HAUSA NOVELRASHIN ADALCI Complete Hausa

RASHIN ADALCI Complete Hausa

08105217201
Hussy Saniey.????
*RASHIN ADALCI 2021*

*NA*

*HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*PAGE 28*

“Kowa ya matso to zan raba.”
Husna ta faɗa cikin ƙarfin hali,zuciyarta sai faman bugawa take dan ita dai ba ta san me za ta ba mutane ba.
“Zaaaa…PRO ta mu fara kawai kowa na kallonki.”
Sulluɓawa ya faɗa dan ya lura kamar ƙarfin haline take yi.
“Zan fara ta kan Chairman.”
Husna ta faɗa cikin tsoro dan har ga Allah ta rasa abin da za ta yi.
“Muna saurarenki.” Iro ya faɗa yana dariya daga inda yake zaune.
Bin Iro private Husna ta yi,”dan Allah Sweet Iro faɗaman yanda zanyi Allah kaina ya kulle”
Husna ta faɗa kamar za ta yi kuka.
“Haba daina ma ka da aji ai mana dariya,na yadda dake Sweet Husnata nasan za ki iya dan haka raba ma kowa na shi,kin ga yanzu idan na faɗa maki to ranar da irin haka ta faru ban kusa dake fa dan haka kiyi haƙuri kiyi abin da ya dace kin ji ko Tawan nasan za ki iya.”
Iro ya faɗa cikin lallashi, shagwaɓewa Husna ta yi ta ce,”to zan yi man na yau kawai dan Allah.”
“A’a Sweet Husnata nima ina so naga yanayin abin da za ki yi idan kinyi ba dai-dai ba zan gyara maki,muje ki cigaba kin ji ko Tawan.”
jinjina kai Husna ta yi ta ɗan samu ƙwarin guiwa dan haka ta gyara kwanciyarta, group ta koma ta fara magana.
“Chairman muna buƙatar motocin da zamu yi amfani dasu wurin mayar da mutane gida fatan babu matsala?”
Tafa mata Muhammad Daura ya yi,sai ga su Sulluɓawa su ma suna tafa mata, Iro kuma jinjina ya yi mata.
“Da gani dai ɗan achaɓa za ki hawo shi ya sa kike neman motar komawa gida.”
Dabai ya faɗa cikin tsokana, emoji mai alamar murguɗa baki ta tura ma shi.
“Gareka Sectary (Iro shine Sectary)”
“Insha Allah Babu wata matsala za’a kawo.”
Chairman ya faɗa yana dariya,dan bai yi tunanin abin da za ta ce ya kawo ba kenan.
“Yauwa muna godiya, Sectary ko ba ka kusa?”
“Ina jinki Hajiya faɗi.” Ibrahim ya faɗa.
“Yauwa duk kajin da za’a ci a wurin mun ɗora maka wannan nauyin da zirga-zirgar abin hawa na karɓo kaya daga hannun waɗanda suka ɗauki nauyi.”
“Komai zan yi shi yanda ake so insha Allah.” Iro ya faɗa yana dariya.
“Gaskiyane PRO aikin ki na tafiya yadda ake so muna jinjina.”
Wannan karon Sulluɓawa da Maryam suka faɗa a tare,har ana yi masu dariya.
