HAUSA NOVELRASHIN ADALCI Complete Hausa

RASHIN ADALCI Complete Hausa

08105217201
Hussy Saniey.????
*RASHIN ADALCI 2021*

*NA*

*HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

 

*PAGE 37*

Bayan Husna ta dawo daga gaidosu Mama,kan gado ta koma domin ta samu ta rage baccin da ke idanuwanta,har bacci ya fara daukarta ta ji wayarta ta fara vibration, tsaki ta yi dan baccine a idanuwanta sosai,ko da ta ɗauki wayar lambar da aka kira ɗazun ce ta sake gani.
Shiru ta yi ta na tunanin ko za ta iya gane wake da wannan lambar,ganin kiran na niyyar tsinkewa ba ta tuna komai ba yasa ta yanke shawarar ɗauka.
“Assalamu Alaikum fatan kin yi sallah lafiya?”
Runtse idanuwanta ta yi lokacin da muryar mutumin ta do ki dodon kunnenta,har cikin ranta ta ji maganar dan ba ƙarya in dai fannin muryane nan dai Allah ya ba shi ita,sai dai fatan ya yi amfani da ita ta hanyar da al’umma zasu amfane.
“Ko baccin ki ke har yanzu.”
Maganar da ya sake yi ce ta maidota cikin hankalinta,ajiyar zuciya ta sauke wadda har sai da ya jiyo sautinta a cikin kunnuwanshi.
“Kai Sweet Husna haka ki ke da nauyin bacci da ma”
Muryarshi ta do ki majiyar kunnuwanta a karo na ukku,dan haka ta yi ƙarfin halin sauke wani gwauron numfashi,dan sai yanzu ta gane da wanda take magana,muskutawa ta yi ta gyara kwanciyarta.
“Eh yanzu na koma,ba wani nauyin bacci gajiyace wallahi ga jiya ka hanani bacci da wuri,ni ban taɓa kai ƙarfe sha biyu a online ba sai jiya da ka tsareni,ka ga kuwa ai dole nayi ramuwar baccin?”
Ta faɗa cikin muryar da ka ji kasan bacci da gajiya sun gama yi ma wanda ya kasance ma mallakinta rubdugu.
Murmushi ya yi wanda har sai da ta jiyo sautin fitarshi a kunnuwanta ya ce,”kai Sweet Husna Kar dai ki faɗaman ke ragguwace”
Ya ida maganar cikin salon tsokana.
Ɓata fuska Husna ta yi tamkar yana kallonta ta ce,”Allah ni ba ragguwa ba ce,dan dai kawai ba ka san aikin da nayi ba a jiya da baka faɗi haka ba.”
Cikin kwantar da murya ya ce,”wasa nake maki Sweet Husna ya zan yi na ce maki ragguwa bayan nasan ke jarumace.”
Ya ƙarasa maganar cikin yanayi na mai son yin dariya amma kuma ya ƙi barin dariyar fitowa.
“Yauwa Sweet Iro!”
Husna ta faɗa cikin fara’a wadda har sai da ya gane.
“Ɗan sake faɗar sunan da ki ka faɗi yanzu!!”
Ya faɗa dan a bazata sunan yazo ma shi,duk da shi yace ta rinƙa kiranshi da shi amma bai yi tunanin za ta faɗa ba,gaskiya ya ji daɗin sunan sosai.
“A’a ba sai na ƙara faɗi ba ai ka ji abin da na ce.”
