RASHIN ADALCI Complete Hausa

08105217201
Hussy Saniey.????
*RASHIN ADALCI 2021*
*NA*
*HUSSY SANIEY*
*____________________________________*
*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*PAGE 33*
Washe gari gaba ɗaya Husna ba ta samu zama ba dan haka sai ba ta samu hawa WhatsApp ba,da marece wurin ƙarfe huɗu sai ga kira ya shigo wayarta,ko da ta duba baƙuwar lamba ta gani kamar ba za ta ɗaga ba sai kuma ta ɗaga.
“Ko dai kina tsoron a saceki ne?”
Wata murya mai cike da barkwanci ta jiyo a cikin kunnenta,ɗan jim ta yi domin ta na so ta gane mai magana, jin ta yi shiru yasa daga chan bangaren aka ƙa ra sakin dariya,”Oh Ni! Fauzee ashe haka ƙawata take da tsoro,idan kina haka ta y zan yi tunanin za ki rinƙa tareman faɗa idan na jawo?”
Sai yanzu Husna ta gane mai magana dan haka ta yi murmushi tare da ƙara dafe wayar a kunnenta,”ba tsoro naji ba Ƙawata na dai tsaya ne dan na gane mai magana amma ba dan wani abu ba.”
“Kai Ƙawata ke dai kawai kin ji tsorone kar ki wani damu ni ce,yakike yau na ga ba ki hau WhatsApp ba shi ne nayi tunanin na kira ki naji ko lafiya Allah yasa dai ban takura maki ba?”
Fauzee Kabir ta faɗa ta na murmushi dan ita Allah ya yi ta irin mutanen nan ne masu fara’a.
“Allah sarki Ƙawata lafiya lau yau dai na ɗan yi busy ne shi yasa ki ka ji shiru da ma zuwa anjima nake tunanin hawa.”
“Allah sarki sannu ya kike?”
Fauzee Kabir ta faɗa cikin nuna kulawa, saƙonta kuwa yaje inda aka tura shi dan Husna ba ƙaramin daɗi ta ji ba da kiran da Fauzee ta yi mata,dan haka ta ƙawata fuskarta da murmushi tamkar suna ganin juna.
“Lafiya lau Ƙawata fatan ke ma kina lafiya? gaskiya bazan iya ɓoye maki ba naji daɗin kiran nan da ki kayi man sosai wallahi nagode Allah ya bar zumunci.”
“Haba…haba! meye abin godiyar dan Allah ki ma yi shiru…yanzu kenan idan da ni ce ban hau ba ke baza ki iya kirana ba?”
Fauzee Kabir ta faɗa ta na ɗan ɗaga sauti, girgiza kai Husna ta yi kamar ta na gaban Fauzee ta ce,”haba ƙawata da gudu zan kira ki kuwa.”
“Yauwa yanzu naji batu mai daɗi Ƙawata.”
Fauzee Kabir ta faɗa ta na dariya,ita ma Husna murmushi ta yi ta gyara zaman ta dan ta ji daɗi.
“Ai ni na manta ma fushi nake da ke shi ne jiya kika gudu muna cikin magana.”
“Ke wallahi bacci naji sosai jiyan shi ne kawai dalili amma kiyi haƙuri.”
Fauzee ta faɗa cikin sanyin murya.
“Nayi tunanin saboda zuwan Ibrahim kika gudu!”
Husna ta faɗa dan ita abun da ta yi tunani kenan.
“Tab! Wai kina nufin Iro lalle ai wallahi ba dan shi na tafi ba,ke Iro fa bai da matsala dan kin ji ina faɗin ya takuraman?wasa nake ma shi yana da hankali kuma ya na da daɗin zama sosai ke ma nasan nan gaba za ki gane haka.”
Fauzee ta faɗa ta na dariya dan ita da gaske dariya Husna ta bata da ta ce saboda Iro ta gudu.
“Allah sarki nima na lura yana da kirki.”
Husna ta faɗa cikin sanyin murya.
“Eh gaskiya yana da hankali dan ni kin ga abokin saurayina ne,amma gaskiya muna wasa da shi sosai bai da matsala wallahi ke ma nasan za kiji daɗin zama da shi sosai.”
Fauzee Kabir ta faɗa ta na murmushi dan har lokacin dariyar ba ta saketa ba.
