Page 1 Wata matashiyar budurwace kwance saman gado, ta fitar da ɗaya hannunta daga cikin bargon da take lullube, ta ɗauke wayarta da ke ajiye gefen filon da ta dora kanta a kai. Tana ɗaukar wayar ta mayar da hannunta cikin bargon ta kara lullubewa har saman kanta, ta kunna datar wayar babu ɓata lokaci messages(sak’onni)su kai ta shigowa tsayawa ta yi har suka gama shigowa wani group da tafi so a dukkannin groups din dake wayarta ta shiga,sallama ta yi cikin group din wani friend(abokinta)dake kusa ya amsa mata sallamar. Gyara kwanciyarta ta yi domin taji dad’in yin chat ɗin, “Abdul ina sauran mutanen group ɗjn suka shigane su fito muyi fira mana?”. Dariya Abdul ya yi kafin ya ce; “kinsan mutanen gidan tsoron sanyi suke suna chan kwance har yanzu basu tashi ba”. Murmushi Husna ta yi tace; “ai na yadda matsoratane sai sun zo kaji yadda zasu cika mana gida da surutu”. Dariya Abdul ya yi nan suka cigaba da firarsu, sun kai wajen minti talatin kafin wani ya shigo. “Kai waye ya faɗa maku sanyine ya boyemu?” Inji wani Mubarak da shigowarshi kenan ya samu suna maganar ya shiga shima,(shima Mubarak yana cikin members ɗin group din). “Husna kin ga ɗaya nan ya fara leƙowa har ya fara cika mana baki koh?” Cewar Abdul Husna ta ce; kyaleshi Abdul borin kunya ne tun yaushe muke nan muna fira ba wanda ya tashi sai yanzu” Mubarak ya ce; “Injiwa yace yanzu nazo? tun ɗazun Ina kwance Ina kallonku”. Husna ta turo irin sticker ɗiin nan wadda ake amfani da ita gurin nuna alamun anyi murguɗin baki. “Ke waki ke murguɗa ma baki? Inji Mubarak. Husna ta sake turo wata sticker ɗin irin ta gwalo kafin daga bisani tace; “da kai nake”. “Ke yarinyar nan kin raina mutane sai na kamaki za kiyi bayani ni dai kike murguɗa ma baki koh?” Murmushi Husna ta sa ke yi kafin tace; “naga zaka zo mana da wata bidi’a ne bayan kaje ka kwashi baccinka amma zaka fara cika mana baki yanzu”. “Husna ke kike tsayawa ma bashi amsa Mubarak ɗinne zai iya jurewa ana magana ya yi shiru?” cewar Abdul “To nagane kai ke sanyata yi man rashin kunya kenan zanyi maganinku gaba daya kuwa” Dariya Abdul ya yi sannan ya ce: “gaskiya ai ta faɗa borin kunya ne kake mana bayan yanzu kazo”. Dariya Husna ta rinƙa yi ma Mubarak tana faɗin “Malam kayi ladab saboda nan dai mun ganoka” Mubarak ya ce; “Hmmm yarinya za kiyi bayani dalla-dalla dani kike zancen”. Abdul ma ya rinƙa dariya ya na fadin “daɗina da kai abokina saurin shiga yanzu har ka sakarmata ta fa yi galaba akan ka kenan” Husna cikin sauri ta turo sticker mai ɗauke da alamun zaro ido tace; “haka ka koma Abdul?” Dariya Abdul ya turo da ita bai ce komai ba. Mubarak ya ce; “ƙyaleni da ita aboki zan rama dani take zancen ai”. Husna tace; “Ni zaku nunawa ban-bancin jinsi bari kakata tazo nasan zata shigar man” “Dalla matsa gefe ai wannan kakar taki ita ma zata taddamu dama ita ke sawa kina mana rashin ji cikin group ɗin nan” inji Mubarak. Husna turo wata sticker ɗin tayi mai alamun mutum zai kai bugu tace; “Eh Ina ruwanka kakar kace ko tawa,kuma babu wanda ya isa ya takura mana gidan nan ni da ita eheeey”. “Haba yarinya jikinki zai gayamaki mu dai kike ma haka koh?” Inji Abdul. Husna tace, “Eh da ku nake ni bari ma nayi tafiyata tunda kakata bata fito ba sai anjimanku”. “Yauwa gara ma kiyi tafiyar taki ko mun huta da yen yen yen ɗinki”, Inji Mubarak. “Ƙara gayamata abokina wannan yarinyar duk ta ishi mutanen gidan nan”, Inji Abdul. Dariya Husna tayi tace; “wallahi kun dai faɗa ne kawai amma ai basu iya rayuwa idan babu ni cikin group ɗin nan ni ce fa farin cikin gidan” “Ke koma gefe kada na dake ki wacece farin cikin ko dai ciwon kanmu ba” cewar Isa da zuwanshi kenan cikin group din ya datsi maganar. “Ƙara gayamata dai Isa wannan yarinyar sai munyi maganinta cikin gidan nan” nji Abdul. “Ha ha ha naku wasane maganina ai sai Allah ba dai ku ba, bayan ma idan babu ni kun rinƙa kiran wai ina Husna baku da natsuwa har sai na hau”, ta fad’a tana dariya saboda tasan ta jawosu kenan. “Je kiyi ta istigifari yarinya dan wannan saɓone ki kayi waye yake ta ke” Inji Isa. “Ban da lokacinka Malam ni dai na faɗa kuma kun sani nice farin cikin gidan nan dan haka na mayi tafiyata” Husna na faɗar haka ta rufe datar wayarta tana dariya saboda ta san ta tsokano su. “Yarinya dole ki ruga tunda kinsan mataki zamu ɗauka amma zaki dawo ai” cewar Mubarak. *Hussy Saniey *???? *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY * Page 2 Husna na sauka online, dariya ta kama yi saboda ta san ta kunna Isa,sai da tayi dariya mai Isar ta sannan ta mik’e ta fara da gyara d’akinta sannan ta fita tsakar gida ta fara aikin da ta san ya zamo ita ke yin shi,sai da ta gama gaba d’aya aikin sannan ta shiga wanka a gurguje kasan cewar rana ta fara yi,cikin sauri ta shiga d’akinta ta shirya domin tafiya makaranta,agogo ta kallah k’arfe goma na safiya cikin sauri ta k’arasa shiryawa,fitowa ta yi daga cikin d’akinta da jikkar da kayan karatunta suke ciki,bisa kujera ta aje jikkarta ta nufi kitchen inda ta jiyo motsin mahaifiyarta. “Mama ba ki k’arasa bane ga shi na makara ina sauri dan ina tsoron ace ba zan samu lecture ba”,ta fad’a ta na mai kai hannu gurin bokitin da Maman ta dama masu kunu. “Ko kin makara Husna ai laifin kine ba zamanki d’aki ki kayi ba”, Mamanta ta fad’a ta na mik’o mata filet d’in da ta zubo mata fanke. “Mama group d’in y’an amana na shiga muka d’an gaisa “, ta fad’a ta na kai kofin kunu bakinta. Girgiza kai Mamanta ta yi ta ce, “ba ki da magana sai ta group yanzu tunda kin gaisa dasu ai hankalinki ya kwanta koh?” Murmushi Husna ta yi ta ce, “Mama kin san a duk duniyar WhatsApp babu group d’in da nake jin dad’in shi kuma nake so har a raina kamar shi”. D’agowa da kai Mamanta ta yi ta ce, “in dai ana son aji dogon sharhi gurinki to a tab’a y’an group d’in y’an amana”. Dariya Husna ta yi ta na tauna fanken bakinta sai da ta had’iyeshi kafin ta ce, “Mama group d’in ne ya yi wallahi mutanen da ke ciki suna da bala’in mutunci”. Kallonta Mamanta ta yi yadda ta hak’ik’ance ta na yab’on mutanen da ko had’uwa dasu ba ta tab’a yi ba sai dai a chat d’in, “Husna kiyi sauri ki gama ki tafi kada ki makara saboda ke ba gajiya za kiyi ba”. “To Mama kin san kuwa d’azun sai da na hayak’a Mubarak dashi da Abdul “, Inji Husna. Kallonta Mamanta ta yi ta ce, “bangane mekike nufi ba?”. Sai da Husna ta cinye fanken da ta sanya ta kora da kunu sannan ta ce, “kwantar da hankalinki Mamana ba wani abu bane kawai dai na ce masu ni ce farin cikin y’an amana ne shine su kai ta musu nasan yanzu sadda zan bud’e data sai naga chapter d’insu kin san Isa ya k’ware da musu”. Bayyanannar ajiyar zuciya Mamanta ta sauke ta ce, “ku dai baku gajiya da shirme”. “Ai Mama dan ma su Umar basu kusa duk su na chan basu tashi bacci ba wani abun ma sai nadawo daga makaranta akwai dirama lokacin kowa ya fito “, Inji Husna. “Kin san wani abu Mama?”, Inji Husna. Kallonta Mamanta ta yi ta ce, “sai kin fad’a “. Murmushi Husna ta yi ta ce, “Mama ina rok’on Allah ya nuna man ranar da zamu had’u da y’an amana gaskiya Mama ranar akwai bidiri bured’ed’e”. Dariya Mamanta ta yi ta ce, “Husna ba ki dai rabuwa da shiririta “. “Kin san Allah dagaske nake Mama ranar zan ji dad’i sosai har a raina kai Allah ya kai damo ga harawa ko be ci ba yai birgima”, Inji Husna ta karasa fad’a ta na sa kin wata dariya irin ta duniyar tai maka dad’i. Kallon Husna mahaifiyarta ta yi cikin ranta ta na jinjina irin soyayyar da yarinyar ta take ma mutanen dake cikin wannan group d’in tun kafin ma su ga junansu, ba ta da maganar yi sai ta group d’in y’an amana. Dariya Husna ta yi ta aje kofin da ta shanye kunu,wanke hannunta ta yi sannan ta kalli Mamanta ta ce, “ Mama na tafi sai na dawo “. Kud’i Mahaifiyarta ta mik’o mata ta ce, “Allah ya tsare hanya Husna a rink’a kula da mutane kin san wurine da ya had’a jinsin mutane kala-kala dan haka a san irin wad’anda ake mu’amala dasu”. Ansar kud’in Husna ta yi ta ce, “ameen Mama kuma insha Allah Mama zan k’ara kiyayewa na tafi sai na dawo”. “Allah ya maido ki lafiya Husna”, Inji Mamanta. Husna da har ta kai ba kin kofar shiga zauren gidan ta juyo ta ce, “ameen Mamata”. Husna fita daga gidansu Adai-daita sahu ta tare zuwa makaranta,cikin sa’a kuwa ta na zuwa ko zama ba ta yi ba lecturer d’in ya shigo, wata naunauyar ajiyar zuciya ta sauke,cikin sauri ta zauna kusa da k’awarta Mieynart,kallonta Mieynart ta yi su kai ma juna murmushi. Mahaifiyar Husna ta na ganin yarinyar ta ta fita daga gida,sai ta shiga tunanin wannan wace irin kauna ce ke tsakanin d’iyarta da mutanen wannan group na y’an amana,Allah yasa su ma haka suke jin soyayyarta cikin ransu. *Hussy Saniey *???? *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *RASHIN ADALCI* 2021 *NA* *Hussy Saniey* Page 3 Husna su na fitowa daga lecture har sauri take domin ta fiddo wayarta daga cikin jikka,sai da ta dauk’o wayar sannan ta kalli Mieynart dake gefenta ta ce,”Mieynart wai kin jiya kuwa Uncle T yazo gidanmu?”. Kallonta Mieynart ta yi cikin sauri ta ce,” dagaske ki ke?wallahi har kin sa gabana ya fad’i to ya aka k’are da yazo”. Murmushi Husna ta yi ta na bud’e datar wayarta ta ce,” gaskiya Mieynart tsoronki ya yi yawa meye abun fad’uwar gaba daga na gayamaki Uncle T yazo ina ga ke ya tadda da yazo?Allah ya bani hakuri ni da yazo ya tirke “. Jan hannun Husna ta yi har sai da suka kai wurin wani benci,zama su kayi sannan Mieynart ta aje jikkarta da handout d’in dake hannunta,kallonta ta maida ga Husna da ke kallon fuskar wayarta hankalinta kwance sai murmushi ta ke faman yi,hassala Mieynart ta yi ta warce wayar daga hannun Husna ta ce,”wai ke Husna meke damunki kin sa hankali ya tashi amma ke sai dannar wayarki kawai kike wannan ai ba hali ba ne me kyau”. Mik’a ma Mieynart hannu husna ta yi ta ce,”ki ban wayata idan har kina so mu yi magana mai muhimmanci dake saboda ina kallon firar da ake group d’in y’an amana ne shiyasa ba wai kuma na sanya masu baki bane saboda ni na had’a maganar shine su ke ta comment akan haka”. Kallon Husna Mieynart ta yi cike da takaici ta ce,”wai ke ba ki da magana sai ta group d’in y’an amana ni fa wallahi har na fara jin haushinsu ke baki da lokacin komai sai nasu ki guji ranar da zasu juya maki baya kin s…”. Cikin sauri Husna ta dad’e bakin Mieynart ta domin Hana ta fad’ar maganar da take shirin fad’a tace,”kada ki ida fad’ar abin da kike so ki fad’a saboda su ba haka suke ba”. Kallonta Mieynart ta yi cikin jin haushi ta ce,”ke Husna kina zama da mutane kuma kina rayuwa da mutane da yawa amma har yanzu kin kasa fahimtar halin mutane a lokacin da suka so juya maka baya”. Gyara zama Husna ta yi sannan ta gyara rik’on jikkarta da ta d’ora saman cinyarta tun lokacin da suka zauna ta ce,”Mieynart nasan me kike hango man amma wad’annan mutanen sun ban-banta da irin mutanen da kike zargi saboda su wad’annan suna da kirki kuma sun san darajar junansu baki ga yadda ake komai a tare ba ko ke in da kin zauna dasu nayi imani za ki ji dad’in zama dasu sosai amma banjin dad’in wannan bahaguwar fahimtar da kike masu a kullum ana so ka rink’a kyautata ma mutane zato ba wai ka munana zato a kansu ba dan Allah ki daina banjin dad’in hakan Allah dagaske nake gayamaki”. Shiru Mieynart ta yi ba tare da ta sake fad’ar komai ba,kallonta Husna ta yi ganin ta k’i kallon inda Husnar take sai kallon mutanen da ke wucewa ta keyi,dafa kafad’ar Mieynart Husna ta yi ta ce,”nasan me kike nuna man Mieynart kuma ina fahimta amma ki sani ba kyau munana zato akan mutane sannan mutanen nan wallahi Mieynart suna da kirki sosai duk wanda ke zaune dasu yana jin dad’in zama dasu sosai kuma ni ban tab’a ganin an samu wani sab’ani garesu ba sai dai kawai fad’an da aka tab’a yi da wadda ta had’a group d’in kuma shima Ina ganin kamar rashin fahimtar junansu da basu yi bane shiyasa har abun ya kai su ga haka”. Cikin sauri Mieynart ta kalli Husna ta ce,”yanzu ina wadda ta had’a group d’in take?”