HAUSA NOVELRASHIN ADALCI Complete Hausa

RASHIN ADALCI Complete Hausa

08105217201
Hussy Saniey.????
*RASHIN ADALCI 2021*

*NA*

*HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*PAGE 39*

A kwana a tashi asarar mai rai, a haka aka cigaba da rayuwa a group ɗin tamkar babu wata rigima da ta taɓa faruwa.
Mutane sun samu natsuwa sosai,dan komai ya wuce ba kamar ɓangaren Husna da Ibrahim soyayya suke mai ban mamaki,har lokacin Husna duka mutum ukku ta sa ni a cikin group ɗin a fuska, Ibrahim, Sardauna,sai Abu Abdul Rahman.
Kwatsam wata rana sai ga Sardauna ya sanyo wata Hadiza Muhammad a gidan(kasancewar shi ma admin ne,da ma admin ukku ne a gidan shi da Maryam Hassan da Umma.)mutane sun mata barka da zuwa an karɓeta kamar yadda aka saba karɓar baƙi a gidan.
Ita ma sun yi sabo da Husna sosai dan Kakus Husna ke kiranta da shi,ita kuma ta na kiran Husna da jikata.
Bayan kwana biyu da sanyo Hadiza Muhammad sai Sardauna ya bata admin,nan fa Umma ta ce ba ta yarda ba,dan ga tsaffin members nan ba’a basu admin ba dan haka ba za’a ba Hadiza Muhammad ba.
Nan fa Abba ya ce shi kuma ba zai cire Hadiza Muhammad daga admin ba, wannan furuci na Sardauna shi ne ya tada rigima sosai a gidan,daga ƙarshe ma sai Umma ta fita daga gidan.
Wannan fita da Umma ta yi shine buɗewar kofofin matsala a gidan,an yi ƙoƙari ƙwarai da gaske wurin ganin Umma ta dawo gidan amma ta yi rantsuwa ta gama zama a gidan.
Har taro aka yi da duka Officials ɗin gidan amma aka ka sa samun damar shawo kan Umma dan har cire Hadiza Muhammad ɗin aka yi daga admin amma dai babu biyan buƙata,wannan haɗuwa da aka yi ita ce ta sanya Husna ta san offials ɗin gidan,amma ban dasu ba ta san sauran members ɗin gidan ba.
Dole aka haƙura aka kyaleta ba dan rai na so ba, group ɗin sai da ya yi tamkar zai mutu cikin ikon Allah kuma da taimakon Husna da Fauzee sai ga shi ya tashi.
Duk da Umma ta fita daga gidan idan aka yi wani abu da ya danganci ƴan group ɗin ta na zuwa.
Yanzu ma ko hidimar bikin da ake a gidan ƴan amana bikin ummar ne yazo shi ne suke tunanin gudummawar da zasu ba ta,dan Umma ta na da kirki sosai wannan dai matsalar da aka samu ce kawai.
Fauzee na da ciwon zuciya da ma yana tashi lokaci bayan lokaci,dan akwai lokacin da aka kwantar da ita asibitin Shika ƴan amana sun so zuwa amma Allah bai yadda ba.
Wayar Husna da Fauzee ta ƙarshe saura ƙwana biyu ta rasu,wata rana da misalin ƙarfe sha ɗaya na dare su na chat sai Fauzee ta ce,
“Wallahi Husna ji nake kamar ciwon nan ba zai bar ni ba dan ni kaɗai nasan abin da nake ji.”
Cikin wasa Husna ta ce,”ki ce mu shirya cin wake da shinkafa?”
Fuskantar da Fauzee ta yi wasa Husna ta ɗauki maganarta yasa ta ce,
“Hmmm! Husna ba wasa nake ba wallahi yanzu fa ina asibiti kuma ko bacci ban iyawa Husna kirjina ke ciwo kamar zan mutu!”
Ta faɗa cikin karaya dan ta sadaƙas da rayuwa.
Cikin zaro idanuwa Husna ta ce,”innalillahi Fauzee amma ki kayi shiru ba ki faɗaman ba?”
Cikin tashin hankali Husna ta yi maganar.
“Banso hankalinki ya tashi yanzu haka ina asibiti ina faɗa maki ne yanzu saboda bansaniba ko wannan ce maganarmu ta ƙarshe!” Fauzee ta faɗa ta na ciye leɓenta na ƙasa.
“Kiyi haƙuri insha Allah za ki samu lafiya Ƙawata tun da kina asibiti likitoci kuma na kula da ke.”
Husna ta faɗa cikin karfafawa Fauzee guiwa.
“Husna asibiti babu abin da zasu iya yi man a halin da nake ciki yanzu,sai asarar kuɗi da ake yi dan nasan mutuwa zan yi wannan ciwon ba zai bar ni ba!”
Fauzee ta faɗa tare da dafe kirji ta na jin yadda numfashinta ke sarƙewa.
“Wannan wacce kalar maganace Fauzee?cuta ai ba mutuwa ba ce,mai lafiya nawa ki ka ji ya mutu ya bar mara lafiya dan haka ki daina wannan maganar ma!”
Husna ta faɗa ta na share hawayen da suka cika mata idanuwa,dan maganar Fauzee ta karya mata da zuciya.
“Wallahi Husna da gaske nake ina ji a jikina mutuwa zan yi dan Allah ki yafeman lokacin da labarin mutuwata ya riske ki,ni dai nasan tawa ta ƙare na yafema kowa dan Allah ki roƙarman gafarar mutane.”
Kalaman Fauzee ba ƙaramin tsoratar da Husna su kayi ba dan haka sai kawai ta kira Fauzee a waya.
Yanda muryar Fauzee ke fita kawai ya sanya Husna ta fashe da kuka,nan fa Fauzee ta yi ta lallashinta,sun tattauna maganganu masu yawa daga ƙarshe kuma su kayi sallama saboda zuwan wani likita ya ce ma Fauzee ta kwanta dan ta na buƙatar hutu,washe gari kuma gaba ɗaya wayar Fauzee a kashe take,daga haka kuma basu ƙara magana ba sai dai da wannan mummunan labarin ya isketa.

