HAUSA NOVELRASHIN ADALCI Complete Hausa

RASHIN ADALCI Complete Hausa

08105217201
Hussy Saniey.????
*RASHIN ADALCI 2021*

*NA*

*HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*PAGE 40*

DAWOWA LABARI
Ajiyar zuciya Husna ta yi lokacin da ta gama tuna rayuwarsu ta baya ita da Fauzee,wasu hawaye masu ɗumine suka wanke mata fuska,ganin abin take tamkar a mafarki wai shi kenan Fauzee ta yi tafiya mai nisan zango,tafiyar da duk wanda ya yi ta ya tafi kenan babu ranar dawowa.
Kukane ya ci karfinta duk yadda taso danneshi amma ya ƙi dannuwa,kanta ta sanya a tsakanin cibiyoyinta ta saki kukan mai tsuma zuciyar mai sauraro,ta daɗe ta na kukan dan ba ta san iya adadin lokacin da ta ɗauka ta na kukan ba.
Ta na cikin wannan yanayin ta lura da wayarta sai haske take kawowa,ka sa ɗaukar wayar ta yi har sai da aka rinƙa kira kamar ba za a daina ba,cikin sanyin jiki ta ja jikinta zuwa inda take hango hasken wayar.
Fuskar wayar ta kalla ganin wanda ke kira yasa ta ɗauka,ta na jiyo lokacin da ya sauke ajiyar zuciya,sun ɗauki sama da sakan talatin babu wanda ya iya faɗar komai,chan dai ta yi ƙarfin halin furta.
“Ina wuni?”
Cikin dashashshiyar muryarta da ba ta fita sosai saboda kukan da take yi.
“Husna kuka ki ke yi koh?”
Shi ma ya faɗa cikin tashi muryar da babu komai sai zallar damuwa.
“Ta ya kake tambayata kuka nake bayan kasan dole nayi ko zan samu sassauci akan halin da nake ciki, da ma Fauzee ta faɗaman wannan ciwon mutuwa za ta yi ashe kuwa da gaske take!”
Husna ta faɗa hawaye na sake wanke mata fuska,dan ba ta da ikon hanasu zuba.
Jim Ibrahim ya yi dan shi kanshi yana cikin yanayi na ruɗu wanda da zai samu dama shi ma da kukan zai yi.
“Husna ba mu da ikon chanza ƙaddarar da Allah ya ɗoramana,lokacin da ya ba mu Fauzee mun ji daɗi mun yi murna,yanzu kuma da ya karɓeta ya kamata mu yi mata addu’a dan ita kaɗai tafi buƙata a garemu!”
Ibrahim ya ida maganar tamkar zai yi kukan shi ma amma saboda ƙarfin hali ya daure,dan shi kanshi ya san sun yi rashi sosai,ya yi wani irin sabo da Fauzee dan tun zuwanta gidan shaƙuwa mai girma ta shiga tsakaninsu.
“Nima ina so na daina kukan Sweet Iro amma wallahi hawayen sun ƙi tsayawa.”
Husna ta faɗa tare da sakin wani mahaukacin kuka,duk idan ta tuna ta rasa Fauzee hankalinta na tashi sosai.
Runtse idanuwana Ibrahim ya yi dan shi kaɗai ya san halin da yake ciki,shi kanshi da zai samu mai rarrashin shi so yake,amma ya zama dole gareshi akan ya samu ya lallashi Husna.
Dan haka cikin sanyin murya wanda damuwace ta haifar masa da shi ya ce,”ashe bazamu iya rungumar duk abin da Allah ya ɗoramana ba,kar ki manta Husna yana daga cikin cikar mumuni shine yarda da ƙaddara mai kyau ko akasinta,dan me mu bazamu yi koyi da abin da addininmu ya koyar damu ba, Husna mutuwa dolece inda Fauzee ta tafi mu ma dole a chan zamu je,kiyi haƙuri ki yi alwalla ki ɗauki alƙur’ani ki karanta mata suratul Rahman har da Yasin kin ji ko Tawan!!”
Ya faɗa cikin wani yanayi dan sautin kukanta dake shiga kunnuwanshi yana ƙara rikitashi.
“Yanzu shi kenan da gaske na rasa aminiyatace?”
Husna ta faɗa tare da fashewa da kuka.
“Ki yi haƙuri haka Allah ya tsara,mu kasance masu karɓar ƙaddara a duk yanda ta zo mana.”
Ibrahim ya faɗa cikin sanyin murya.
“To na karɓi wannan ƙaddarar Allah ya jiƙanki Fauzee!”
Husna ta faɗa ta na share hawayen dake zuba akan fuskarta.
“Yauwa Tawan je kiyi alwalla ki zo ki ɗauki qur’ani ki karanta,insha Allah za ki ji sauƙi saboda shi qur’ani warakane.”
Ibrahim ya faɗa cikin sigar lallashi.
“To shi kenan zanyi insha Allah.”
Husna ta faɗa ta na ƙoƙarin danne kukan dake taso mata amma ina ta makara dole ta sake shi,shiru Ibrahim ya yi dan ya kula Husna ta na cikin yanayin da bai kamata a hana ta kukan ba,duba da ganin kukan na ta ba irin wanda aka haramta bane mai kururuwa,sai da ta ɗauki lokaci mai tsawo kafin ya samu ya shawo kanta da ƙyar.

