RASHIN ADALCI Complete Hausa

08205217201
Hussy Saniey.????
*RASHIN ADALCI 2021*
*NA*
*HUSSY SANIEY*
*____________________________________*
*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*PAGE 43*
Taso ƙwarai da gaske wayarta ta kasance tare da ita,amma ga shi Mama ta hana ta wayarta,har hawaye sai da ta yi na jin haushi,ta na wannan tuƙuburin bacci mai nauyi ya yi awon gaba da ita,dan harda maganin bacci Mama ta haɗa mata,aikuwa nan ma ta yi baccin mai nauyi dan ko da la’asar da ƙyar Mama ta tada ta,ko da ta gama sallar ma nan kan darduma ta yi bacci.
Ba ita ta farka ba sai wurin ƙarfe shidda da ƴan mintoci,aikuwa ta ji jikinta ya mata daɗi sosai,wanka ta sake yi da ruwa mai ɗumi,nan ma ba ta shafa mai ga jikinta ba,sai ta nufi tsakar gida ta zauna inda Mama ke yanka alayyahu, rinƙa haɗa ma Mama ta yi da haka har suka gama,ganin ta ɗan saki jikinta yasa Mama ta bata wayarta tare da mata gargaɗin ka da ta ganta ta na kuka,babu musu ta amince,sai bayan ta gama sallar isha’i sannan ta buɗe data.
Sakonni ta iske na masu yi mata ta’aziyya sosai,a hankali ta rinƙa bi tana amsawa har ta gama,sai ta shiga group ɗin ƴan amana,tun safe har yanzu babu wata magana mai yawa da aka yi, ƴar maganar ma dai gaisuwa ce suka yi ma junansu.
Sallama ta yi tare da yi masu ta’aziyya,nan aka fito ana amsawa ashe duk suna kusa amma jimami yasa kowa ya yi shiru.
Fita ta yi daga group ɗin saboda wani tunani da yazo mata a rai,wurin lambobinta ta shiga nan ta tsaya a wurin lambar Fauzee,sai kawai ta ji hawaye sun zuɓo mata,ba tare da ta damu da ta gogeba ta danna kira,sai da ta kira sau biyu kafin a ɗaga jin muryar Maman Fauzee yasa ta ƙara tabbatar ma kanta babu Fauzee a wannan duniyar.
Katse mata tunani maganar Maman Fauzee ta yi,”ɗiyata ya jikinki? ɗazun mun yi waya da Mamanki take faɗaman ba ki da lafiya.”
Kamar wadda aka ta da daga bacci haka Husna ta firgita,nan ta kama inda-inda.
“Ma…ma…da… sauƙi!”
Husna ta yi maganar da muryarta da ko fita sosai ba ta yi,dan ba dan Maman Fauzee ta saurara sosai da ba ta jin mai Husna ke faɗa.
Tausayin yarinyar ya kama Maman Fauzee ta ce,”kiyi haƙuri ɗiyata,mu ma dole haƙuri muka yi wanda ya ba mu Fauzee ya karɓe kayanshi dan ya fi mu sonta, addu’a kaɗai zamu bi ta da ita,dan muma zaman jiran tamu mutuwar muke koyi haƙuri da ma haka rayuwa take wata ran akwai mu wata rana kuma za’a wayi gari babu mu kin ga dai alama akan ƙawarki dan haka sai dai mu yi fatan samun kyakkyawan ƙarshen.”
Mama Fauzee ta ida maganarta tare da share hawayen da suka zuɓo mata akan fuskarta,dan ita kaɗai ta san halin da take ciki,ta na yin ƙarfin haline kawai dan mutane su samu natsuwa,dan ta lura ba ƙaramin bugu mutuwar Fauzee ta yi ma mutane ba.
“To shi kenan Mama insha Allah zan kasance mai yi mata addu’a duk da dai nayi to zan ƙara,naji ma ƴan amana na maganar zamu zo nan Kaduna.”
Husna ta faɗa a hankali,dan Maman wannan karon ba ta ji mai Husna ta faɗa ba sai da ta ƙara maimaita mata.
“Eh sun faɗaman da muka yi waya dasu,dan har ma Baban gida yazo ɗazun da shi aka yi jana’iza.”
Mama ta faɗa ta na danne wani abu da ke taso mata.
“Allah sarki ashe yazo Allah ya ba shi lada ita kuma Allah ya jaddada rahamarshi a gareta!”
Ta ƙarasa maganar tare da fashewa da kuka,dan ta kasa daurewa duk ƙoƙarin da tayi amma ta kasa.
