HAUSA NOVELRASHIN ADALCI Complete Hausa

RASHIN ADALCI Complete Hausa

08105217201
Hussy Saniey.????
*RASHIN ADALCI 2021*

*NA*

*HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*PAGE 30*

Fira Husna da Abdul Mai kasuwa ke yi sosai sai tsokanarta yake ita kuma ta na biye ma shi.
Ko kaɗan ba ta san Iro na online ɗin ba saboda ya sha yi mata magana akan Abdul.
“Hajiya wannan firar ta isa haka nan ki sauka!”
Saƙon Iro ne da ya shigo mata ta private yanzu,murmushi ta yi dan ta gane abin da yasa ya ce mata haka.
“Ƴallabai ba ka ga fira nake da mutane ba?”
Ta faɗa ta na danne dariyar da ke taso mata.
“Fira ko zance?”
Ibrahim ya faɗa cikin kishi,dan ya tsani ya ga ta na magana da Abdul mai kasuwa saboda tsohon saurin Husna ne.
“Fira dai ƴallabai.”
Husna ta ba shi amsa ta na dariya.
“To na ce a daina ta dan gaskiya bazan ɗauka ba!!”
Ya faɗa cikin tsantsan kishi.
“To ƴallabai yanzu me kake so ayi?”
Husna ta faɗa saboda ta ga ranshi ya ɓaci.
“Ki sauka haka nan!”
Ya faɗa cikin ba da umarni.
“Kai kuma sai ka tsaya amma ni ka koreni?”
Husna ta faɗa cikin jinjina ƙarfin hali irin na Iro.
“Ni na faɗa maki?”
Iro ya tambayi Husna.
Kafin ta ba shi amsa sai ta ga kiranshi ya shigo cikin ƙaramar wayarta, ɗauka ta yi cikin dariya ta ce,”kai Sweet Iro kishinka ya yi yawa.”
“Babu wani kishi da ya yi yawa.”
Ibrahim ya faɗa yana dariya shi ma.
“Yanzu in ba kishi ba meye wannan muna cikin fira kazo ka hana?”
Husna ta faɗa ta na murmushi.
“Dan kin raina ni ma a gabana kike fira da shi?”
Ibrahim ya faɗa da iyakar gaskiyarshi.
“Babu wani raini Sweet Iro ya man magana ta ya zan yi shiru na kyaleshi?”
“Ko ba ki shiru ba amma kuna gaisawa ai sai ki kyaleshi,ko da yake tsohuwar zuma ta motsa ai!”
Iro ya ida maganar cikin kishi.
“Aikuwa dai ka san da tsohuwar zuma ake magani!”
Husna ta faɗa cikin jin haushi saboda ba tun yau ba take faɗa ma shi ya daina yi mata haka ba.
“Ta ya zan manta Hajiya ai shi ne ma dalilin da yasa na tambaya.”
Ibrahim ya faɗa yana dariya.
“Hakan da kayi ya yi kyau haka ake so ai!”
Husna na faɗin haka ta kashe wayarta,kiranta Ibrahim ya yi amma ta ƙi ɗagawa,wasa-wasa sai da ya yi mata kira goma lokacin ta ɗauka ta na kumbura fuska.
“Lafiya kake takuraman?”
Ta faɗa cikin ɗaure fuska kamar yana gabanta.
“Ke dan ki raina ni shi ne za ki kasheman waya kuma ina kiranki amma ki ƙi ɗagaman kira!”
Shi ma ya faɗa cikin jin haushi.
“Amma so nawa ina gayamaka ka daina yi man maganar Abdul?”
Husna ta faɗi kamar za ta yi kuka.
“Kina tunanin zan daina bayan na ga yanzu sai shishshige maki ya ke yi!!”
Muryarshi kawai za ta tabbatar maka da tsantsan kishin dake ranshi.
“Ni dai idan ya yi man magana zan ma amsa shi.”
Husna ta faɗa da iyakar gaskiyarta dan wallahi in dai Abdul ya mata magana ba za ta yi shiru ba,dan wannan ma ai wulaƙanci ne.
“Zan yi maganin abun da kaina,ki turoman lambar Baba Abu zan yi magana da shi akai kuɗin nan kawai yanzu bayan sallar an sanya bikin!!”
Ibrahim ya faɗa cikin jin haushi.
“Kai Sweet Iro tun yanzu? Gaskiya a bari sai bayan sallar an kawo kuɗin.”
Husna ta faɗi kamar za ta yi kuka.
“Saboda ba ki sona koh? Kallonki kawai nake yarinya duk abin da kike yi yanzu,inda Abdul me ai da ba ki ce ba yanzu ba!”
Yana faɗin haka ya kashe wayarshi gaba ɗaya,ko da Husna ta kira sai ta ji ta switch off dole ta haƙura,shiru ta yi ta na tunani ganin babu mafita yasa ta nufi ɗakin Mama.
Zaune ta tadda Mama ta na yankan farce,shiga ta yi cikin ɗakin ta amshi abin yankan ta zauna ta cigaba da yanke ma Mama farcen, nan take sanar da Mama yadda suka yi da Iro.
Faɗa Mama ta rinƙa yi ma ta akan abin da ta aikata.
Haƙuri ta ba Mama akan hakan hakan ba za ta ƙara faruwa ba,kuma za ta bashi haƙuri.
Sai da ta kammala ma Mama gyaran sannan ta koma ɗakinta,wayarta ta jawo ta sake kiran wayarshi har lokacin kashe take dan haka sai kawai ta tura ma shi text na ban haƙuri tare da lambar Baba Abu.
Tun lokacin da Husna ta sauka daga online ba ta sake hawa ba sai dare wurin ƙarfe takwas,har lokacin kuma basu yi waya da Ibrahim ba.
Ta na hawa online har ta tafi inbox ɗin shi dan ta yi ma shi magana sai ta ga ana salati cikin group ɗin ƴan amana,cikin sauri ta shiga group ɗin saƙonnin ta fara dubawa gabanta na faɗuwa,ka sa jurewa ta yi sai kawai ta yi ƙasa gaba ɗaya abin da ta yi tozali da shine yasa ta sakin wayarta ƙasa ta fashe.

