HAUSA NOVELRASHIN ADALCI Complete Hausa

RASHIN ADALCI Complete Hausa

08105217201
Hussy Saniey.????
*RASHIN ADALCI 2021*

*NA*

*HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*PAGE 25*

Tafiyar minti goma sha biyar ta kai su unguwarsu Hajiya Kaka, ƙofar gida Baba Abu ya yi parking ɗin motarsa, Husna ta fara fitowa daga cikin motar.
Cikin gidan Hajiya Kaka ta shiga da sallama,tsakar gidan babu kowa sai daga cikin ɗaki ta jiyo muryar Hajiya Kaka na amsa mata sallama,kai tsaye ɗakin ta nufa.
“Wai neman me kike man da har kika hanani rawar gaban hantsina yau ko dai tafiyar ce tazo?”
Husna ta faɗa lokacin da ta ke shiga cikin ɗakin Hajiya Kaka,a zaune ta iske Hajiya Kaka cikin shirin fita dan har mayafi ta yafa ma jikinta.
“Dallah chan ai da tafiya ta zanyi tun yaushe na kira uwarki nace ta turoman ke amma sai yanzu kika gadamar zuwa….da ma gidan Hajiya Falmata zanje shi ya sa nayi kiranki saura kaɗan nayi tafiya ta!”
Hajiya Kaka ta faɗa cikin nuna alamun ƙosawa da zaman da ta yi.
Cikin sauri Husna ta ƙarasa ta rungume Hajiya Kaka ta ce,”haba ai ke ba ma kin fara wannan ɗanyen aikin ba na tafiya ki bar ni ka ga tsohuwa mai ran ƙarfe uwar gidan Alhaji Musa.”
Husna ta ƙarasa faɗa ta na gyarama Hajiya Kaka zaman mayafinta,wanda rungumar da ta yi mata ya sanya ya ɗan zame.
Ture hannunta Hajiya Kaka ta yi ta miƙe tsaye ta na gyara riƙon yar ƙaramar jikkar hannunta,babu komai cikin jikkar sai yar ƙaramar wayarta da goro sai kuwa ƴan kuɗaɗenta.
“Za ki wuce mu tafi ko sai kin ƙara ɓataman lokaci gaskiya wannan mijinki yana tare da aiki,ace Mace duk inda za kaje da ita sai ta ɓata maka lokaci Allah ya kyauta Mali dai!”
Hajiya Kaka ta faɗa tare da tilla goronta a baki,fita daga ɗakin ta yi ta tsaya tsakar gidan tare da ƙwalama wadda ke ma ta aikace-aikace kira.
“Ramatu!”
“Na’am Hajiya gani na ɗan kewayane ina ta sauri na fito tun da naji muryar Husna ta shigo.”
Ramatu ta faɗa lokacin da ta fito daga kewayensu hannunta riƙe da buta,bisa wani katako ta ɗora butar da alama anyi shine saboda ajiyarta dan ga butoci nan da yawa aje.
“Manta da wanchan mai shiriritar da yanzu na daɗe da dawowa amma kin ga har yamma ta yi ban tafi ba kuma Wallahi ban son tafiyar yammacin nan,ki ɗora tuwon alkamar da yawa saboda yau muna da baƙi anjima.”
“Ke da Husna ai ba’a shiga tsakaninku Hajiya idan mutum ya shiga sai yaji kunya,insha Allah zan yi kamar yadda ki ka umarta kafin ku dawo ma insha Allah na kammala, Allah ya maido ku lafiya.”