Ita ma Maman Fauzee hawayen ne suka zuɓo mata dan ɗiyarta take tunawa,zaman Babansu Fauzee a kusa da ita yasa ta share hawayenta,cikin ƙarfin hali ta ce,”Ameen Husna ki kwanta kiyi bacci kin ga baki da lafiya gobe mun yi magana.”
“To Mama nagode Allah ya bada haƙurin rashi sai anjima.”
Husna na faɗar haka kuka mai ƙarfi ya kwacemata,dan Maman Fauzee na jin kukan ita ma hawayen suka sake zuɓo mata,kuka sosai Husna ta yi,dan ji take kamar yanzu aka faɗi mata rasuwar.
Tunawa da Sardauna da Husna ta yi yasa ta tsaida kukanta,kiran wayarshi ta yi kamar ba zai ɗaga ba chan kuma aka ɗaga,daga yanda ta ji muryarshi ta san shi ma kukan yake,nan fa ta kasa magana kawai ta kashe wayarta ta na sakin kuka mai ban tausayi,wai yanzu babu Fauzee a cikin wannan duniyar,maganar da tafi juyawa a ranta kenan,jin ta na kuka ta kashe wayarta yasa Sardauna tura ma Ibrahim text akan ya lallashi Husna.
Shi Ibrahim bai ma san Husna ta karɓi wayarta ba,dan ya kira ya kai sau biyar sai dai Mama ke ɗagawa shi yasa ya jinkirta da kiran da yake faman yi mata.
Kiranta ya yi ta na kallo amma ta kasa ɗagawa saboda kukan da take dan ko ta ɗaga baza ta iya magana ba,nan fa numfashinta ya fara sama kamar mai cutar numfashi,hakan ya yi dai-dai da shigowar Mama ɗakin dan ta dubata ta ji ta shiru tunda ta shigo ɗakin,kafin Mama ta ƙaraso inda take har ta faɗo daga saman gado,cikin sauri Mama ta isa inda take,kasa ɗagata Mama ta yi sai dai ta kama hannunta, dai-dai saitin agogon hannunta ta taɓa amma sai taji babu motsi,saman hancin Husna Mama ta kai hannunta amma nan ma babu numfashi.
08105217201
Hussy Saniey.????
Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/LmbGi3TbkTF2sUurNrJ8zZ
*RASHIN ADALCI 2021*
*NA*
*HUSSY SANIEY*
*____________________________________*
*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*PAGE 42*
Ƙarfin maganin da Husna ta sha,ga baccin da ba ta samu yi ba a daren jiya yasa ko minti biyar da kwanciya ba ta yi ba bacci ya yi awon gaba da ita.
Ko da Mama ta leƙo dubata ta ga bacci take sai ta gyara mata bargo,da za ta fita har sai da ta ja mata kyauren ɗakin saboda ta san Husna in ta na bacci ba ta son hasken,aikuwa ta yi bacci mai nauyi dan ba ita ta farka ba sai wurin ƙarfe ɗaya da rabi,shi ma kun san jiki da jini duk lokacin da ka saba sallah da ya yi cikin ikon Allah ko kana baccine sai ka tashi.
Da addu’a a bakinta ta farka,kallon ɗakin take yi kamar yau ta fara ganinshi,sai lokacin ta tuna da a ɗakin Mama take,agogon dake manne a jikin gado ta kalla,ganin yanda lokaci ya ja yasa ta tashi daga kwanciyar da take,ta mamakin baccin da ta yi take yi,tunaninta ya yanke ganin haske ya haske mata idanuwa har sai da ta runtse idanuwanta,ganin haka yasa Mama sakin labulen ɗakin ta shigo ciki.
“Kin tashi ashe? da ma shigowa nayi na tada ki kiyi sallah dan har an kira yanzu kin ji sun tada sallah,”
Mama ta faɗa tare da kai hannu jikin Husna,jin babu zafi a jikin yasa ta yi murmushi ta ce,”Alhamdullih jikin ma babu zafi yanzu ga ruwa chan na haɗa maki kije kiyi wanka dan ki ji ƙarfin jikinki.”
“To Mama.”
Husna ta faɗa ta na yaye bargon dake jikinta,saukowa ta yi daga kan gadon ta fara tafiya a hankali,har ta nufi hanyar fita daga ɗakin Mama ta ce,”Husna ki shiga toilet ɗin nan ɗakin dan ciki ma na haɗa maki ruwan.”
“To Mama amma bari na ɗauko kayana.”
Husna ta yi maganar cikin muryarta da har yanzu ba ta fita sosai.
“Je kiyi wankan bari na ɗauko maki kayana.”