. Husna ta ce,”ta fita daga group d’in tun bayan da suka yi wannan rigimar “. Murmushi Mieynart ta yi ta ce,”wannan abun kad’ai da yasa ta fita ya isa mai hankali yasa a gane akwai matsala”. Husna kallonta ta maida ga mutanen dake wucewa wasu kuma na hurd’ar gabansu ba tare da ta juyo ba ta ce,”Mieynart wallahi bansan ai nafin matsalar da ta faru ba amma dai wasu sun d’an gayaman wani abu wai saboda ko an ba wata admin ne ke ni dai banji wani cikakken bayani ba”. Murmushi Mieynart ta yi ta ce,”Husna ba wai ina son rabaki da wad’annan mutanen bane amma *gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah*dan haka ku shiga hankalinku wallahi”. Ajiyar zuciya Husna ta sauke ta ce,”To Mieynart abin da yasa kika ga ban fita daga group d’in ba kinga bansan meya had’a su ba kinga ai bana shiga tsakaninsu ba amma dai kamar yadda kika fad’a d’in zan yi kokari ina kiyayewa”. “Hakan dai ya kamata saboda kinsan *Banza ba ta kai Zomo kasuwa* duk abin da zai sanya wadda ta had’a group d’in ta bar shi to ba k’aramin abu bane dan haka kuma sai kun yi taka tsan-tsan”. Mik’ewa tsaye Husna ta yi ta rataya jakarta a saman kafad’a ta ce,”insha Allah zan kasance mai lura akan hakan in naga da matsala sai na fita salin alin nima ki tashi mu tafi masallaci mu yi sallah kada lokaci ya k’ure mana”. Mik’ewa Mieynart ta yi ita ma ta ce,”muje masallacin sai ki gayaman yadda ku kayi da Uncle T d’in kafin lokaci ya k’ure mana”. “To shikenan mu fara zuwa mu sayi ruwa sai mu wuce masallacin dama k’ishirwa nake ji tun d’azun wallahi “,Inji Husna. Tafiya su kayi domin zuwa sayen ruwa,suna tafiya suna fira a tsakaninsu inda suka had’u da wad’anda suka sani su tsaya su gaisa da haka har suka isa inda ake saida ruwa. Hussy Saniey.???? *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* RASHIN ADALCI 2021 NA HUSSY SANIEY PAGE 4 Bayan fitowarsu Husna daga masallaci,zama su ka yi gaban Hall d’in da zasu yi lecture,suna zama Mieynart ta kalli Husna ta ce,”ba ki gayaman yadda ku kayi da Uncle T ba”. Murmushi Husna ta saki kafin ta juyo ta fuskanci Mieynart ta ce,”K’awata Uncle T fa ya fad’a tarkon ki”. Zaro idanuwanta Mieynart ta yi ta dafe kirji ta ce,”K’awata ba mu irin wannan wasan fad’a man gaskiya dan Allah “. Hannunta Husna ta rik’e ta ce,”dan Allah ji yadda kika koma cikin mintina k’alilan sai kace wadda aka aiko ma da sak’on mutuwa”. Ajiyar zuciya Mieynart ta sauke ta ce,”wallahi abin ne ya ban mamaki mutumin da girman kai da miskilanci su kai ma shi yawa shine har za ki iya fad’ar ya fad’a tarkona wai shin ma meya gayamaki da har kike wannan maganar”. Dariya Husna ta saki cikin son tsokanar Mieynart ta ce,”ya fad’a man ya lura kina son shi shiyasa zai tausaya maki ya aureki”. Wata irin zabura da Mieynart ta yi har sai da ta tsorata Husna ta ce,”na shiga ukku K’awata k’aryata ta k’are na gama yawo dagaske haka ya fad’a maki?”ta k’arasa fad’a idanuwanta cike da hawaye wanda a ko wane lokaci suna iya zubar da ruwa. Dariya Husna ta k’ara kwashewa da ita sannan ta mik’e ta rik’o hannun Mieynart ta ce,dallah ni har kin ban tsoro wallahi ji yadda fuskarki ta koma gaskiya ke ba k’aramar matsoraciya ba ce “. “Dan Allah ki fad’a man gaskiya Husna wallahi hankalina ya tashi sosai idan ya gane ina son shi ai babu k’ima ni kuwa kin san duk abin da zai sanya na rasa k’imata na tsane shi,”Mieynart ta fad’a ta koma inda ta tashi ta zauna tare da share gumin saman fuskarta. Kallonta Husna ta yi ta sake fashewa da dariya ta ce,”kin ganki kuwa kin zama wata kalar tausayi ina ma nayi maki video dan na rink’a kallo duk in na tuna”. “Wallahi ba kiji dad’in halinki ba Husna amma da ni kike zancen zan rama,”Mieynart ta fad’a tare da d’aukar jikkarta ta nufi hanyar shiga cikin Hall d’in da zasu yi lecture dan ta lura Husna iskanci take ji shiyasa take mata haka da ta cigaba da zama tana kunnata ga ra ta koma cikin Hall d’in ta zauna ita d’aya yafi mata sauki kujerar baya ta samu ta zauna dan nanne babu cinkison mutane da yawa. Husna ganin Mieynart ta shige Hall,sai ta kama dariya ta ce,”zan fad’a maki gaskiyar yadda muka yi amma sai na gama wana ki yarinya”. Wayarta ta fiddo daga cikin jikka,Data ta bud’e sai da sak’onnin suka gama shigowa sannan ta rink’a binsu d’aya bayan d’aya ta na mai da masu da amsa,sai da ta gama dasu sannan ta shiga group d’in y’an amana. Kamar yadda ta tsammata hakance ta kasance kuwa duk wanda ya shigo yaga firarsu sai ya d’ora tashi a sama,wani sak’one da d’aya daga cikin admin d’in gidan ya turo shine yaja ra’ayinta inda yake cewa gaskiya ne maganarta ita ce farin cikin y’an amana. Amsa ta bashi da fad’ar,”yauwa Abba fad’a masu dai dan haka su rink’a lallabani”. Sak’on na tafiya kamar jira suke sai aka fara comment,sak’on Abdul ya fara shigowa wayarta inda ya ce,”dallah matsa malama in ba damun mu da kike yi ba mekike mana da har za ki wani ce kece farin cikin y’an amana,”daga k’asan sak’on sai ya turo sticker d’in dake nuna alamar an harari mutum. Kafin ta ba shi amsa sai ga Hadiza Muhammad(ita ce wadda Husna ke cema kakarta)ta turo sak’on a in da take cewa,”wannan ka dai fad’a san ranka amma ai kowa yasan jikata ita ce farin cikin mutanen gidan nan. Dariya Husna ta tura sannan ta ce,”yauwa My Kakus fad’a masu dai ki suna kishine da son da ake nunaman a gidan?”. Ibrahim da shigowar shi gidan kenan ya ce,”gaskiya K’anwata (Hadiza yake nufi)ke kike sa yarinyar nan ta na abin da ta gadama ya kamata ki rink’a yi mata fad’a”. “Haba Yaya me jikar tawa ta yi ne daga ta fad’i gaskiya ai dagaske ita ce farin cikin mutanen gidan nan,”Hadiza Muhammad ta fad’a. “Kai gaskiya ni y’ar gatace nayi abin da nake so a cikin gidan nan saboda ina da Kakata mai sona da son ganin farin cikinta,”Husna ta fad’a ta na k’ara sakin dariyar nishad’i. “Zan kama kine yarinya jikinki zai gayamaki,”Inji Ibrahim yake fad’a ma Husna. Sticker mai alamar kuka Husna ta tura ta ce,My Kakus kinji abin da yake fad’a koh?”. “Haba Yaya dan Allah ka kyaleman jikata ta yi abin da take so,”Inji Hadiza Muhammad. “Yauwa My Kakus shiyasa nake sonki saboda kina son farin cikina,”Inji Husna. “K’anwata wannan jikar taki ta raina mutane ki barni nayi maganinta kawai,”Inji Ibrahim. “Yaya dan Allah ka kyaleman jikata naga ai wasane take yi ba gashi ba har kun fito da kun bar gidan shiru,”Inji Hadiza Muhammad. “Hmmm baza ki gane bane K’anwata amma taci albarkacinki,” Inji Ibrahim. “Yauwa nagode Yaya ga amanarta nan na bar maka zan fita naje unguwa,”Inji Hadiza Muhammad. “Wallahi ban so My Kakus nima lecture zan shiga ki bar ni wurinshi dan ya rink’a cin zalin d’ina in yaga ba ki nan koh?”Inji Husna. “Kin taimaki kanki yarinya da kin yaba ma aya zak’inta a hannuna,” Inji Ibrahim. “Kai Yaya! Amma shikenan tunda ita ma lecture za ta shiga sai anjimanku ni na tafi,” Inji Hadiza Muhammad. “Malam Iroro na bar maka tsaron gidan salon ka tafi yawo ka barshi ba kowa,”Husna ta fad’a daga k’asa ta sanya sticker irinta alamar an yi ma mutum gwalo. “Da ki tsaya mana yarinya da kin gane Allah d’ayane yarinya,”Inji Ibrahim. Husna tunda ta fad’a mashi magana bata k’a fad’ar komai ba sai dariya da ta kamayi,rufe Data ta yi ta nufi Hall. *Hussy Saniey *???? Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/LmbGi3TbkTF2sUurNrJ8zZ *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* PAGE 5 Bayan fitowar Husna daga lecture wuri ta samu ta zauna,zamanta da kamar minti biyar Mieynart ta fito tare da wani ɗan Department ɗinsu,hannu Husna ta ɗagama Mieynart saboda ta lura Mieynart ba ta gantaba sai waige-waigen inda za ta hangota take,wanda ke tare da Mieynart ne ya lura da Husna da ke ta ɗagomasu hannu,”Mieynart kin ga Husna chan zaune saman dakali ta na ɗago mana hannu”. Kai tsaye inda ya nuna mata Husna zaune suka nufa,Husna na ganin sun tunkaro inda take sai ta miƙe tsaye ta nufosu,tsayawa su Mieynart su kayi har ta iso inda suke. “Wai me ku ka tsaya yi a cikin Hall tun ɗazun ina jiran ku,”inji Husna da ta ƙaraso inda suke. Gyara tsayuwa Sadam ya yi yace,”wannan calculation ɗin muka tsaya har sai da muka gama”. “Mu yi sauri ka da Bus ta cika kuma kun ga sai mun yi tafiyar ƙasa idan ba mu iske ba”, Husna ta faɗa ta na kallonsu Mieynart. “Mu yi sauri gaskiya ni Allah so nake naje gida da wuri akwai inda zanje”,inji Mieynart. “Kun tsaya kuna ta surutu da yanzu mun yi nisa a tafiyar mu”,inji Sadam Jerawa su kayi gaba ɗayansu su na tafiya,fira suke yi nan Husna ke sanar dasu yadda su kayi da ƴan group ɗin su,cikin sigar jan faɗa Sadam ya kalli Husna ya ce,”gaskiya Husna ƴan group ɗinku su na da kirki”. Cikin jin daɗin yabon da aka masu ta ce,”dan ma ba ka cikin group ɗin Allah da sai kaji kamar ai ta zama idan ana fira”. “Gaskiya Husna har naji ina son shiga group ɗin nan saboda na ga wacce wainar ake toyawa”,inji Sadam. Cikin matsanancin jin daɗi Husna ta dakata da tafiyar da take ta ce,”dagaske kana son shiga na bada lambar wayarka a sanya ka a group ɗin”. Murmushi Sadam ya yi saboda ganin yadda Husna ta ɗauki maganar da muhimmanci ya ce,”wasa nake maki Husna kin san ni bana son shiga cikin kowane group saboda matsalolin da ke faruwa a ciki”. Tun kafin ya ƙarasa maganarshi Husna ke girgiza kai sannan ta ce,”wallahi su ba haka suke ba duk wanda ya zauna dasu zai so gobe ma ya zauna dasu su na da mutunci sosai Babban daɗin guda kuma shine sun san darajar mutane ban taɓa ganin sun wulaƙanta wani ba dan haka in dai kana son shiga wallahi na bada lambarka kawai idan aka sanya ka sai kaji daɗin zama dasu fiye ma da yadda nake faɗa maka”. Dariya Sadam ya yi sannan ya ce,”kar ki damu Husna tun da kina ciki ai zan rinƙa jin labarin su hakan ma yana sanyani nishaɗi aminiyar”,ya juya wurin Mieynart da ke ta faman ɓoye dariyarta dan ka da Husna ta gani amma ka sa ɓoyuwa dariyar ta yi har sai da ta saketa a fili. Harararta Husna ta yi ta ce,”kin dai ji haushin gulma wallahi yanzu meye abin dariya anan toh?”. Girgiza kai Mieynart ta yi tare da haɗiye dariyar da take yi sannan ta harari Husna ta ce,”dan kin ga ina dariya shikenan kuma babu da wanda nake sai ke kenan ko Hajiyata?”