HAUSA NOVELRASHIN ADALCI Complete Hausa

RASHIN ADALCI Complete Hausa

 

Hussy Saniey.????
*RASHIN ADALCI 2021*

*NA*

*HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

 

*PAGE 7*

Shigarta ɗaki kenan wayarta ta ɗauki ƙara,fiddo wayar ta yi daga cikin jikka,fuskar wayar ta kalla ganin mai kiran yasa ta yin murmushi,ka ra wayar ta yi a kunne bayan ta ɗauka.

“Hello Assalamu Alaikum,” Husna ta faɗa cikin fara’a.

Daga ɗayan bangaren aka amsa mata,”wa’alaikissalam Hajiya yau ina kika shige sai nemanki ake ko dai ɓacewa ki kayi?”

Gefen gado Husna ta zauna cikin dariya ta ce,”da ma ai na faɗa maku ba zaku iya rayuwa idan babu ni ba saboda ni ce farin cikinku ga shi kuma yanzu kun kasa natsuwa saboda ban kusa damu.”

Daga cikin wayar aka ba ta amsa da,”kalli wannan yarinyar abin da kike faɗa,ke ce farin cikin namu ko dai baƙin ciki?yarinya duk kin bi kin damu mutane shine kike iƙirarin ke ce farin cikin mu?”

Wata dariya Husna ta fashe da ita,cikin son ta ƙular dashi ta ce,”haba Iroro ai kowa yasan ni ce farin cikin ƴan amana ga shi kun kasa nutsuwa da baku ganni ba kai kafi kowa ma kasa jurewa har sai da ka kirani.”

Daga chan bangaren wanda ta kira da Iroro ya ce,”ke kalli wannan yarinyar waye ya kasa natsuwar?”

Cikin sauri Husna ta ce,”Iroro mana shi ya kasa jurema rashina.”

“Ba ki da lafiya yarinyar nan nine ma zan gaza jurewa rashinki?” Iro ya faɗa.

Cikin dariya Husna ta ce,”ga shi nan kuwa ka gaza jurewa gaskiya ni mai sa’a ce a rayuwa tunda har kuna gaza jurema rashina a kusa daku.”

“Ji wannan yarinyar sai wata magana kike wadda bansan kanta ba idan kin gama ƴan maganganun ki zan iya kashe wayata?” Inji Iro.

“Baka da matsala Iroro tunda ka ji lafiyata hankalin ka ya kwanta nasan ka samu natsuwa zaka iya kashewa yanzu!” Husna ta faɗa cikin son ƙular da Iro.

“Ke dai kika sani da ƴan maganganun ki,” ya faɗa tare da katse kiran wayar.

Dariya Husna ta kama yi saboda ta san ta ƙular da Iro,tashi ta yi ta shiga wanka,ba ta ɗauki dogon lokaci ba ta fito,sai da ta yi alwallar sallar magrib saboda lokaci saura kaɗan ya ida,cikin sauri ta sanya doguwar rigar atampa,wayarta ta ɗauka ta buɗe data.

Saman gado ta kwanta,sai da messages suka gama shigowa sannan ta shiga group ɗin ƴan amana,kamar yadda ta zata hakan ce ta kasance ba’a yi magana sosai ba,da ma duk in dai ba ita ke online ba to zaka ga ba’a cika magana sosai ba,duba maganganun ta yi gaba ɗaya ba wasu maganganu bane sai ƴan gaishe-gaishene ga duk wanda ya ɗan leƙo cikin group ɗin.

Sallama ta yi cikin group ɗin,kamar ana jiran zuwanta sai ga mutane biyu sun fara amsawa, ɗaya daga cikinsu ne ya ce,”farin cikin ƴan amana yau ina kika shigane muka ji ki shiru.”

Murmushi ta yi kamar yana ganinta sannan ta tura ɗan emojin nan mai nuna alamar tsalle ta ce,”naje makaranta yau sai yanzu na dawo Abdul Mai kasuwa mai ku ka ajeman na Garba?”

“Allah sarki sannu kin dawo lafiya?yanzu kuwa za’a tarbeki tarba mai kyau kuwa,” Abdul Dabai ya faɗa wanda zuwanshi kenan.

Abdul mai kasuwa ya turo emojin kankana da lemo sannan ya ce,”ga kayan marmari nan ki ɗan taɓa zanje masallaci na dawo naji an fara kiran sallah.”

“Ina godiya mai kasuwa nima bari naje nayi sallar na dawo yau akwai fira dan haka kowa ya dawo online da anyi sallah,”Husna ta faɗa.

