HAUSA NOVELRASHIN ADALCI Complete Hausa

RASHIN ADALCI Complete Hausa

“Bakomi Abba ai zaman tare kenan ka kyautatama wanda kake tare da shi nima nagode da yabonku a gareni sai anjima.” Bata jira amsar Chairman ba ta kashe wayarta,tsakar gida ta fito dan cigaba da aikinta

Hussy Saniey.????
*RASHIN ADALCI 2021*

*NA*

*HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*PAGE 18*

Wuta Husna ta hura ta cigaba da suyar fanke,sai da ta soya ya kai rabi sannan ta jiyo sautin Fadila na sallama,hanyar zaure ta kalla tare da amsawa.
“Wa’alaikissalam Fadilarmu!” Husna ta faɗa cikin murna.
“Allah sarki Husna sannu da aiki,dan Allah kiyi haƙuri Husna mun barki da aiki sannu….!” Maryam ta faɗa cikin sigar lallashi.
“Kai My Anty har kin sanya naji kunya…ni fa abin da yasa ki ka ga na fara saboda kin san halin Abba da zumuɗi har fa ya kirani wai an gama?”
Husna ta faɗa tare da tsame fanken da ke cikin kasko.
“Husna ke da wa ke magana?”
Mama ta faɗa lokacin da take fitowa daga cikin ɗakinta.
“Mama su Anty Maryam ne fa…!”
Husna ta faɗa ta na nuna su Fadila dake tsaye bakin kofar zaure tun ɗazun,duk maganar da su ke da Husna da ma basu shigo ba.
Da kallo Mama ta bi inda Husna ke nuna mata,su Maryam ta gani tsaye su na kallonta,ta buɗe baki ta ce.
“Ke dai Husna na ga ranar da za kiyi hankali yanzu ki iya ki ce masu su shigo amma sai hakan ta gagareki sai dai ki tsaresu da labari tun kafin su shigo cikin gidan… Maryam ku shigo mana kun biye ma shirmen Husna kun yi tsaye,in ba yi hankalin ce maku ku shigo ba ai sai ku shigo ko!!”
Mama ta ƙa ra sa faɗa ta na kallon su Maryam dake tsaye su na mata murmushi.
“Kiyi haƙuri Mama shigowa zamu yi da ma…ina wuni Mama”
Fadila ta faɗa tare da durƙusawa ta na gaida Mama.
“Lafiya lau Fadila ya Mamarku?” Mama ta faɗa.
Maryam ma durƙusawa ta yi ta ce,”Mama ina wuni ya gida ina su Auter?”
Kallonta Mama ta yi ta ce,”lafiya lau Alhamdullih su Auter sun tafi Makaranta ya Hajiyarku?”
Duƙar da kai Husna ta yi ta ce,”lafiya lau ta ke ta ce ma a gaisheku.”
“Masha Allah muna,amsawa ku shigo daga ciki mana”
Mama ta faɗa tare da komawa cikin ɗakinta saboda su samu damar sakewa.
Mama na shiga ɗakinta su Fadila suka taho har inda Husna ke sanya fanke cikin kaskon dake kan wuta, Abaya Maryam ta ɗora saman igiyar shanyar dake ɗaure a tsakar gidan.
“Kawo ki huta My Husna ai kin yi ƙoƙari har kin ku sa toyewa duka”
Maryam ta faɗa tare da ƙoƙarin amsar abin da Husna ke tsame fanken.
“Kai My Anty daga zuwanku ko hutawa ba zaku zauna ku yi ba….balle ku sha ruwa sai kawai ku kama aiki!”
Husna ta faɗa tare da riƙe abin tsamar.
“Haba Husna dan Allah ki sakar mata mu ƙarasa aikin nan ai kinyi ƙoƙari,mu ida wane kawai ya rage zamu yi saboda duk kin toya yafi rabi”
Fadila ta faɗa tare da cire abayarta inda Maryam ta ɗora ta ta nan ita ma ta ɗora.
Ganin sun dage akan sai ta bar masu ya sanya Husna ta sakar masu abin tsamar,abayoyinsu ta ƙwashe daga saman igiyar ta nufi ɗakinta dasu domin ta ajiye masu a chan nan waje kuma saboda ka da su ɗauki zafin rana.

 

*NA*

*HUSSY SANIEY*

PAGE 6

Shiru zaman ya kasance a tsakaninsu,babu wanda ke da ƙwarin guiwar yin wata fira,zaman minti goma sai ga Bus ta zo,su na shiga cikin Bus ɗin Husna ta chanza kujerar zama,da kallo su ka bi ta dashi saboda abin da bai taɓa faruwa a tsakaninsu ba,duk rintsi wuri ɗaya suke zama amma yau ga shi Husna ta raba masu wurin zama.
Husna na kallon yadda su ke bin ta da kallo, ɗauke kanta ta yi kamar ba ta san suna yi ba,a haka tafiyar ta kasance babu daɗi,kowa da abin da yake saƙawa a cikin zuciyarsa.
Ko da aka zo inda suke sauka,Bus na tsayawa Husna ce farkon fita,bayanta su Mieynart suka bi,lokacin da suka fito har ta tsaida Keke napep.
Ji ta yi an riƙe mata Abaya ta baya,juyowa ta yi suka haɗa idanuwa da Mieynart,ɗaure fuska Husna ta ƙara yi ta ce,”sakeni zan wuce!”

