HAUSA NOVELRASHIN ADALCI Complete Hausa

RASHIN ADALCI Complete Hausa

Ƙin ɗaga kiran ta yi har sai da ya yi mata kira ukku,a kira na huɗu ne ta ɗaga ƙin magana ta yi sai shine ya fara magana,”kin yi dai-dai wallahi har na rinƙa kiranki amma ki gaza ɗaga man kira daga ƙarshe ma sai ki ka kashe wayar saboda kin raina ni har kin gayaman!”Ibrahim ya faɗa cikin fushi.

Ita ma Husna ɗaure fuska ta yi kamar yana a gabanta ta ce,”me kake tunanin zan faɗa maka idan na ɗaga bayan sai baka haƙuri nake amma sai shareni kake yi!” ta ƙarasa faɗa kamar za ta yi kuka.

Cikin kwantar da murya Ibrahim ya ce,”amma ke abin da kika aikata kin kyauta kenan sai da na fadamaki aiki nake mai muhimmanci amma ki ka sanya na aje aikin nazo,sanin kanki ne duk group ɗin ke kaɗai ce za ki iya man irin wannan kiran na bar abin da nake yi nazo dan na saurareki,kin kyauta kenan ni abin da kika man kuma dan rashin son gaskiya na maki magana kuma kin ɗauki zuciya hakan dai-dai ne?”
“Nasan ban kyauta ba amma tunda na baka haƙuri ai ya kamata kai ma ka haƙura koh?” Husna ta faɗa cikin muryar kuka.

“Meye abin kuka kuma yanzu daga magana Husna?haba Sweet Husnata daina kinji koh!dan Allah ki taimaka ki daina kukan nan bana so!”Ibrahim ya faɗa cikin muryar lallashi.
“Zan daina Sweet Irona amma sai kai ma ka daina fushi dani,”Inji Husna ta faɗa.

“Hmmm! Yarinya wallahi kin ga wurin baccina shi ya sa ki man laifi kuma ki hanani nuna fushina zan riƙe kine ai,”Ibrahim ya faɗa cikin raha.
“Haba Sweet Irona ai nasan ka yafeman,dan haka ka ma daina faɗa kada wasu su ji su yi mana dariya,”Husna ta faɗa cikin muryar dariya.
“Hmmm! Yarinya daga baya kenan ai an riga da an jimu kuma,” Ibrahim ya faɗa.

“Na shiga ukku Sweet Irona wa ya jimu dan Allah ka ma daina faɗa ni babu wanda ya isa yaji tsakaninmu!!!” Husna ta faɗa cikin sauri.
“Ke matsalata da ke matsoraciyace shi ya sa ake cin ki da yaƙi,”Ibrahim ya faɗa yana dariya.
Ita ma dariyar ta yi sannan ta ce,”Ni da kai ai duk ɗaya muke mu matsorata ne Sweet Iro dan haka ka ma daina faɗar ni ɗaya ce matsoraciyar.”

“To shi ke nan yarinya za kiyi man bayani ne gobe zan zo idan muka tashi daga karatu,”Ibrahim ya faɗa.
“Yauwa naji daɗi Sweet Irona da ma nayi missing ɗin ka kwana biyu,”Husna ta faɗa.
“Amma shi ne baki gayaman ba?”Ibrahim ya faɗa.
“Ai bari nayi mu gama magana sai na faɗa maka,”Husna ta ba shi amsa.
“To shi ke nan sai Allah ya kaimu wayata ba kuɗi yanzu kiyi bacci mai daɗi ina sonki Sweet Husnata,”Ibrahim ya faɗa ba tare da ya ji amsar ta ba.

 

Hussy Saniey.????
*RASHIN ADALCI 2021*

*NA*

*HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

 

*PAGE 12*

Ibrahim na kashe wayar,da kallo Husna ta bi wayar ta na murmushi,har cikin zuciyarta take mamakin soyayyarta da Ibrahim,mutane da yawa na faɗin soyayya a tsakaninsu ba za ta taɓa yiwu ba,amma ita da shi suna ƙaryata mutane saboda su dai su na son junansu,ta na ganin wannan duk zancen mutane ne.

Agogo ta kalla, ƙarfe goma sha ɗaya da ƴan mintuna,ganin bata jin bacci yasa ta buɗe data,sai da saƙonni suka gama shigowa sannan ta fara mai da amsa,kan group ɗin ƴan amana ta zo,shiga ta yi nan ta tadda mutane duk sun tofa albarkacin bakinsu akan abin da ta yi ɗazun.

Saƙo aka turo mata a private ta na dubawa ta ga Chairman na group ɗin ƴan amana,sallama ya yi mata,”Aslm Husna ykk?”
“Wassalam Abba Abba ydrn,”Husna ta faɗa (kasancewar haka take kiranshi).
“Lafiya lau Alhamdullih Husna ta mu ta yan amana,”Inji Chairman.
“Mash Allah Abba Abba,”Husna ta faɗa.

