HAUSA NOVELRASHIN ADALCI Complete Hausa

RASHIN ADALCI Complete Hausa

“Bakomi Abba ai zaman tare kenan ka kyautatama wanda kake tare da shi nima nagode da yabonku a gareni sai anjima.” Bata jira amsar Chairman ba ta kashe wayarta,tsakar gida ta fito dan cigaba da aikinta

Hussy Saniey.????
*RASHIN ADALCI 2021*

*NA*

*HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*PAGE 18*

Wuta Husna ta hura ta cigaba da suyar fanke,sai da ta soya ya kai rabi sannan ta jiyo sautin Fadila na sallama,hanyar zaure ta kalla tare da amsawa.
“Wa’alaikissalam Fadilarmu!” Husna ta faɗa cikin murna.
“Allah sarki Husna sannu da aiki,dan Allah kiyi haƙuri Husna mun barki da aiki sannu….!” Maryam ta faɗa cikin sigar lallashi.
“Kai My Anty har kin sanya naji kunya…ni fa abin da yasa ki ka ga na fara saboda kin san halin Abba da zumuɗi har fa ya kirani wai an gama?”
Husna ta faɗa tare da tsame fanken da ke cikin kasko.
“Husna ke da wa ke magana?”
Mama ta faɗa lokacin da take fitowa daga cikin ɗakinta.
“Mama su Anty Maryam ne fa…!”
Husna ta faɗa ta na nuna su Fadila dake tsaye bakin kofar zaure tun ɗazun,duk maganar da su ke da Husna da ma basu shigo ba.
Da kallo Mama ta bi inda Husna ke nuna mata,su Maryam ta gani tsaye su na kallonta,ta buɗe baki ta ce.
“Ke dai Husna na ga ranar da za kiyi hankali yanzu ki iya ki ce masu su shigo amma sai hakan ta gagareki sai dai ki tsaresu da labari tun kafin su shigo cikin gidan… Maryam ku shigo mana kun biye ma shirmen Husna kun yi tsaye,in ba yi hankalin ce maku ku shigo ba ai sai ku shigo ko!!”
Mama ta ƙa ra sa faɗa ta na kallon su Maryam dake tsaye su na mata murmushi.
“Kiyi haƙuri Mama shigowa zamu yi da ma…ina wuni Mama”
Fadila ta faɗa tare da durƙusawa ta na gaida Mama.
“Lafiya lau Fadila ya Mamarku?” Mama ta faɗa.
Maryam ma durƙusawa ta yi ta ce,”Mama ina wuni ya gida ina su Auter?”
Kallonta Mama ta yi ta ce,”lafiya lau Alhamdullih su Auter sun tafi Makaranta ya Hajiyarku?”
Duƙar da kai Husna ta yi ta ce,”lafiya lau ta ke ta ce ma a gaisheku.”
“Masha Allah muna,amsawa ku shigo daga ciki mana”
Mama ta faɗa tare da komawa cikin ɗakinta saboda su samu damar sakewa.
Mama na shiga ɗakinta su Fadila suka taho har inda Husna ke sanya fanke cikin kaskon dake kan wuta, Abaya Maryam ta ɗora saman igiyar shanyar dake ɗaure a tsakar gidan.
“Kawo ki huta My Husna ai kin yi ƙoƙari har kin ku sa toyewa duka”
Maryam ta faɗa tare da ƙoƙarin amsar abin da Husna ke tsame fanken.
“Kai My Anty daga zuwanku ko hutawa ba zaku zauna ku yi ba….balle ku sha ruwa sai kawai ku kama aiki!”
Husna ta faɗa tare da riƙe abin tsamar.
“Haba Husna dan Allah ki sakar mata mu ƙarasa aikin nan ai kinyi ƙoƙari,mu ida wane kawai ya rage zamu yi saboda duk kin toya yafi rabi”
Fadila ta faɗa tare da cire abayarta inda Maryam ta ɗora ta ta nan ita ma ta ɗora.
Ganin sun dage akan sai ta bar masu ya sanya Husna ta sakar masu abin tsamar,abayoyinsu ta ƙwashe daga saman igiyar ta nufi ɗakinta dasu domin ta ajiye masu a chan nan waje kuma saboda ka da su ɗauki zafin rana.