Husna ta faɗa ta na turo bakinta gaba cikin alamun jin kunya,dan ita kanta sai da ta faɗa lokacin kuma wata kunya ta lulluɓeta.
“Dan Allah ki sake faɗa kin ji Sweet Husna sau ɗaya kawai za ki sake!”
Ya faɗa cikin sanyin murya da kuma lallashi.
“Sweet Iro!”
Ta faɗa ta na rufe idanuwanta sai kuma ta dage bakinta kamar wadda ba ta so faɗa ba.
“Kai gaskiya ban taɓa jin wanda ya kirani ba na ji kiran ya ratsa man ɓargo ba irin wannan kiran da ki kayi man ba,nagode kwarai sweet Husnata,sai dai wani abu guda kuma ki daina kirana da Iro dan waccan yarinyar kaɗai ta sanya man shi.”
Ya faɗa cikin jin daɗi dan jin shi yake wani nishaɗi na shigarshi ta kowacce gaba dake a jikinshi,dan haka ya sake bajewa akan gadonshi dan ya ji daɗin firar.
“A’a ni dai da Iro zan rinƙa kiranka,ita kuma ai da Iroro take kiranka ka ga akwai banbanci kenan koh?”
Husna ta yi maganar cikin shagwaɓa dan ba ƙarya ita kanta ta na jin daɗin wannan yanayin da take ciki.
“Eh akwai banbanci sosai,amma me yasa ba za ki kirani da Ibrahim ɗina ba?”
Ya faɗa yana ƙara jawo bargon da yake gefenshi,lulluɓewa ya yi har kan jikinshi.
“Na fi jin daɗin sunan ai.”
Husna ta faɗa a takaice,ita kanta ba ta san me yasa take son kiranshi da Iro ba.
“To ki daina gaskiya.”
Ya faɗa yana murmushi.
“A’a bazan iya dainawa ba ina jin daɗin sunan.”
Husna ta faɗa ta na sakin dariya ƙasa-ƙasa.
“To shi kenan ki cigaba da faɗa in dai hakan zai sanyaki cikin farin ciki na amince ki rinƙa kira.”
Ibrahim ya faɗa cikin wata irin murya wadda shi kanshi bai san yana da ita ba,ai kuwa muryarshi ta yi tasiri wurin Husna dan har tsakar kai take jin maganganun shi.
“Ko dai da gaske ba ka so ina kiranka da shi na daina?”
Husna ta faɗa cikin sanyin murya.
“A’a ina so ki cigaba da kirana da shi tunda kina so nima naji ya man daɗi sosai ina godiya!”
Ibrahim ya faɗa cikin wani yanayi mai wuyar fassarawa,shi kanshi ba zai iya gane a yanayin da yake ba kawai dai yasan yana cikin wani shauƙine.
“To shi kenan zan rinƙa kiranka da Sweet Iro.”
Husna ta faɗa ta na sakin hamma,jin hammarta ya ankarer da Ibrahim bacci take ji.
“To shi kenan Nagode ki kwanta kiyi bacci nima zan ɗan kwanta zuwa anjima sai na fita shago.”
Ya faɗa ba dan ya gaji da firar ba sai dai kawai yanda ya ji ta na hammane yasa dole zai haƙura.
“To sai anjima nagode kwarai Allah yasa ka da alkhairi.”
Husna na faɗar haka ba ta tsaya jiran jin abin da zai faɗa ba ta kashe wayarta,rufe idanuwanta ta yi da addu’ar bacci ya yi gaba da ita.

