HAUSA NOVELRASHIN ADALCI Complete Hausa

RASHIN ADALCI Complete Hausa

08105217201
Hussy Saniey.????
*RASHIN ADALCI 2021*

*NA*

*HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*PAGE 29*

“Haba Husna gaskiya ba za ki ɗauki wannan ba saboda ya yi maki girma da yawa kin kuwa san nawa ake decoration balle ga harda wasu kyauta kuma kin ɗauka gaskiya A’a ba za’a yi haka ba.”
Chairman ya faɗa dan dagaske yake abun da Husna ta ɗauka ya yi yawa duba da ba aiki take ba kuma ba ta sana’a.
“Ni ma dai haka na gani gaskiya a chanza mata wani.”
Hadiza Muhammad ta faɗa dan duk wanda zai faɗi gaskiya ya san wannan ai ya yi yawa.
“A’a zan iya ba sai an chanza man ba.”
Husna ta faɗa dan ita dai ta san za ta iya abin da ta faɗa.
“Wallahi sai an chanza shi kin ji ma na rantse ni na ɗauki decoration ɗin ke sai ki kawo Dj ɗin dan gaskiya wannan aikin mazane babu yadda za’a yi mu bar maki ke kaɗai.”
Sulluɓawa ya faɗa saboda yasan halin Husna idan ta kafe akan abu shi ya sa ya yi saurin rantsuwa dan ma ta saki tun da wuri.
“Yauwa Sulluɓawa ka kyauta gaskiya abin da kayi.”
Chairman ya faɗa,dan ya ji daɗin abin da Sulluɓawa ya yi har kullum ƴan group suna alfahari da Sulluɓawa dan bai jin ƙyashin kashe kuɗi.
“Maganar kyautar da za’a ba amarya kuma mun yi magana da Zee Abba ta nuna ta na son bada gudunmawa to yanzu sai na ce ta siyo mana agogo sai aka a sanya hoton amaryar kawai mun gama wannan maganar Husna mun gode Allah yasa ka da alkhairi.”
Ibrahim ya faɗa dan shi kanshi abin da yasa farko bai yi magana ba saboda ka da ace dan Husna ce shi ya sa zai ce a chanza amma yaji daɗin yadda komai yazo cikin sauƙi.
“Amma gaskiya ban ji daɗin abin da ku kai man ba wallahi,ai ni nace zan iya ba sai a sanyaman ido ba a gani amma shi ne kai Sulluɓawa har da saurin rantsuwa…!”
Husna ta faɗa dan gaskiya taso a barta ta yi decoration ɗin wurin dan da kanta taso yi.
“Malama mun gama wannan maganar kuma shi kenan sai dai a tari gaba kawai Allah yasa ka ma kowa da alkhairi Allah ya ƙara haɗa kawunnan mu.”
Muhammad Daura ya faɗa,dan kullum yana yaba ma yan group ɗin nan akan jajircewarsu akan duk abin da ya taso a cikin group ɗin ana haɗa ƙarfi da ƙarfi ayi maganin abin.