Sai da ya tabbatar ta ɗan samu natsuwa sannan ya kashe wayarshi,yana kashewa ya fara neman masu motar da zasu yi tafiya a cikinta,dan su na so ranar sadaka suje Kaduna su yi ma iyayen Fauzee gaisuwa.
Bayan Ibrahim ya kashe wayarshi nan Husna ta miƙe ta je ta ɗauro alwalla,inda ta tashi ta dawo qur’ani ta ɗauka ta fara karatu.
Nan fa mutane su kai ta kiranta wayata saboda sanin yadda suka shaƙu da Fauzee, wannan kiran da ake mata shi ne ya maido mata da kukanta baya,dole Mama ta zo ta tafi da ita ɗakinta.

 

08105217201
Hussy Saniey.????
‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/LmbGi3TbkTF2sUurNrJ8zZ

*RASHIN ADALCI 2021*

*NA*

*HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

 

*PAGE 41*

Husna ba ta taɓa cin karo da dare mai tsayi a rayuwarta kamar daren yau ba,ta yi kuka har idanuwanta suka daina zubar da ruwa,daga ƙarshe sai miƙewa ta yi ta kabbara sallah,da nafilfili ta raya wannan daren.
Husna na gama sallar asuba ta hau WhatsApp,ta san mutuwa ɗaya ce kuma ba’a wasa da ita amma har yanzu ganin abun take kamar mafarki take,ta na fatan ta tashi daga wannan mummunan mafarkin,sai dai shigarta group ɗin ƴan amana yasa ta ida tabbatar ma da kanta ba mafarki take ba, hawayene ke ta sintiri akan fuskarta,yanzu shi kenan Fauzee ta yi tafiyar da babu ranar dawowa.
Kallon hotunan Fauzee da aka turo take yi ta na tuna rayuwarsu,duk in ta kalli hotunan babu abin da ke tada mata hankali irin idan ta ga an sanya RIP,duk in ta kalli waɗannan kalmomin suna matuƙar ta da mata hankali,fita ta yi ta koma private ta rinƙa bin chat ɗinsu ta na dubawa,hawaye kuwa tamkar an buɗe lalataccen famfo haka suke zuba.
Jin kanta na mata wata irin sarawa yasa ta miƙe ta na layi tamkar wadda ta sha wani abu, haɗa hanya ta rinƙa yi,saura kaɗan su yi karo da Mama dake ƙoƙarin shigowa hannunta riƙe da kofi,ganin yadda Husna ke laluben hanya yasa ta kama hannunta,maido ta cikin ɗakin ta yi sai ta zaunar da ita.
“Husna ina za ki je haka bayan kin san ba ki da lafiya?”
Mama ta yi maganar ta na ƙare ma Husna kallo,ganin yadda duk ta zabge a cikin dare guda amma ramar da ta yi har ta fito.
“Kaina…ke…ciwo nake so naje ɗakina na kwanta.”
Husna ta faɗa tamkar mai koyon magana,dan muryar ta yi ƙasa da yawa sai ka saurara sosai ka ke jin abin da take faɗa.
“To shi kenan gama shan shayin nan sai ki sha magani ki kwanta.”
Mama ta yi maganar tare da ɗauko kofin da ta shigo da shi.
Girgiza kai Husna ta yi,”Mama bazan iya sha ba bakina ɗaci gareshi amma bani maganin sai na sha,kaina kamar zai ɓare biyu nake ji.”
Husna ta ƙarasa maganar ta na yamutsa fuskarta.
“Ki yi haƙuri Husna ki daure ki sha shayin sai ki sha maganin kin ga ko jiya ba ki ci komai ba haka nan ki ka kwanta.”