“Ai da ma za ki ga wani ya iya mu’amala da mutane.”
Husna ta faɗa dan ba ta san komai game da group ɗin ba,tun da ita jiyane aka sanyata.
“Eh hakane gaskiya to shi ma bai da matsala, Husna wane gari kike?”
Fauzee ta juya akalar maganar ta zuwa ga tambaya.
“Katsina nake ke fa?”
Husna ta faɗa a taƙaice.
“Wayyyoooooo Ƙawata mun samu ban-banci ni Kaduna nake,gaskiya naso ace Kaduna kike da cikin satin nan sai mun haɗu,amma kin ga yawancin ƴan group ɗin duk ƴan nan Katsina ne,kun rinƙa haɗuwa ana zumunci!”
“Da ma ana haɗuwa ne yan group ɗin?”
Husna ta tambayi Fauzee saboda ita dai ba ta san ana haka ba.
“Sosaima duk sallah ƴan group ɗin na haɗa partyn sallah haka kuma idan wani abu ya samu wani suna zuwa!”
Fauzee ta faɗi cikin farin ciki,mamaki sosai Husna ta rinƙa yi,ganin Fauzee ta ɗan damu akan rashin kasancewar su gari ɗaya yasa Husna jin ƙaunarta a cikin ranta.
“Kai ban so haka ba nima naso ace Kadunar nake amma bakomi wata rana sai ki ga mun haɗu.”
Cikin kulawa Husna ta faɗi dan ta lura yanayin Fauzee ya ɗan chanza.
“Hakane kuma ai insha Allah wata rana zamu haɗu,ke ka da na cika ki da surutu da yawa,amma dan Allah da kin gama abin da kike ki hau saboda ban san na sake hawa na ga ke ba ki hau ba sai anjima.”
Fauzee ta faɗa ta na dariya saboda ta ji daɗin firar da suka yi da Husna
“To shi kenan insha Allah da na ida zan hau sai anjima.”
Husna na faɗin haka ta kashe wayarta,shiru ta yi ta na mamakin yadda har sabo ya fara shiga tsakaninsu.
08105217201
Hussy Saniey.????
*RASHIN ADALCI 2021*
*NA*
*HUSSY SANIEY*
*____________________________________*
*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*PAGE 34*
Husna na katse wayar mamakin kirkin Fauzee take ta yi daga haɗuwa group amma kalli kalar mutuncin da ta yi mata,gaskiyar Umma (wadda ta sanyata a group ɗin)da ta ce duk masu hankali ta sanya a group ɗinta.
Ɗakin Mama Husna ta shiga,zaune ta iske Mama na linkin kayan wanki,gefen Mama ta samu wuri ta zauna,wasu kayan ta ɗauka ta fara linkewa ita ma.
Ɗagowa ta yi ta ga Mama sai kallonta ta ke yi, murmushi Husna ta yi dan ganin yadda Mama ke bin ta da kallo.
“Kai Mama kamar na chanza maki sai kallona kike!”
Husna ta faɗa tare da ɗaukar kayan da Mama ta linke,wadrop ta buɗe ta fara ƙoƙarin sanya kayan ciki.
“Gani na yi kin shigo sai murmushi kike ke ɗaya ko dai ta samu ne?
Mama ta faɗa ba tare da ta kalli inda Husna ta ke ba,rigar da ta linke ta aje a gefenta,wata ta ɗauka ta na linkewa.
“Mama wallahi wani mutunci aka yi man wanda nake ta mamakinshi.”
Husna ta faɗa bayan ta saka kayan da ta ɗauka cikin wadrop.
“Mutuncin kuma Husna wa ya yi maki toh?”
Juyowa Mama ta yi ta na kallon Husna tare da tsayawa da linkin kallabin da ke hannunta.
“Mama shekaran jiya ba na faɗa maki mun haɗu da Umma a gidan Kadarko ba?”
Husna ta faɗa ita ma tare da maido hankalinta gaba ɗaya akan Mama.
Jinjina kai Mama ta yi ta ce,”eh kin faɗa meyafaru kuma.”