08105217201
Hussy Saniey.????
*RASHIN ADALCI 2021*

*NA*

*HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

 

*PAGE 44*

 

Ruwa masu sanyi Mama ta zuba ma Husna a fuska,ruwan na sauka akan fuskarta,ajiyar zuciya mai ƙarfi ta yi, buɗe idanuwanta ta yi tana ƙarema rufin ɗakin kallo.
“Sannu Husna.”
Muryar Mama ta do ki dodon kunnenta,a hankali ta maido dubanta akan fuskar Mama,kallo ɗaya ta yi ma fuskar Mama ta ɗauke kanta,dan ba ƙaramin tausayin Mama ba ne ya ratsata, lumshe idanuwanta ta yi a hankali ta ce,”Mama ki yi haƙuri dan Allah wallahi na ka sa jurewa ne shi yasa kike ganin kamar ban jin maganarki amma insha Allah na maki alƙawari daga yanzu na daina kukan nan.”
Ta ida maganarta ba ta san lokacin da wasu hawaye masu ɗumi suka wanke mata fuska ba, murmushin ƙarfin hali Mama ta yi.
“Ki ɗauki ƙaddara Husna,da ma haka rayuwa take sai ki ga yau kin rayu da wani gobe kuma da waninsa za ki rayu.”
Tashi Husna ta yi daga kwancen da take,kallon Mama ta yi duk sai ta ga ma Mamar duk ta fa ɗa.
“Hakane Mama kuma na karɓi wannan ƙaddarar da hannu bibbiyu insha Allah,sai dai alfarma ɗaya nake so ki yi man Mama,dan Allah ka da ki ce A’a.”
Kallon ƴan sakanni Mama ta yi ma Husna,sai kuma ta saki murmushi.
“Faɗi abin da kike so in dai bai fi ƙarfina ba zan maki shi insha Allah.”
Gyara zama Husna ta yi tare da riƙo hannun Mama,kallon fuskar Mama Husna ta yi tare da ƙara narke fuska,yanda ta yi kallo ɗaya za ka yi mata ta baka tausayi.
“Mama dan Allah ki taimakeni kamar yanda Allah ya taimakeka,idan za’a gaisuwa ki roƙar man Baba ya barni naje ka da ku hanani dan Allah Mama, wallahi Mama ina so na haɗu da iyayen Fauzee tun da ita Allah bai ƙaddara haɗuwa ta da ita ba.”
Ta ƙarasa maganar cikin yanayi na mai son yin kuka,dafa kafaɗarta Mama ta yi ganin yanda ta koma kalar tausayi,dan haka sai Mama ta sakar mata wani murmushi mai kwantar da hankali.
“Ba zamu hana ki zuwa ba Husna,sai dai mu yi fatan Allah ya kai ku lafiya ya dawo mana daku lafiya,yaushe ne zaku yi tafiyar?”
Duk da tana cikin wani hali amma sai da ta ji daɗin barinta da aka yi,dan har sai da fuskarta ta gaza ɓoyewa.
“Ibrahim dai ya faɗa man ranar sadaka za a je amma dai zan ƙara tambayarshi sai naji.”
“Yauwa Husna ni dai abin da nake so dake dan Allah ki sanya ma ranki dauriya,idan kika aikata haka zamu kasance cikin jin daɗi.”
Mama ta yi maganar tana ƙoƙarin tashi daga zaunen da take.