Murmushi Mieynart ta yi,”Husna ban taɓa ganin haka a wurinki ba saboda haka kiyi haƙuri hakan bazata ƙara faruwa ba insha Allah.”
Girgiza kai Husna ta yi ta ce,”bakomi ya wuce sai Allah ya kaimu gobe.”
Kafin Mieynart ta ce wani abu har Husna ta shige cikin keke napep ɗin,ta na shiga mai keke napep yaja suka tafi,sai da suka ɓace sannan Mieynart ta kalli Sadam ta ce,”tun da nake da Husna ba ta taɓa nunaman taji haushin abu ba irin yau,gsky bansan wannan wace irin ƙauna ba ce take ma waɗannan bayin Allah ba.”
Cikin mamaki Sadam ya ce,”ni kaina abin nan ya matuƙar ɗaure man kai,wai Husna ce ta iya nuna mana ɓacin ranta saboda mun kushe wasu!”
Mieynart ta riƙe haba ta ce,”abin da yafi ɗaure man kan kenan,fatana dai Allah ya sanya yadda take son su haka su ma suke mata irin wannan son.”
Gyara tsayuwa Sadam ya yi tare da ɗaga ma wani mai mashin hannu,duban shi ya maido ga Mieynart ya ce,”ameen dan gaskiya abin ya ban mamaki sosai.”
Tsayuwar mai mashin gabansu shi ya hana Mieynart magana, Sadam ya kalli Mieynart dake tsaye amma da gani kasan ba ta cikin yanayi mai daɗi ya ce,”Mieynart idan naje gida zamu yi waya akan wannan case ɗin kar ki damu kinji koh?”
Numfashi Mieynart ta sauke ta ce,”Sadam dagaske hankali na ya tashi saboda Husna duk yadda kake ganinta ba ta da haƙuri to wallahi ta na da kawaici ba abu kaɗan ke sanyawa ta nuna ɓacin ranta ba.”
Hawan mashin Sadam ya yi sai da ya zauna sosai sannan ya ce,”kar ki damu Mieynart zamu yi magana idan na koma gida ai dole mu tabbatar Husna ta sauko daga fushin nan saboda wallahi yau ban ji daɗin yadda muka rabu ba.”
Gyara riƙon jikka Mieynart ta yi ta ce,”nima abin da yafi ɗaga man hankali kenan amma insha Allah idan ta kama har gida zan taddata sai na bata haƙurin kaje idan mun koma mun yi waya sai anjima Allah ya kiyaye hanya.”
Littafin da ke hannun shi ya ɗora bisa cinya,ya kalli Mieynart ya ce,”ki bari idan naje gidan duk yadda ta kama sai ayi kawai kinji kin ga napep chan kije ki hau ki gaida Mama.”
Bayan wucewar Sadam babu daɗewa ta samu Keke napep,ta tafi gidansu lokacin har an kusa fara kiran sallar magrib.
**************
Husna na isa ƙofar gidansu,mai Keke napep ɗin ta sallama sannan ta shiga cikin gidansu,da sallama ta shiga,Mama na zaune ta na ɗaurin kunun Aya,kallo ɗaya Mama ta yi ma Husna ta san akwai matsala a tattare da Husnar.
Ganin irin kallon da Mama ke bin ta da shi ya sanya Husna washe baki ta ce,”Mama sannu da aiki na dawo.”
Cikin kallon tuhuma Mama ta ce,”yauwa lafiyar ki ƙlau kuwa Husna! kin ga yadda kika yi?”
Cikin ƙoƙarin ɓoye damuwarta, Husna ta yafa ma fuskarta murmushin ƙarfin hali ta ce,”lafiya lau nake Mama kawai tsabar gajiyace kawai ta maidani haka kamar marar lafiya amma lafiya lau nake babu wani abu Mama.”
Ba dan Mama ta yadda ba ta ce,”ki je ki ɗan watsa ruwa ki zo ki ci abinci nasan dai kina jin yunwa?”
Murmushi Husna ta ɗan yi duk don son ɓoye damuwarta ta ce,”zan dai watsa ruwa Mama amma ba na jin yunwa na ci abinci a makaranta Mieynart ta zo mana da shi.”
Kallonta kawai Mama ta tsaya tana yi saboda zai yi wuya Husna ta dawo daga makaranta ba ta ci abinci ba,wani lokacin har janta ake ace an manta ba’a aje mata abincin ba,ganin irin kallon da Mama ke bin ta da shi ya sanya kawai ta shige ɗaki,dan tsab Mama na iya gano abin da take ƙoƙarin ɓoyewa,kuma ko kaɗan bata san hakan ta kasance.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button