08205217201
Hussy Saniey.????
*RASHIN ADALCI 2021*

*NA*

*HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*PAGE 38*

Tun daga wannan ranar Husna da Ibrahim su ka yi wani irin sabo mai ban mamaki,wanda ya kai duk in ɗaya ya hau online to ɗayan ko ya hau ba zai yi chat ba,zai ji babu daɗi har sai ɗayan yazo,duk ƴan gidansu Ibrahim sun san Husna haka ita ma gidansu an san Ibrahim.
Group ɗin ƴan amana group ne wanda ya haɗa mutane waɗanda suka san darajar kansu,shi yasa lokaci ɗaya Husna ta zama tauraruwa a cikin gidan,dan duk ranar da ba ta hau online da wuri ba an rinƙa jajenta kenan daga ƙarshe har sai an samu wani ya kirata,duk mutanen gidan suna girmama junansu ba kin gwargwado,shi yasa Husna ta yi sabo dasu sosai,ko a gida Husna ba ta da labarin ba dawa sai na ƴan amana.
Fauzee Kabir kuwa ita ce babbar ƙawar Husna a cikin group ɗin,sai Maryam Hassan wadda suke yawan gaisawa a cikin group ɗin.
A hankali shaƙuwar da ke tsakanin Ibrahim da Husna ta rikiɗe ta zama soyayya,duk ƴan group ɗin kowa yasan da wannan soyayyar,dan haka kowa yake masu fatan alkhairi,mutane da yawa su na addu’a akan Allah ya ɗorar da wannan soyayya,dan yanzu dai Husna da Fauzee kowa yana burin su auri samarinsu na gidan,a cewarsu wai ayi komai tuwona mai na.
Amincin da ke tsakanin Fauzee da Husna ya kai har iyayensu suka haɗa,duk da ba gari ɗaya su ke ba amma su na gaisawa sosai.
Wata rana aka yi wani baƙo a cikin group ɗin ƴan amana mai suna Abdullahi amma Abdul ake kiranshi.
Abdul mutum ne mai dizgi da son nuna shi wani ne,hakan yasa wata rana su kayi rigima da Fauzee Kabir a cikin gidan, wannan rigimar ita ta ɗaga hankalin kowa da ke gidan,inda Fauzee ta yi zuciya ta bar magana a gidan ƴan amana.
Nan ne fa aka rigima mai girma ta ɓarke a tsakaninsu inda wasu ke cewa sai dai a fidda Abdul daga gidan,nan wasu kuma su ka nuna ba su yadda ba.
Wannan abu shi ya kawo saɓani sosai,dalilin wannan rigimarce har aka samu matsala tsakanin Husna da Ibrahim,sai kuma gidan ya ida rikicewa inda Husna ta yi iƙirarin rabuwa da Ibrahim.
An sha rikici sosai da ƙyar Umma(wadda ta buɗe group ɗin)ta samu ta shawo kan matsalar ta hanyar cire Abdul daga gidan.
Wannan hukuncin ne yasa hankalin mutane ya kwanta,amma dai Husna da Ibrahim basu shirya ba,dan tsakaninsu kowa na taƙama da zuciya.
Wannan rabuwar da su kayi ne ya sanya Abdul Mai kasuwa yazo ya nuna yana son Husna,ba ta sonshi amma dan ta ba Ibrahim haushi sai ta amsa ma shi,nan fa aka fara buga soyayya a private.
Wani lokaci har a group su kan ɗan yi magana amma dai ba wata ta soyayya ba,sanin abin duniya ba ya ɓoyuwa yasa maganar soyayyar Husna da mai kasuwa ta fasu cikin gidan kowa ya ji,nan ma sai aka fara rigima wasu na ganin cin amana ne,rigimar ba ta yi tsawo ba aka kwantar da ita inda Abdul mai kasuwa ya ƙaryata akan cewa shi ba soyayya suke da Husna ba.
Wannan magana da ya yi ita ce ta sanya Husna ta fusata ta yi rantsuwa akan sun gama soyayya,wannan shi ne dalilin rabuwar Husna da Abdul mai kasuwa.
Bayan rabuwar Husna da Abdul mai kasuwa sai kuma Ibrahim ya sake dawowa,bai je kai tsaye ba amma idan ana magana a group yana ƙoƙarin sanya Husna,idan kuma ita ke magana yana sanya baki da haka dai ya samu ya shawo kanta da ƙyar,shi ma sai da wasu daga cikin ƴan group ɗin suka sanya baki babu yadda Husna za ta yi dole ta haƙura suka dawo da soyayyarsu.
A chan bayan fage kuma ashe Maryam Hassan bala’in son Ibrahim take babu wanda ya sani sai shi da ya gane,ko wasa ake a group idan Husna da Fauzee su na yi ma shi to Maryam ita ke kare ma shi tana cewa Broz ba haka yake ba,babu wanda hankalinshi ya kai akan abin da take yi duk kowa ya ɗauka saboda ta na kiranshi Yayanta shi yasa.
Daga baya Sardauna ya fahimci halin da ake ciki,yaso fahimtar da Maryam amma bai san ta inda zai fara ba saboda bata fito fili ta nuna ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button