HAUSA NOVELRASHIN ADALCI Complete Hausa

RASHIN ADALCI Complete Hausa

08105217201
Hussy Saniey.????
*RASHIN ADALCI 2021*

*NA*

*HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*PAGE 49*

Da daddare wurin ƙarfe goma Husna na chat,kawai sai ta ga Chairman ya kira sunanta a gidan ƴan amana,shiga ta yi tare da amsawa sai ya ce mata,”Husna wai ina Sakwara ta ne?”
Ran Husna ya kai kololuwar ɓaci ta ce,”Chairman ban yi ka je ka kai kuɗinka ka siya mana ka fa dameni!”
“Ke fa ba ki da kunya wallahi Husna,” Chairman ya faɗa,a wannan lokacin ita ma Husna ranta a ɓace yake sai ta ce,”eh ba kai ƙarya ba,ban san kunya ba amma idan kaje kasuwa sai ka siyoman!”
“Aikuwa yanzu za ki ji ta in dai kunya ce,” Chairman ya faɗa, Husna ba ta yi sanya ba wurin maida ma shi da martani ba dan haka sai ta ce,”insha Allah babu kunyar da zan ji dan ban aikata abin jin kunyar ba.”
“Ibrahim, Maryam, Husna ku fito ina da tambaya,menene hukuncin maci amana? Mu ci gaba da zama da shi ko mu koreshi?” Chairman ya faɗa,kafin kowa ya yi magana sai Husna ta riga ba shi amsa ta ce,”in dai an tabbatar da cin amana ya yi tabbas zama da shi bai da amfani!”
“Yauwa yanzu kuwa kowa zai ga maciya amanar gidan nan,dan haka muna ba kowa haƙuri dan mun san zamu ɓata ma wani rai,”
Chairman ya faɗa,sai Husna ta ce,”amma koma waye idan aka gabatar da shi ya kamata a ba shi ikon kare kanshi.”
“Wannan maciya amana,macijiya ba kowa ba ce face Husna tsohuwar PRO ta gidan ƴan amana,ba mu yi wannan abun da niyyar ƙage ba har sai da muka tabbatar ta hanyar manyan hujjoji,duk wanda yake so ya tabbatar kuma zai iya tuntubar Maryam Ɗan Ali.”
Wannan shi ne doguwar wasiƙar da Anty Maryam ta turo,wata irin faɗuwar gaba ce ta riski Husna,ku san sakin wayarta ta yi tare da salati mai ƙarfi,ko ina na jikinta rawa yake,magana take so ta yi amma ta gagara yin typing ɗin,dan dole ta danna voice da muryarta dake cike da tashin hankali.
“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un…Allahumma ajirni fi…musibati wa’akalibni khairan minha…me na aikata da zafi da na chanchanci a jefeni da wannan miyagun kalmomin?”
Husna ta yi maganar cikin tsantsan tashin hankali,kafin ta sake yin wata maganar sai ta ga record ɗin Chairman ya shigo,dan haka sai ta duba ga abin da ya ce,”ba mu da lokacin sauraren duk wasu kalamai naki na borin kunya,yanzu zamu fitar da ke dan yanzu ba ki da gurbin zama a cikin gidan nan, Husna ko lahira ban fatan Allah ya sake haɗa mu dake,nayi danasanin saninki a rayuwata.”
Kafin ta ba shi amsa har an yi removing ɗinta daga gidan ƴan amana,zuwa wannan lokacin hawaye sun daɗe suna zarya akan fuskarta, babban tashin hankalinta shi ne akwai mutanen dake ganinta da mutunci sosai amma ta san ya zuwa yanzu mutuncinta ya daɗe da zubewa a fuskarsu,sai tunani take na son lalabo laifin da ta aikata,ita dai ta san babu wani abu da ta yi idan ma akwai to bai wuce magana da Zarah ba,idan kuma wannan ce ai ya kamata a bata dama domin ta kare kanta,kuka take har da shessheka,wata dubara ce ta faɗo mata a rai,cikin sauri ta danna kiran Chairman amma har sau biyar bai ɗaga ba,kuma tana ganinshi a online ɗin,nan fa ta bi Anty Maryam private tana tambayarta abin da ta aikata,sai Maryam ta ce,” Husna kin ci amanarmu,kin sanyani cikin tashin hankalin da ban taɓa shiga cikin shi ba,nayi kuka sosai amma babu abin da zan ce maki sai kije Allah ya isa!”
“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!! Dan Allah Anty Maryam ki faɗaman me na aikata maku da zafi haka?”
Husna ta faɗa wasu sabbin hawaye na sake kwaranya akan fuskarta, Maryam ta sake maido mata amsa da cewa,”har ma kina da bakin tambayata? To bari na turomaki sai ki gani.”
Nan Maryam ta turomata da screen shot ɗin chat ɗinsu da Zarah,har ma da wayar da suka yi da marece,amma abin da ya bata mamaki shi ne yanda babu maganar Zarah sai maganarta kawai,nan fa hankalinta ya ƙara tashi,nan mutane suka rinƙa yi mata magana akan ba za su yarda ba sai sun bi mata haƙƙinta,zuwa wannan lokacin Husna wani ciwon kai mai tsanani ya dirar mata, hankalinta bai ƙara tashi ba sai da aka turo mata screen shot ɗin maganganun da mutane suka yi bayan fitarta,nan ta ga wasu na nuna rashin amincewa akan abin da aka mata,wasu kuma na ba da goyon baya,babban abin da ya ƙara ta da mata da hankali sai mummunan raddin da Ibrahim ya yi,kuka Husna ta yi shi a wannan daren har hawayenta suka ƙafe,yanda ta ga dare haka ta ga rana,duk da ƙoƙarin Abdul Dabai da Abdul Mai kasuwa,da wasu daga cikin ƴan group ɗin,ta ga ƙauna sosai a wannan daren har ma da wurin mutanen da ba ta magana dasu a cikin gidan,amma suna bayanta tunda duk maganar da aka yi a group suna turo mata ta san duk abin da ke faruwa,ta yi mamaki sosai yanda har wannan lokacin Ibrahim bai mata magana ba.