Ramatu ta faɗa ta na murmushi,dan ta gama sanin halin Hajiya Kaka ba’a shiga tsakaninsu da Husna,yanzu sun sanya ka sha kunya idan ka shiga tsakaninsu kuma Hajiya Kaka ba ta iya tafiya unguwa dole sai da Husna dan duk cikin jikokinta Husna ta fi shiga jikinta.
“Haba Baba Ramatu ai ni yau wannan tsohuwar ta ɓataman shirina,ina ƴan group ɗin ƴan amana da nake ba ki labari?to yau da zamu haɗu dasu amma wannan tsohuwar ta ɓataman shirina ai ni dai gaskiya ba’a dubaman ba!”
Husna ta faɗa lokacin da take fitowa daga cikin ɗakin Hajiya Kaka.
“Mtssss! Haka ma za ki faɗa? ba dan nasan kina son zuwa gidan Hajiya Falmata ba ai da babu abin da zai sanya na tsaya jiranki amma ko yanzu kina iya tafiyarki…tun da ke dama abin arziƙi bai karɓeki ba!”
Hajiya Kaka ta faɗa ta na hura hanji alamar ta shaƙa,gyaran murya Baba Abu ya yi wanda ya daɗe a tsaye yana sauraren dramar Hajiya Kaka da Husna wanda inda sabo duk sun saba da jinta,juyawa gaba ɗayansu suka yi dan ganin wanda ya yi gyaran muryar.
Sai lokacin Husna ta tuna da tare suka zo,ida shigowa ya yi har ƙasa ya tsugunna ya gaida Hajiya Kaka,ita kuma Ramatu ta gaidashi saboda ya girmeta.
“Hajiya ku taho sai na aje ku tunda hanyar nayi.”
Baba Abu ya faɗa har lokacin kanshi na duƙe a ƙasa.
“Daga zuwanka sai kuma ka juya ka shiga mana ko ruwa ka sha.”
Hajiya Kaka ta faɗa ta na nufar ɗakinta,dakatar da ita Baba Abu ya yi ya ce,”A’a Hajiya ai tare da Husna muka zo yanzu kuma daga nan gida na wuce da ma na biyone na gaidaki.”
“Amma wannan yarinya akwai sakarai amma ba ta sanar dani ba tare ku ka zo,kai ni dai wannan yarinya na ga ranar da zata yi hankali!”
Hajiya Kaka ta faɗa cikin jimami,dariya Husna ta saki ta ce,”haba Hajiya Kaka duk hankalin da ake faɗar ina dashi amma ke ba ki gani ba tab gaskiya idanuwanki sun kwana biyu!”
“Ki bani idanuwan ubanki sai na rinƙa gani dasu Husna!”Hajiya Kaka ta faɗa cikin fushi.
Ganin ta fara hassala ya sa Baba Abu yi ma Husna nuni akan ta fita waje,shi kuma ya samu da kyar ya lallashi Hajiya Kaka suka fito dan da har ta ce ta fasa tafiyar in dai da Husna za’a je(sai ka ce ba ita ta kira Husnar ba).
Shi dai Baba Abu haƙuri ya ba Hajiya Kaka har ya samu lallaɓata sai da ya kai su ƙofar gidan Hajiya Falmata ya ajesu,sai da ya ga shigarsu sannan ya juya motarshi ya yi gaba yana dariyar dramar Hajiya Kaka da Husna.

