RASHIN ADALCI Complete Hausa

Hussy Saniey.????
*RASHIN ADALCI 2021*
*NA*
*HUSSY SANIEY*
*____________________________________*
*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*PAGE 21*
Cikin sarƙewar halshe Husna ta ce,”Ma…ma…kin…san fa in…da zanje kuma duk ba wannan ba ta ya zan iya faɗama su Abba bazan samu zuwa ba…?”
Mama ta bi Husna da kallon tausayi ba dan komai ba sai dan yadda ta san Husna ta ƙwallafa ranta ga tafiya wurin gaisuwar nan,cikin dauriya ta ce,”Husna nayi bakin ƙoƙari na amma Hajiya ta kafe akan lalle sai kin je yanzu ta na son ganinki,kin san ban da ikon ja da maganar Hajiya saboda ba tsarata ba ce,kiyi haƙuri kiyi sauri ki shirya idan da rabo in kika je ko da a gidan gaisuwar ne sai ku haɗe.” Mama na kai wa nan ta juya ta na sake duba taliyar,saboda idan ta na kallon fuskar Husna tausayin Husnar ke ƙara shigarta.
Husna ganin Mama ta juya mata baya ya sa ta fahimci babu wani taimako da za ta samu daga wurin Maman,dan haka jiki a saɓule ta juya tsakar gida inda su Maryam ke tuyar fanken ta nufa.
Kallo ɗaya Fadila ta yi ma fuskar Husna ta fahimci ba ta cikin hayyacinta,da ƙafa Fadila ta zunguri Maryam wadda ba ta san abin da ke faruwa ba sai ƙoƙarin sauke kaskon daga kan wuta take yi, ɗagowa Maryam ta yi bayan ta juya man kaskon cikin wani kwano sai ta aje kaskon a gefe, Maryam ba ta sauke ke idanuwanta a ko ina ba sai akan fuskar Husna,cikin sauri Maryam ta ce,”My Husna lafiya kuwa na ga yanzu kika bar nan wurin lafiya lau amma yanzu da gani kina cikin damuwa meke faruwa ne?”
Shiru Husna ta yi har sai da ta janyo jarka da suke zuba ruwa a ciki ta zauna sannan ta ce,”ina cikin matsala wallahi Anty Maryam…kakarmu ta kira yanzu wai ta na son ganina, Mama ta gayamata zanje gaisuwa idan na dawo sai naje kiran da ta ke man amma ta ce ita ba ta yarda ba yanzu take son ganina,ni wallahi na rasa yadda zan yi saboda yanzu da na ƙi zuwa Mama za ta ɗora ma laifin,ko ma ta ce Mama ta hanani zuwa.”
Idanuwa su Fadila suka zuba ma fuskar Husna yadda kasan a kan fuskar ne zasu samu mafita,chan dai Fadila ta nisa tare da sauke gwauron numfashi ta ce,”Husna kar ki damu kije kiran da take maki ko dan ki fidda Mama daga zargi idan Allah yasa za ki je sai ki ga kinje ɗin idan ma ba kije ba haka Allah ya rubuta dan haka kar ki damu.”
Fadila na yin shiru Maryam ta ce,”maganar ki haka take Sis ga ra taje ɗin dan rashin zuwan na ta yana iya haifar da matsala babba dan haka mafitar kawai ita ce kiyi haƙuri kije.”
Girgiza kai Husna ta yi cikin raunin murya ta ce,”wallahi ban ji daɗin wannan kiran ba kuma Wallahi saboda Mama kaɗai zanje dan idan ban je ba abin akanta zai ƙare,wai duk burin da na ci yau amma Allah bai rubuta dani za’a je gaisuwar ba shi kenan Allah yasa haka shi yafi zama alkhairi.”
“Ameen Husna sai haƙuri dan mu ma bamu ji daɗin rashin zuwan nan naki ba amma bakomi ai ga bikin Umma nan za’a yi kuma nasan shi kowa sai yaje.”Fadila ta faɗa cikin wani yanayi.
“To shi kenan Allah ya kaimu ba ri in watsa ruwa sai na wuce,”Husna ta faɗa tare da miƙewa tsaye ta nufi ɗakinta.
Da kallo su Fadila suka bi bayanta da shi har sai da ta shige ɗakinta.
Hussy Saniey.????
*RASHIN ADALCI 2021*
*NA*
*HUSSY SANIEY*
*____________________________________*
*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*PAGE 23*
Ƙanen mahaifin Husna ne Baba Abu ya shigo,cikin sauri Husna ta ƙarasa inda yake ta karɓi kayan hannunsa tare da yi masa sannu da zuwa,jawota Husna ya yi a jikinsa fuskarsa ɗauke da murmushi.
