HAUSA NOVELRASHIN ADALCI Complete Hausa

RASHIN ADALCI Complete Hausa

Cikin mamaki Mama ta ke bin Husna da kallo,Husnar da bata son aiki ko kaɗan,duk in za’a sanyata aiki a gidan ba ta yin shi cikin daɗin rai,dan in ma kana da zuciya baka sanya Husna aiki,dan ba ta yin shi sai Mama ta mata jan ido a lokacin zata yi shi,yau ga Husna ba tare da an sanyata ba ta na aiki,lalle dole a jinjina ma waɗannan mutanen.

Dariya Husna ta yi ta ce,”Mama sai kallona kike!”
“Ba dole na kalleki ba Husna wannan aiki da ki kayi cikin lokaci,”Mama ta faɗa ta na ɓoye mamakinta.
“Kin ga yanzu Mama lokacin da su Maryam zasu zo ta tashi sai tuya kaɗai zamu fara yi,”Husna ta faɗa cikin fara’a.
“Hakane Allah ya taimaka,”Mama ta faɗa ta na komawa ɗakinta saboda wayarta da ke ƙara.

Hussy Saniey.????
*RASHIN ADALCI 2021*

*NA*

*HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*PAGE 16*

Husna na ganin shigar Mama ɗakinta ita ma sai ta nufi na ta ɗakin,ta na shiga ɗakin kan doguwar kujerar dake ɗakinta ta zauna, hannu ta miƙa ta ɗauki fankaceciyar wayarta dake ajiye a gefen gado, agogon wayar ta kalla gani ta yi har ƙarfe goma sha ɗaya da ƴan mintuna.
Data ta buɗe sannan ta shiga WhatsApp, saƙonni su kai ta shigowa a wayar sai da ta jira su ka gama shigowa sannan ta fara maida amsa.
Group ɗinsu na ƴan amana ta shiga don duk yau ba ta shiga ba,mutane ta iske na fira sallama ta yi ita ma,cikin sauri Dabai ya ce,”yar halak kin ƙi ambato yanzu nake maganarki.”
“Gulmata dai za ka ce kayi kawai Malam.”
Cikin son ƙular da Dabai Husna tai maganar.

“Ke matsalata da ke abin arziƙi bai karɓeki ba daga an ma damu dake sai kuma ki fara wulaƙanci!” Dabai ya faɗa cikin jin haushi.
Dariya Husna ta kama yi saboda ta san ta fara ƙular da shi dan haka ta ce,”ai matsalar ba ka iya daina yi man magana idan kuma kana iyawa to daga yau kar ka ƙara.”
“Ke ɗin ke bazan iya daina yi ma magana ba to ke wacece da har zan kasa daina yi maki magana dallah Malama matsa chan gefe ka da ma na maujeki!!”Dabai ya ƙarasa maganar cikin jin haushi.

“Gaskiya Abdul Dabai Husna ta ga wurin baccinka” cikin son ƙara hayaƙa Dabai Mustapha Madina ya faɗa.
“Ka kyaleta ai yau ta guji haɗuwarmu ni da ita,wai ma dan ta raina ni wai ban iya daina yi mata magana wallahi yarinyar nan kin ci abinci!!” cikin jin haushin Husna, Dabai ya ƙarasa maganar kamar zai yi kuka.

“Ai ba ƙarya nayi ma shi ba Musty kuma a gabanshi na faɗa ba bayan idonshi ba…”Husna ta yi maganar cikin dariya da son ƙara cusama Dabai haushi.
“Ban da lokacinki yarinya amma abu ɗaya zan faɗa maki shi ne ki guji haɗuwarmu idan anjima…” Cikin jin haushi Dabai ya yi maganar saboda da ma kowa yasan Dabai da saurin hayaƙa.

“Gaskiyarki ɗiyata ai kowa ya san Dabai ba zai iya daina yi maki magana ba” Nana Aisha ta faɗa wadda zuwanta kenan cikin gidan ta yadda ana maganar kawai ta sanya baki.
“Yauwa Momy faɗa masa dai kowa ya gane abin da yake nufi…”Husna ta faɗa ta na dariya saboda tasan yau ta kai Dabai ƙarshe.
“Ke wannan Nana A’ishar ke kike sanya wannan Husna Husnar ta raina mutane hakanan kun kasa yi ma yarinya tarbiyyar girmama manyan…”Dabai ya faɗa.