“Dan Allah Husna taimako nake nema wurinki,”inji Chairman.
“Wane irin taimako kake nema Abba?”inji Husna.
“Dan Allah Husna gobe za’a je gaisuwar gidansu mai Shari’a to shine muke so dan Allah a samu abin da za’a kai masu,kuma kin ga babu kuɗi aje yanzu a asusun group,”inji Chairman.

“Eh hakane Abba yanzu ya kake ganin za’a yi kenan?”inji Husna.
“Husna idan babu takura dan Allah fanke muke so kiyi mana idan akwai kuɗi hannunki,”Inji Chairman.
“To shi ke nan Abba wurin ƙarfe nawa za’a yi?”inji Husna.

“Idan dai son samune Husna wurin ƙarfe ukku an gama komai zuwa ƙarfe huɗu kuma mun tafi,amma Husna kuɗin fulawar da man sai idan an dawo za’a ba ki,”inji Chairman.
“Ba damuwa Abba insha Allah za’a yi komai yadda ya kamata,”inji Husna.
“To ke kaɗai za kiyi ko su Maryam su zo nan gidanku su taya ki?”inji Chairman.
“Abba lafiya lau zasu iya zuwa,”inji Husna.
“To shi ke nan zan masu magana sai su zo da wuri dan ku gama akan lokaci,”inji Chairman.
“To Allah ya kaimu goben lafiya,”inji Husna.

Banƙwana su kayi sannan ta sauka,sai bayan sun gama maganar ne ta fara tunanin inda za ta samu kuɗin da za’a yi amfani da su wurin fanken, dan ita dai yanzu ba ta maganin ko Naira,tunani ta shiga yi ganin dai ba ta samu mafita ba yasa ta miƙewa domin ta je wurin Mama,ta na fitowa tsakar gida ta ga Mama ta rufe ƙofar ɗakinta.

Ɗaki ta dawo ta kwanta bisa gado,har ta kwanta ta tuna da ba ta yi alwalla ba,tashi ta yi taje ta ɗauro alwalla sannan ta rufe ƙofar ɗakinta,ruwa ta ɗauko ta sha sannan ta hau kan gado, addu’a ta yi ta shafe jikinta ta kwanta ta na tunanin yadda za ta yi goben wurin kuɗin amma ta san Allah zai rufa asiri duk ma yadda za’a yi insha Allah ta san sai ta yi fanken.

 

Hussy Saniey.????
*RASHIN ADALCI 2021*

*NA*

*HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

 

*PAGE 13*

Husna na idar da sallar asuba ɗakin Mama ta nufa, sallama ta fara yi jin gyaran murya yasa ta shiga cikin ɗakin,akan sallaya ta iske Maman ta na azkar,a gefen Maman ta zauna bisa lokar gado,zamanta babu daɗewa Mama ta kammala azkar ɗinta,inda Husna ke zaune ta kalla ta na mamakin abin da ya kawo Husna ɗakinta a wannan lokacin,(ba ta shiga cikin ɗakin a irin wannan lokacin daga bakin kofar ɗaki take tsayawa ta gaisheta sai ta juya).

“Ina ƙwana Mama?”inji Husna.
“lafiya lau Husna lafiya meyafaru na ganki yanzu ko kina buƙatar wani abu ne!”Mama ta faɗa ta na ƙa ra bin Husna da kallon mamaki.
“lafiya lau Mama babu wata matsala, alfarma dai nazo nema wurinki,”Husna ta faɗa tare da saukowa daga saman lokar da take zaune.

Bin ta da kallon mamaki Mama ta ci-gaba da yi har ta zauna kan ledar da ke malale a tsakar ɗakin,”alfarma kuma Husna ina jin ki mekikeso?”
“Mama yau ake sadakar kwana ukku ta Babansu Mai Shari’a…..”Husna ta faɗa ta na bin Mama da kallo ta na son ganin yadda Mama za ta ɗauki abin.
“Ke nake saurare kin fara magana kuma kin yi shiru ko dai akwai matsala ne Husna?”Mama ta faɗa tare da tsare Husna da idanuwa.
“Mama jiya bayan na shiga ɗaki aka yanke shawarar mu ƴan amana zamu yi fanke wanda za’a kai gidan sadaka yau,to shine Abba ya ce babu kuɗi a hannu idan da hali nayi daga baya sai a bani kuɗin,ni kuma babu kuɗi a hannuna shine nazo ki ara mana idan aka bada sai na maido maki,”Husna na kai wa nan ta yi shiru cikin ranta ta na addu’ar dacewa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button