08105217201
Hussy Saniey.????
*RASHIN ADALCI 2021*

*NA*

*HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*PAGE 50*

Lokacin da gari ya waye, Husna ko idanuwanta ba ta iya buɗewa saboda tsabar kukan da ta sha,ga kanta na wani irin yi mata a zaɓaɓɓen ciwo,rikicine mai yawa ya tashi a gidan ƴan amana dan sun nuna basu yarda ba akan hukuncin da aka yanke ma Husna ba.
In da su kuma offials ɗin suka yi shiru suka kyale kowa,ganin hakan bai hana members magana ba dole suka sanya admins suka rufe gidan,wurin ƙarfe goma na safe dole aka sada Husna asibiti saboda yanda numfashinta ke sarƙewa, hankalin ahalinta ya tashi sosai dan likita ya sanar dasu damuwace tai mata yawa,nan aka tsare Husna akan ta faɗi abin da ke damunta amma sai ta nuna ita ba ta da damuwar komai,dole ba dan an so ba aka kyaleta.
A haka Husna ta gama jinyar jikinta a gadon asibiti,ko a lokacin damuwa ce fal ranta,tana daurewane saboda iyayenta,saboda zuwan wasu daga cikin gidan ƴan amana ganinta shi ne ya hana a gane matsalata samu dasu,har lokacin kuma Ibrahim bai kirata ba,sai a bakin Dabai ne take jin wai Ibrahim soyayya suke shi da Maryam, wannan labarin sai da ya kusa maida Husna akan gadon asibiti,bayan ƙwana biyu da jin wannan maganar, Ibrahim ya turo mata da saƙon fasa bikinsu,in da yake sanar da ita ya yafe duk kayan da aka kawo.
Nan fa hankalin Husna yai mummunan tashi,ta shiga damuwa sosai wanda kallo ɗaya za kai mata ka tausaya mata,ko magana sai dole take yin ta,ita har gobe ta rasa gane dalilin da yasa suka aikata mata haka,in akan maganar da suka yi da Zarah ne ai da amincewar Chairman ta yi ma Zarah magana,iyayen Husna sun tsareta akan ta sanar dasu abin da ya haɗata da Ibrahim amsa ɗaya take basu shi ne ba ta sani ba,shi ma ko da aka tuntuɓeshi sai ya ce ba komai,jin haka yasa iyayen Husna hassala suka kyaleshi.
A haka Husna ta ɗauki komai ta fauwalama Allah,har lokacin kullum sai ta yi kuka dan ita dai ba ta ga abin da ta aikata ba,wata rana suna magana da Dabai nan take fadamasa ita fa sai ta gano dalilin da yasa suka aikata mata haka,nan yake ɗaukar mata alƙawari akan sai ya gano mata koma miye,bayan ƙwana biyar da yin maganarsu sai ga shi kuwa ya gano dalilin,ashe saboda Maryam na son Ibrahim shi yasa ita da Chairman suka aikata haka dan su raba Husna da Ibrahim ɗin, girgiza kai kawai Husna ta yi ba ta sake cewa komai ba,sai dai cikin ranta take ce wa,”da sun sani da basu zubar man da mutuncina ba,amma bakomi akwai Allah.”
Wannan fitar da Husna da aka yi daga cikin gidan ƴan amana,sai mutane da yawa suka fita daga gidan dan zuwa yanzu kowa yasan dalilin Chairman da Maryam na aikata ma Husna haka,rayukan mutane ya ɓaci sosai dan haka su kai ta fita, waɗanda suka zauna kuma sai suka daina magana,ganin haka yasa Chairman ya sanya offials suka kawo masu sabbin members,haka kuwa aka yi nan aka cika gidan da mutane masu yawa.