“Ki ce yau akwai fira kenan?”inji Abdul mai kasuwa.

“Sosaima dan yau naga laɓe aka yi a gidan nan
dan haka sai an yi ƙara’i,”Husna ta faɗa.

“To shi ke nan sai anjima bari na tafi,”inji Abdul mai kasuwa.

Ita ma Husna data ta kashe ta shimfiɗa abin Sallah,Abaya ta sanya ta hau kan dardumar, sallar magrib ɗin ta gabatar.

 

Hussy Saniey.????
*RASHIN ADALCI 2021*

*NA*

*HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

 

*PAGE 8*

Husna na idar da Sallah ta miƙe ta fita tsakar gidansu,babu kowa a tsakar gidan,kai tsaye kitchen ta nufa abinci ta zubo a plate, ɗakinta ta koma ta zauna gefen gado abincinta ta ɗaura kan cinyarta,wayarta ta ɗauko ta buɗe Data,saƙonni su kai ta shigowa dubawa ta cigaba da yi har sai da ta gama ba kowa amsa sannan ta shiga group ɗin ƴan amana,tun lokacin da ta sauka babu wanda ya ƙa ra magana a ciki dan maganarta ita ce ta ƙarshe a gidan.

Fita ta yi ba tare da ta yi magana ba,abincinta ta ida cinyewa taje ta maida ƙwanon a kitchen,kiran sallar isha’i ta ji an fara dan haka ta ɗaura alwalla ta shiga ɗaki,bayan ta gama sallar ta miƙe ta yi shirin bacci,wayarta ta jawo ta sake kunna Data har lokacin babu wanda ya ƙa ra magana a group ɗin.

“Assalamu Alaikum” ta yi sallama a cikin group ɗin,Info din group ta shiga nan ta ga akwai mutane online amma basu da yawa.

Ganin an ɗauki lokaci babu wanda ya yi magana ya sa ta yin murmushi,fita ta yi taje cikin contact ɗinta, lambar Chairman ɗin group ɗin ta danna ma kira.

Ringing ukku ya ɗaga,”hello Assalamu Alaikum Abba ya kike?”
“Wa’alaikissalam lafiya lau Husna yakike?”Chairman ya faɗa daga cikin wayar.
Murmushi ta yi ta ce,”lafiya qlau nake Abba idan baka wani abu dan Allah ka hau online a kaje group ɗin ƴan amana.”
“Husna lafiya dai koh?”Chairman ya faɗa daga cikin wayar.
“Lafiya lau Abba babu komai ni dai dan Allah ka hau akwai abin da ya taso na gaggawa,”Husna ta faɗa.
“To shikenan Husna gani nan zan hau,”Chairman ya faɗa cikin sauri.
“yauwa sai ka hau ina jiranka yanzu,”Husna ta faɗa tare da kashe wayarta.

Mai da akalar kiran ta yi ga wayar Ibrahim (Iro) ringin ɗaya ya ɗauka ya ce,”hello.”
Dariya ta yi ta ce,”Oh kai Iro! kamar kana jira daga kira sai ka ɗauka.”
“Waye zai zauna jiran kiran naki Malama sake magana dai,”Iro ya faɗa.
“Ni dai ba wannan ba dan Allah ka hau online yanzu ka zo group ɗin ƴan amana akwai abin gaggawa da ya taso yanzu,”Inji Husna ta faɗa.
“Lafiya mai ke faruwane kike nemana cikin gaggawa,”Inji Iro ya faɗa cikin zaƙuwa da son jin abin da ke faruwa.
“Lafiya lau kawai dai wani abune,idan dai ka zo sai ka ji duk abin da ke faruwa,”Husna ta faɗa.
“Ki gayaman mai ke faruwa yanzu aiki nake bazan samu damar hawa ba,”Inji Iro.
“Ka daure dan Allah ka hau akwai abin da ya faru,”Husna ta faɗa cikin yanayin damuwa.
“To shikenan gani nan zan hau muje group ɗin naji meke faruwa,”Inji Iro.
“Yauwa Iro muje gani nan nima,”Husna ta faɗa.

Kashe wayar Husna ta yi,haka ta rinƙa bin mutane ta na kiransu akan su hau online yanzu, sai da ta gama kiran kowa sannan ita ma ta nufi group ɗin,ta na shiga ta ga kowa ya hallara ita kawai ake zaman jira.

*Hussy Saniey*.????
*RASHIN ADALCI 2021*

*NA*

*HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button