Mama ta yi maganar ta na kai ma Husna kofin a baki,babu yanda Husna ta iya dole ta buɗe bakinta,sau biyu ta kurɓi shayin ta janye kanta,ƙa ra kai mata kofin a baki Mama ta yi sai ta girgiza kanta alamar ya isheta.
“Ki daure ki sha Husna sai ki sha magani kin ga babu komai a cikin ki!”
Mama ta faɗa cikin sanyin murya,dan ba ƙaramin tausayin Husna take ji ba,kallo ɗaya za kai ma fuskar Husna ka yi saurin ɗauke kanka,dan duk ta kumbura ga idanuwanta sun yi shishshige ciki,duk da kasancewar Husna baƙa amma sai da fuskarta ta yi ja.
“Mama na ƙoshi ki bani maganin dan Allah!”
Husna ta faɗa wasu hawaye na sake zubowa akan fuskarta,hannu ta sa cikin sauri ta goge dan gudun ka da Mama ta gani amma ta makara saboda idanuwan Mama akan ta su ke tun ɗazun.
“Husna bazan fasa yi maki nasiha ba,duk musulmin ƙwarai an san shi da karɓar ƙaddara ko wacce iri ce,a yanzu kuka babu abin da zai chanza Husna, Allah ya riga da ya yanke abin da yake dai-dai a garemu sai dai mu bi da addu’a kawai, Allah shi yafi mu sanin dai-dai a rayuwarmu,lokacin da ya haɗa ku bai yi shawara da kowa ba haka lokacin da ya karɓeta bai yi shawara da kowa ba,a yau Husna ko ke Allah ya buƙata babu tsumi babu dabara dole sai kin tafi,dan haka kuka ba naki bane addu’a kaɗai Fauzee ke buƙata daga gareki,dan haka kiyi haƙuri ki daina wannan kukan kin ji Husnata!”
Mama ta faɗa cikin sigar lallashi.
“Zan daina Mama insha Allah kuma zan ta yi Mama Fauzee addu’a dan nuna soyayya ta a gareta.”
Husna ta faɗa da muryarta wadda kuka ya disasheta.
“Yauwa ɗiyar albarka karɓi shayin ki shanye sai ki sha maganin ki kwanta insha Allah kan zai sauka.”
Mama ta yi maganar cikin karayar zuciya,ta san ɗiyarta ta yi sabo da Fauzee sosai,duk wanda ke tare da Husna sai yasan Fauzee duk da kasancewar su ba’a gari ɗaya ba amma akwai shaƙuwa mai girma a tsakaninsu,ganin yanda Mama ta shiga damuwa yasa Husna ɗaukar kofin shayin ta ɗaga,ba ta sauke kofin ba sai da ta shanye shi tsab,duk da ba ta jin daɗin shi akan halshenta amma haka ta daure, miƙa hannu ta yi ta karɓi magani,shi ma nan take ta shanye shi,hakan ya ma Mama daɗi kuwa sosai,dan haka ta kama hannun Husna ta mai da ta akan gadonta.
Taimaka ma Husna ta yi har sai da ta kwanta,bargo Mama ta yafa ma Husna a jikinta dan ta san Husna ba ta iya bacci sai ta lulluɓe,sai da Mama ta tabbatar Husna ta ji daɗin kwanciyar sannan ta fita ta baro mata ɗakin.
Shiru Husna ta yi kamar ta na bacci, waya take son yi amma babu hali tun da ta ga lokacin da Mama ta fita da wayar,dan haka ta lumshe idanuwanta kamar ta na bacci.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button