HAUSA NOVELRASHIN ADALCI Complete Hausa

RASHIN ADALCI Complete Hausa

08105217201
Hussy Saniey.????
*RASHIN ADALCI 2021*

*NA*

*HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*PAGE 48*

Washe gari Husna ba ta samu damar hawa WhatsApp ba sai da marece,tana hawa kai tsaye gidan ƴan amana ta shiga,nan ta ga an yi tagging ɗinta,dubawa ta yi sai ta ga Chairman ne yake kiranta,amsawa ta yi cikin sa a kuwa yana online sai ya maido mata da amsa.
“Chairman irin wannan kira haka ko ta samu ne?”
Husna ta faɗa tare da amfani da emojin dariya,ko sakon goma ba a yi ba sai ga amsa Chairman ya maido mata da ita.
“Lafiya lau farin cikin ƴan amana dama so nake na faɗamaki Sakwara nake son ci.”
“Ba ka da matsala in dai Sakwara ce,yanzu ba mu da doya amma idan aka kawomana zan yi maka.”
Husna ta faɗa tare da gyara kwanciyar ta,babu jimawa Chairman ya sake maido mata da amsa.
“To shi kenan Husna dama nasan ke kaɗai ce mai mutuncin da za ta iya yi man.”
Dariya Husna ta yi ta ce,”ba ruwana Chairman in dai ni ce to insha Allah za ka ci Sakwara.”
“Chairman idan an yi maka Sakwarar ina ci,” Anty Maryam ta faɗa,sai yanzu Husna ta san Maryam ɗin na online.
“Ha ba yarinya ba ki cinta,amma dai zan ba ki siɗin ƙwano.”
Chairman ya yi maganar yana dariya,kafin ta ba shi amsa sai ga Ibrahim ya yi sallama,mamaki ya kama Husna da ma yana online amma ta ma shi magana bai amsa ta ba,dama yau ta kirashi da safe yana waya da ya gama kuma bai kirata ba,kasancewarta a busy yasa ba ta damu ba,kuma ta san in dai ya gani zai kira,dan haka da ta ga bai kira ba sai ta yi tunanin ko wani abu yake, ƙarar shigowar saƙon da Chairman ya turo ne yasa ta maido hankalinta akan chat ɗin.
“Kai Sectary ya daga jin an yi maganar Sakwara har ka fito?” Chairman ya faɗa tare da yin dariya.
“Zuwa ya yi domin a yammashi shi ma,kar ka damu idan aka kawo za a baka.”
Maryam ta yi maganar,babu daɗewa sai ga amsa Ibrahim ya turo da ita,”A’a ni ban ci sai dai idan ke za ki yi man to zan ci.”
“Kar ka damu zan maka Sakwarar mai daɗi kuwa.”
Maryam ta faɗa, sosai mamaki ya kama Husna na wannan maganar da ake yi,sai ta danne ba ta ce komai ba,ganin ranta ma zai ɓaci sai kawai ta sauka daga online ɗin,amma zuciyarta fal tunanin abin da ya faru,haka dai ta share komai daga cikin zuciyarta,ba ta sake hawa ba sai wurin ƙarfe goma sha ɗaya na dare,ko da ta shiga group ɗin sai ta ga ana ta maganar Sakwara,abin ya matuƙar tsaya ma ta a rai,kyalewa kawai ta yi,har lokacin kuma Ibrahim bai kirata ba,dubawa ta yi kuma ta ganshi yana online,dan haka sai ta yi ma shi sallama,ya buɗe ya duba amma sai bai maido mata da reply ba,ganin haka sai ta kyaleshi kawai ta sauka,rufe datarta ta yi ta kwanta.
Washe gari da safe wurin ƙarfe goma na safiya ta sake hawa online,ko da ta shiga gidan ƴan amana sai ta ga Chairman na ƙwalama ta kira,ko da ta duba lokacin da ya kirata ɗin sai ta ga ƙarfe ɗaya da rabi,ranta ya ɓaci sosai sai ta ce,”Akwai matsalane kake kirana tsakar dare?”
Cikin sa a kuwa yana online ɗin sai ya maido mata da amsa,”lafiya lau wai Sakwarar nake maki tuni ka da ki manta.” Chairman ya faɗa.
Ran Husna ya ɓaci sosai dan yanzu ta tabbatar akwai abin da ke faruwa,dan haka sai ta maida ma shi da martani.
“Na fasa yin Sakwarar ka kai kuɗi ka siyo!”
Husna ta faɗa ranta a ɓace,amsa ya maido mata ya ce,”a’a Husna ba mun yi haka da ke ba.”
Shiru Husna ta yi ba ta ce ma shi komai ba,sai ta fara tunanin meye matsalar,nan take tunanin ko dai sun yi magana da Zarah shi ne suka ji haushi,dan haka sai ta yanke shawarar kiran Zarah,tana kira ringing ukku Zarah ta ɗauka.
“Assalamu Alaikum Zarah yakike ya gida?”
Husna ta faɗa a hankali,daga chan ɓangaren Zarah ta amsa mata da,”lafiya lau Husna.”
“Zarah dan Allah tambayarki zan yi,kin masu Chairman maganar nan kuwa?” Husna ta yi maganar cikin sanyin murya.
“Eh na kirasu na ce masu Nagode da abin da suke yi man,” Zarah ta yi maganar a hankali.
“Okay! Su ya suka ce maki?” Husna ta tambayi Zarah.
“Babu abin da suka ce,ni kuma na kashe wayata lafiya dai koh?”
Zarah ta tambayi Husna, girgiza kai Husna ta yi tamkar Zarah na ganinta sai ta ce,”babu komai kawai dai na ga ana man wasu abubuwane wanda gaskiya ba zan jura ba.”
“Wane abubuwa kenan?” Zarah ta tambaya.
“Ke share kawai Zarah sai anjima nagode.”
Husna tana faɗar haka ta kashe wayarta,duk da haka dai abin ya ƙi barin zuciyar Husna.