 

*PAGE 19*

Husna na shiga ɗakinta saman doguwar kujerar ɗakin ta ɗora abayoyinsu bayan ta linke masu,fitowa ta yi ta nufi kitchen,filet ta ɗauka tare da shiga falon Mama ta ɗauko ruwa tare da kunun Aya ta ɗora a saman filet,tsakar gida inda suke ta dawo.
“Ga ruwa ku sha Anty Maryam tun da kun ƙi bari mu huta!”
Husna ta faɗa tare da jawo wata kujerar roba har gaban Fadila dake zaune gefen Maryam ta ɗora filet ɗin sama.
“Sannu da ƙoƙari Husna”
Anty Maryam ta faɗa ta na janye robar gabanta saboda ta cika.
“Kai Anty Maryam wallahi har kun sanya na fara jin kunya wai meye abin yi man sannu har haka wannan abun fa duk yi wa kaine!”
Husna ta faɗa tare da miƙewa ta na nufar kitchen.
Da kallo su ka bita har ta shige cikin kitchen ɗin,sai da ta shige sannan suka maido kallon ga junansu Fadila ta ce,”gaskiya Husna na da ƙoƙari sosai.”
“Eh wallahi shi ya sa su Abba ke yabonta sosai ke ba ma Abba ba duk wanda ke cikin group ɗin yana yabonta Allah dai ya bar zumunci kawai”
Maryam ta faɗa tare da ɗaukar ledar ruwa ta na sha.
“Ameen ya rabbi! Kin san wannan fanken kyauta take yin shi kuwa?”
Fadila ta tambayi Maryam dake shan ruwa.
Cikin zaro ido Maryam ta ce,”kyauta kuma Fadila? ba ance sai anje ba za’a haɗa mata kuɗin ba?”
“Wallahi Sis mun yi waya da Chairman lokacin ina kan hanya yake faɗaman wai Mamarsu Husna ta bada kayan fanke ta ce a bar kuɗin”
Fadila ta faɗa tare da gyarama Maryam kwandon da ake sanya fanken dan ya tsane kafin a sanya a roba.
“Gaskiya Sis waɗannan mutanen na da kirki sosai dan wallahi wannan sayayyar fanken idan kuɗin ne zamu kashe sun fi dubu biyar amma gaskiya Allah yasa ka masu da mafificin alkhairi”
Maryam ta faɗa cikin alamun jin daɗi saboda da ma aro kuɗi ta yi saboda ko da ance su bada kuɗin da aka haɗa.
“Ke dai bari Sis wallahi zasu kai yadda kaya su kayi tsada yanzu,kuma wallahi yanzu da zan fito sai da na aro dubu ɗaya da ɗari biyar saboda ka da ace ka ba da kuɗi kuma ba ka dasu(saboda idan za’a yi wani abu wurin biki ko suna ko rasuwa officials ke haɗa kuɗi su yi abu).
Fadila ta faɗa da iyakacin gaskiyarta.
“Wallahi Sis kamar kin shiga cikin zuciyata ni ma sai da na aro kuɗin wurin Mama sannan na fito kin ga yanzu sai in maida mata kuɗinta,amma fa naji daɗi wallahi kuma Sis ita Husna kullum cikin hidimtawa ƴan amana take da kuɗinta da jikinta amma ita har yanzu ko naira ba’a taɓa kashe mata ba kuma bata taɓa nuna damuwa ba!”
Maryam ta faɗa cikin sanyin murya.
“Ke dai bari Sis gaskiya ta na ƙoƙari sosai kuma in kika lura ita kowa na ta ne babu ruwanta ban taɓa jin ta yi rigima da wani ba a cikin gidan ƴan amana ba tun da take amma….”
Maganar Maryam ta datse ne saboda labulen ɗakin Mama da aka ɗaga,duk kallon kofar suke gaba ɗayansu da fatan babu wanda yaji me suke tattaunawa ba.