08105217201
Hussy Saniey.????
*RASHIN ADALCI 2021*

*NA*

*HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*PAGE 32*

TUNA BAYA
A ranar wata talata da misalin ƙarfe tara na dare, Husna ta hau WhatsApp sai ta ga wata ƙawarta Umma ta sanyata a wani group mai suna ƴan amana,shiga group ɗin ta yi ta yi sallama.
“Assalamu Alaikum yakuke fatan kuna lafiya,sunana Asma’u amma an fi kirana da Husna fatan zan samu karɓuwa a gareku.”
Babu daɗewa sai ga wata mai suna Fauzee ta amsa mata.
“Oyoyo Husna mun ji daɗin zuwanki gidanmu insha Allah za ki samu karɓuwa.”
Murmushi Husna ta yi dan ta ji daɗin yadda aka karɓeta.
“Masha Allah nima naji daɗin zuwana tun da ga shi har na samu ƙawa.”
“Haba ƙawata ai ba ki kaini jin daɗi ba duk gidan nan ban da Ƙawa amma yanzu ga shi Allah ya kawoman ke gaskiya naji daɗi dole yau a zo a ɗan yi celebration.”
Fauzee ta faɗa cikin alamun jin daɗi,dan lokaci ɗaya ta ji Husna ta ƙwanta mata a rai,dan haka ta cigaba da magana.
“Ƙawata dan Allah turo hotonki na gani nima ba ri na turo maki nawa.”
Fauzee Kabir ta faɗa ta na ƙoƙarin shiga gallery ɗin wayarta.
“To shi kenan nima ga shi nan zan turo maki ƙawata.”
Husna ta faɗa ta na mamakin yadda lokaci ɗaya sabo ke neman shiga tsakaninsu,dan ita ko group ba ta taɓa shiga ba wannan shi ne shigarta group na farko a duniyar WhatsApp.
Hoton ta tura haɗe da faɗin,”ƙawata ga hoton nan.”
Bayan minti biyu da tura hoton sai ga Fauzee ma ta turo na ta, buɗewa Husna ta yi a fili ta furta masha Allah saboda ba ƙarya Fauzee ta yi kyau.
“Masha Allah ƙawata irin wannan kyan gaskiya na samu kyakkyawar ƙawa!”
Fauzee Kabir ta faɗa cikin jin daɗi dan dagaske ba ƙarya Husna ta yi mata kyau duk da kasancewarta baƙa amma baƙin mai kyau ne.
“Kai ƙawata kin sanya naji kunya ina kyan a nan?”
Husna ta faɗa ta na murmushi kamar Fauzee Kabir na a gabanta.
“Haba ƙawata da gaske kin yi kyau.”
Fauzee ta faɗa cikin tabbatar ma da Husna ta yi kyau.
“To nagode ƙawata amma dai kin fi ni kyau.”
Husna ta faɗa da iyakar gaskiyarta.
“Haba ƙawata ta ina nafi ki kyan gaskiya ke ba ki ma san kyau ba.”
Fauzee Kabir ta faɗa ta na dariya saboda so take firarsu ta yi tsayi.
“Haba ƙawata ga ma zagina ke fa farace kuma kin san farar mace alkyabbar mata dan kowa ya san na kin fini kyau.”
Husna ta faɗa saboda ita dai ta san Fauzee Kabir ta fita kyau sosai.