“Ina ɗiyata za ta je ta sha ƙwalliya kamar za ta je gasar kyau?”
Ya faɗa cikin salon tsokana,dariya Husna ta yi tare da jan mayafinta ta rufe fuska da shi.
“Kai Baba ina ni ina zuwa gasar kyau ai da an koroni.”
“No…no…kar ma ki fara wannan maganar ni yarinyata kyakkyawace za ta iya zuwa ko ina a yaba da kyawunta ai mu jininmu mai kyau ne a ko ina muna iya shiga…”
Ya ƙarasa maganar ta re da kallonsu Fadila da ke tsaye suna kallonshi tun lokacin da ya shigo,mai da kallonshi ya yi wurin Husna ya ce.
“Ɗiyata ƙawayenki ne wannan ko na ga ma kamar fita zaku yi?”
“Eh…ƙawayena ne Baba,fanke muka yi da za’a kai gidan gaisuwa shine suka zo muka yi aikin har ma mun gama.”
Husna ta faɗa tare da zuwa ta buɗe masa kular da aka cika da fanken.
“Ina wuni Baba?”
Maryam da Fadila suka haɗa baki wurin gaida Baba Abu,cikin fara’ar dake ɗauke akan fuskarsa(Kasancewar sa mutum mai fara’a da wuya ka ganshi babu fara’a a fuskarshi,shi ya sa yaran family ɗinsu ke ganin girmansa sosai dan ko da yaushe zai ga yaro to sai ya yi ƙoƙarin ganin yaro ya saki jiki da shi,kai har yaran unguwa basu da matsala da shi kowa dai Baba Abu.)
“Ɗiyata miƙo man fanken nan na ɗan ci naji kun iya?”
Ya faɗa tare da jawo kujera ya zauna akai,filet Husna ta nufi kitchen dan ta ɗauko,gane abin da take nufi yasa ya ce”ɗiyata ina kuma za kije ni da nace ki bani fanke.”
“Filet zan ɗauko Baba na sanya maka.”
Husna ta faɗa ba tare da ta juyo ba.
“Kin ga dawo nan, miƙo man guda ɗaya ma ya isheni.”
“Baba ɗaya kuma?ka bari a ɗauko a sanya maka dai.”
Husna ta faɗa ta na sake nufar kitchen,saurin dakatar da ita ya yi,”idan dai ba za’a bani guda ɗayan da na nema ba to ki barshi nagode kin man rowa kuma.”
“A’a Baba ba haka bane amma bari na baka wanda kake so ɗin.”
Husna ta faɗa tare da nufar kular,jan kular ta yi har gabanshi ta ce,”Baba ka ɗauka to ga kular nan a gabanka.”
“Wai Husna Muryar wa nake ji tun ɗazun cikin gidan nan?”Mama ta faɗa daga cikin ɗakinta.
“Mama Baba Abu ne yazo.”
Husna ta maida ma Mama amsa.
“Baba Abu kuma! (da yake haka Maman ke kiranshi)Kai Husna kina fama da shiririta amma ki kawo shi ɗaki abu sai ya gagara sai dai ki tsare shi tsakar gida da magana Allah ya dai-dai ta maki tunaninki!”
Mama ta faɗa cikin alamun faɗa, fitowa ta yi daga ɗakin ganinshi zaune da kular fanke a gabanshi yasa Mama ƙara cewa,
“Yanzu Baba Abu kai ma sai ka biyema Husna kayi zaune anan?”
Sai da ya kai fanken dake hannunshi a baki sannan ya yi Murmushi ya ce,”ba laifinta bane ni na zauna nan Hajiya…!”
“Ka shigo daga ciki mana.”
Mama ta faɗa ta na kallonshi, murmushi Baba Abu ya yi sannan ya miƙe tsaye,”da ma hanya ta biyo dani nan sai na ga kawai bari na shigo na ga Daughter.”
Girgiza kai Mama ta yi dan tasan Baba Abu da ma akwai zumunci,”amma dai ai ka tsaya ka sha ruwa koh?”
“Bar ruwan nan Hajiya akan hanya nake ina ma so na biya ta gidan Hajiya kaka daga nan.”
Kafin kowa ya yi magana Husna ta ce,”lah…! Baba nima gidan Hajiya kaka zan je yanzu.”
Cikin mamaki ya kalleta sai ya juya ya kalli abokanta.
“Gidan Hajiya kaka kuma ba gaisuwa zaku je ba ko duk unguwa ɗaya ne?”
Shiru ya ratsa wurin babu wanda ya ce komai,ganin haka yasa Baba Abu kallon Husna ya ce,”faɗaman meke faruwane?”
Shiru Husna ta yi ta gagara furta komai sai gabanta dake ta faɗuwa.