“Yauwa muna godiya,gareka Treasurer (Sulluɓawa)”
“Ma’am faɗi na aikata abin da kike so Hajiya da girman kujerarki.”
Sulluɓawa ya faɗa yana jiran jin mai za’a ce ya kawo.
“Yauwa muna buƙatar Dj mai Mc daga gareka.”
Husna ta faɗa cikin ranta ta na addu’ar Allah yasa ta yi abin da ya kamata.
“Insha Allah kun samu Hajiya.”
“Yauwa sai kai Shehu (Muhammad Daura take nufi).”
“Ina jinki ƙanwar Shehu mekike so?”
“Muna buƙatar ruwa katon goma a wurinka.”
“Insha Allah zan kawo kamar yadda aka buƙata.”Muhammad Daura ya faɗa.
“Yauwa mun gode Allah yasa ka da alkhairi.”
“Gareka Welfare 1(Abdul Dabai)”
“Ina jinki ƴar yarinya.” Dabai ya faɗa yana dariya dan yasan ya tsokanota dan bata san yana ce mata yarinya.
“Mtssss…! Chan ma ga yarinya,muna buƙatar Venue a wurinka da tables ɗin zama.”
“Angama yarinya za’a samu insha Allah.”
“Yauwa mun gode yaro!”
Husna ta faɗa dan ta san shi ma ya tsani ace ma shi yaro.
“Yauwa gareki Welfare 2(Maryam)”
“Ina jinki My Husna.”
“Yauwa muna buƙatar lemu katon goma a wurinki.”
“Insha Allah za’a samu.”
Maryam ta faɗa.
“Yauwa mun gode,kai nayi tuya zan manta da albasa ina Kakata?”
“Gani kusa dake Jikata me kikeso a wurina?”
“Yauwa My Kakus Cake muke so mai kyau a wurinki.”
“Insha Allah za’a samu.”
“Yauwa mun gode,wai ina Xulaihah ki fito mana ki karɓa.”
“Gani nan kusa Husna ke nake saurare.” Zulaihat ta faɗa dan babu ma wanda ya lura da zuwanta sai yanzu,dan ita in dai ba abu mai muhimmanci ake ba baka cika ganinta ba.
“Yauwa matso snacks muke so a wurinki,samosa hamsin, spring grill hamsin,daugnut hamsin.”
“Insha Allah zan kawo Allah ya shige mana gaba.”
“Ameen nagode,ina Mustapha Madina gareka.”
“Gani Hajiya Husna.” Mustapha ya faɗa dan lokacin da yazo ana magana shi ya sa bai ce komai ba ya tsaya yana saurare.
“Yauwa kai muna son kai mana Tags guda talatin da biyar dan duka members ɗin group ɗin iyakarmu kenan sai ka haɗo mana da ledar take away guda ɗari,sai tishu da robali fatan babu matsala.”
Husna ta faɗa gabanta na faɗuwa, Allah dai yasa ta raba dai-dai.
“Babu matsala Hajiya insha Allah zan kawo.”
Mustapha Madina ya faɗa yana jin daɗin ba’a ba shi abubuwa masu wahala ba.
“Yauwa mun gode yanzu sai ni kuma,insha Allah zan ɗauki nauyin decoration da kyautar da za’a ba amarya.”
Lokaci guda kowa ya zaro idanuwa saboda jin uban aikin da Husna ta ɗaukar ma kanta.