“Ina manyan suke ai ni ban ga manya a nan ba balle har na girmamawa…” Husna ta faɗa cikin sauri.
“Ni ɗiyata nayi mata tarbiyya mai kyau kuma ni ban ga rainin da ta yi ma mutane ba,kawai dai nasan ɗiyata ba ta ɗaukar raini shine kawai abin da nasani.” Nana A’ishah ta faɗa.

“Ke Husna ki kiyayeni duk nan gidan akwai wanda kika raina irina kuma zan ɗauki mataki wallahi!” Dabai ya faɗa cikin jin haushi.
Sannan ya cigaba da magana,”ke nan wannan ita ce tarbiyyar da kike faɗin kin ba ta?to gaskiya ki chanza tarbiyya saboda nan dai kowa ya san babu.”

“Ni ban da lokacinka na tafi in yi aikin gabana,kai kuma sai ka zauna ka tsare mana group ka da kuma a tafi yawo, Momyna sai anjima na tafi aiki zanyi,” Husna na faɗin haka ta fita daga group ɗin.

Hussy Saniey.????
*RASHIN ADALCI 2021*

*NA*

*HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

 

*PAGE 17*

Husna na fita daga WhatsApp, contact ɗinta ta shiga lambar Maryam ta danna ma kira,bugu ɗaya ana biyu Maryam ta ɗauka,”My Husna kin ga har yanzu ba mu zo ba koh?” Maryam ta faɗa cikin fara’a.
“Eh wallahi Anty Maryam kuma ga rana ta fara yi wai dan mu gama da wuri shi ya sa saboda nasan yanzu fulawar ma har ta tashi.” Husna ta faɗa.
“To insha Allah My Husna gamu nan tafe Fadila nake jira ita ma kuma ta na kan hanya.” Maryam ta faɗa.
“To shi ke nan sai kun zo Anty Maryam.” Husna ta faɗa tare da kashe wayar.

Husna na kashe waya ta aje wayar a gefen ta,tsakar gida ta nufa dan duba halin da fulawar ke ciki,kamar yadda ta zata hakan ce ta kasance har ta tashi sosai,maidawa ta yi ta rufe,store ɗinsu ta nufa ta ɗauko murhu ta aje inda suke ajewa idan zasu yi sanwar murhu,gyara murhun ta yi tare da shirya itatuwa a ciki,kalanzir da ashana ta ɗauko ta na cikin buɗe galan ɗin kalanzir ɗin ta ji wayarta na ƙara,fasa zuba kalanzir ɗin ta yi ta rufe galan ɗin, ɗaki ta nufa cikin sauri amma duk da haka ta na shiga wayar na karawa.

Wayar ta ɗauka dan duba wanda ya kirata,bisa hannun kujera ta zauna ta na duba wayar, Chairman ta gani ƙoƙarin kiranshi ta fara kafin ta kira sai ga kiran ya sake shigowa,ɗagawa ta yi tare da yin sallama.
“Assalamu Alaikum Chairman ka tashi lafiya?”
“Wa’alaikissalam lafiya lau Alhamdullih Husna kun fara aikin dai ko kin ga yanzu har ƙarfe sha biyu ta yi muna so zuwa ƙarfe biyu da wani abu azo a ɗauka kin san yanzu an maida addu’ar ƙarfe ukku kada kuma a makara,”Chairman ya faɗa cikin sanyin murya.
“Kar ka damu Abba insha Allah ba zamu makara ba yanzu haka fulawar ta tashi,su Maryam kawai nake jira su ƙaraso kuma har wuta ma yanzu zan hura na fara kafin su iso,”Husna ta faɗa.
“Yauwa Husna sannu da aiki idan aka haɗu sai a ba ki kuɗin kayan da kika kashe,yanzu nawa kika kashe?” Chairman ya faɗa.

“A’a Abba ba sai an biya ba Mama ta bada duka kayan ta ce a bar kuɗin,”Husna ta gayama Abba.
“Allah sarki Mama mun gode ƙwarai Allah ya saka da mafificin alkhairi ki ce muna godiya kafin mu zo,dan dole mu shigo Mu yi mata godiyar wannan hidima da muka ɗora mata…!”Chairman ya faɗa cikin tsananin farin ciki.
“Bakomi Abba zan faɗa mata insha Allah sai kun zo ɗin bari naje na fara aikin chan kafin su ƙaraso saboda Fadila kaɗai ake kira.”Husna ta faɗa.

“To shi ke nan Husna sannu da ƙoƙari gaskiya muna alfahari da shigowarki cikinmu,har abada ƴan amana baza su manta da karamcinki a garesu ba.” Abba ya faɗa cikin tsananin farin ciki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button