“Insha Allah Mama ba zan kuma ba,ai kin gama man komai tun da kika bar ni zuwa Kaduna.”
Husna ta yi maganar kamar ba ita bace ta suma yanzu ba,har cikin ran Mama ta ji daɗin yanda Husna ta saki jikinta,nasiha ta ƙara yi mata sosai,sai da Mama ta tabbatar Husna ta yi laushi sosai,lokacin ta fita daga ɗakin ta bar ta zaune.
Shiru Husna ta yi tana jinjina wannan rayuwar a cikin ranta,dole ƴan magana ke ce wa ba gidan zama ba ce duniya,yanzu kamar ba a yi Fauzee ba a duniya,sai dai a bi ta da addu’a kawai,lalle rayuwa ba ta da tabbas.
Ta ɗauki tsawon lokaci ta na wannan tunanin,ganin babu abin da yake ƙara mata sai damuwa yasa ta jawo wayarta,kai tsaye gidan ƴan amana ta shiga,yanzu ma dai babu wata fira,dan haka ta fito, Ibrahim ta kira dan ta ji yanda tafiyar za ta kasance,sun daɗe sosai suna tattaunawa akan yanda za a yi tafiyar,inda daga ƙarshe aka samu matsaya.
Ranar sadaka suna gama sallar asuba suka fito daga gidajensu,in da suka yi zasu haɗu chan kuwa suka haɗun,su gomane zasu yi tafiyar,da yake motar babba ce sai ta ɗaukesu babu ɓata lokaci suka hau hanya,cikin ikon Allah ƙarfe biyu a gidansu Fauzee ta yi masu.
Duk da gidan cike yake da mutane kasancewar ranar akai sadaka,hakan bai hana su samu tarba mai kyau daga wurin iyayen Fauzee ba,gaskiya iyayen Fauzee sun ya ba da kirkin mutanen sosai,duk da sun san ƴarsu ba za ta yi tarayya da mutane marasa mutunci ba,nan fa aka dasa sabon kuka saboda labarin da Maman Fauzee ke basu na yanda akai rasuwar,sun yi kuka sosai ji suke tamkar yanzu ne abin ke faruwa,daga ƙarshe suka ba zukatansu haƙuri,an yi doguwar addu’a akan Allah ya sanyaya makwancin Fauzee,ana yin sallar la’asar kuma suka yi shirin komawa gida,nan fa dauriyar Maman Fauzee ta ƙare,dan rungume Husna ta yi tana kuka mai cin rai,ganin kukan da Maman Fauzee ke yi duk sai jikinsu ya yi sanyi, da ƙyar aka raba Husna da Maman Fauzee,har suka shiga Mota Husna na kuka.
Yan da ƴan cikin Motar ke ƙoƙarin jan Husna da magana yasa tun tana sharewa har sai da ta saki jikinta,basu suka shigo garin Katsina ba sai ƙarfe takwas na dare,har ƙofar gida aka kai kowa.
Husna na shiga gida ta zauna nan fa ta fara basu labarin kirkin iyayen Fauzee, Mama ta ji daɗi sosai har ta kira Maman Fauzee tai mata godiya,nan take nuna mata ai an zama ɗaya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button