Hussy Saniey.????
*RASHIN ADALCI 2021*

*NA*

*HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*PAGE 20*

Mama ce ta fito hannunta ɗauke da filet da kofi da alama wanda ta yi amfani da shi ne da safe,cikin sauri Fadila taje da nufin ta karɓi kayan dake hannun Mamar.
“Haba ki bar shi Fadila zan kai da kaina”
Mama ta faɗa ta na murmushi.
“A’a Mama ki kawo na kai dai”
Fadila ta faɗa tare da riƙe filet ɗin.
“To shi ke nan Fadila nagode Allah ya yi maku albarka.”
Mama ta faɗa tare da sakar ma Fadila filet ɗin,dubanta ta maida wurin Maryam dake aiki ta juyo wurin Fadila da har ta kai kofar kitchen.
“Ina Husna ta shigane ta sakar maku aikin kuma?”
Mama ta tambaya tare da bin tsakar gidan da kallon ko za ta ga Husna.
“Ta na kitchen!”
Maryam ta faɗa ta na cigaba da aikinta.
“Husna!”
Mama ta ƙwalama Husna kira.
“Na’am Mama gani”
Husna ta fito cikin sauri da tawul a hannunta ta na tsane lema.
“Me kike yi kitchen kika bar masu aiki?”
Mama ta faɗa tare da tsare Husna da idanuwa.
“Taliya na ɗora masu Mama kafin a ida tuyar nima na gama dafawa.”
Husna ta faɗa tare da janye robar da aka cika da fanke gefe.
“Yauwa kin yi tunani mai kyau nima da abin da zance maki kenan a nemar masu abin da zasu ci tunda kin yi wannan tunanin kuma shi ke nan je ki ci-gaba da aikin.”
Mama ta faɗa ta na juyawa domin komawa cikin ɗakinta.
Ganin Mama ta koma ɗakinta yasa Husna komawa wajen Anty Maryam,duba ƙullun fulawar ta yi ta kalli Anty Maryam ta ce,
“Sannu Anty Maryam kin ma kusa ƙarasawa ba ri na ɗauko kular da za’a zuba fanken ciki na ɗauraye”
Ta faɗa ta na komawa kitchen ɗin,bakin kofar shiga suka haɗe da Fadila dake ƙoƙarin fitowa,gefe Husna ta matsa ta ba Fadila hanya.
Shigarta kitchen babu daɗewa ta fito da wata babbar kula ta ɗauraye ta sannan ta kife kular dan ta tsane.
“Fadilarmu bari naje na duba sanwar kafin ku ƙarasa nima na gama.”
Husna ta faɗa tare da nufar hanyar shiga kitchen ɗin.
Har ta kusa shiga kitchen ɗin taji ƙarar wayarta,juyawa ta yi ta nufi ɗakinta,saman dressing mirror ta nufa saboda nan take jiyo ƙarar wayar.
Fuskar wayar ta kalla ganin Iro ne yasa ta ɗauka ta ka ra a kunne tare da sallama.
“Wa’alaikissalam yakike ya aikin?”Iro ya faɗa.
“Lafiya lau Sweet Iro ga aiki nan har mun kusa ƙarasawa.”
Ta faɗa ta na murmushi.
“Allah ya shiryaki taɓa ganin aikin da ki kayi babu raki ba sai wannan!”
Iro ya faɗa tare da gyara kwanciyar shi akan gado.
“Sweet Iro nima har mamakin hakan nake yi kawai dai nasan hakan ya faru ne saboda ƴan group ɗin da nake so…!”
Husna ta faɗa cikin dariya.
“Yau dai hankalin ki zai kwanta tunda yau za ki ga kowa da kowa” Iro ya faɗa.
“Eh wallahi har na ƙagara anjima ta yi!” Husna ta faɗa cikin nuna alamun ɗoki.
“To sai anjima ɗin da ma na kira kine dan naji ya kike sai kun ida ɗin,”Iro ya faɗa.
“To shi ke nan nagode ka kularman da kanka” Husna ta faɗa.
“Insha Allah nima kiyi man alfarmar kulaman da kanki!” Iro ya faɗa cikin lallashi.
“Ba ka da matsala sweet Iro sai kun zo”
Husna ta faɗa tare da datse wayarta,cikin sauri ta nufi kitchen dan duba sanwar da ta ɗora.
Cikin kitchen ɗin ta tadda Mama har ta sauke tukunyar,kallonta Mama ta yi ta ce,”ina kika shiga ki ka bar sanwar kan wuta ba dan Allah yasa na shigo ba da har sai taliyar dahe sosai.”
“Ibrahim ya kirani yanzu kiyi haƙuri kawo na tsane taliyar…!”
Husna ta faɗa tare da ƙoƙarin amsar tukunyar.
Kallonta Mama ta yi ta ce,”ba ri na ƙarasa maki ki je ki shirya Hajiya ke son ganinki yanzu naso na faɗamata ta bari da daddare kije amma ta kafe akan yanzu take son ganinki!”
Cikin sauri Husna ta saki ludayin dake hannunta….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button