“To zan kawo Dj kamar yadda ku ka buƙata amma wallahi sai na haɗo da mai hoto dan Allah kar ku ce A’a kun dai ji na rantse koh?”
Husna ta faɗa dan gaskiya ta na son wannan partyn ya bada kala sosai kowa,duk wanda yazo ya ji daɗin wurin.
“Babu matsala ki kawo muna godiya sosai.”
Maryam da ta ji daɗin mai hoton da za’a kawo shi ya sa ta riga kowa amsawa dan gaskiya su sun manta da wani hoto ma sai yanzu da Husna ta yi maganar babu abin da zasu iya ce ma Husna sai dai addu’ar gamawa da iyayenta lafiya.
“Yauwa kuma duk wanda yasan abin da zai kawo ba mai lalacewa bane muna buƙatar abin tun saura ƙwana ukku partyn.”
Husna ta faɗi dan ba ta son a samu matsala ko kaɗan.
“Eh gaskiya kin yi maganar da nake son yi yanzu dan Allah ayi ƙoƙarin yin abun cikin lokaci.”
Chairman ya faɗa dan kowa yasan Chairman akwai zumuɗi akan abu,duk in za’a yi abu to fa Chairman ya rinƙa kiran wayar mutum kenan har sai an gama.
“Matan za ka faɗamawa dan sune masu shirita.”
Dabai ya faɗi cikin son tsokano matan ai kuwa ya ci nasara,dan gaba ɗaya suka taso ma shi.
“Kai wa ya kai ka daɗewa ma ko tafiya za’a yi sai ka ɓatama mutane lokaci!”
Zulaihat ta faɗa dan sun taɓa tafiya da Dabai aikuwa sun daɗe suna kiranshi.
“Yauwa zulaihat faɗamasa dai!”
Husna ta faɗa duk da bata cikin group ɗin lokacin da aka yi tafiyar.
“Dillah Malama ware! Kin ma san lokacin da aka yi?”
Dabai ya tambayi Husna.
“Eh kin san lokacin Husna.”
Zulaihat ta faɗa dan son tarema Husna.
“Yauwa zulaihat faɗa masa dai ai shi ma ya san na san lokacin.”
Husna ta faɗa ta na dariya.
“Malama ki ma mutane shiru wai waya kasa dake ne ma?”
Dabai ya tambayi Husna.
“Malam ban da lokacin ka.”
Husna ta faɗi.
“Yauwa Husna sannu da ƙoƙari ba ri mu ware tunda an gama sai mu koma bacci.”
Chairman ya faɗa dan bacci yake ji sosai.
“To shi kenan Chairman namu na ƴan amana,wai ya jikin Fauzee Kabir?”
Husna ta amsa ma Chairman.
“Da sauƙi duk da dai tun shekaran jiya rabon da mu yi magana da ita amma zuwa anjima zan kirata.”
Chairman ya faɗa yana sauka.
“Allah ya bata lafiya.”
Husna ta faɗa tare da komawa chan Main group ɗinsu na ƴan amana.

