HAUSA NOVELRASHIN ADALCI Complete Hausa

RASHIN ADALCI Complete Hausa

Page 1

Wata matashiyar budurwace kwance saman gado, ta fitar da ɗaya hannunta daga cikin bargon da take lullube, ta ɗauke wayarta da ke ajiye gefen filon da ta dora kanta a kai.

Tana ɗaukar wayar ta mayar da hannunta cikin bargon ta kara lullubewa har saman kanta, ta kunna datar wayar babu ɓata lokaci messages(sak’onni)su kai ta shigowa tsayawa ta yi har suka gama shigowa wani group da tafi so a dukkannin groups din dake wayarta ta shiga,sallama ta yi cikin group din wani friend(abokinta)dake kusa ya amsa mata sallamar.
Gyara kwanciyarta ta yi domin taji dad’in yin chat ɗin, “Abdul ina sauran mutanen group ɗjn suka shigane su fito muyi fira mana?”.

Dariya Abdul ya yi kafin ya ce; “kinsan mutanen gidan tsoron sanyi suke suna chan kwance har yanzu basu tashi ba”.

Murmushi Husna ta yi tace; “ai na yadda matsoratane sai sun zo kaji yadda zasu cika mana gida da surutu”.

Dariya Abdul ya yi nan suka cigaba da firarsu, sun kai wajen minti talatin kafin wani ya shigo.

“Kai waye ya faɗa maku sanyine ya boyemu?” Inji wani Mubarak da shigowarshi kenan ya samu suna maganar ya shiga shima,(shima Mubarak yana cikin members ɗin group din).

“Husna kin ga ɗaya nan ya fara leƙowa har ya fara cika mana baki koh?” Cewar Abdul

Husna ta ce; kyaleshi Abdul borin kunya ne tun yaushe muke nan muna fira ba wanda ya tashi sai yanzu”

Mubarak ya ce; “Injiwa yace yanzu nazo? tun ɗazun Ina kwance Ina kallonku”.

Husna ta turo irin sticker ɗiin nan wadda ake amfani da ita gurin nuna alamun anyi murguɗin baki.

“Ke waki ke murguɗa ma baki? Inji Mubarak.

Husna ta sake turo wata sticker ɗin irin ta gwalo kafin daga bisani tace; “da kai nake”.

“Ke yarinyar nan kin raina mutane sai na kamaki za kiyi bayani ni dai kike murguɗa ma baki koh?”

Murmushi Husna ta sa ke yi kafin tace; “naga zaka zo mana da wata bidi’a ne bayan kaje ka kwashi baccinka amma zaka fara cika mana baki yanzu”.

“Husna ke kike tsayawa ma bashi amsa Mubarak ɗinne zai iya jurewa ana magana ya yi shiru?” cewar Abdul

“To nagane kai ke sanyata yi man rashin kunya kenan zanyi maganinku gaba daya kuwa”

Dariya Abdul ya yi sannan ya ce: “gaskiya ai ta faɗa borin kunya ne kake mana bayan yanzu kazo”.

Dariya Husna ta rinƙa yi ma Mubarak tana faɗin “Malam kayi ladab saboda nan dai mun ganoka”

Mubarak ya ce; “Hmmm yarinya za kiyi bayani dalla-dalla dani kike zancen”.

Abdul ma ya rinƙa dariya ya na fadin “daɗina da kai abokina saurin shiga yanzu har ka sakarmata ta fa yi galaba akan ka kenan”

Husna cikin sauri ta turo sticker mai ɗauke da alamun zaro ido tace; “haka ka koma Abdul?”

Dariya Abdul ya turo da ita bai ce komai ba.

Mubarak ya ce; “ƙyaleni da ita aboki zan rama dani take zancen ai”.

Husna tace; “Ni zaku nunawa ban-bancin jinsi bari kakata tazo nasan zata shigar man”

“Dalla matsa gefe ai wannan kakar taki ita ma zata taddamu dama ita ke sawa kina mana rashin ji cikin group ɗin nan” inji Mubarak.

Husna turo wata sticker ɗin tayi mai alamun mutum zai kai bugu tace; “Eh Ina ruwanka kakar kace ko tawa,kuma babu wanda ya isa ya takura mana gidan nan ni da ita eheeey”.

“Haba yarinya jikinki zai gayamaki mu dai kike ma haka koh?” Inji Abdul.

Husna tace, “Eh da ku nake ni bari ma nayi tafiyata tunda kakata bata fito ba sai anjimanku”.

“Yauwa gara ma kiyi tafiyar taki ko mun huta da yen yen yen ɗinki”, Inji Mubarak.

“Ƙara gayamata abokina wannan yarinyar duk ta ishi mutanen gidan nan”, Inji Abdul.