08105217201
Hussy Saniey.????
*RASHIN ADALCI 2021*

*NA*

*HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*PAGE 47*

A haka aka gama bikin Umma,sai dai fatan zaman lafiya tsakanin ango da amarya,bayan bikin Umma da sati ɗaya aka shirya zuwa gidanta cin cin-cin da dubulan.
Ranar asabar da misalin ƙarfe huɗu na marece suka je gidan,sun samu tarba mai kyau daga wurin ango,inda yai masu jagora har cikin gidan,nan dai aka gaisa cikin girmama juna,bayan gama gaisuwar nan fa aka gabatar masu da abinci, abincine mai rai da lafiya.
Fried rice da Cus-cus aka dafa masu,sai farfesu naman kaza,ga haɗaɗɗen zoɓo da ka tanadar masu,nan fa suka ci suka sha.
Fira aka ɗora da ita,nan fa aka shiririce basu baro gidan ba sai da aka fara kiran sallar magrib,sun yaba ƙwarai da irin tarbar da suka samu a wurin Umma,inda kowa ya taho da ledarshi cike da dubulan.
A kwana a tashi a haka dai ake ta gudanar da rayuwar,yau fari gobe baƙi,a wannan tsakanin abubuwa da yawa sun faru ciki kuwa harda sabbin mutanen da aka kawo gidan ƴan amana,bayan waɗanda aka yi ma aure,dan bayan bikin Umma sai da aka yi bikin mutum biyu,Asiya da Zulaihat kuma duk sai da ƴan amana suka haɗa masu party ga bikinsu.
Ana haka wayar Husna ta samu matsala,dan haka ta daina chat har lokacin kuma idan wani abu ya faru a gidan ƴan amana tana zuwa,cikin wannan lokacin ne aka sanya bikinta da Ibrahim,sa bikin da ya girgiza mutane dan basu yi tsammanin soyayyar gaske ake yi ba,duk dai an ɗauka iyakarta cikin gidan ƴan amana.
Nan fa mutane suka rinƙa fitowa suna nuna murnarsu,wasu kuma baƙin cikine fal ransu,sanya bikin da sati guda aka yi Asharalle, ƴan amana sun nuna ba jinta sosai a wannan wurin,dan su zuba kuɗi kamar ba gobe,a nan ne Husna ta ga baƙin fuskokin da aka sanya bayan daina chat ɗinta (har lokacin ba ta koma yin chat ba).
Yin Asharalle da ƙwana biyu matar Sulluɓawa ta haihu,ranar suna daga islamiyya Chairman ya ɗauki Husna suka tafi,akan hanya aka biya aka ɗauki wata sabuwar member mai suna Zarah,nan suka rinƙa fira da Husna kamar ba yau ce ranar da suka fara haɗuwa ba.
Su Maryam aka biya aka ɗauka,nan fa Husna ta ɗan lura da Maryam ta chanza mata, Husna ba ta kawo komai a ranta ba,ko da ta tambayi Maryam lafiya sai ta ce mata bata jin daɗine,dan haka sai ta yi mata addu’ar samun lafiya,amma abin da ya ba Husna mamaki sai ta ga lafiya lau take magana da sauran mutane,sai ta kyale kawai dan ta yadda akan Maryam ba ta da lafiyar.
Akan hanyarsu ta dawowane ana fira nan Husna ta ji ashe Chairman da Zarah har soyayya suka yi,amma yanzu sun rabu,bayan an sauke Maryam a gidansu ne Zarah ke ba Husna labarin abin da ya haɗasu,sai Zarah ta ce Husna ta yi masu Shari’a, Chairman ma ya yarda da wannan abun da Zarah ta yi,ita kuma Husna nan fa duk inda taji mutum ya yi ba dai-dai sai ta faɗa masa,basu rabu ba har sai da Husna ta maida wannan soyayyar.