08105217201
Hussy Saniey.????
*RASHIN ADALCI 2021*

*NA*

*HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*PAGE 27*

 

Bayan shigar Husna ɗakinta kai tsaye saman gado ta ƙwanta,wayarta ta jawo ta buɗe data dan gaskiya ta yi missing ɗin chat dan jiya gidan Hajiya Kaka ba ta hau ba babu network har ta yi bacci.
Minti goma ta bada har sai da saƙonni suka gama shigowa,duk wanda ya mata magana ta rinƙa ba amsa har ta kammala da masu yi mata magana private, group ɗinsu na ƴan amana officials ta ga saƙonni da yawa,sanin ba’a fira a ciki sai idan magana mai muhimmanci ce yasa ta yi saurin shiga ciki.
Tun da ga magana ta farko ta fara bi har taje ƙarshe,an yi magana akan yadda za’a gabatar da bikin Umma ɗaya daga cikin offials ɗin gidan,bikin saura ƙwana ashirin da sun so jiya idan aka haɗu a gidan gaisuwa sai su yi maganar amma hakan ba ta samu ba.
Yanzu dai an aje magana akan anjima zasu yi maganar lokacin kowa na nan,dubawa ta yi ta ga ai kowa na online sai ta yi sallama a gidan.
“Assalamu Alaikum ykk fatan kuna lafiya na ga tattaunawar da ku kayi gaskiya abin ya yi kyau sosai Allah ya ƙara haɗa kanmu,ni dai abin da zance akan haka na ce me zai hana ga bikin mu ma mu haɗa mata party na ƴan amana sai ta gayyato wasu daga cikin ƙawayenta amma ya ku ke gani?”
Ko minti biyar da yin maganar ba’a yi ba sai ga Ibrahim ya yi magana.
“Gaskiya kin yi magana mai kyau Husna idan aka yi hakan nasan za ta ji daɗi sosai.”
“Yauwa Ibrahim ni ma haka nake tunani amma ba ri sauran su zo sai muji abin da zasu faɗa.”
“Gaskiya ne mutunniyata gaskiya shawararki ta yi ina goyon bayanki ɗari bisa ɗari.”
Dabai ya faɗa wanda tun da aka fara maganar sai yanzu ya sanya baki.
“Yauwah ƙanwata hakan ma shawarace mai kyau.” Muhammad Daura ya faɗa.
Nan fa duk wanda yazo sai ya yi na’am da wannan shawarar,ganin haka yasa Chairman ya ce,”to wani hanzari ba gudu ba yanzu ya ku ke ganin zamu ɓilloma al’amarin party ɗin yadda zai ƙayatar?”
“Ni a ganina tunda mu tara ne offials mai zai hana kowa ya ɗauki nauyin wani abu sai mu ga abin da ya rage ko ya ku ka gani.”
Husna ta faɗa da addu’ar Allah ya sanya shawararta ta samu karɓuwa.
“Yauwa Husna hakan ma dai-dai ne.”
Maryam ta faɗa.
“Eh gaskiya ayi hakan kawai zai fi.”
“To shi kenan yanzu waɗanne abubuwa ku ke ganin ana buƙata a wurin?”
Dabai ya faɗa.
“Ni abin da nake ganin muna buƙata sune;snacks, drink’s,ruwa,take away,dj, venue, decoration,kamar waɗannan sune manyan abubuwan da muke buƙata a yanzu!”
Hadiza Muhammad ta faɗa,ita ma tunda aka fara maganar ba ta ce komai ba sai yanzu.
“Yauwa Kakata kuma ya kamata ayi tags a ba kowa dan gudun idan an haɗu ka da ai ta tambayar juna wanene Wannan amma idan aka ba mutum da sunanshi sai ya liƙa tunda ƙarami za’a yi.” Husna ta faɗa.
“Yauwa amarya ma ya kamata a bata kyautar wani abu wanda za ta rinƙa tunawa da ƴan amana idan ta kallah.” Chairman ya faɗa.
“Gaskiya ne mutanena shawarwarin ku duk sun yi gaskiya kun yi ƙoƙari Allah ya bar zumunci.” Sulluɓawa ya faɗa wanda zuwanshi kenan gidan yanzu.
“Kuma gaskiya muna so mu yi amfani da tables dan haka idan san samune venue ɗin da za’a samu ya kasance harabace inda zamu yi shi saboda mun fi jin daɗi,kuma ya kamata a yanka chake ko ya ku ka gani.”
Husna ta faɗa,ta na gyara kwanciyarta.
“Yauwa PRO ta mu gaskiya aikin ki na kyau.”
Chairman ya yi maganar har cikin ranshi yana jin daɗin yadda Husna ke basu goyon baya da shawarwari masu kyau.
“To yanzu sai kowa ya ɗauki abin da zai kawo,ko da yake ga Chairman nan ya faɗa ma kowa abin da zai kawo kawai.”Husna ta yi tambayar dan ganin kowa ya hallara.
“A’a gaskiya wannan aikin na kine PRO raba mana kawai.”
Chairman ya faɗa saboda yasan za ta yi abin da ya kamata.
“A’a gaskiya ga manya nan su zaɓa mana dan ni dai ban iya komai ba nan.” Husna ta faɗa da iyakar gaskiyarta.
“A’a gaskiya tun da ance ki zaɓa kawai ki zaɓa.”
Maryam ta faɗa,nan fa kowa ya kama dole Husna ta raba ma kowa abin da zai kawo,shiru ta yi ta na tunanin yadda za ta iya irin wannan aikin.
“Ke muke jira Hajiya.”Ibrahim ya faɗa saboda yasan yanzu ta na chan ta na zare idanuwa,nan fa kuma aka yi chaaa akan ta fito ta raba ta ba kowa nasa, ƙara tsurewa Husna ta yi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button