HAUSA NOVELRASHIN ADALCI Complete Hausa

RASHIN ADALCI Complete Hausa

 

08105217201
Hussy Saniey.????
*RASHIN ADALCI 2021*

*NA*

*HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*PAGE 36*

“Na amince da me?”
Husna ta faɗa cikin sauri dan sai yanzu ta gane katoɓarar da ta yi tun farko na amincewa da abin da zai faɗa.
Dariya Ibrahim ya rinƙa yi har da ƙyaƙyatawa dan ya lura da Husna ta ji tsoro
“Meye na saurin magana Hajiya ki bari na faɗa mana dan kin san dai ba ki isa ba dai ki ƙi amincewa!”
Girgiza kai kawai Husna ta yi cikin shan ƙamshi irin kar ya raina ta ɗin nan ta ce,”ina jinka faɗi!”
“Yauwa jaruma haka nake son ji.”
Ya faɗa dan ya lura ƙarfin haline kawai yasa ta maganar.
“Faɗi kawai Malam ina son kwantawa dare ya yi.”
Husna ta faɗa tare da ɗaure fuska tamkar a gabanshi take.
“Kwantar da hankalinki ba wani abu bane kawai so nake daga yau ki rinƙa kirana da Sweet Ibrahim kin ga ni ma da Sweet nake kiranki wannan shi ne kawai sharaɗin!”
Ibrahim ya faɗa yana dariya dan yasan ya gama wana ta,shi kanshi ya rasa dalilin da yasa yake so ta rinƙa kiranshi da haka,duk da jiyane ya santa amma hakanan yake jin ta har cikin ranshi.
“Kin yi shiru Malama ke nake saurare kin dai san ba ki isa ki ƙi amincewa ba dan haka ko a gaban waye haka za ki rinƙa kirana da shi.”
Ya sake faɗa ganin ta yi shiru duk da kuma ya ga ta duba maganar ta shi.
“To shi kenan na amince amma kai ma kar ka sake takurama Ƙawata.”
Husna ta faɗa ta na murmushi dan ba ta yi tunanin abin da zai faɗa ba kenan.
“To kin ga idan ki kayi haka to kin wanke ƙawarki.”
“Ba damuwa na amince bacci nake ji zan kwanta.”
Husna ta faɗa ta na hamma dan da gasken baccin take ji,dan ita ba ma’abociyar chat ɗin tsakar dare ba ce duk rintsi ba ta wuce ƙarfe sha ɗaya amma yanzu har sha biyu ta yi.
“To shi kenan ki yi bacci mai daɗi.”
Ibrahim ya faɗa cikin jin daɗin firar da suka yi,ji yake kamar sun shekara da sanin juna.
“To nagode sai da safe.”
Husna na faɗar haka ta kashe datarta ta kwanta,babu daɗewa bacci ya yi awon gaba da ita.
Tun da Husna ta kwanta ko sau ɗaya ba ta farka daga baccin ba,duk da kasancewar ta na yawan tashi shan ruwa cikin dare amma yau ko sau ɗaya ba ta tashi ba,hakan ya farune har da gajiyar da ta yi.
Chan cikin bacci ta ji wayarta da ta sanya ƙarƙashin fillo ta na vibration,ko idanuwanta ba ta buɗe ba ta shiga laluben wayar,cikin sa’a kuwa ta jawota ko duba sunan waye ba ta yi ba ta kanga wayar a kunne.
“Hajiya ki tashi ki yi sallah ka da lokacinta ya wuce kina ta bacci.”
Wata baƙuwar murya ta ji ta faɗa,dan ita dai a iya saninta ba ta san wani mai irin wannan muryar ba.
“Hajiya ko baccin bai isheki ba?”
Aka sake faɗa daga chan bangaren.
Cikin muryar bacci Husna ta ce,”wacce sallah kuma yanzu?”
“Sallar Asuba ko kin yi?”
Janye wayar Husna ta yi daga kunnenta dan so take ta gane wake magana,ita dai babu wanda ya taɓa kiranta da asuba bare ta yi tunanin ko shi ne,ganin lambace babu suna ya sanya ta maida wayar a kunne.
“To shi kenan na tashi yanzu zan yi.”
Ta faɗa ta na ƙoƙarin tashi daga kwancen da take.
“Yauwa ya kamata dai nima ga liman nan zai ta da Sallah sai anjima.”
Yana faɗin haka ya kashe wayarshi.
Tsurama wayar Husna idanuwa ta yi cikin ranta ta na mamakin waye wannan ya kirata,dan ita har a lokacin ba ta gane ko waye ba.
Kallon agogon da ke manne a bangon ɗakinta ta yi,ganin lokacin sallah ya yi yasa ta miƙewa ta nufi toilet,cikin ranta ta na godema ko ma waye ya tada ta dan tasan da ƙila yau sai ta makara wurin yin sallah,ko kuma idan masallacin ƙofar gidansu an tada sallar ta ji.
Cikin ranta ta na ƙara jinjina irin baccin da ta yi yau,dan ita zai yi wuya ta kwanta ba ta farka ba.
Da waɗannan tunane-tunanen ta yi alwallah ta fito,abin sallah ta shimfiɗa ta kabbara sallah.

