wallahi Hajiya ba siya mana ya yi ba hayace,”Hayar…..

Hajiya ce ta sake jifarta da wayarta dake hannun ta “karya zanyi maki kenan dan ubanki?”

Aliya cikin sauri ta dauki wayar tare da fadin haba Hajiya wayarki kar tayi lahani mana.

Hameeda wacce tausayin Salma ya kamata haka kawai taji ba gaskiya bane abinda Hajiya take fada ba,dan haka ta saci wayar Nafisa tayi cikin daki ta fada bandaki domin yin abinda ya dace.

Aliya ta kalli Hajiya kiyi hakuri bari in zuba maku abinci.

Sakawa Maman ku dan ni bazanci abincin nan ba sai anyita ta kare yau din nan.

Nafisa tace”gwara ayita ta kare domin kada kowa ta yadda kiri kiri hmm”

Aliya tace “aikuwa bayin kansa bane bakiji abinda akace bane”

Amna wadda ta yadda da zancen nan dari bisa dari ta kalli Salma cikin tsana indai tana gidan nan kam nidai bazan zauna ba dan a gaskiya banason asirce asircen nan da akeyi.

Hameeda ta kira sau uku kafin ya daga tace Yaya don Allah kazo gida yanzun nan ga Salma nan an tsareta su Hajiya ne”

Gaban Shatima ya fadi ya manta da tsanar da Hajiya tayiwa Salma, yace “nagode Hameeda ganinan zuwa.”

Lokacin tashinshi beyi ba haka dole ya tashi yaje gida da gaggawa domin kashe waccen wutar wadda shedan ya rura a cikin sa ya dauki uzuri gaggawa ya fita bema san irin gudun da yakeyi ba kawai saidai ya ganshi a layinsu,yana parking lokacin Mustapha ya fito daga falon Aliya.

Shatima ya nufi gurinshi “inasu Hajiya?” Mustapha yace suna falon Nafisa.

Shatima yace “to bari inje mu gaisa” Mustapha ya biyoshi domin ya gama cin abincinshine.tun daga baranda yakejin muryoyinsu daya bayan daya.

Hajiya tana fadin”ba bakin dan akuya ba ko bakin dan jakane kukayi asiri dashi yau sai kin bar gidan nan”.

Cikin kuka Amna take fadin”yanzu zan kira Dadyna nima yazo ya daukeni dan bazaiyiwu in zauna ba,Ina tsoron asiri”.

Nafisa take fadin” jiya nan fa saida nayi mafarki da ita gaskiya bazan iya tuno meya faru a mafarkin ba amma tabbas ita na gani,ni kaina idan tana gidan nan to wallahi Mama saidai mu tafi daku yau din nan.”

Mustapha ne yafara shiga hakanne ya hana Aliya magana taso tayi magana dan ta hangoshine a tsaye.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button