HAUSA NOVELRASHIN ADALCI Complete Hausa

RASHIN ADALCI Complete Hausa

 

Hussy Saniey.????
*RASHIN ADALCI 2021*

*NA*

*HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*PAGE 22*

Ajiyar zuciya Maryam ta sauke ta maido dubanta akan fuskar Fadila ta ce,”tsakani da Allah Husna ta ban tausayi, da gani dan bata da yadda za ta yi ne shi ya sa kawai za take kiran da kakarsu ke mata,kalli duk ya yadda ta zama kalar tausayi…”
“Ai dole ta zama Sis kin ga yau kowa ya ci burin yaɗuwa da Husna dan ita ce babu wanda ya sani,kin ga tun da ta zo gidan ƴan amana ba’a yi wani taro ba,mu officials ne fa kawai muka sanya ta sanmu a fuska,amma kin ga Allah bai yadda ba!”
Fadila ta faɗa fuskarta na nuna damuwa,dan har ga Allah ita ma taso ace yau anje gaisuwar nan tare da Husna amma sai ga yadda Allah ya tsara.
“Allah sarki gaskiya abin ba daɗi dan ko jiya ina ji ta na jan Dabai,akan yau idan muka je salan ya ƙi zuwa da sauri ya karɓi jikkarta.”
Maryam ta faɗa da iyakar gaskiyarta,dan Allah kaɗai yasan yadda kowa ya ci burin zuwa wurin gaisuwar ba dan komai ba sai dan yadda zasu yi zumunci sosai,sabbin zuwa kuma duk su haɗu da waɗanda basu sani ba.
Tattaunawa suka rinƙa yi akan yadda gidan nasu na ƴan amana ke ta samun cigaba tunda aka sanya Husna a gidan,ko da ana magana a ciki amma zuwan Husna gidan gaskiya ya sanya yanzu mafi rinjayen members ɗin na fitowa ayi fira dasu,kowa na yabawa da ƙoƙarin da Husna ke yi a gidan,kowa janta wasa yake ga ƙarin abin da yafi burgesu da ita shine ta iya wasa sosai ba ta fushi.
Sun ɗauki lokaci mai yawa suna tattaunawa,har Husna ta fito sanye da doguwar rigar material ja,mayafi da jakka da takalman ƙafarta duk baƙaƙe ta yi kyau sosai.
Fuskarta kadaran kadahan ta ƙaraso wurinsu ta ce, Anty Maryam wai ba dai har an gama ba?”
“Kai My Husna tun kafin ki shiga ɗaki fa aka gama ashe ba ki lura ba?”Maryam ta faɗa ta na kallon Husna.
“Lah! Wallahi ban lura ba Anty Maryam ba ri na juye a kular da za’a sanya shi,sannunku da aiki”
Husna ta faɗa tare da aje gyalenta bisa igiyar shanya ta ɗora jikkarta a kan jarka da ta tashi ɗazun,wurin da ta kife kular dan ta tsane taje ta ɗauko,fanken ta zuba har sai da ta cikata.
Kallonsu Fadila ta yi ta ce,”Anty Maryam wannan ɗan kaɗan ɗin kuma ku sai ku ɗauke shi dan nasan idan ku kaje chan dai ba ci zaku yi ba.”
Ta faɗa tare da karkata bakin robar dan su ga fanken da ta ragemasu.
“Husna ba’a ba Mama fanken ba fa kuma kika juye.”
Fadila ta faɗa tare da taso ta ƙaraso kusa da Husna.
“Ke ba sai an ba Mama ba nasan ma ba zata karɓa ba.”
Husna ta faɗa tare da aje robar hannunta ta nufi wani towel dake shanye kan igiyar ta goge hannunta da ya yi masƙin mai.
“Gaskiya wannan ba magana ba ce Husna a kai mata dai.”Maryam ta faɗa.
“Allah ku bar shi kawai ba sai an bata ba.”Husna ta faɗa tare da rataya gyalenta akai.
“Sis ɗauki fanken nan ki kai ma Mama a ɗaki kyale Husna wane kalar ba za ta ci ba?”
Husna ta buɗe baki ta yi magana ke nan aka yo sallama tare da shigowa,jin Muryar wanda ke sallamar ne ya sanya gaban Husna ya yi wata irin faɗuwa ta kasa amsa sallamar har ya shigo cikin gidan ta na bin shi da kallo.
Amma ta kasa furta ko da kalma ɗaya ce.