. Bugu Husna ta kai ma Mieynart ta ce,”idan ba dani kike ba to da wa kike nan in ba ni dake magana ba kuma ai nasan akan me kike man dariya banza ai ban ce ki bada lambarki a sanya ki ba bare ki kama yi man wannan banzar dariyar ta ki”, Husna ta ƙarasa faɗa a hassale. Ganin yadda Husna ta hassala ya sanya Mieynart ta haɗiye dariyarta lokaci guda,matsowa ta yi kusa da Husna sannan ta da fa ma Husna kafaɗa ta ce,”meye abin fushi kuma Ƙawata daga magana amma tunda ba ki so shikenan na yi shiru”. Sadam ma matsowa ya yi inda suke shima tare da ƙoƙarin haɗiye ta shi dariyar ya ce,”gaskiya Mieynart ba ki kyauta ba meye abin dariya nan bayan ma ba dake ake maganar ba dan dai k…”,saurin dakatawa da maganar shi ya yi saboda wata dariya da ta taho ma shi ya yi,dan lura da yadda Husna ke ta ƙara murtuke fuska. “Nagode maku sosai ni dai ku ka maida mahaukaciyar ƙarfi da yaji ko dan kun ga ina baku labari shine har abin ya zama abin tsokana ko bakomi nagaode laifinane da nake gayamaku duk wani abu da ya danganceni”,ta ida faɗar maganar a matuƙar hassale. Jinin jikinsu su ka sha saboda ganin yadda take maganar acikin fushi,dan haka sai suka koma bata haƙuri,ko saurarensu Husna ba ta yi ba ta cigaba da tafiya. Bayanta su ka biyo babu mai magana a tsakanin su saboda ganin yadda Husna ta hassala,nan wurin Bus stop su ka tsaya dan jiran Bus. *Hussy Saniey*.???? *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* PAGE 6 Shiru zaman ya kasance a tsakaninsu,babu wanda ke da ƙwarin guiwar yin wata fira,zaman minti goma sai ga Bus ta zo,su na shiga cikin Bus ɗin Husna ta chanza kujerar zama,da kallo su ka bi ta dashi saboda abin da bai taɓa faruwa a tsakaninsu ba,duk rintsi wuri ɗaya suke zama amma yau ga shi Husna ta raba masu wurin zama. Husna na kallon yadda su ke bin ta da kallo, ɗauke kanta ta yi kamar ba ta san suna yi ba,a haka tafiyar ta kasance babu daɗi,kowa da abin da yake saƙawa a cikin zuciyarsa. Ko da aka zo inda suke sauka,Bus na tsayawa Husna ce farkon fita,bayanta su Mieynart suka bi,lokacin da suka fito har ta tsaida Keke napep. Ji ta yi an riƙe mata Abaya ta baya,juyowa ta yi suka haɗa idanuwa da Mieynart,ɗaure fuska Husna ta ƙara yi ta ce,”sakeni zan wuce!” Murmushi Mieynart ta yi,”Husna ban taɓa ganin haka a wurinki ba saboda haka kiyi haƙuri hakan bazata ƙara faruwa ba insha Allah.” Girgiza kai Husna ta yi ta ce,”bakomi ya wuce sai Allah ya kaimu gobe.” Kafin Mieynart ta ce wani abu har Husna ta shige cikin keke napep ɗin,ta na shiga mai keke napep yaja suka tafi,sai da suka ɓace sannan Mieynart ta kalli Sadam ta ce,”tun da nake da Husna ba ta taɓa nunaman taji haushin abu ba irin yau,gsky bansan wannan wace irin ƙauna ba ce take ma waɗannan bayin Allah ba.” Cikin mamaki Sadam ya ce,”ni kaina abin nan ya matuƙar ɗaure man kai,wai Husna ce ta iya nuna mana ɓacin ranta saboda mun kushe wasu!” Mieynart ta riƙe haba ta ce,”abin da yafi ɗaure man kan kenan,fatana dai Allah ya sanya yadda take son su haka su ma suke mata irin wannan son.” Gyara tsayuwa Sadam ya yi tare da ɗaga ma wani mai mashin hannu,duban shi ya maido ga Mieynart ya ce,”ameen dan gaskiya abin ya ban mamaki sosai.” Tsayuwar mai mashin gabansu shi ya hana Mieynart magana, Sadam ya kalli Mieynart dake tsaye amma da gani kasan ba ta cikin yanayi mai daɗi ya ce,”Mieynart idan naje gida zamu yi waya akan wannan case ɗin kar ki damu kinji koh?” Numfashi Mieynart ta sauke ta ce,”Sadam dagaske hankali na ya tashi saboda Husna duk yadda kake ganinta ba ta da haƙuri to wallahi ta na da kawaici ba abu kaɗan ke sanyawa ta nuna ɓacin ranta ba.” Hawan mashin Sadam ya yi sai da ya zauna sosai sannan ya ce,”kar ki damu Mieynart zamu yi magana idan na koma gida ai dole mu tabbatar Husna ta sauko daga fushin nan saboda wallahi yau ban ji daɗin yadda muka rabu ba.” Gyara riƙon jikka Mieynart ta yi ta ce,”nima abin da yafi ɗaga man hankali kenan amma insha Allah idan ta kama har gida zan taddata sai na bata haƙurin kaje idan mun koma mun yi waya sai anjima Allah ya kiyaye hanya.” Littafin da ke hannun shi ya ɗora bisa cinya,ya kalli Mieynart ya ce,”ki bari idan naje gidan duk yadda ta kama sai ayi kawai kinji kin ga napep chan kije ki hau ki gaida Mama.” Bayan wucewar Sadam babu daɗewa ta samu Keke napep,ta tafi gidansu lokacin har an kusa fara kiran sallar magrib. ************** Husna na isa ƙofar gidansu,mai Keke napep ɗin ta sallama sannan ta shiga cikin gidansu,da sallama ta shiga,Mama na zaune ta na ɗaurin kunun Aya,kallo ɗaya Mama ta yi ma Husna ta san akwai matsala a tattare da Husnar. Ganin irin kallon da Mama ke bin ta da shi ya sanya Husna washe baki ta ce,”Mama sannu da aiki na dawo.” Cikin kallon tuhuma Mama ta ce,”yauwa lafiyar ki ƙlau kuwa Husna! kin ga yadda kika yi?” Cikin ƙoƙarin ɓoye damuwarta, Husna ta yafa ma fuskarta murmushin ƙarfin hali ta ce,”lafiya lau nake Mama kawai tsabar gajiyace kawai ta maidani haka kamar marar lafiya amma lafiya lau nake babu wani abu Mama.” Ba dan Mama ta yadda ba ta ce,”ki je ki ɗan watsa ruwa ki zo ki ci abinci nasan dai kina jin yunwa?” Murmushi Husna ta ɗan yi duk don son ɓoye damuwarta ta ce,”zan dai watsa ruwa Mama amma ba na jin yunwa na ci abinci a makaranta Mieynart ta zo mana da shi.” Kallonta kawai Mama ta tsaya tana yi saboda zai yi wuya Husna ta dawo daga makaranta ba ta ci abinci ba,wani lokacin har janta ake ace an manta ba’a aje mata abincin ba,ganin irin kallon da Mama ke bin ta da shi ya sanya kawai ta shige ɗaki,dan tsab Mama na iya gano abin da take ƙoƙarin ɓoyewa,kuma ko kaɗan bata san hakan ta kasance. Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 7* Shigarta ɗaki kenan wayarta ta ɗauki ƙara,fiddo wayar ta yi daga cikin jikka,fuskar wayar ta kalla ganin mai kiran yasa ta yin murmushi,ka ra wayar ta yi a kunne bayan ta ɗauka. “Hello Assalamu Alaikum,” Husna ta faɗa cikin fara’a. Daga ɗayan bangaren aka amsa mata,”wa’alaikissalam Hajiya yau ina kika shige sai nemanki ake ko dai ɓacewa ki kayi?” Gefen gado Husna ta zauna cikin dariya ta ce,”da ma ai na faɗa maku ba zaku iya rayuwa idan babu ni ba saboda ni ce farin cikinku ga shi kuma yanzu kun kasa natsuwa saboda ban kusa damu.” Daga cikin wayar aka ba ta amsa da,”kalli wannan yarinyar abin da kike faɗa,ke ce farin cikin namu ko dai baƙin ciki?yarinya duk kin bi kin damu mutane shine kike iƙirarin ke ce farin cikin mu?” Wata dariya Husna ta fashe da ita,cikin son ta ƙular dashi ta ce,”haba Iroro ai kowa yasan ni ce farin cikin ƴan amana ga shi kun kasa nutsuwa da baku ganni ba kai kafi kowa ma kasa jurewa har sai da ka kirani.” Daga chan bangaren wanda ta kira da Iroro ya ce,”ke kalli wannan yarinyar waye ya kasa natsuwar?” Cikin sauri Husna ta ce,”Iroro mana shi ya kasa jurema rashina.” “Ba ki da lafiya yarinyar nan nine ma zan gaza jurewa rashinki?” Iro ya faɗa. Cikin dariya Husna ta ce,”ga shi nan kuwa ka gaza jurewa gaskiya ni mai sa’a ce a rayuwa tunda har kuna gaza jurema rashina a kusa daku.” “Ji wannan yarinyar sai wata magana kike wadda bansan kanta ba idan kin gama ƴan maganganun ki zan iya kashe wayata?” Inji Iro. “Baka da matsala Iroro tunda ka ji lafiyata hankalin ka ya kwanta nasan ka samu natsuwa zaka iya kashewa yanzu!” Husna ta faɗa cikin son ƙular da Iro. “Ke dai kika sani da ƴan maganganun ki,” ya faɗa tare da katse kiran wayar. Dariya Husna ta kama yi saboda ta san ta ƙular da Iro,tashi ta yi ta shiga wanka,ba ta ɗauki dogon lokaci ba ta fito,sai da ta yi alwallar sallar magrib saboda lokaci saura kaɗan ya ida,cikin sauri ta sanya doguwar rigar atampa,wayarta ta ɗauka ta buɗe data. Saman gado ta kwanta,sai da messages suka gama shigowa sannan ta shiga group ɗin ƴan amana,kamar yadda ta zata hakan ce ta kasance ba’a yi magana sosai ba,da ma duk in dai ba ita ke online ba to zaka ga ba’a cika magana sosai ba,duba maganganun ta yi gaba ɗaya ba wasu maganganu bane sai ƴan gaishe-gaishene ga duk wanda ya ɗan leƙo cikin group ɗin. Sallama ta yi cikin group ɗin,kamar ana jiran zuwanta sai ga mutane biyu sun fara amsawa, ɗaya daga cikinsu ne ya ce,”farin cikin ƴan amana yau ina kika shigane muka ji ki shiru.” Murmushi ta yi kamar yana ganinta sannan ta tura ɗan emojin nan mai nuna alamar tsalle ta ce,”naje makaranta yau sai yanzu na dawo Abdul Mai kasuwa mai ku ka ajeman na Garba?” “Allah sarki sannu kin dawo lafiya?yanzu kuwa za’a tarbeki tarba mai kyau kuwa,” Abdul Dabai ya faɗa wanda zuwanshi kenan. Abdul mai kasuwa ya turo emojin kankana da lemo sannan ya ce,”ga kayan marmari nan ki ɗan taɓa zanje masallaci na dawo naji an fara kiran sallah.” “Ina godiya mai kasuwa nima bari naje nayi sallar na dawo yau akwai fira dan haka kowa ya dawo online da anyi sallah,”Husna ta faɗa. “Ki ce yau akwai fira kenan?”inji Abdul mai kasuwa. “Sosaima dan yau naga laɓe aka yi a gidan nan dan haka sai an yi ƙara’i,”Husna ta faɗa. “To shi ke nan sai anjima bari na tafi,”inji Abdul mai kasuwa. Ita ma Husna data ta kashe ta shimfiɗa abin Sallah,Abaya ta sanya ta hau kan dardumar, sallar magrib ɗin ta gabatar. Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 8* Husna na idar da Sallah ta miƙe ta fita tsakar gidansu,babu kowa a tsakar gidan,kai tsaye kitchen ta nufa abinci ta zubo a plate, ɗakinta ta koma ta zauna gefen gado abincinta ta ɗaura kan cinyarta,wayarta ta ɗauko ta buɗe Data,saƙonni su kai ta shigowa dubawa ta cigaba da yi har sai da ta gama ba kowa amsa sannan ta shiga group ɗin ƴan amana,tun lokacin da ta sauka babu wanda ya ƙa ra magana a ciki dan maganarta ita ce ta ƙarshe a gidan. Fita ta yi ba tare da ta yi magana ba,abincinta ta ida cinyewa taje ta maida ƙwanon a kitchen,kiran sallar isha’i ta ji an fara dan haka ta ɗaura alwalla ta shiga ɗaki,bayan ta gama sallar ta miƙe ta yi shirin bacci,wayarta ta jawo ta sake kunna Data har lokacin babu wanda ya ƙa ra magana a group ɗin. “Assalamu Alaikum” ta yi sallama a cikin group ɗin,Info din group ta shiga nan ta ga akwai mutane online amma basu da yawa. Ganin an ɗauki lokaci babu wanda ya yi magana ya sa ta yin murmushi,fita ta yi taje cikin contact ɗinta, lambar Chairman ɗin group ɗin ta danna ma kira. Ringing ukku ya ɗaga,”hello Assalamu Alaikum Abba ya kike?” “Wa’alaikissalam lafiya lau Husna yakike?”Chairman ya faɗa daga cikin wayar. Murmushi ta yi ta ce,”lafiya qlau nake Abba idan baka wani abu dan Allah ka hau online a kaje group ɗin ƴan amana.” “Husna lafiya dai koh?”Chairman ya faɗa daga cikin wayar. “Lafiya lau Abba babu komai ni dai dan Allah ka hau akwai abin da ya taso na gaggawa,”Husna ta faɗa. “To shikenan Husna gani nan zan hau,”Chairman ya faɗa cikin sauri. “yauwa sai ka hau ina jiranka yanzu,”Husna ta faɗa tare da kashe wayarta. Mai da akalar kiran ta yi ga wayar Ibrahim (Iro) ringin ɗaya ya ɗauka ya ce,”hello.” Dariya ta yi ta ce,”Oh kai Iro! kamar kana jira daga kira sai ka ɗauka.” “Waye zai zauna jiran kiran naki Malama sake magana dai,”Iro ya faɗa. “Ni dai ba wannan ba dan Allah ka hau online yanzu ka zo group ɗin ƴan amana akwai abin gaggawa da ya taso yanzu,”Inji Husna ta faɗa. “Lafiya mai ke faruwane kike nemana cikin gaggawa,”Inji Iro ya faɗa cikin zaƙuwa da son jin abin da ke faruwa. “Lafiya lau kawai dai wani abune,idan dai ka zo sai ka ji duk abin da ke faruwa,”Husna ta faɗa. “Ki gayaman mai ke faruwa yanzu aiki nake bazan samu damar hawa ba,”Inji Iro. “Ka daure dan Allah ka hau akwai abin da ya faru,”Husna ta faɗa cikin yanayin damuwa. “To shikenan gani nan zan hau muje group ɗin naji meke faruwa,”Inji Iro. “Yauwa Iro muje gani nan nima,”Husna ta faɗa. Kashe wayar Husna ta yi,haka ta rinƙa bin mutane ta na kiransu akan su hau online yanzu, sai da ta gama kiran kowa sannan ita ma ta nufi group ɗin,ta na shiga ta ga kowa ya hallara ita kawai ake zaman jira. *Hussy Saniey*.