“Malama kin fa dameta da magana ki barta ta huta mana,baƙuwa sannu da zuwa muna maki barka da kasancewar ki a gidan ƴan amana.”
Wani ya yi maganar wanda ta ga sunanshi ya sanya Ibrahim Muhammad.
“Kai kuma ina ruwanka Iroro daga zuwanka za ka wani sako mana baki!”
Fauzee Kabir ta faɗa cikin tsokana.
“Nagode kwarai nima naji daɗin kasancewata a cikinku.”
Husna ta faɗa ta na murmushi saboda har ga Allah ta lura mutanen gidan su na da kirki.
“Ke zan sanya ayi maki ɗaukar amarya idan ba ki kiyayeni ba, baƙuwa bakomi mu ma mun ji daɗi sai dai kiyayi wannan yarinyar dan bata girmama manyanta shi ya sa zamu tillata ta taga dan haka ka da ki biye mata.”
Ibrahim ya faɗa cikin son tunzura Fauzee Kabir.
“Ƙawata kyaleshi ka da ki biye abin da yake faɗa kin ga abin da nake gayamaki ƴan gidan nan sun takuraman sai yanzu da ki kazo gaskiya naji daɗi ni ma na samu mai tare man ko Darling?”
Fauzee ta faɗa cikin alamun a tausayamata.
“Kar ki damu My Fauzee daga yau zan rinƙa tare maki kin ji koh.”
Husna ta faɗa ta na dariyar dramar Fauzee da Ibrahim.
“Kar ki yadda da abin da take faɗa Sweet Husna.”
Ibrahim ya faɗa dan ya tunzura Fauzee.
“Danƙari! Wai sweet jama’a kun ji wani nai man suna koh? My Husna kar ki biyema duk abin da zai faɗi a hankali za ki gane irin takurar da ake man.”
Fauzee Kabir ta faɗa cikin sigar zama kalar ban tausayi.
“Kalleta kamar wata salaha!”
Ibrahim ya faɗa cikin dariya.
“Gaskiya ka fara takurama Ƙawata ban son haka!”
Husna ta faɗa ma Ibrahim ta na ɗaure fuska.
“Ni ka ga tafiya ta sai dai kayi da wata ba dai ni ba!”
Fauzee Kabir ta faɗa tare da sauka daga online.
“Sweet Husna kar ki shiga cikin wannan maganar ki kyaleta.”
Ibrahim ya faɗa yana dariya.
“Ni dai gaskiya ban ji daɗi ba yanzu ka ga ka korar man ƙawa.”
Husna ta faɗa saboda da gasken ba ta ji daɗin tafiyar Fauzee ba.
“Kyale wannan yarinyar za ta dawone ai.”
Ibrahim ya faɗa yana dariya saboda ganin yadda Husna ta damu.
“Ni ma tafiya zan yi sai da safe bacci nake ji.”
Husna ta faɗa saboda sai ta ji duk group ɗin ya isheta.
“Saboda tafiyar waccan yarinyar shi ne za ki tafi?”
Ibrahim ya tambayi Husna saboda ya ga da gaske tafiyar za ta yi.
“A’a ba saboda haka bane bacci nake ji sai da safe.”
Husna na faɗin haka ko amsar Ibrahim ba ta tsaya jira ba ta kashe data,har ta kwanta kuma sai ta ji babu daɗi yanda ko sallama basu yi da Fauzee ba,da wannan tunanin bacci ya yi gaba da ita.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button