Mama ta faɗa ta na fita daga ɗakin.
Bayanta Husna ta bi da kallo har cikin ranta ta na jin tausayin mahaifiyarta,duk lokacin da Husna ba ta lafiya ko ta na cikin damuwa Mama sai ta fita shiga wani hali,shi yasa lokutta da dama take ƙoƙari ƙwarai wurin danne damuwarta,jin motsin Mama na ta fito daga ɗakinta yasa cikin sauri Husna ta shige toilet,har sai da Mama ta ji kamar ƙarar rufe ƙofar dan haka ta kalli ƙofar amma jin ƙarar ruwan da Husna ta taɓa sai ta yi tunanin ko kunnuwanta ne suka ji mata haka,da ma Husna ta taɓa ruwan ne saboda ta kauda ma Mama tunanin yanzu ta shigo kuma ta samu nasara.
Ba ta wani jima sosai a toilet ɗin ba ta fito,ta ji daɗin jikinta sosai dan jin ta take wani sakarai,gefen gado ta iske kayanta da Mama ta ɗauko mata,jin gyaran muryar da liman ya yi na shirin ta da Sallah yasa ta saurin sanya kayan,ko mai ba ta shafa ba sai turare da ta ɗauka ta sanya ma jikinta,jin an tada sallah yasa ta shimfiɗa darduma ta kabbara sallah ita ma.
Ko da aka gama sallah ba ta tashi daga inda take zaune ba,sai ma ta jingina bayanta da katakon gado,lumshe idanuwanta ta yi ta na tunanin halin da take ciki,duk da tasan yanzu an daɗe da kai Fauzee maƙwancinta amma har yanzu kamar wasa take ganin abun,hawaye ta ji na sauka akan fuskarta,ka sa tsaida su ta yi dan haka ta barsu suna zuba,jin motsin Mama ta nufo ɗakin yasa ta yi saurin goge hawayen fuskarta.
Mahaifiya ba wasa ba,kallo ɗaya tai ma fuskar Husna ta san ta yi kuka,dan haka ta zauna kusa ta ita,ta rinƙa yi ma Husna nasiha da nuna mata illar kukan da take yi,sun daɗe Mama na mata nasiha,har sai da Mama ta tabbatar yarinyarta ta samu natsuwa sannan ta miƙe tsaye ta nufi fita daga ɗakin.
“Ba ri na kawo maki abinci kin ji koh?”
“Mama dan Allah ki bar abincin ki bani ruwan shayi kaɗai ma ya isa!”
Husna ta yi maganar kamar za ta fasa kuka,dan har ga Allah ba ta jin bakinta zai iya tauna wani abu a yanzu.
“A’a Husna ki daure dai ki ci abinci yaushe shayi zai iya riƙe maku ciki.”
Mama ta faɗa tare da juyowa ta kalli Husna.
“Mama ki dai bani shayin zan fi iya shan shi dan bakina ɗaci yake man!”
Husna ta faɗa tare da marairacewa,dan Mama ta ji tausayin ta,haƙarta kuwa ta cimma ruwa dan Mama ta kuwa ji tausayin na ta,dan haka ba tare da Mama ta sake faɗin komai ba ta juya ta fita,babu daɗewa sai ga Mama ta dawo da kofi da filet riƙe a hannunta.
Sai da ta aje kofin da filet ɗin sannan Husna ta ga ashe wainar ƙwai ce,tura mata kayan gabanta Mama ta yi tare da tsareta da idanuwa.
Ganin babu wasa a fuskarta yasa Husna jan kofin shayin da yaji madara ta kai bakinta,duk da shayin ya mata daɗi a baki amma sai ta ji bata sha’awar shan shi, ɗagowa ta yi ta kalli Mama ganin yadda fuskarta take a ɗaure yasa ta sunkuyar da kai, wainar ƙwan ta jawo ta fara cusama cikinta har ta cinye ƙwan ta kuma shanye shayin ba ta sake gigin kallon Mama ba.
Babu wanda ya yi magana sai Mama da ta ɓallo magani ta miƙo mata,babu musu ta karɓa ta kora da ruwa,ganin Mama ta tattare kayan ta na niyyar fita yasa ta ƙara narke fuskarta.
“Mama wayata fa dan Allah.”
Ba tare da Mama ta tsaya saurarenta ba ta fita daga ɗakin,wasu hawaye masu ɗumine suka wanke mata fuska.
Sake jingina bayanta da gado ta yi ta lumshe idanuwanta,dan gaskiya ba ta so haka ba,wayarta take so dan tana son amfani da ita.