08105217201
Hussy Saniey.????
*RASHIN ADALCI 2021*

*NA*

*HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*PAGE 35*

Da misalin ƙarfe goma na dare Husna ta gama duk wani abu da ya zame mata al’ada,sai lokacin Husna ta samu zarafin buɗe Data, WhatsApp ta shiga sai da ta yi jira na ƴan mintoci saboda saƙonnin dake shigowa,bayan gama shigowar saƙonnin kai tsaye group ɗin ƴan amana ta shiga,nan ta iske dai babu wata magana mai yawa,firar duk Fauzee Kabir da Ibrahim Muhammad ne suka ɗan yi wasa,sai kuma maganganun wasu mutane da ta gani,dubawa ta yi ta ga Fauzee Kabir ba ta online dan ha sai ba ta ce komai ba ta fita daga cikin group ɗin.
Hankalinta ta mayar wurin chat da take yi da mutane a private,ta na cikin chat ɗin ne wani saƙo ya shigo mata, ba ta samu damar dubawa ba Saboda maganar da take yi da wata ƙawarta,bayan minti biyar da shigowar saƙon aka sake turo wani.
Dan haka ta yanke shawarar dubawa,ta na buɗe saƙon sai ta ga sallama ce aka fara yi mata daga baya kuma aka turo mata wai ta tafi taje ta kwanta.
Mamaki ya kamata dan haka ta duba sunan wanda ya turo mata saƙon ganin ko waye ya sanyata yin murmushi.
Kafin ta samu damar ba da amsa wani ya ƙara shigowa,”Hajiya da ma ke matsoraciyace ashe?”
Ita dariya ma ya bata,dan haka sai ta tura emojin nan na dariya sai ta ce,”meye abin da zan ji ma tsoron toh?”
“Ga shi kin ji tsoron kuwa,idan kuma ba tsoro kika ji ba faɗaman me ya hana ki amsa sallamata?”
“Haba dai ni babu tsoron da naji,wai wake magana ne?”
Husna ta yi tambayar duk da ta gane ko waye tun da har group ɗin da suka haɗu sai da ta duba ta gani.
“Kam ina nufin ba ki ma gane da wa kike magana ba?”
Ya faɗa duk da yasan basu taɓa chat ba kuma ba ta da lambarshi,amma ai yana tunanin ta na iya duba sunanshi da kuma daga inda suka haɗu.
“Ta ya zan gane bayan bansan ko waye ba?”
Husna ta mayar masa da tambayar da ya yi mata ta na murmushi.
“Hmmm! Kai Sweet Husna ka da dai wannan yarinyar ta fara koyamaki halinta?”
Ya faɗa da tabbacin yanzu za ta gane ko waye shi.
“Wacce yarinya kenan?”
Husna ta faɗa ta na dariya dan ta fahimci wa ya ke nufi, ɗayan gefen kuma ta na mamakin sunan da yake kiranta da shi.
“Fauzee Kabir mana dan naga yanzu ta zama ƙawarki.”
Ya faɗa dan yasan ya zuwa yanzu ta gama gane daga inda yake.
“Gaskiya kana takurama Ƙawata!”
Husna ta yi maganar cikin son tsokano shi.
“Yarinyar ce ta raina manyanta shi yasa nake takura mata.”
Shi ma ya maida mata amsa yana murmushi tamkar a gabanta yake.
“A’a gaskiya ka daina takurama Ƙawata ko da yake bansaniba ko ku kalar taku salan soyayyar kenan?”
Husna ta faɗa duk da Fauzee Kabir ta faɗa mata abokin saurayinta ne,hakanan ta ji ta na son jin abin da zai faɗa ma ta shi ma.
“Ke waye saurayin na ta gaskiya Sweet Husna ba dan ke ki kayi wannan maganar ba da na ɗauki mataki mai tsauri!”
Ibrahim Muhammad ya faɗa yana dariya dan ya lura ita ma Husnar ta iya wasa.
“To ba gaskiya na faɗa ba ai da anga wannan salon naku ansan na masoyane.”
Husna ta faɗa cike da barkwanci.
“Ke da gaske ba budurwata ba ce asalima yarinyar abokina ce kuma yana nan a cikin group ɗin,ke ma za ki san shi sunanshi Sardauna amma an fi kiranshi da Abba.”
Ibrahim ya faɗa cikin son ta yadda da abin da yake faɗa.
“Allah sarki! Allah ya barsu tare,to gaskiya ka daina takuramata ka ga jiya ma muna cikin fira ka zo ka korar man ita!”
Husna ta faɗa da alamun damuwa a tare da ita.
“To tun da naga kin damu zan daina takuramata amma sai da sharaɗi ɗaya idan kin amince babu matsala?”
Ya faɗa yana dariya dan shi kaɗai yasan wane tarko zai ɗana mata.
Ba tare da damuwar komai ba Husna ta ce,”ina jinka faɗi kawai na aikata.”
“Kin tabbata za ki aikata?”
Ibrahim ya tambayi Husna fuskarshi ɗauke da murmushin mugunta.
“Me kake ji ma wani ɗar kawai ka faɗa na aika.”
Husna ta faɗa cikin nuna irin ta kai ɗin nan.
“Kin tabbata ka da sai na faɗa kuma ki zo ki ce a’a dan bazan yadda ba?”
“Kar ka ji komai kawai ka faɗi ni kuma na aikata?”
Husna ta sake tabbatar ma shi da maganarta.
“Ba aikatawa za kiyi ba kawai amincewa za kiyi?”
Ya faɗa yana dariya dan yasan ya sanya mata tarko da baza ta iya bijirema buƙatar shi ba.
“Kar ka wani damu faɗa na amince,sai wani zagaye-zagaye kake yi ko kana shakkar ƙawance mune?”
Husna ta faɗa ita a dole ga mai ƙawa.
“A’a bana shakka yanzu dai za ki tabbatar man da abin da kika faɗa,dan haka so nake ki amince da….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button