Nan fa Zarah da Husna suka zama ƙawaye, Chairman ya ji daɗin wannan sulhu da Husna ta yi masu sosai,nan suka koma soyayya shi da Zarah, kasancewar shi da Zarah duk basu da haƙuri sai kuma suka sake samun saɓani fiye da na farkon.
Wata rana yaron Abu Abdul Rahman bai da lafiya zasu je ganinshi,akan hanya nan take jin labarin rabuwar a bakin Chairman da Maryam,inda Maryam ke faɗin akan wannan saɓanin Zarah sai zarya take a gidansu wai ta sasanta su,shi kuma Chairman na faɗin Zarah ba ta da kamun kai duk ta liƙe ma shi,ko da Husna ta ji maganar ta yi yawa sai take nuna masu hakan bai dace ba su daina,ba a shiga faɗan masoya nan fa Maryam ta ɗaure fuska, Husna ba ta damu ba saboda zuwa yanzu ta saba da chanjin da Maryam ke nuna mata,ta yi tambayar akan abin da ya faru kuma har ta gaji,nan Chairman ke faɗar da gaske Zarah ta liƙe ma shi,sai Husna ta ce,”aikuwa Chairman da zan ba Zarah shawara ta ji da nace ta rabu da kai!”
Dan Husna ta ji haushin yanda ake muzanta Zarah a cikin mutane,duk da ba a gabanta bane amma dai kowa ya san Zarah.
“Da kuwa har kyauta sai nayi maki.”
Chairman ya faɗa dan bai yi tunanin Husna da gaske za ta iya gayama Zarah ba.
“Insha Allah kuwa sai na faɗa mata.”
Husna ta faɗa cikin jin haushi,Ahaka aka yi wannan tafiyar dai babu daɗi.
Bayan wasu kwanaki Ibrahim ya sai ma Husna waya,dan haka ta koma yin chat,wata rana da daddare sai ga Zarah ta yi ma Husna sallama,nan suka gaisa tare da tambayar bayan saduwa,nan ne Zarah ke faɗama Husna ai sun rabu da Chairman, Husna ba ta nuna ta san sun rabun ba sai ta yi mata jaje,nan Zarah ke nuna mata Chairman sai bibiyarta yake yi,sai Husna ta ce,”Zarah da zan ba ki shawara ki ji da nace ki rabu da Abba,tun da dai tarayyar ku ta ƙi yiwuwa.”
Sai Zarah take ce wa,”Husna ai na rabu da Chairman shi ne dai ya liƙeman kullum sai ya man magana.”
“Zarah wannan rayuwar ba ta yiwuwa a haka,an rasa gane mai gaskiya a tsakaninku,shi ya ce ke kike liƙe ma shi ke kuma kin ce shi yake liƙe maki.”
Husna ta faɗa dan ita Husna ba ruwanta da ɓoye-ɓoye,kai tsaye take abu.
“Wallahi ƙarya ne amma ke waya faɗa maki?”
Zarah ta tambayi Husna, Husna kuma ta amsa mata da Chairman ya faɗa,kuma da gaske yake tun da har gidansu Maryam Zarar na zuwa akan ta sasanta su.
“Na shiga ukku ƙarya ne wallahi ban taɓa yi ma kowa magana ba akan tsakanina da Chairman ba,Amma sai nayi masu magana dan ƙarya suke man.”
Zarah ta faɗa dan dagaske ba ta taɓa zuwa gidansu Maryam ba,ita kuma Husna ta ce,”to shi kenan kina iya yi masu maganar dan ni dai su suka faɗaman.”
“Zan kuwa yi masu Nagode.” Zarah ta faɗa.
“Bakomi Zarah ke dai idan ma kina liƙe ma shin ki daina,saboda ke macece kuma Mace da kunya aka santa.”
Husna ta faɗa,nan suka yi sallama ita da Zarah.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button