“To ranar ne take faɗaman za ta sanyani a group ɗinta mai suna ƴan amana,da har na ce mata a’a sai ta ce ai group ɗin duk masu hankali ne a ciki,to jiya da daddare bayan naje zan kwanta sai na hau WhatsApp,ina dubawa kuwa sai na ga ta sanyani a group ɗin,sai ga shi kuwa na tabbatar da maganarta wallahi Mama mutanen na da kirki sosai.”
Husna ta faɗa ta na zama gefen gadon Mama,sai ya kasance su na fuskantar juna ita da Mama.
“Kai Husna cikin daren jiya kaɗai har kin tabbatar da su na da kirki?”
Mama ta faɗi ta na cigaba da linke kayanta.
“Allah Mama su na da kirki sosai kin san me yasa na ce haka Mama?”
Husna ta faɗa ta na kishingiɗawa jikin katakon gado, fuskarta ɗauke da murmushi wanda kallo ɗaya za ka yi mata kasan ta na cikin farin ciki.
“A’a sai kin faɗa Husna ina saurarenki.”
Mama ta faɗa ita ma fuskarta da murmushin saboda ganin ɗiyarta mace ƙwalli ɗaya tal(Husna ita kaɗai ce mace a gidansu sauran duk mazane) a duniya ta na cikin farin ciki.
“Mama ba ri na faɗamaki dan ki tabbatar ke ma.”
Husna ta faɗa ta na dariya ganin yadda Mama ke murmushi ita ma.
“Ina jinki.” Mama ta faɗi har lokacin akwai murmushi a fuskarta.
“Mama jiya bayan na ga group ɗin sai na shiga nayi sallama,da yin sallamata ba’a ɗauki wani tsawon lokaci ba sai ga wata Fauzee Kabir ta amsa man,nan muka ɗan yi magana da ita,ta na nunaman yadda ta ji daɗin zuwana a gidan,wai ta samu ƙawa saboda gidan ba ta da Ƙawa,kin san wani abu Mama?”
Husna ta faɗa ta na kallon Mama.
Girgiza kai Mama ta yi fuskarta cike da murmushi,dan ta ƙosa Husna ta ida faɗa mata labarin.
“Yauwa Mama yanzu kuwa zan faɗa maku.”
Husna ta faɗa tare da tashi daga kishingiɗawar da ta yi ta koma zaune,ba tare da ta jira Mama ta yi magana ba ta cigaba da maganarta.
“Muna cikin magana da Fauzee Kabir ta na faɗaman irin yadda ta ji daɗin zuwana gidan dan duk takura mata ake babu mai tare mata,sai kuwa ga wani shi kuma sunanshi Ibrahim Muhammad, Mama ya na zuwa shi ma sai ya fara nuna yadda yaji daɗin zuwana gidan,amma Mama kin ga yadda yake jan Fauzee wasa har sai da ta gudu,gaskiya Mama su na da kirki sosai jiya kaɗai Mama amma na ga ya ba da ƙoƙarinsu.”
Husna ta ida faɗar maganar fuskarta ɗauke da murmushi,zuru ta yi ma Mama ta na jiran jin abin da Mamar za ta faɗa.
Gyara zamanta Mama ta yi ta na kallon Husna,nisawa ta yi sannan ta ce,”Husna ban hana ki mu’amala da mutane ba amma Husna ki rinƙa kiyayewa kin san zamani ya chanza yanzu ba’a yadda da mutane sosai.”
“Hakane Mama kin san ina bakin ƙoƙarina wurin kiyayewa amma insha Allah zan ƙara, ɗazun Fauzee Kabir ta kirani wai ta ga duk yau ban hau online ba.”
Husna ta ƙarasa maganar fara’ar da ke fuskarta na raguwa.
Ganin haka yasa Mama sakin murmushi dan ta kwantar ma Husna da hankali sai ta ce,”Allah sarki gaskiya ta na da kirki Allah ya yi mana jagora Allah ya tsaremanaku a duk inda ku ke,ku ma sai ku ƙara tsare mutuncin kanku.”
Mama na faɗar haka ta cigaba da linkin kayanta,ganin kamar Husna ta shiga damuwa yasa Mama ta rinƙa jan ta da fira har sai da ta ga ta saki jikinta sun cigaba da aikinsu.
Su na aikin suna fira har suka ida,sai lokacin Husna ta yi ma Mama sallama ta koma ɗakinta