Dariya Husna tayi tace; “wallahi kun dai faɗa ne kawai amma ai basu iya rayuwa idan babu ni cikin group ɗin nan ni ce fa farin cikin gidan”

“Ke koma gefe kada na dake ki wacece farin cikin ko dai ciwon kanmu ba” cewar Isa da zuwanshi kenan cikin group din ya datsi maganar.

“Ƙara gayamata dai Isa wannan yarinyar sai munyi maganinta cikin gidan nan” nji Abdul.

“Ha ha ha naku wasane maganina ai sai Allah ba dai ku ba, bayan ma idan babu ni kun rinƙa kiran wai ina Husna baku da natsuwa har sai na hau”, ta fad’a tana dariya saboda tasan ta jawosu kenan.

“Je kiyi ta istigifari yarinya dan wannan saɓone ki kayi waye yake ta ke” Inji Isa.

“Ban da lokacinka Malam ni dai na faɗa kuma kun sani nice farin cikin gidan nan dan haka na mayi tafiyata” Husna na faɗar haka ta rufe datar wayarta tana dariya saboda ta san ta tsokano su.

“Yarinya dole ki ruga tunda kinsan mataki zamu ɗauka amma zaki dawo ai” cewar Mubarak.

*Hussy Saniey *????
*____________________________________*

*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*RASHIN ADALCI 2021*

*NA*

*HUSSY SANIEY *

Page 2

Husna na sauka online, dariya ta kama yi saboda ta san ta kunna Isa,sai da tayi dariya mai Isar ta sannan ta mik’e ta fara da gyara d’akinta sannan ta fita tsakar gida ta fara aikin da ta san ya zamo ita ke yin shi,sai da ta gama gaba d’aya aikin sannan ta shiga wanka a gurguje kasan cewar rana ta fara yi,cikin sauri ta shiga d’akinta ta shirya domin tafiya makaranta,agogo ta kallah k’arfe goma na safiya cikin sauri ta k’arasa shiryawa,fitowa ta yi daga cikin d’akinta da jikkar da kayan karatunta suke ciki,bisa kujera ta aje jikkarta ta nufi kitchen inda ta jiyo motsin mahaifiyarta.

“Mama ba ki k’arasa bane ga shi na makara ina sauri dan ina tsoron ace ba zan samu lecture ba”,ta fad’a ta na mai kai hannu gurin bokitin da Maman ta dama masu kunu.

“Ko kin makara Husna ai laifin kine ba zamanki d’aki ki kayi ba”, Mamanta ta fad’a ta na mik’o mata filet d’in da ta zubo mata fanke.

“Mama group d’in y’an amana na shiga muka d’an gaisa “, ta fad’a ta na kai kofin kunu bakinta.

Girgiza kai Mamanta ta yi ta ce, “ba ki da magana sai ta group yanzu tunda kin gaisa dasu ai hankalinki ya kwanta koh?”

Murmushi Husna ta yi ta ce, “Mama kin san a duk duniyar WhatsApp babu group d’in da nake jin dad’in shi kuma nake so har a raina kamar shi”.

D’agowa da kai Mamanta ta yi ta ce, “in dai ana son aji dogon sharhi gurinki to a tab’a y’an group d’in y’an amana”.

Dariya Husna ta yi ta na tauna fanken bakinta sai da ta had’iyeshi kafin ta ce, “Mama group d’in ne ya yi wallahi mutanen da ke ciki suna da bala’in mutunci”.

Kallonta Mamanta ta yi yadda ta hak’ik’ance ta na yab’on mutanen da ko had’uwa dasu ba ta tab’a yi ba sai dai a chat d’in, “Husna kiyi sauri ki gama ki tafi kada ki makara saboda ke ba gajiya za kiyi ba”.

“To Mama kin san kuwa d’azun sai da na hayak’a Mubarak dashi da Abdul “, Inji Husna.

Kallonta Mamanta ta yi ta ce, “bangane mekike nufi ba?”.

Sai da Husna ta cinye fanken da ta sanya ta kora da kunu sannan ta ce, “kwantar da hankalinki Mamana ba wani abu bane kawai dai na ce masu ni ce farin cikin y’an amana ne shine su kai ta musu nasan yanzu sadda zan bud’e data sai naga chapter d’insu kin san Isa ya k’ware da musu”.

Bayyanannar ajiyar zuciya Mamanta ta sauke ta ce, “ku dai baku gajiya da shirme”.

“Ai Mama dan ma su Umar basu kusa duk su na chan basu tashi bacci ba wani abun ma sai nadawo daga makaranta akwai dirama lokacin kowa ya fito “, Inji Husna.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button