08105217201
Hussy Saniey.????

*RASHIN ADALCI 2021*

*NA*

*HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*PAGE 26*

Sun daɗe a gidan Hajiya Falmata sosai sai gab da magrib suka baro gidan,akan hanya Husna sai mita take ma Hajiya Kaka akan daɗewar da suka yi dan ita gidansu take son ƙwana,banza Hajiya Kaka ta yi da ita ko ƙala ta ƙi ce mata har suka iso gida.
Suna shigowa masallacin ƙofar gidan Hajiya Kaka ana kiran sallah,saboda haka su na shiga gidan basu zauna ba, alwalla suka hau ƙoƙarin yi.
Bayan an gama sallar magrib Husna ta miƙe ta ce gida za ta tafi,nan fa Hajiya Kaka ta rinƙa faɗa akan babu inda za taje saboda dare ya yi,duk ƙoƙarin da Husna ta yi na san ganin ta tafi gida hakan ba ta samu ba,dole ta haƙura ta kwana a gidan,gari na wayewa wurin ƙarfe goma kuma ta ce gidansu za ta tafi,duk faɗan da Hajiya Kaka ke yi na ta zauna ta yi kalaci ƙin kulata Husna ta yi,dole Hajiya Kaka ta sanya mata idanuwa ta tafi.
Ta na zuwa gida ta iske Mama zaune akan sallaya ta gama sallar walha,kallo ɗaya Mama ta yi mata ta ɗauke kanta,dan ta san wannan kaɗan ne daga aikin Husna,zai yi wuya taje wani wuri ta ƙwana idan kuwa har ta kama dole ta ƙwana ɗin to tun da safe za ta baro wurin.
Ganin Mama na lazimi yasa ta nufi kitchen dan wata muguwar yunwa take ji,ba ta samu komai ba dan haka ta ɗora ruwan zafi Lipton da kayan ƙamshi ta sanya ta na tsaye har ya tafasa ta juye a kofi, ɗakin Mama ta dawo har lokacin Mama bata tashi daga inda ta isketa ba,gefe ta aje kofin ta koma kitchen ta ɗauko kayan shayi ta koma ɗakin Mama.
Da kallo Mama ta ke bin ta har ta kammala haɗa shayin ta soma sha,sai da ta gama komai sannan ta ƙwashe ta maida su kitchen ɗin,kai tsaye ɗakin Mama ta komo Lokacin Mama ke naɗe sallayar,dan haka ta samu wuri ta zauna ta ce,
“Mama ina ƙwana?”
“Yanzu Husna ba za ki daina halinki ba ace ki ƙwana wuri amma tunda safe ki baro shi ko karyawa ba ki tsaya kin yi ba salan ki ja man zagi?”
Mama ta faɗa ranta a ɗan ɓace,ta san dole sai Hajiya Kaka ta yi faɗan fitowar Husna ko karyawa ba ta tsaya ta yi ba.
“Mama ni fa lokacin ban jin yunwa.”
Husna ta faɗa ta na turo baki gaba,hannu Mama ta sanya ta doke bakin ta ce,”kin ci gidanku kina nufin daga gidan Hajiya Kaka zuwa nan gidan ne har kika ji yunwa Allah dai ya shiryaki tun da kin dawo gidan sai ki ɗauki abin da za ki ɗauka a cikinsa!”
“Mama wai ina su Abba da Awu ban gansu ba?”
Husna ta faɗa dan son kore maganar tahowarta daga gidan Hajiya Kaka.
“Abba ya tafi makaranta,Awu kuma ya fita waje bai dai yi nisa ba dan bai daɗe da fita ba wani abu zasu yi maki ne?”
Mama ta ƙarasa maganar da tambayar Husna.
Girgiza kai Husna ta yi ta ce,”babu abin da zasu man na dai ga ban gansu bane shine kawai na tambayesu… Mama Baba tun ɗazun ya fita?”
“Eh tun wurin ƙarfe tara ya fita bai je gidan Hajiya Kaka bane?” Mama ta amsa ma Husna.
“Eh bai je ba har na baro gidan ƙila sai anjima zai je ko kuma bayan tahowata ya isa.”
“A’a sai dai idan bari ya yi sai da marece ya je amma inda chan ya nufa ai da ya iske ki tunda tun ɗazun ya fita.”
“To Allah ya maidoshi lafiya bari naje na ɗan ƙwanta Mama bacci nake ji…su Abba sun ce a ƙara yi maki godiya.”
Husna ta faɗa lokacin har ta miƙe tsaye.
“Kin samu zuwa gidan gaisuwar kuwa jiyan?”
Mama ta tambayi Husna.
“A’a banje ba,gidan Hajiya Falmata na raka Hajiya Kaka kuma bamu baro gidan ba sai magrib, lokacin naso na taho gida Hajiya Kaka ta hana.”
Husna ta faɗa ta na nufar hanyar fita daga ɗakin.
“Yanzu ai ga shi kin dawo gidan sai hankalinki ya kwanta.”
Mama ta faɗa ta na zama akan kujera.
Murmushi Husna ta yi ba tare da tace komai ba ta fita daga ɗakin,kai tsaye ɗakinta ta nufa.
Girgiza kai Mama ta yi bayan tafiyar Husna,dan inda sabo ya kamata ace kowa ya saba dan zai yi wuya ka ga Husna taje wuri ta ƙwana,ƙallafar gida gareta ko wuri taje ta rinƙa faɗin a tashi a tafi gida tun ta na ƙarama.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button