Bayan wata huɗu,komai ya faru a wannan watannin a gidan ƴan amana,ciki kuwa har da rabuwar soyayyar Maryam da Ibrahim,in da sabbin members ɗin da suka kawo basu magana,nan fa suka ciresu aka sake sabon zubi,nan ma dai ƴar gidan jiyan,dan haka suka yanke shawarar maido tsaffin members ɗin gidan,dan haka suka shirya zuwa har gida suna ba tsaffin members haƙuri,ko da suka zo gidansu Husna sun ba ta haƙuri sosai har sai da zuciyarta ta yi sanyi,in da ta amince za ta koma gidan,amma cikin ranta ta yi niyyar sake fita,haka dai aka maida Husna cikin gidan ƴan amana,amma tamkar babu ita cikin gidan saboda ba ta magana ko kaɗan,nan aka sake yi mata magana akan rashin maganarta,nan take sanar dasu za ta ci-gaba,haka kuwa aka yi ta kan yi sallama har ma wani lokaci ta ɗan yi labari da wanda ke kusa,har lokacin kuma basu magana da Ibrahim da Maryam amma idan ta yi sallama suna amsawa,komawarta da sati biyu ta sake barin gidan saboda zamanta na tuna mata da abubuwan da suka faru,har yanzu ta kasa manta yanda abubuwan suka kasance,duk lokacin da ta kallesu tana jin zafi a ranta,dan haka ta fita daga gidan, wannan fitar da ta yi ce fa, Chairman ya bi ta yake bata haƙuri da sanar da ita ba laifinshi bane,kuma ya aikata hakan ne saboda Maryam amma ta yi haƙuri,nan ta nuna ma shi babu komai,amma dai gaskiya ba za ta sake zama a gidan ba,ta dai masu alƙawari duk in za su yi wata hidima aka gayyaceta za ta je,ba dan sun so ba kuwa suka amince.
Bayan wasu watanni aka tashi bikin wata A’isha,nan ƴan amana suka gayyaci Husna zuwa bikin babu musu kuwa ta amince,har gida aka zo aka ɗauketa,ko da zuwansu kuwa irin mutanen da ta gani cikin gidan ƴan amana sai da ta yi hawaye,saboda gidan ya lalace duk ƴan bariki aka tara cikin gidan,iskanci dai kala-kala ake yi a gidan yanzu,sai dai kawai ta bisu da addu’ar shiriya, Wata uku da zuwanta bikin kuma aka yi bikinta, ƴan amana sun zo har suka kawo mata kyauta,amma dai duk wanda ya sansu a da ya ga ƴan group ɗin a yanzu sai ya yi hawaye,saboda babu mutanen kirki sosai a gidan,duk wanda Husna ta sani a gidan yanzu babu shi a ciki,daga Chairman sai Maryam kaɗai ne a cikin tsaffin members ɗin gidan,ita kanta Maryam ɗin ta yi laushi sosai,tun tana kunyar haɗa ido da Husna har dai ta saki jikinta saboda yanda Husna ke janta a jiki,bayan mutane sun watsene Maryam ta samu kebewa da Husna,nan take roƙon Husna gafara akan abubuwan da ta aikata mata,nan Husna ke nuna mata ba komi ai Bawa bai wuce ƙaddararsa,kuma Ibrahim Allah ya rubuta da ma ba mijinta bane,ga shi yanzu ta samu wani har ta yi aurenta,ita ma yana mata addu’ar Allah ya kawo mata miji ta yi aurenta,kuka Maryam ta fashe da shi tare da yi ma Husna godiya,shiru Husna ta yi bayan tafiyar Maryam,babu abin da take tunani sai abubuwan da suka faru a baya,amma ita dai babu abin da za ta ce da Allah sai godiya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button