08105217201
Hussy Saniey.????
*RASHIN ADALCI 2021*

*NA*

*HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*PAGE 31*

“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un Fauzee!! Hasbunallahu wai dagaske ne?”
Kawai sai ta fashe da wani matsanancin kuka,wanda har sai da saurin ya kai kunnen Mama da ke ɗakinta zaune,ji ta yi kamar kunnuwanta na jiyo mata kukan Husna ba ta tabbatar ba sai da ta ƙara saurarawa lokacin ta tabbatar.
Cikin sauri Mama ta iso ɗakin,halin da ta iske Husna ciki shi ya sanya gabanta ya yi wata irin faɗuwa,cikin rawar jiki Mama ta riƙe kafaɗun Husna ta juyo da ita su na fuskantar juna.
“Lafiya Husna meke faruwa?”
Sautin muryar Mama ne ya daki dodon kunnuwan Husna, faɗawa Husna ta yi a jikin Mama ta saki wani wahalallan kuka.
“Dan Allah Husna ki natsu ki faɗaman meke faruwa!”
Mama ta furta cikin sanyin murya,amma ina Husna ba ta san ta na yi ba,kuka Husna ke yi mai ban tausayi cikin kuka ta ke faɗar.
“Fauzee Kabir innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!!”
Abin da kawai take mai-maita wa kenan a bakinta,lallashinta Mama ke yi amma kamar ƙara zugata take yi,sun ɗauki lokaci mai tsawo a haka.
Ɗagowa Husna ta yi ta kalli Mama ta ce,”Mama Fauzee Kabir ta rasu Mama!kai innalillahi wa’inna ilaihirraji’un Mama babu Fauzee shi kenan ta tafi ta barmu Mama!!”
Ta faɗa tare da sake durƙushewa ƙasa ta na kuka,ita kanta Mama sai da bugun zuciyarta ya chanza dan kowa ya san irin amintar da ke tsakanin Husna da Fauzee Kabir.
Kuka Husna ke yi kamar ranta zai fita, Mama ta ka sa rarrashinta saboda ita kanta mutuwar ta daketa,dole Husna ta yi kuka saboda akwai shaƙuwa mai ƙarfi a tsakaninsu.
“Mama dagaske Fauzee ta mutu?”
Husna ta tsurama Mama idanuwa tamkar a fuskar Maman za ta ga amsar tambayarta.
“Husna ke wa ya faɗa maki Fauzee ta rasu?”
Mama ta tambayi Husna cikin sanyin murya.
“Mama…a group… Umma ta sanar kuma kin…san ƴar uwarsu Fauzee ce ba ri ma ki gani.”
Husna ta faɗa tare da jawo wayarta da ta yi ratsa-ratsa, kunna wayar ta yi sai da ta jira ta gama loading sannan ta shiga WhatsApp, group ɗinsu ta shiga nan fa ta ƙara tabbatarwa dan mutane sai kuka ake.
Miƙa ma Mama wayar ta yi ta ce,”ki duba Mama ki gani dagaske ne gobe za’a yi jana’izarta da safe… Mama shi kenan mun rabu ni da Fauzee… innalillahi wa’inna ilaihirraji’un Mama!!”
Husna ta ida maganar ta na sakin wani irin kuka mai tsuma zuciya,babu abin da ke mata yawo akai irin yadda suka yi rayuwa ita da Fauzee,amma yanzu duk ya zama tarihi kenan,abin da yafi ɗaure mata kai ko shekaran jiya sai da ta kira Fauzee amma ba ta ɗaga ba,ita kuma sai ba ta sake kira ba ashe shi kenan babu sauran magana a tsakaninsu.
“Husna kiyi haƙuri bari na kira wayar Mamanta dan mu tabbatar.”
Mama na maganar ta na latsa wayarta,cikin Sa’a ta shiga bugu ɗaya ana biyun aka ɗaga,daga yanda ta ji muryar Maman Fauzee jikin Mama ya yi sanyi.
“Assalamu Alaikum ina wuni Maman Husna?”
Maman Fauzee ta faɗa cikin muryarta da ko fita sosai ba ta yi.
“Wa’alaikissalam Maman Fauzee yanzu Husna ke faɗaman wani al’amari da babu daɗin ji.”
Maman Husna ta faɗa cikin sanyin murya.
Murmushin ƙarfin hali Maman Fauzee ta yi ta ce,”to ya za’a yi da al’amarin Ubangiji ai sai dai mu yi godiya a gareshi amma Fauzee ta amsa kiran mahaliccinta gata nan kwance a gaba amma babu rai!”
Maman Fauzee ta ƙarasa maganar hawaye na zubowa a saman fuskarta,hannu ta sanya ta share ta cigaba da magana.
“Ina ganin abin tamkar mafarki Maman Husna amma nasan gaskene bazan iya chanza ƙaddarar Allah ba.”
Mama ta ja numfashi cikin ƙarfin hali ta ce,”hakane Maman Fauzee kiyi haƙuri addu’a kawai Fauzee ke buƙata a yanzu, Allah yasa kwanciya hutuce agareta!”
“Ameen Maman Husna nagode kwarai ga mutane chan sun zo bari naje wurinsu.”
Maman Fauzee ta faɗa tare da kashe wayarta.
Jikin Husna ya yi sanyi sosai,ta ƙara tabbatarwa duniya ba wurin zama ba ce,yanzu shi kenan babu Fauzee har ta zama tarihi a cikin duniya kenan lalle rayuwa abin tsoroce.
Mama ta daɗe ta na lallashin Husna,har sai da ta ga zuciyarta ta ɗan yi sanyi,ruwa mai sanyi Mama ta je ta kawo ma Husna ta sha, ƙara yi mata nasiha Mama ta yi da nuna mata muhimmancin haƙuri da babu wani abu da Fauzee ke buƙata sai addu’a.
Ganin Husna ta ɗan samu natsuwa yasa Mama ta koma ɗakinta,bayan fitar Mama shiru Husna ta yi ta na tuna rayuwarsu ita da Fauzee.
Fauzee ita ce lokacin da aka sanyata a gidan ƴan amana ta fara yi mata barka da zuwa gidan tun daga lokacin suka saba sosai.
Lumshe idanuwanta ta yi kamar a mafarki ta fara tariyar rayuwarsu da Fauzee, ɗaya bayan ɗaya ta fara tuna rayuwarsu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button