Hussy Saniey.????
*RASHIN ADALCI 2021*

*NA*

*HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*PAGE 24*

“kiyi magana mana Husna lafiya dai koh?”
Baba Abu ya faɗa fuskarshi da alamun damuwa.
“Kyale shiriritar Husna Baba Abu wai fa Hajiya Kaka ke son ganinta shine take wannan abun,in ba dan rashin hankali ba meye abin damuwar?ai kamata ya yi ki gaggauta zuwa dan kiji kiran da ake ba wai ki tsaya shiririta ba!”
Mama ta faɗa cikin faɗa dan ita ba ta ga abin damuwa a nan ba, murmushi Baba Abu ya yi tare da dafa kafaɗar Husna.
“Kar ki damu ɗiyata kije kiran da Hajiya kaka ke maki saboda ba mu san dalilin kiran ba kiyi haƙuri kin ji ɗiyata!”
Baba Abu ya faɗa cikin sigar lallashi,share mata hawayen da suka fara zubo mata a fuska Baba Abu ya yi.
“zo muje sai na kai ki ma da kaina kinji ɗiyata…!”
Baba Abu ya faɗa cikin sanyin murya,kallon ƙawayen Husna ya yi sai ya maida dubanshi gareta ya ce”tare da ƙawayenki zamu je?”
Wasu sabbin hawayen suka sake zuɓo ma Husna a fuska, girgiza kai ta yi.
“A’a…ba…tare zamu ba ni kaɗai zan…je su gidan gaisuwar zasu tafi…!”
Husna ta faɗa cikin muryar kuka, girgiza kai Baba Abu ya yi dan sai yanzu ya fahimci inda kukan na Husna ya nufa dan haka sai ya kwantar da murya ya ce.
“Kiyi haƙuri ɗiyata idan muka je kika ji kiran da Hajiya kaka ke maki sai ki wuce chan gidan gaisuwar kin ji ko kar ki damu…!”
Jinjina kai Husna ta yi ba tare da ta ce komai ba,har Mama ta buɗe baki ta yi magana ƙarar wayar Fadila ta katse mata maganar,gaba ɗaya kallon inda Fadilar take su kayi,daga wayar Fadila ta yi ganin su Chairman ne.
“Gamu kofar gidan.”
Daga chan cikin wayar ta ji murya Chairman ya faɗa.
“To shi kenan gamu nan.”
Fadila ta faɗa tare da kashe wayar, kallon Husna ta yi ta ce,”ga ma su Chairman nan sun zo.”
Shiru Husna ta yi sai ajiyar zuciya kawai da take yi,ganin haka yasa Mama ta ce,”Fadila ki ce masu su shigo su ɗauki kular da kansu dan wannan kayan sun maku nauyi sai dai su zo su ɗauka.”
“To Mama bari na sanar masu.”
Fadila ta faɗa tare da ɗaukar abayarta ta sanya,wajen ta nufa,babu daɗewa sai ga ta ita dasu Chairman su ukku ne, Chairman, Ibrahim,Baban gida har ƙasa suka duƙa suka gaida Baba Abu da Mama.
“Mama mun gode ƙwarai Allah ya yi maku sakayya da gidan aljannah mun ga abin arziƙi mun gode Allah ya ƙara buɗi na alkhairi.”
Baban gida ya faɗa kanshi a ƙasa, murmushi Mama ta yi ta ce,”Baba komai nima nagode.”
“Muke da godiya Mama Allah ya ƙara girma muna godiya sosai.”
Ibrahim ya faɗa cikin jin kunyar Mama,kafin Mama ta yi magana Chairman ya ce,”gaskiya muna godiya da wannan hidima da ake damu tabbas mun san mun haɗu da ɗiyar da ta fito daga gidan karamci babu abin da zamu ce sai dai Allah ya yi sakayya da gidan aljannah.”
“Ameen nagode ƙwarai da addu’ar ku, kar ku damu ai Ɗa duk na kowane yadda zan ma Husna abu haka kuma zan maku dan haka ku daina yi man godiya,fatana dai duk inda ku ka tsinci kanku ku kasance masu tare mutuncinku.”
Mama ta faɗa fuskarta da murmushi,su ma sunkuyar da kai ƙasa suka yi amma kana hango murmushin dake kwance akan fuskarsa.
“Insha Allah zamu kasance masu kiyayewa muna godiya ƙwarai da gaske.”
Suka haɗa baki wurin faɗa dan matar ta ƙara ƙima a idanuwansu,nan ne suka gane inda Husna ta gado halinta.
“Ku tashi ku tafi lokaci na ƙurewa yamma ta kawo jiki sai dai kuyi haƙuri Husna bazata samu zuwa ba kakarsu ke kiranta amma wani lokacin insha Allah zata je kuyi haƙuri…!”
Mama ta faɗa cikin lallashi,daga inda take ta na hango yadda fuskarsu ta chanza amma dai hakan nan suka daure.
“To Mama mun gode,bakomi wata ranar sai taje ai wani abun yafi gaban wani hakan ma muna godiya.”
“Ku yi haƙuri ita ma ba taso hakan ta faru ba amma insha Allah gaba zata halarta,ga kular nan gabanku ku ɗauka Allah ya kiyaye hanya.”
Baba Abu ya faɗa wanda tunda ga gaisuwar da ya amsa bai sake magana ba, miƙewa gaba ɗayansu suka yi,mutum biyu suka ɗauki kular sauran su ka bisu a baya.
Baba Abu ma miƙewa ya yi ya ce,”to Hajiya mu ma zamu wuce sai mun dawo.”
Ya faɗa tare da kama hannun Husna suka nufi hanyar fita daga gidan.
“Allah ya kiyaye hanya to a gaidasu Baby da Mamansu.”
Mama ta faɗa cikin ɗan ɗaga murya saboda har sun fice daga gidan,ko da suka fita har su Chairman sun shiga Mota sun tada,hannu kawai ta ɗaga masu suna haɗa ido da Iro ta kashe ma shi ido ɗaya,sai kuma suka saki murmushi a tare,mota suka shiga nan Baba Abu ya tada suka wuce.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button