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 9* Dariya ta rinƙa yi ita kaɗai a ɗaki,ganin yadda kowa ya hallara a cikin group ɗin ana jiranta,voice ta yi ta ce,”innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!! innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!!! wai jama’a yau kun ji zafin rana gaskiya yau naji zafi kamar zan zaucewa.” Voice ɗin ta tura,dariya ta ci gaba da yi,cikin sauri kowa ya buɗe voice ɗin, Chairman ya fara turo voice,Husna ta buɗe voice ɗin,”amma wallahi wannan Husnar….ke gaskiya sai dai ki yi haƙuri amma dai ke Banza ce…. wallahi da ki ka fara salati nayi zaton mutuwa aka yi za ki sanar damu.” “Kai yanzu Chairman ni kake ce ma banza?”Husna ta tambaya ta na dariya saboda ta san ta kai su ƙarshe. Hadiza Muhammad (wadda Husna ke ce ma jakarta)ta ce,”kai jikata wallahi kin burgeni da ki ka masu haka da sun bar mana gida babu kowa.” “Ke yanzu mai makon ki yi mata faɗa sai ki zauna kina gayamata ga ra da ta yi haka?”Inji Iro. Cikin dariya Husna ta ce,”My Kakus gani nayi sun bar mana gida shiru babu kowa amma yanzu ga shi har sun zo.” “Gaskiya wannan yarinyar sai an chanzoki wallahi ina sauraren maganar gabana na faɗuwa wallahi ba ki yi ba,”Abdul Dabai ya faɗa yana dariya. “Kai My Husna gaskiya kin tsorata mu da yawa,”Inji Anty Maryam ta faɗa ta na dariya. “Ke dai bari Sis ni kaina ba ki ji yadda na tsorata ba wallahi da naji salatin,”Fadila ta faɗa ta na murmushi. “Wannan yarinyar gaskiya kin raina mutane muna aiki amma ki ka sanya muka bar aikinmu akan wannan shirmen!”Iro ya faɗa cikin jin haushi. “Haba Yayana ba ga shi yanzu har kun zo ana magana ba ai Allah ya ma jikata albarka,”Hadiza Muhammad ta faɗa. “Ke kike sanyata take raina mutane kenan to zan sanya a je har gida a yi mata ɗaukar amarya,”Iro ya faɗa. “Wallahi Husna da ina kusa da ke yau da sai kin sha bugu saboda naga rashin bugune ke damunki,yarinya duk kin bi kin raina mutane to zamu yi maganinsu,”Abdul mai kasuwa ya faɗa. “Kina wuta Husna gaskiya ina yin ki ko garin babu kowa,gaskiya da gaske ke ɗin ce farin cikin ƴan amana,”Mustapha Madina ya faɗa. “Yauwa musty shi ya sa nake sonka,ka dai faɗa masu idan su sun manta ni ce farin cikinsu,”Husna ta faɗa. “Ina farin cikin yarinya kin zo duk kin ta da mana hankali sannan za ki kira kanki da farin cikinmu?” Iro ya faɗa wanda da alama har yanzu bai huce daga cikin haushin da ya ji ba. “Kai Iroro wai kishi kake da ni?ko dai ana so ko ba’a so dole ni ce farin cikin ƴan amana dan haka Malam ka haƙura kawai kayi mubaya’a!”Husna ta faɗa da son ƙa ra hayaƙa Ibrahim. “Dallah Malama ki je ki kwanta duk kin dame mu da hayaniya,”Inji Iro. Cikin dariya Husna ta ce,”kan ka ake ji Malam ni ban da lokacinka!”Inji Husna. “Ke waye ba ki da lokacin na sa?” Inji Iro. Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 10* Husna sai dariya take ita ɗaya saboda ta san yau ta hassala Iro,idanuwanta suka sauka akan saƙon da Iro ya turo mata yanzu cikin sauri ta buɗe,gani ta yi ya ce mata,”ke dai kin raina mutane saboda kin ga kowa na tattalinki ba kamar waccan Kakar ta ki.” Husna cikin dariya ta maida ma shi da amsa,”Haba sweet Irona ta ya zan raina ka ai ban isa ba!” “Haba yarinya daga baya kenan wallahi ki kiyaye haɗuwata dake saboda har yanzu gabana bai daina faɗuwa ba nayi tunanin mutuwa za ki sanar amma shine za ki zo da wannan shirmen!”Iro ya faɗa da alama har lokacin bai gama sauka ba. Voice Husna ta danna ta ce,”haba sweet Iro tuba nake kasan ni da kai five and six ne,ka tausayaman mana ka yi haƙuri,” ta tura masa tare da sake ƙwashewa da dariya. Amsa ya maido mata da cewa,”haba yarinya za ma kiyi bayani idan na riƙe ki dan haka ki roƙi Allah kada mu haɗu shine kawai mafita amma idan dai muka haɗu sai kin gane shayi ruwane yarinya.” Cikin marerecewa kamar ta na a gabansa ta tura masa da saƙo kamar haka,”haba Sweet Irona kai fa nawa ne dan haka ka da ka bari wasu su ji su yi mana dariya mana kaji Sweet Irona.” Bayan kamar minti biyu Ibrahim ya sake turo da saƙo ya ce,”yarinya duk wannan marairecewar ba amfanin da za ta yi dan haka ki ma daina kawai ki jira sakamako.” Ƙara shagwaɓewa Husna ta yi kamar ta na a gabanshi ta ce,”dan Allah Sweet Irona kayi haƙuri ka ga dai ni taka ce nasan kuma a kowane lokaci kai mai tausayine a gareni dan Allah Sweet Irona na tuba bazan sake ba ka ji sweetyna!” Amsa Ibrahim ya maido mata da ita ya ce,”yarinya kin yi sa’a zan tausaya maku saboda ka da Mama ta shiga damuwa idan na sanya aka maki ɗaukar amarya dan haka kin ci albarkacinta.” Husna na duba saƙon cikin sauri ta maido ma shi da amsa ta ce,”lalle ma Sweet Iro to aikuwa tunda ka ce haka ban tuba ɗin ba,gobe ma sai na ƙa ra yin wanda ya fi wannan ɗin!” Dariya Ibrahim ya yi saboda da ma yasan halin Husna zai yi wuya ta bari a gane ta karaya akan abu,sai da ya tsagaita da dariyar sannan ya ce,”haka ki ka faɗa ko?” “Eh haka na faɗa ka ɗauki mataki!”Husna ta faɗa. “Ki ka sake mai-maita wa kuma?”inji Ibrahim. “Eh yadda ka ji haka na faɗa ko akwai damuwane?”Husna ta faɗa. Dariya Ibrahim ya kama yi sannan ya ce,”haba Sweet Husnata ni ne fa Sweet Ironki!” “Bawani Sweet Irona bayan sai lallashinka nake amma ka ƙi yin haƙurin sannan za ka wani ce kai ne nima ai Ni ce!”Husna ta faɗa da alamun ta fara hassala. Ibrahim na ganin wanann saƙon ya san ta hassala,dan haka bai sake tura mata wani saƙon ba sai waya ya kirata,amma ta ƙi ɗauka sai ma ta rinƙa datse kiran,sun yi haka ya kai sau goma,daga ƙarshe ma wayarta ta kashe gaba ɗaya. Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 11* Husna na kashe wayar ta kama dariya saboda tasan Ibrahim na chan yana ta kiran wayarta,ta san duk lokacin da suka yi irin haka hankalinsa tashi ya ke sosai,Husna na cikin tunanin yadda hankalin Ibrahim ke tashi idan ta yi fushi sai ta ji ƙaramar wayarta na ƙara,ta manta shafi ba ta kashe wayarba,duk da dama ta yi tunanin shine amma ta na ganin lambarshi ce sai da taji gabanta ya faɗi. Ƙin ɗaga kiran ta yi har sai da ya yi mata kira ukku,a kira na huɗu ne ta ɗaga ƙin magana ta yi sai shine ya fara magana,”kin yi dai-dai wallahi har na rinƙa kiranki amma ki gaza ɗaga man kira daga ƙarshe ma sai ki ka kashe wayar saboda kin raina ni har kin gayaman!”Ibrahim ya faɗa cikin fushi. Ita ma Husna ɗaure fuska ta yi kamar yana a gabanta ta ce,”me kake tunanin zan faɗa maka idan na ɗaga bayan sai baka haƙuri nake amma sai shareni kake yi!” ta ƙarasa faɗa kamar za ta yi kuka. Cikin kwantar da murya Ibrahim ya ce,”amma ke abin da kika aikata kin kyauta kenan sai da na fadamaki aiki nake mai muhimmanci amma ki ka sanya na aje aikin nazo,sanin kanki ne duk group ɗin ke kaɗai ce za ki iya man irin wannan kiran na bar abin da nake yi nazo dan na saurareki,kin kyauta kenan ni abin da kika man kuma dan rashin son gaskiya na maki magana kuma kin ɗauki zuciya hakan dai-dai ne?” “Nasan ban kyauta ba amma tunda na baka haƙuri ai ya kamata kai ma ka haƙura koh?” Husna ta faɗa cikin muryar kuka. “Meye abin kuka kuma yanzu daga magana Husna?haba Sweet Husnata daina kinji koh!dan Allah ki taimaka ki daina kukan nan bana so!”Ibrahim ya faɗa cikin muryar lallashi. “Zan daina Sweet Irona amma sai kai ma ka daina fushi dani,”Inji Husna ta faɗa. “Hmmm! Yarinya wallahi kin ga wurin baccina shi ya sa ki man laifi kuma ki hanani nuna fushina zan riƙe kine ai,”Ibrahim ya faɗa cikin raha. “Haba Sweet Irona ai nasan ka yafeman,dan haka ka ma daina faɗa kada wasu su ji su yi mana dariya,”Husna ta faɗa cikin muryar dariya. “Hmmm! Yarinya daga baya kenan ai an riga da an jimu kuma,” Ibrahim ya faɗa. “Na shiga ukku Sweet Irona wa ya jimu dan Allah ka ma daina faɗa ni babu wanda ya isa yaji tsakaninmu!!!” Husna ta faɗa cikin sauri. “Ke matsalata da ke matsoraciyace shi ya sa ake cin ki da yaƙi,”Ibrahim ya faɗa yana dariya. Ita ma dariyar ta yi sannan ta ce,”Ni da kai ai duk ɗaya muke mu matsorata ne Sweet Iro dan haka ka ma daina faɗar ni ɗaya ce matsoraciyar.” “To shi ke nan yarinya za kiyi man bayani ne gobe zan zo idan muka tashi daga karatu,”Ibrahim ya faɗa. “Yauwa naji daɗi Sweet Irona da ma nayi missing ɗin ka kwana biyu,”Husna ta faɗa. “Amma shi ne baki gayaman ba?”Ibrahim ya faɗa. “Ai bari nayi mu gama magana sai na faɗa maka,”Husna ta ba shi amsa. “To shi ke nan sai Allah ya kaimu wayata ba kuɗi yanzu kiyi bacci mai daɗi ina sonki Sweet Husnata,”Ibrahim ya faɗa ba tare da ya ji amsar ta ba. Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 12* Ibrahim na kashe wayar,da kallo Husna ta bi wayar ta na murmushi,har cikin zuciyarta take mamakin soyayyarta da Ibrahim,mutane da yawa na faɗin soyayya a tsakaninsu ba za ta taɓa yiwu ba,amma ita da shi suna ƙaryata mutane saboda su dai su na son junansu,ta na ganin wannan duk zancen mutane ne. Agogo ta kalla, ƙarfe goma sha ɗaya da ƴan mintuna,ganin bata jin bacci yasa ta buɗe data,sai da saƙonni suka gama shigowa sannan ta fara mai da amsa,kan group ɗin ƴan amana ta zo,shiga ta yi nan ta tadda mutane duk sun tofa albarkacin bakinsu akan abin da ta yi ɗazun. Saƙo aka turo mata a private ta na dubawa ta ga Chairman na group ɗin ƴan amana,sallama ya yi mata,”Aslm Husna ykk?” “Wassalam Abba Abba ydrn,”Husna ta faɗa (kasancewar haka take kiranshi). “Lafiya lau Alhamdullih Husna ta mu ta yan amana,”Inji Chairman. “Mash Allah Abba Abba,”Husna ta faɗa. “Dan Allah Husna taimako nake nema wurinki,”inji Chairman. “Wane irin taimako kake nema Abba?”inji Husna. “Dan Allah Husna gobe za’a je gaisuwar gidansu mai Shari’a to shine muke so dan Allah a samu abin da za’a kai masu,kuma kin ga babu kuɗi aje yanzu a asusun group,”inji Chairman. “Eh hakane Abba yanzu ya kake ganin za’a yi kenan?”inji Husna. “Husna idan babu takura dan Allah fanke muke so kiyi mana idan akwai kuɗi hannunki,”Inji Chairman. “To shi ke nan Abba wurin ƙarfe nawa za’a yi?”inji Husna. “Idan dai son samune Husna wurin ƙarfe ukku an gama komai zuwa ƙarfe huɗu kuma mun tafi,amma Husna kuɗin fulawar da man sai idan an dawo za’a ba ki,”inji Chairman. “Ba damuwa Abba insha Allah za’a yi komai yadda ya kamata,”inji Husna. “To ke kaɗai za kiyi ko su Maryam su zo nan gidanku su taya ki?”inji Chairman. “Abba lafiya lau zasu iya zuwa,”inji Husna. “To shi ke nan zan masu magana sai su zo da wuri dan ku gama akan lokaci,”inji Chairman. “To Allah ya kaimu goben lafiya,”inji Husna. Banƙwana su kayi sannan ta sauka,sai bayan sun gama maganar ne ta fara tunanin inda za ta samu kuɗin da za’a yi amfani da su wurin fanken, dan ita dai yanzu ba ta maganin ko Naira,tunani ta shiga yi ganin dai ba ta samu mafita ba yasa ta miƙewa domin ta je wurin Mama,ta na fitowa tsakar gida ta ga Mama ta rufe ƙofar ɗakinta. Ɗaki ta dawo ta kwanta bisa gado,har ta kwanta ta tuna da ba ta yi alwalla ba,tashi ta yi taje ta ɗauro alwalla sannan ta rufe ƙofar ɗakinta,ruwa ta ɗauko ta sha sannan ta hau kan gado, addu’a ta yi ta shafe jikinta ta kwanta ta na tunanin yadda za ta yi goben wurin kuɗin amma ta san Allah zai rufa asiri duk ma yadda za’a yi insha Allah ta san sai ta yi fanken. Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 13* Husna na idar da sallar asuba ɗakin Mama ta nufa, sallama ta fara yi jin gyaran murya yasa ta shiga cikin ɗakin,akan sallaya ta iske Maman ta na azkar,a gefen Maman ta zauna bisa lokar gado,zamanta babu daɗewa Mama ta kammala azkar ɗinta,inda Husna ke zaune ta kalla ta na mamakin abin da ya kawo Husna ɗakinta a wannan lokacin,(ba ta shiga cikin ɗakin a irin wannan lokacin daga bakin kofar ɗaki take tsayawa ta gaisheta sai ta juya). “Ina ƙwana Mama?”inji Husna. “lafiya lau Husna lafiya meyafaru na ganki yanzu ko kina buƙatar wani abu ne!”Mama ta faɗa ta na ƙa ra bin Husna da kallon mamaki. “lafiya lau Mama babu wata matsala, alfarma dai nazo nema wurinki,”Husna ta faɗa tare da saukowa daga saman lokar da take zaune. Bin ta da kallon mamaki Mama ta ci-gaba da yi har ta zauna kan ledar da ke malale a tsakar ɗakin,”alfarma kuma Husna ina jin ki mekikeso?” “Mama yau ake sadakar kwana ukku ta Babansu Mai Shari’a…..”Husna ta faɗa ta na bin Mama da kallo ta na son ganin yadda Mama za ta ɗauki abin. “Ke nake saurare kin fara magana kuma kin yi shiru ko dai akwai matsala ne Husna?”Mama ta faɗa tare da tsare Husna da idanuwa. “Mama jiya bayan na shiga ɗaki aka yanke shawarar mu ƴan amana zamu yi fanke wanda za’a kai gidan sadaka yau,to shine Abba ya ce babu kuɗi a hannu idan da hali nayi daga baya sai a bani kuɗin,ni kuma babu kuɗi a hannuna shine nazo ki ara mana idan aka bada sai na maido maki,”Husna na kai wa nan ta yi shiru cikin ranta ta na addu’ar dacewa. Murmushi Mama ta yi cikin ranta ta na ƙara jinjina irin wannan soyayya da ƴarta ke ma waɗannan mutane,duk abin da ya dangancesu ta na ba shi muhimmanci sosai,dama ta yi mamakin abin da ya fiddo Husna yanzu dan haka ta ce,”ai muna da fulawa da mai a gidan nan kuma jiya an kawo suga dan haka idan dai fulawar tiya ukku za ta isheku sai ki ɗiba kawai.” Cikin farin cikin da ya kasa ɓoyuwa ta ce,”Nagode kwarai Mama Allah yasa ka da mafificin alkhairi Allah ya ƙara buɗi na alkhairi.” “Ameen ya Allah sai ki tashi kije ki kwanta ko yau ba ki komawa baccin?”Mama ta faɗa tare da miƙewa tsaye ta na linke sallaya. “Zan koma Mama anjima Maryam da Fadila za su zo tare zamu yi aikin dasu,”Husna dake miƙewa tsaye ta faɗa ta na kallon Mama. “To shi ke nan Allah ya kawosu lafiya,”daga haka Mama ta nufi wadrop ta saka sallaya. Ganin haka yasa Husna fita ta koma ɗakinta wayarta da ke kan gado ta ɗauka,kira biyar ta gani ta na dubawa ta ga Iro ne,dama ta yi tunanin shine saboda yau bai tada ita sallah ba(haka suke yi cikinsu duk wanda ya riga tashi shi ke tada ɗaya). Murmushi ta yi cikin ranta ta ce yau akwai chakwakiya kenan tsakanin ta da Iro. Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 14* Kira ta danna masa bugu ɗaya ya ɗauka,ko sallamar da take bai amsa ba ya fara tambayar ta,”lafiya kike?ina kika shigane ina ta kira ba ki ɗagaba fatan dai kina lafiya?” Ya ƙarasa faɗa cikin alamun damuwa. Wani ƙasaitaccen murmushi ta ƙawata fuskarta da shi sannan ta ce,”kai Sweet Irona irin wannan ruɗewa haka…?” “Malama ki amsa man tambaya!…”ya faɗa cikin fushi. Dariya ta sa ki cikin jin daɗi ta ce,”kwantar da hankalinka babu abin da ke damuna kuma bani da wata matsala,naje ɗakin Mamane na bar wayata nan ɗakina.” Wata wawuyar ajiyar zuciya Ibrahim ya saki,wadda har sai da Husna na jiyota,cikin shan mur tamkar wanda yake a gabanta ya ce, “Amma wannan wane irin zamane kika yi a chan daga zuwa ki gaisheta sai ki nemi wuri kiyi zaune ko aiki ta sanyaki?” Dariya Husna ta yi wadda har sai da ya jiyo sautin dariyar sannan ta ce,”A’a na tsaya mun yi maganar fanken da za’a yi idan anjima a kai gidan rasuwa…” “Ke aka sanya kiyi fanken?” Bai bari ta ƙarasa faɗar maganarta ba ya jefa mata tambayar da ta sanyata yin shiru. “Eh mun yi magana da Abba jiya bayan mun gama waya da kai,” ta faɗa cikin sanyin murya. “Amma kin san ke za kiyi fanken har muka gama waya baki sanar dani ba!” Ya faɗa cikin alamun fushi. Kwantar da muryarta ta yi fiye da farko ta ce,”Sweet Iro na faɗa maka sai bayan mun gama waya da kai sannan mu kayi magana da Abba.” “To yaushe ya kawo maki kayan yin fanken ko sai anjima?” Yana faɗin haka ya yi shiru yana jiran amsar da za ta ba shi. “A’a ya ce nayi daga baya za’a ban kuɗin saboda yanzu asusu babu kuɗi, kuma lokaci ya ƙure ba’a yi maganar nawa zamu haɗa ba sai daga baya za’a yi maganar,”ta faɗa cikin sanyin murya. “Ke ina kika samu kuɗin da za kiyi hidimar dasu bayan ko jiya ba ki da kuɗi?” Ya faɗa cikin sauri. “Abin da yasa naje wurin Mama kenan dan ta araman to sai kuma ma ta ce a ɗebi kayan gida ayi dasu ba sai an siyo ba kuma a bar kuɗin,”Husna ta faɗa. “Banganeba wane kayan gidan za’a ɗiba?” Ibrahim ya tambayi Husna. “Kai Sweet Iro kamar ba da Hausa nake maka bayani ba? Muna da fulawa da Mai sai suger shine Mama ta ce a ɗiba ayi kawai,”Husna ta faɗa cikin shagwaɓa. “Yanzu ke wannan hidimar kika ɗora masu ba ki san yanayin da ake ciki ba?”Ibrahim ya faɗa. “Kai Sweet Irona ita fa ta ce a ɗiba wallahi ni bance mata ta bamu ba,rancen kuɗi kaɗai naje ta ban,”Husna ta faɗa tare da kishingiɗawa jikin katakon gado. “Allah ya so ki yarinya bake kika tambayeta ba da jikinki ya faɗa maku,”Ibrahim ya faɗa. “Naji dai tun da ban aikata ba sai a bi wani sarkin ba dai ni ba,”Husna ta faɗa ta na dariya. “To zan kwanta ban daɗe da dawowa daga masallaci ba,ke ɗaya za kiyi fanken ko har dasu Maryam?” Ibrahim ya tambayi Husna. “Eh ni da Maryam da Fadilane amma sai wurin ƙarfe sha biyu saboda mu gama da wuri,”Husna ta faɗa. “To shi kenan sai anjima ki kular man da kanki,”yana faɗin haka ya kashe wayarshi. Kallon wayar Husna ta yi ta na murmushi cikin ranta ta ce sweet Iro ba dai rigima ba,Allah ya barmu tare ta faɗa tare da kwanciya domin ita ma baccin take ji,aikuwa ta na kwanciya babu daɗewa bacci ya dauketa. Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 15* Sai wurin ƙarfe tara da ƴan mintuna sannan Husna ta tashi daga bacci,ta na tashi sharar ɗakinta ta fara yi sannan ta fito tsakar gida,sai da ta sharo ɗakin Mama sannan ta sharo wani ɗaki sai ta haɗa da tsakar gidan. Ta na ida sharar kayan wanke-wanke ta haɗa ta wanke,ta na gama wanke-wanke wanka ta shiga,ba ta daɗe a wurin wankan ba ta fito,yau jin ta take yi cikin walwala da annabawa,babu abin da ke mata daɗi a rai sai idan ta tuna yau za ta ga mutanen gidan ƴan amana,duk cikin gidan mutum huɗu ta sani a fuska daga Maryam, Ibrahim, Umar Sulluɓawa sai Abba. Kallo ɗaya za kai mata ka ga tarin farin cikin da take ciki,ko ayyukan ma yau cikin karsashi take gudanar dashi,shi ya sa ko Lokaci mai tsawo ba ta ɗauka ba ta kammala,ta na fitowa daga wanka doguwar riga kawai ta sanya. Ƙafafuwanta kawai ta shafa ma mai sai turare da ta fesa, kitchen ta shiga flaks ɗin ruwan zafi ta buɗe ta zuba dai-dai cikinta sannan ta rufe,wurin da kayan tea suke aje taje ta haɗa bread dake aje gefe da alama na ta ne ta ɗauka. Ɗakinta ta dawo ta zauna,ta na kalacin ta na tunanin yadda za ta haɗu da mutanen da take tsananin so a rayuwarta,da haka har ta kammala kalacin ta ɗauraye kayan da ta ɓata sannan ta maida komai inda yake. Agogo ta kalla ganin har sha ɗaya da rabi ya sanyata nufar store ɗinsu,fulawa ta auno tiya ukku cikin wata Babbar roba ta zuɓo fulawar,yis ta ɗauko tsakar gida ta dawo ta har ta zauna sai ta tuna da ta bata ɗauko gishiri ba sai ta koma,bayan ta ɗauko ta zauna cikin sauri ta ke kwaɓa fulawar cikin lokaci kaɗan ta gama kwaɓin,amma fa ta jigatu saboda kafaɗunta duk sun gaji. Bayan ta gama kwaɓin ta ja robar ta kaita saitin rana,dawowa ta yi domin ta gyara inda ta ɓata,ta na cikin gyaran wurin Mama ta fito daga ɗakinta ta ce, “Wai aikin me kike haka cikin gidan Husna tun ɗazun nake jin motsinki?” Ɗagowa ta yi daga duƙen da take ta ce,”Mama kin manta yau akwai aikin fanke shi ya sa na fito da wuri ga shi ma har na kwaɓa.” Cikin mamaki Mama ta ke bin Husna da kallo,Husnar da bata son aiki ko kaɗan,duk in za’a sanyata aiki a gidan ba ta yin shi cikin daɗin rai,dan in ma kana da zuciya baka sanya Husna aiki,dan ba ta yin shi sai Mama ta mata jan ido a lokacin zata yi shi,yau ga Husna ba tare da an sanyata ba ta na aiki,lalle dole a jinjina ma waɗannan mutanen. Dariya Husna ta yi ta ce,”Mama sai kallona kike!” “Ba dole na kalleki ba Husna wannan aiki da ki kayi cikin lokaci,”Mama ta faɗa ta na ɓoye mamakinta. “Kin ga yanzu Mama lokacin da su Maryam zasu zo ta tashi sai tuya kaɗai zamu fara yi,”Husna ta faɗa cikin fara’a. “Hakane Allah ya taimaka,”Mama ta faɗa ta na komawa ɗakinta saboda wayarta da ke ƙara. Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 16* Husna na ganin shigar Mama ɗakinta ita ma sai ta nufi na ta ɗakin,ta na shiga ɗakin kan doguwar kujerar dake ɗakinta ta zauna, hannu ta miƙa ta ɗauki fankaceciyar wayarta dake ajiye a gefen gado, agogon wayar ta kalla gani ta yi har ƙarfe goma sha ɗaya da ƴan mintuna. Data ta buɗe sannan ta shiga WhatsApp, saƙonni su kai ta shigowa a wayar sai da ta jira su ka gama shigowa sannan ta fara maida amsa. Group ɗinsu na ƴan amana ta shiga don duk yau ba ta shiga ba,mutane ta iske na fira sallama ta yi ita ma,cikin sauri Dabai ya ce,”yar halak kin ƙi ambato yanzu nake maganarki.” “Gulmata dai za ka ce kayi kawai Malam.” Cikin son ƙular da Dabai Husna tai maganar. “Ke matsalata da ke abin arziƙi bai karɓeki ba daga an ma damu dake sai kuma ki fara wulaƙanci!” Dabai ya faɗa cikin jin haushi. Dariya Husna ta kama yi saboda ta san ta fara ƙular da shi dan haka ta ce,”ai matsalar ba ka iya daina yi man magana idan kuma kana iyawa to daga yau kar ka ƙara.” “Ke ɗin ke bazan iya daina yi ma magana ba to ke wacece da har zan kasa daina yi maki magana dallah Malama matsa chan gefe ka da ma na maujeki!!”Dabai ya ƙarasa maganar cikin jin haushi. “Gaskiya Abdul Dabai Husna ta ga wurin baccinka” cikin son ƙara hayaƙa Dabai Mustapha Madina ya faɗa. “Ka kyaleta ai yau ta guji haɗuwarmu ni da ita,wai ma dan ta raina ni wai ban iya daina yi mata magana wallahi yarinyar nan kin ci abinci!!” cikin jin haushin Husna, Dabai ya ƙarasa maganar kamar zai yi kuka. “Ai ba ƙarya nayi ma shi ba Musty kuma a gabanshi na faɗa ba bayan idonshi ba…”Husna ta yi maganar cikin dariya da son ƙara cusama Dabai haushi. “Ban da lokacinki yarinya amma abu ɗaya zan faɗa maki shi ne ki guji haɗuwarmu idan anjima…” Cikin jin haushi Dabai ya yi maganar saboda da ma kowa yasan Dabai da saurin hayaƙa. “Gaskiyarki ɗiyata ai kowa ya san Dabai ba zai iya daina yi maki magana ba” Nana Aisha ta faɗa wadda zuwanta kenan cikin gidan ta yadda ana maganar kawai ta sanya baki. “Yauwa Momy faɗa masa dai kowa ya gane abin da yake nufi…”Husna ta faɗa ta na dariya saboda tasan yau ta kai Dabai ƙarshe. “Ke wannan Nana A’ishar ke kike sanya wannan Husna Husnar ta raina mutane hakanan kun kasa yi ma yarinya tarbiyyar girmama manyan…”Dabai ya faɗa. “Ina manyan suke ai ni ban ga manya a nan ba balle har na girmamawa…” Husna ta faɗa cikin sauri. “Ni ɗiyata nayi mata tarbiyya mai kyau kuma ni ban ga rainin da ta yi ma mutane ba,kawai dai nasan ɗiyata ba ta ɗaukar raini shine kawai abin da nasani.” Nana A’ishah ta faɗa. “Ke Husna ki kiyayeni duk nan gidan akwai wanda kika raina irina kuma zan ɗauki mataki wallahi!” Dabai ya faɗa cikin jin haushi. Sannan ya cigaba da magana,”ke nan wannan ita ce tarbiyyar da kike faɗin kin ba ta?to gaskiya ki chanza tarbiyya saboda nan dai kowa ya san babu.” “Ni ban da lokacinka na tafi in yi aikin gabana,kai kuma sai ka zauna ka tsare mana group ka da kuma a tafi yawo, Momyna sai anjima na tafi aiki zanyi,” Husna na faɗin haka ta fita daga group ɗin. Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 17* Husna na fita daga WhatsApp, contact ɗinta ta shiga lambar Maryam ta danna ma kira,bugu ɗaya ana biyu Maryam ta ɗauka,”My Husna kin ga har yanzu ba mu zo ba koh?” Maryam ta faɗa cikin fara’a. “Eh wallahi Anty Maryam kuma ga rana ta fara yi wai dan mu gama da wuri shi ya sa saboda nasan yanzu fulawar ma har ta tashi.” Husna ta faɗa. “To insha Allah My Husna gamu nan tafe Fadila nake jira ita ma kuma ta na kan hanya.” Maryam ta faɗa. “To shi ke nan sai kun zo Anty Maryam.” Husna ta faɗa tare da kashe wayar. Husna na kashe waya ta aje wayar a gefen ta,tsakar gida ta nufa dan duba halin da fulawar ke ciki,kamar yadda ta zata hakan ce ta kasance har ta tashi sosai,maidawa ta yi ta rufe,store ɗinsu ta nufa ta ɗauko murhu ta aje inda suke ajewa idan zasu yi sanwar murhu,gyara murhun ta yi tare da shirya itatuwa a ciki,kalanzir da ashana ta ɗauko ta na cikin buɗe galan ɗin kalanzir ɗin ta ji wayarta na ƙara,fasa zuba kalanzir ɗin ta yi ta rufe galan ɗin, ɗaki ta nufa cikin sauri amma duk da haka ta na shiga wayar na karawa. Wayar ta ɗauka dan duba wanda ya kirata,bisa hannun kujera ta zauna ta na duba wayar, Chairman ta gani ƙoƙarin kiranshi ta fara kafin ta kira sai ga kiran ya sake shigowa,ɗagawa ta yi tare da yin sallama. “Assalamu Alaikum Chairman ka tashi lafiya?” “Wa’alaikissalam lafiya lau Alhamdullih Husna kun fara aikin dai ko kin ga yanzu har ƙarfe sha biyu ta yi muna so zuwa ƙarfe biyu da wani abu azo a ɗauka kin san yanzu an maida addu’ar ƙarfe ukku kada kuma a makara,”Chairman ya faɗa cikin sanyin murya. “Kar ka damu Abba insha Allah ba zamu makara ba yanzu haka fulawar ta tashi,su Maryam kawai nake jira su ƙaraso kuma har wuta ma yanzu zan hura na fara kafin su iso,”Husna ta faɗa. “Yauwa Husna sannu da aiki idan aka haɗu sai a ba ki kuɗin kayan da kika kashe,yanzu nawa kika kashe?” Chairman ya faɗa. “A’a Abba ba sai an biya ba Mama ta bada duka kayan ta ce a bar kuɗin,”Husna ta gayama Abba. “Allah sarki Mama mun gode ƙwarai Allah ya saka da mafificin alkhairi ki ce muna godiya kafin mu zo,dan dole mu shigo Mu yi mata godiyar wannan hidima da muka ɗora mata…!”Chairman ya faɗa cikin tsananin farin ciki. “Bakomi Abba zan faɗa mata insha Allah sai kun zo ɗin bari naje na fara aikin chan kafin su ƙaraso saboda Fadila kaɗai ake kira.”Husna ta faɗa. “To shi ke nan Husna sannu da ƙoƙari gaskiya muna alfahari da shigowarki cikinmu,har abada ƴan amana baza su manta da karamcinki a garesu ba.” Abba ya faɗa cikin tsananin farin ciki. “Bakomi Abba ai zaman tare kenan ka kyautatama wanda kake tare da shi nima nagode da yabonku a gareni sai anjima.” Bata jira amsar Chairman ba ta kashe wayarta,tsakar gida ta fito dan cigaba da aikinta Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 18* Wuta Husna ta hura ta cigaba da suyar fanke,sai da ta soya ya kai rabi sannan ta jiyo sautin Fadila na sallama,hanyar zaure ta kalla tare da amsawa. “Wa’alaikissalam Fadilarmu!” Husna ta faɗa cikin murna. “Allah sarki Husna sannu da aiki,dan Allah kiyi haƙuri Husna mun barki da aiki sannu….!” Maryam ta faɗa cikin sigar lallashi. “Kai My Anty har kin sanya naji kunya…ni fa abin da yasa ki ka ga na fara saboda kin san halin Abba da zumuɗi har fa ya kirani wai an gama?” Husna ta faɗa tare da tsame fanken da ke cikin kasko. “Husna ke da wa ke magana?” Mama ta faɗa lokacin da take fitowa daga cikin ɗakinta. “Mama su Anty Maryam ne fa…!” Husna ta faɗa ta na nuna su Fadila dake tsaye bakin kofar zaure tun ɗazun,duk maganar da su ke da Husna da ma basu shigo ba. Da kallo Mama ta bi inda Husna ke nuna mata,su Maryam ta gani tsaye su na kallonta,ta buɗe baki ta ce. “Ke dai Husna na ga ranar da za kiyi hankali yanzu ki iya ki ce masu su shigo amma sai hakan ta gagareki sai dai ki tsaresu da labari tun kafin su shigo cikin gidan… Maryam ku shigo mana kun biye ma shirmen Husna kun yi tsaye,in ba yi hankalin ce maku ku shigo ba ai sai ku shigo ko!!” Mama ta ƙa ra sa faɗa ta na kallon su Maryam dake tsaye su na mata murmushi. “Kiyi haƙuri Mama shigowa zamu yi da ma…ina wuni Mama” Fadila ta faɗa tare da durƙusawa ta na gaida Mama. “Lafiya lau Fadila ya Mamarku?” Mama ta faɗa. Maryam ma durƙusawa ta yi ta ce,”Mama ina wuni ya gida ina su Auter?” Kallonta Mama ta yi ta ce,”lafiya lau Alhamdullih su Auter sun tafi Makaranta ya Hajiyarku?” Duƙar da kai Husna ta yi ta ce,”lafiya lau ta ke ta ce ma a gaisheku.” “Masha Allah muna,amsawa ku shigo daga ciki mana” Mama ta faɗa tare da komawa cikin ɗakinta saboda su samu damar sakewa. Mama na shiga ɗakinta su Fadila suka taho har inda Husna ke sanya fanke cikin kaskon dake kan wuta, Abaya Maryam ta ɗora saman igiyar shanyar dake ɗaure a tsakar gidan. “Kawo ki huta My Husna ai kin yi ƙoƙari har kin ku sa toyewa duka” Maryam ta faɗa tare da ƙoƙarin amsar abin da Husna ke tsame fanken. “Kai My Anty daga zuwanku ko hutawa ba zaku zauna ku yi ba….balle ku sha ruwa sai kawai ku kama aiki!” Husna ta faɗa tare da riƙe abin tsamar. “Haba Husna dan Allah ki sakar mata mu ƙarasa aikin nan ai kinyi ƙoƙari,mu ida wane kawai ya rage zamu yi saboda duk kin toya yafi rabi” Fadila ta faɗa tare da cire abayarta inda Maryam ta ɗora ta ta nan ita ma ta ɗora. Ganin sun dage akan sai ta bar masu ya sanya Husna ta sakar masu abin tsamar,abayoyinsu ta ƙwashe daga saman igiyar ta nufi ɗakinta dasu domin ta ajiye masu a chan nan waje kuma saboda ka da su ɗauki zafin rana. *NA* *HUSSY SANIEY* PAGE 6 Shiru zaman ya kasance a tsakaninsu,babu wanda ke da ƙwarin guiwar yin wata fira,zaman minti goma sai ga Bus ta zo,su na shiga cikin Bus ɗin Husna ta chanza kujerar zama,da kallo su ka bi ta dashi saboda abin da bai taɓa faruwa a tsakaninsu ba,duk rintsi wuri ɗaya suke zama amma yau ga shi Husna ta raba masu wurin zama. Husna na kallon yadda su ke bin ta da kallo, ɗauke kanta ta yi kamar ba ta san suna yi ba,a haka tafiyar ta kasance babu daɗi,kowa da abin da yake saƙawa a cikin zuciyarsa. Ko da aka zo inda suke sauka,Bus na tsayawa Husna ce farkon fita,bayanta su Mieynart suka bi,lokacin da suka fito har ta tsaida Keke napep. Ji ta yi an riƙe mata Abaya ta baya,juyowa ta yi suka haɗa idanuwa da Mieynart,ɗaure fuska Husna ta ƙara yi ta ce,”sakeni zan wuce!” Murmushi Mieynart ta yi,”Husna ban taɓa ganin haka a wurinki ba saboda haka kiyi haƙuri hakan bazata ƙara faruwa ba insha Allah.” Girgiza kai Husna ta yi ta ce,”bakomi ya wuce sai Allah ya kaimu gobe.” Kafin Mieynart ta ce wani abu har Husna ta shige cikin keke napep ɗin,ta na shiga mai keke napep yaja suka tafi,sai da suka ɓace sannan Mieynart ta kalli Sadam ta ce,”tun da nake da Husna ba ta taɓa nunaman taji haushin abu ba irin yau,gsky bansan wannan wace irin ƙauna ba ce take ma waɗannan bayin Allah ba.” Cikin mamaki Sadam ya ce,”ni kaina abin nan ya matuƙar ɗaure man kai,wai Husna ce ta iya nuna mana ɓacin ranta saboda mun kushe wasu!” Mieynart ta riƙe haba ta ce,”abin da yafi ɗaure man kan kenan,fatana dai Allah ya sanya yadda take son su haka su ma suke mata irin wannan son.” Gyara tsayuwa Sadam ya yi tare da ɗaga ma wani mai mashin hannu,duban shi ya maido ga Mieynart ya ce,”ameen dan gaskiya abin ya ban mamaki sosai.” Tsayuwar mai mashin gabansu shi ya hana Mieynart magana, Sadam ya kalli Mieynart dake tsaye amma da gani kasan ba ta cikin yanayi mai daɗi ya ce,”Mieynart idan naje gida zamu yi waya akan wannan case ɗin kar ki damu kinji koh?” Numfashi Mieynart ta sauke ta ce,”Sadam dagaske hankali na ya tashi saboda Husna duk yadda kake ganinta ba ta da haƙuri to wallahi ta na da kawaici ba abu kaɗan ke sanyawa ta nuna ɓacin ranta ba.” Hawan mashin Sadam ya yi sai da ya zauna sosai sannan ya ce,”kar ki damu Mieynart zamu yi magana idan na koma gida ai dole mu tabbatar Husna ta sauko daga fushin nan saboda wallahi yau ban ji daɗin yadda muka rabu ba.” Gyara riƙon jikka Mieynart ta yi ta ce,”nima abin da yafi ɗaga man hankali kenan amma insha Allah idan ta kama har gida zan taddata sai na bata haƙurin kaje idan mun koma mun yi waya sai anjima Allah ya kiyaye hanya.” Littafin da ke hannun shi ya ɗora bisa cinya,ya kalli Mieynart ya ce,”ki bari idan naje gidan duk yadda ta kama sai ayi kawai kinji kin ga napep chan kije ki hau ki gaida Mama.” Bayan wucewar Sadam babu daɗewa ta samu Keke napep,ta tafi gidansu lokacin har an kusa fara kiran sallar magrib. ************** Husna na isa ƙofar gidansu,mai Keke napep ɗin ta sallama sannan ta shiga cikin gidansu,da sallama ta shiga,Mama na zaune ta na ɗaurin kunun Aya,kallo ɗaya Mama ta yi ma Husna ta san akwai matsala a tattare da Husnar. Ganin irin kallon da Mama ke bin ta da shi ya sanya Husna washe baki ta ce,”Mama sannu da aiki na dawo.” Cikin kallon tuhuma Mama ta ce,”yauwa lafiyar ki ƙlau kuwa Husna! kin ga yadda kika yi?” Cikin ƙoƙarin ɓoye damuwarta, Husna ta yafa ma fuskarta murmushin ƙarfin hali ta ce,”lafiya lau nake Mama kawai tsabar gajiyace kawai ta maidani haka kamar marar lafiya amma lafiya lau nake babu wani abu Mama.” Ba dan Mama ta yadda ba ta ce,”ki je ki ɗan watsa ruwa ki zo ki ci abinci nasan dai kina jin yunwa?” Murmushi Husna ta ɗan yi duk don son ɓoye damuwarta ta ce,”zan dai watsa ruwa Mama amma ba na jin yunwa na ci abinci a makaranta Mieynart ta zo mana da shi.” Kallonta kawai Mama ta tsaya tana yi saboda zai yi wuya Husna ta dawo daga makaranta ba ta ci abinci ba,wani lokacin har janta ake ace an manta ba’a aje mata abincin ba,ganin irin kallon da Mama ke bin ta da shi ya sanya kawai ta shige ɗaki,dan tsab Mama na iya gano abin da take ƙoƙarin ɓoyewa,kuma ko kaɗan bata san hakan ta kasance. Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 7* Shigarta ɗaki kenan wayarta ta ɗauki ƙara,fiddo wayar ta yi daga cikin jikka,fuskar wayar ta kalla ganin mai kiran yasa ta yin murmushi,ka ra wayar ta yi a kunne bayan ta ɗauka. “Hello Assalamu Alaikum,” Husna ta faɗa cikin fara’a. Daga ɗayan bangaren aka amsa mata,”wa’alaikissalam Hajiya yau ina kika shige sai nemanki ake ko dai ɓacewa ki kayi?” Gefen gado Husna ta zauna cikin dariya ta ce,”da ma ai na faɗa maku ba zaku iya rayuwa idan babu ni ba saboda ni ce farin cikinku ga shi kuma yanzu kun kasa natsuwa saboda ban kusa damu.” Daga cikin wayar aka ba ta amsa da,”kalli wannan yarinyar abin da kike faɗa,ke ce farin cikin namu ko dai baƙin ciki?yarinya duk kin bi kin damu mutane shine kike iƙirarin ke ce farin cikin mu?” Wata dariya Husna ta fashe da ita,cikin son ta ƙular dashi ta ce,”haba Iroro ai kowa yasan ni ce farin cikin ƴan amana ga shi kun kasa nutsuwa da baku ganni ba kai kafi kowa ma kasa jurewa har sai da ka kirani.” Daga chan bangaren wanda ta kira da Iroro ya ce,”ke kalli wannan yarinyar waye ya kasa natsuwar?” Cikin sauri Husna ta ce,”Iroro mana shi ya kasa jurema rashina.” “Ba ki da lafiya yarinyar nan nine ma zan gaza jurewa rashinki?” Iro ya faɗa. Cikin dariya Husna ta ce,”ga shi nan kuwa ka gaza jurewa gaskiya ni mai sa’a ce a rayuwa tunda har kuna gaza jurema rashina a kusa daku.” “Ji wannan yarinyar sai wata magana kike wadda bansan kanta ba idan kin gama ƴan maganganun ki zan iya kashe wayata?” Inji Iro. “Baka da matsala Iroro tunda ka ji lafiyata hankalin ka ya kwanta nasan ka samu natsuwa zaka iya kashewa yanzu!” Husna ta faɗa cikin son ƙular da Iro. “Ke dai kika sani da ƴan maganganun ki,” ya faɗa tare da katse kiran wayar. Dariya Husna ta kama yi saboda ta san ta ƙular da Iro,tashi ta yi ta shiga wanka,ba ta ɗauki dogon lokaci ba ta fito,sai da ta yi alwallar sallar magrib saboda lokaci saura kaɗan ya ida,cikin sauri ta sanya doguwar rigar atampa,wayarta ta ɗauka ta buɗe data. Saman gado ta kwanta,sai da messages suka gama shigowa sannan ta shiga group ɗin ƴan amana,kamar yadda ta zata hakan ce ta kasance ba’a yi magana sosai ba,da ma duk in dai ba ita ke online ba to zaka ga ba’a cika magana sosai ba,duba maganganun ta yi gaba ɗaya ba wasu maganganu bane sai ƴan gaishe-gaishene ga duk wanda ya ɗan leƙo cikin group ɗin. Sallama ta yi cikin group ɗin,kamar ana jiran zuwanta sai ga mutane biyu sun fara amsawa, ɗaya daga cikinsu ne ya ce,”farin cikin ƴan amana yau ina kika shigane muka ji ki shiru.” Murmushi ta yi kamar yana ganinta sannan ta tura ɗan emojin nan mai nuna alamar tsalle ta ce,”naje makaranta yau sai yanzu na dawo Abdul Mai kasuwa mai ku ka ajeman na Garba?” “Allah sarki sannu kin dawo lafiya?yanzu kuwa za’a tarbeki tarba mai kyau kuwa,” Abdul Dabai ya faɗa wanda zuwanshi kenan. Abdul mai kasuwa ya turo emojin kankana da lemo sannan ya ce,”ga kayan marmari nan ki ɗan taɓa zanje masallaci na dawo naji an fara kiran sallah.” “Ina godiya mai kasuwa nima bari naje nayi sallar na dawo yau akwai fira dan haka kowa ya dawo online da anyi sallah,”Husna ta faɗa. “Ki ce yau akwai fira kenan?”inji Abdul mai kasuwa. “Sosaima dan yau naga laɓe aka yi a gidan nan dan haka sai an yi ƙara’i,”Husna ta faɗa. “To shi ke nan sai anjima bari na tafi,”inji Abdul mai kasuwa. Ita ma Husna data ta kashe ta shimfiɗa abin Sallah,Abaya ta sanya ta hau kan dardumar, sallar magrib ɗin ta gabatar. Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 8* Husna na idar da Sallah ta miƙe ta fita tsakar gidansu,babu kowa a tsakar gidan,kai tsaye kitchen ta nufa abinci ta zubo a plate, ɗakinta ta koma ta zauna gefen gado abincinta ta ɗaura kan cinyarta,wayarta ta ɗauko ta buɗe Data,saƙonni su kai ta shigowa dubawa ta cigaba da yi har sai da ta gama ba kowa amsa sannan ta shiga group ɗin ƴan amana,tun lokacin da ta sauka babu wanda ya ƙa ra magana a ciki dan maganarta ita ce ta ƙarshe a gidan. Fita ta yi ba tare da ta yi magana ba,abincinta ta ida cinyewa taje ta maida ƙwanon a kitchen,kiran sallar isha’i ta ji an fara dan haka ta ɗaura alwalla ta shiga ɗaki,bayan ta gama sallar ta miƙe ta yi shirin bacci,wayarta ta jawo ta sake kunna Data har lokacin babu wanda ya ƙa ra magana a group ɗin. “Assalamu Alaikum” ta yi sallama a cikin group ɗin,Info din group ta shiga nan ta ga akwai mutane online amma basu da yawa. Ganin an ɗauki lokaci babu wanda ya yi magana ya sa ta yin murmushi,fita ta yi taje cikin contact ɗinta, lambar Chairman ɗin group ɗin ta danna ma kira. Ringing ukku ya ɗaga,”hello Assalamu Alaikum Abba ya kike?” “Wa’alaikissalam lafiya lau Husna yakike?”Chairman ya faɗa daga cikin wayar. Murmushi ta yi ta ce,”lafiya qlau nake Abba idan baka wani abu dan Allah ka hau online a kaje group ɗin ƴan amana.” “Husna lafiya dai koh?”Chairman ya faɗa daga cikin wayar. “Lafiya lau Abba babu komai ni dai dan Allah ka hau akwai abin da ya taso na gaggawa,”Husna ta faɗa. “To shikenan Husna gani nan zan hau,”Chairman ya faɗa cikin sauri. “yauwa sai ka hau ina jiranka yanzu,”Husna ta faɗa tare da kashe wayarta. Mai da akalar kiran ta yi ga wayar Ibrahim (Iro) ringin ɗaya ya ɗauka ya ce,”hello.” Dariya ta yi ta ce,”Oh kai Iro! kamar kana jira daga kira sai ka ɗauka.” “Waye zai zauna jiran kiran naki Malama sake magana dai,”Iro ya faɗa. “Ni dai ba wannan ba dan Allah ka hau online yanzu ka zo group ɗin ƴan amana akwai abin gaggawa da ya taso yanzu,”Inji Husna ta faɗa. “Lafiya mai ke faruwane kike nemana cikin gaggawa,”Inji Iro ya faɗa cikin zaƙuwa da son jin abin da ke faruwa. “Lafiya lau kawai dai wani abune,idan dai ka zo sai ka ji duk abin da ke faruwa,”Husna ta faɗa. “Ki gayaman mai ke faruwa yanzu aiki nake bazan samu damar hawa ba,”Inji Iro. “Ka daure dan Allah ka hau akwai abin da ya faru,”Husna ta faɗa cikin yanayin damuwa. “To shikenan gani nan zan hau muje group ɗin naji meke faruwa,”Inji Iro. “Yauwa Iro muje gani nan nima,”Husna ta faɗa. Kashe wayar Husna ta yi,haka ta rinƙa bin mutane ta na kiransu akan su hau online yanzu, sai da ta gama kiran kowa sannan ita ma ta nufi group ɗin,ta na shiga ta ga kowa ya hallara ita kawai ake zaman jira. *Hussy Saniey*.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 9* Dariya ta rinƙa yi ita kaɗai a ɗaki,ganin yadda kowa ya hallara a cikin group ɗin ana jiranta,voice ta yi ta ce,”innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!! innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!!! wai jama’a yau kun ji zafin rana gaskiya yau naji zafi kamar zan zaucewa.” Voice ɗin ta tura,dariya ta ci gaba da yi,cikin sauri kowa ya buɗe voice ɗin, Chairman ya fara turo voice,Husna ta buɗe voice ɗin,”amma wallahi wannan Husnar….ke gaskiya sai dai ki yi haƙuri amma dai ke Banza ce…. wallahi da ki ka fara salati nayi zaton mutuwa aka yi za ki sanar damu.” “Kai yanzu Chairman ni kake ce ma banza?”Husna ta tambaya ta na dariya saboda ta san ta kai su ƙarshe. Hadiza Muhammad (wadda Husna ke ce ma jakarta)ta ce,”kai jikata wallahi kin burgeni da ki ka masu haka da sun bar mana gida babu kowa.” “Ke yanzu mai makon ki yi mata faɗa sai ki zauna kina gayamata ga ra da ta yi haka?”Inji Iro. Cikin dariya Husna ta ce,”My Kakus gani nayi sun bar mana gida shiru babu kowa amma yanzu ga shi har sun zo.” “Gaskiya wannan yarinyar sai an chanzoki wallahi ina sauraren maganar gabana na faɗuwa wallahi ba ki yi ba,”Abdul Dabai ya faɗa yana dariya. “Kai My Husna gaskiya kin tsorata mu da yawa,”Inji Anty Maryam ta faɗa ta na dariya. “Ke dai bari Sis ni kaina ba ki ji yadda na tsorata ba wallahi da naji salatin,”Fadila ta faɗa ta na murmushi. “Wannan yarinyar gaskiya kin raina mutane muna aiki amma ki ka sanya muka bar aikinmu akan wannan shirmen!”Iro ya faɗa cikin jin haushi. “Haba Yayana ba ga shi yanzu har kun zo ana magana ba ai Allah ya ma jikata albarka,”Hadiza Muhammad ta faɗa. “Ke kike sanyata take raina mutane kenan to zan sanya a je har gida a yi mata ɗaukar amarya,”Iro ya faɗa. “Wallahi Husna da ina kusa da ke yau da sai kin sha bugu saboda naga rashin bugune ke damunki,yarinya duk kin bi kin raina mutane to zamu yi maganinsu,”Abdul mai kasuwa ya faɗa. “Kina wuta Husna gaskiya ina yin ki ko garin babu kowa,gaskiya da gaske ke ɗin ce farin cikin ƴan amana,”Mustapha Madina ya faɗa. “Yauwa musty shi ya sa nake sonka,ka dai faɗa masu idan su sun manta ni ce farin cikinsu,”Husna ta faɗa. “Ina farin cikin yarinya kin zo duk kin ta da mana hankali sannan za ki kira kanki da farin cikinmu?” Iro ya faɗa wanda da alama har yanzu bai huce daga cikin haushin da ya ji ba. “Kai Iroro wai kishi kake da ni?ko dai ana so ko ba’a so dole ni ce farin cikin ƴan amana dan haka Malam ka haƙura kawai kayi mubaya’a!”Husna ta faɗa da son ƙa ra hayaƙa Ibrahim. “Dallah Malama ki je ki kwanta duk kin dame mu da hayaniya,”Inji Iro. Cikin dariya Husna ta ce,”kan ka ake ji Malam ni ban da lokacinka!”Inji Husna. “Ke waye ba ki da lokacin na sa?” Inji Iro. Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 10* Husna sai dariya take ita ɗaya saboda ta san yau ta hassala Iro,idanuwanta suka sauka akan saƙon da Iro ya turo mata yanzu cikin sauri ta buɗe,gani ta yi ya ce mata,”ke dai kin raina mutane saboda kin ga kowa na tattalinki ba kamar waccan Kakar ta ki.” Husna cikin dariya ta maida ma shi da amsa,”Haba sweet Irona ta ya zan raina ka ai ban isa ba!” “Haba yarinya daga baya kenan wallahi ki kiyaye haɗuwata dake saboda har yanzu gabana bai daina faɗuwa ba nayi tunanin mutuwa za ki sanar amma shine za ki zo da wannan shirmen!”Iro ya faɗa da alama har lokacin bai gama sauka ba. Voice Husna ta danna ta ce,”haba sweet Iro tuba nake kasan ni da kai five and six ne,ka tausayaman mana ka yi haƙuri,” ta tura masa tare da sake ƙwashewa da dariya. Amsa ya maido mata da cewa,”haba yarinya za ma kiyi bayani idan na riƙe ki dan haka ki roƙi Allah kada mu haɗu shine kawai mafita amma idan dai muka haɗu sai kin gane shayi ruwane yarinya.” Cikin marerecewa kamar ta na a gabansa ta tura masa da saƙo kamar haka,”haba Sweet Irona kai fa nawa ne dan haka ka da ka bari wasu su ji su yi mana dariya mana kaji Sweet Irona.” Bayan kamar minti biyu Ibrahim ya sake turo da saƙo ya ce,”yarinya duk wannan marairecewar ba amfanin da za ta yi dan haka ki ma daina kawai ki jira sakamako.” Ƙara shagwaɓewa Husna ta yi kamar ta na a gabanshi ta ce,”dan Allah Sweet Irona kayi haƙuri ka ga dai ni taka ce nasan kuma a kowane lokaci kai mai tausayine a gareni dan Allah Sweet Irona na tuba bazan sake ba ka ji sweetyna!” Amsa Ibrahim ya maido mata da ita ya ce,”yarinya kin yi sa’a zan tausaya maku saboda ka da Mama ta shiga damuwa idan na sanya aka maki ɗaukar amarya dan haka kin ci albarkacinta.” Husna na duba saƙon cikin sauri ta maido ma shi da amsa ta ce,”lalle ma Sweet Iro to aikuwa tunda ka ce haka ban tuba ɗin ba,gobe ma sai na ƙa ra yin wanda ya fi wannan ɗin!” Dariya Ibrahim ya yi saboda da ma yasan halin Husna zai yi wuya ta bari a gane ta karaya akan abu,sai da ya tsagaita da dariyar sannan ya ce,”haka ki ka faɗa ko?” “Eh haka na faɗa ka ɗauki mataki!”Husna ta faɗa. “Ki ka sake mai-maita wa kuma?”inji Ibrahim. “Eh yadda ka ji haka na faɗa ko akwai damuwane?”Husna ta faɗa. Dariya Ibrahim ya kama yi sannan ya ce,”haba Sweet Husnata ni ne fa Sweet Ironki!” “Bawani Sweet Irona bayan sai lallashinka nake amma ka ƙi yin haƙurin sannan za ka wani ce kai ne nima ai Ni ce!”Husna ta faɗa da alamun ta fara hassala. Ibrahim na ganin wanann saƙon ya san ta hassala,dan haka bai sake tura mata wani saƙon ba sai waya ya kirata,amma ta ƙi ɗauka sai ma ta rinƙa datse kiran,sun yi haka ya kai sau goma,daga ƙarshe ma wayarta ta kashe gaba ɗaya. Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 11* Husna na kashe wayar ta kama dariya saboda tasan Ibrahim na chan yana ta kiran wayarta,ta san duk lokacin da suka yi irin haka hankalinsa tashi ya ke sosai,Husna na cikin tunanin yadda hankalin Ibrahim ke tashi idan ta yi fushi sai ta ji ƙaramar wayarta na ƙara,ta manta shafi ba ta kashe wayarba,duk da dama ta yi tunanin shine amma ta na ganin lambarshi ce sai da taji gabanta ya faɗi. Ƙin ɗaga kiran ta yi har sai da ya yi mata kira ukku,a kira na huɗu ne ta ɗaga ƙin magana ta yi sai shine ya fara magana,”kin yi dai-dai wallahi har na rinƙa kiranki amma ki gaza ɗaga man kira daga ƙarshe ma sai ki ka kashe wayar saboda kin raina ni har kin gayaman!”Ibrahim ya faɗa cikin fushi. Ita ma Husna ɗaure fuska ta yi kamar yana a gabanta ta ce,”me kake tunanin zan faɗa maka idan na ɗaga bayan sai baka haƙuri nake amma sai shareni kake yi!” ta ƙarasa faɗa kamar za ta yi kuka. Cikin kwantar da murya Ibrahim ya ce,”amma ke abin da kika aikata kin kyauta kenan sai da na fadamaki aiki nake mai muhimmanci amma ki ka sanya na aje aikin nazo,sanin kanki ne duk group ɗin ke kaɗai ce za ki iya man irin wannan kiran na bar abin da nake yi nazo dan na saurareki,kin kyauta kenan ni abin da kika man kuma dan rashin son gaskiya na maki magana kuma kin ɗauki zuciya hakan dai-dai ne?” “Nasan ban kyauta ba amma tunda na baka haƙuri ai ya kamata kai ma ka haƙura koh?” Husna ta faɗa cikin muryar kuka. “Meye abin kuka kuma yanzu daga magana Husna?haba Sweet Husnata daina kinji koh!dan Allah ki taimaka ki daina kukan nan bana so!”Ibrahim ya faɗa cikin muryar lallashi. “Zan daina Sweet Irona amma sai kai ma ka daina fushi dani,”Inji Husna ta faɗa. “Hmmm! Yarinya wallahi kin ga wurin baccina shi ya sa ki man laifi kuma ki hanani nuna fushina zan riƙe kine ai,”Ibrahim ya faɗa cikin raha. “Haba Sweet Irona ai nasan ka yafeman,dan haka ka ma daina faɗa kada wasu su ji su yi mana dariya,”Husna ta faɗa cikin muryar dariya. “Hmmm! Yarinya daga baya kenan ai an riga da an jimu kuma,” Ibrahim ya faɗa. “Na shiga ukku Sweet Irona wa ya jimu dan Allah ka ma daina faɗa ni babu wanda ya isa yaji tsakaninmu!!!” Husna ta faɗa cikin sauri. “Ke matsalata da ke matsoraciyace shi ya sa ake cin ki da yaƙi,”Ibrahim ya faɗa yana dariya. Ita ma dariyar ta yi sannan ta ce,”Ni da kai ai duk ɗaya muke mu matsorata ne Sweet Iro dan haka ka ma daina faɗar ni ɗaya ce matsoraciyar.” “To shi ke nan yarinya za kiyi man bayani ne gobe zan zo idan muka tashi daga karatu,”Ibrahim ya faɗa. “Yauwa naji daɗi Sweet Irona da ma nayi missing ɗin ka kwana biyu,”Husna ta faɗa. “Amma shi ne baki gayaman ba?”Ibrahim ya faɗa. “Ai bari nayi mu gama magana sai na faɗa maka,”Husna ta ba shi amsa. “To shi ke nan sai Allah ya kaimu wayata ba kuɗi yanzu kiyi bacci mai daɗi ina sonki Sweet Husnata,”Ibrahim ya faɗa ba tare da ya ji amsar ta ba. Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 12* Ibrahim na kashe wayar,da kallo Husna ta bi wayar ta na murmushi,har cikin zuciyarta take mamakin soyayyarta da Ibrahim,mutane da yawa na faɗin soyayya a tsakaninsu ba za ta taɓa yiwu ba,amma ita da shi suna ƙaryata mutane saboda su dai su na son junansu,ta na ganin wannan duk zancen mutane ne. Agogo ta kalla, ƙarfe goma sha ɗaya da ƴan mintuna,ganin bata jin bacci yasa ta buɗe data,sai da saƙonni suka gama shigowa sannan ta fara mai da amsa,kan group ɗin ƴan amana ta zo,shiga ta yi nan ta tadda mutane duk sun tofa albarkacin bakinsu akan abin da ta yi ɗazun. Saƙo aka turo mata a private ta na dubawa ta ga Chairman na group ɗin ƴan amana,sallama ya yi mata,”Aslm Husna ykk?” “Wassalam Abba Abba ydrn,”Husna ta faɗa (kasancewar haka take kiranshi). “Lafiya lau Alhamdullih Husna ta mu ta yan amana,”Inji Chairman. “Mash Allah Abba Abba,”Husna ta faɗa. “Dan Allah Husna taimako nake nema wurinki,”inji Chairman. “Wane irin taimako kake nema Abba?”inji Husna. “Dan Allah Husna gobe za’a je gaisuwar gidansu mai Shari’a to shine muke so dan Allah a samu abin da za’a kai masu,kuma kin ga babu kuɗi aje yanzu a asusun group,”inji Chairman. “Eh hakane Abba yanzu ya kake ganin za’a yi kenan?”inji Husna. “Husna idan babu takura dan Allah fanke muke so kiyi mana idan akwai kuɗi hannunki,”Inji Chairman. “To shi ke nan Abba wurin ƙarfe nawa za’a yi?”inji Husna. “Idan dai son samune Husna wurin ƙarfe ukku an gama komai zuwa ƙarfe huɗu kuma mun tafi,amma Husna kuɗin fulawar da man sai idan an dawo za’a ba ki,”inji Chairman. “Ba damuwa Abba insha Allah za’a yi komai yadda ya kamata,”inji Husna. “To ke kaɗai za kiyi ko su Maryam su zo nan gidanku su taya ki?”inji Chairman. “Abba lafiya lau zasu iya zuwa,”inji Husna. “To shi ke nan zan masu magana sai su zo da wuri dan ku gama akan lokaci,”inji Chairman. “To Allah ya kaimu goben lafiya,”inji Husna. Banƙwana su kayi sannan ta sauka,sai bayan sun gama maganar ne ta fara tunanin inda za ta samu kuɗin da za’a yi amfani da su wurin fanken, dan ita dai yanzu ba ta maganin ko Naira,tunani ta shiga yi ganin dai ba ta samu mafita ba yasa ta miƙewa domin ta je wurin Mama,ta na fitowa tsakar gida ta ga Mama ta rufe ƙofar ɗakinta. Ɗaki ta dawo ta kwanta bisa gado,har ta kwanta ta tuna da ba ta yi alwalla ba,tashi ta yi taje ta ɗauro alwalla sannan ta rufe ƙofar ɗakinta,ruwa ta ɗauko ta sha sannan ta hau kan gado, addu’a ta yi ta shafe jikinta ta kwanta ta na tunanin yadda za ta yi goben wurin kuɗin amma ta san Allah zai rufa asiri duk ma yadda za’a yi insha Allah ta san sai ta yi fanken. Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 13* Husna na idar da sallar asuba ɗakin Mama ta nufa, sallama ta fara yi jin gyaran murya yasa ta shiga cikin ɗakin,akan sallaya ta iske Maman ta na azkar,a gefen Maman ta zauna bisa lokar gado,zamanta babu daɗewa Mama ta kammala azkar ɗinta,inda Husna ke zaune ta kalla ta na mamakin abin da ya kawo Husna ɗakinta a wannan lokacin,(ba ta shiga cikin ɗakin a irin wannan lokacin daga bakin kofar ɗaki take tsayawa ta gaisheta sai ta juya). “Ina ƙwana Mama?”inji Husna. “lafiya lau Husna lafiya meyafaru na ganki yanzu ko kina buƙatar wani abu ne!”Mama ta faɗa ta na ƙa ra bin Husna da kallon mamaki. “lafiya lau Mama babu wata matsala, alfarma dai nazo nema wurinki,”Husna ta faɗa tare da saukowa daga saman lokar da take zaune. Bin ta da kallon mamaki Mama ta ci-gaba da yi har ta zauna kan ledar da ke malale a tsakar ɗakin,”alfarma kuma Husna ina jin ki mekikeso?” “Mama yau ake sadakar kwana ukku ta Babansu Mai Shari’a…..”Husna ta faɗa ta na bin Mama da kallo ta na son ganin yadda Mama za ta ɗauki abin. “Ke nake saurare kin fara magana kuma kin yi shiru ko dai akwai matsala ne Husna?”Mama ta faɗa tare da tsare Husna da idanuwa. “Mama jiya bayan na shiga ɗaki aka yanke shawarar mu ƴan amana zamu yi fanke wanda za’a kai gidan sadaka yau,to shine Abba ya ce babu kuɗi a hannu idan da hali nayi daga baya sai a bani kuɗin,ni kuma babu kuɗi a hannuna shine nazo ki ara mana idan aka bada sai na maido maki,”Husna na kai wa nan ta yi shiru cikin ranta ta na addu’ar dacewa. Murmushi Mama ta yi cikin ranta ta na ƙara jinjina irin wannan soyayya da ƴarta ke ma waɗannan mutane,duk abin da ya dangancesu ta na ba shi muhimmanci sosai,dama ta yi mamakin abin da ya fiddo Husna yanzu dan haka ta ce,”ai muna da fulawa da mai a gidan nan kuma jiya an kawo suga dan haka idan dai fulawar tiya ukku za ta isheku sai ki ɗiba kawai.” Cikin farin cikin da ya kasa ɓoyuwa ta ce,”Nagode kwarai Mama Allah yasa ka da mafificin alkhairi Allah ya ƙara buɗi na alkhairi.” “Ameen ya Allah sai ki tashi kije ki kwanta ko yau ba ki komawa baccin?”Mama ta faɗa tare da miƙewa tsaye ta na linke sallaya. “Zan koma Mama anjima Maryam da Fadila za su zo tare zamu yi aikin dasu,”Husna dake miƙewa tsaye ta faɗa ta na kallon Mama. “To shi ke nan Allah ya kawosu lafiya,”daga haka Mama ta nufi wadrop ta saka sallaya. Ganin haka yasa Husna fita ta koma ɗakinta wayarta da ke kan gado ta ɗauka,kira biyar ta gani ta na dubawa ta ga Iro ne,dama ta yi tunanin shine saboda yau bai tada ita sallah ba(haka suke yi cikinsu duk wanda ya riga tashi shi ke tada ɗaya). Murmushi ta yi cikin ranta ta ce yau akwai chakwakiya kenan tsakanin ta da Iro. Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 14* Kira ta danna masa bugu ɗaya ya ɗauka,ko sallamar da take bai amsa ba ya fara tambayar ta,”lafiya kike?ina kika shigane ina ta kira ba ki ɗagaba fatan dai kina lafiya?” Ya ƙarasa faɗa cikin alamun damuwa. Wani ƙasaitaccen murmushi ta ƙawata fuskarta da shi sannan ta ce,”kai Sweet Irona irin wannan ruɗewa haka…?” “Malama ki amsa man tambaya!…”ya faɗa cikin fushi. Dariya ta sa ki cikin jin daɗi ta ce,”kwantar da hankalinka babu abin da ke damuna kuma bani da wata matsala,naje ɗakin Mamane na bar wayata nan ɗakina.” Wata wawuyar ajiyar zuciya Ibrahim ya saki,wadda har sai da Husna na jiyota,cikin shan mur tamkar wanda yake a gabanta ya ce, “Amma wannan wane irin zamane kika yi a chan daga zuwa ki gaisheta sai ki nemi wuri kiyi zaune ko aiki ta sanyaki?” Dariya Husna ta yi wadda har sai da ya jiyo sautin dariyar sannan ta ce,”A’a na tsaya mun yi maganar fanken da za’a yi idan anjima a kai gidan rasuwa…” “Ke aka sanya kiyi fanken?” Bai bari ta ƙarasa faɗar maganarta ba ya jefa mata tambayar da ta sanyata yin shiru. “Eh mun yi magana da Abba jiya bayan mun gama waya da kai,” ta faɗa cikin sanyin murya. “Amma kin san ke za kiyi fanken har muka gama waya baki sanar dani ba!” Ya faɗa cikin alamun fushi. Kwantar da muryarta ta yi fiye da farko ta ce,”Sweet Iro na faɗa maka sai bayan mun gama waya da kai sannan mu kayi magana da Abba.” “To yaushe ya kawo maki kayan yin fanken ko sai anjima?” Yana faɗin haka ya yi shiru yana jiran amsar da za ta ba shi. “A’a ya ce nayi daga baya za’a ban kuɗin saboda yanzu asusu babu kuɗi, kuma lokaci ya ƙure ba’a yi maganar nawa zamu haɗa ba sai daga baya za’a yi maganar,”ta faɗa cikin sanyin murya. “Ke ina kika samu kuɗin da za kiyi hidimar dasu bayan ko jiya ba ki da kuɗi?” Ya faɗa cikin sauri. “Abin da yasa naje wurin Mama kenan dan ta araman to sai kuma ma ta ce a ɗebi kayan gida ayi dasu ba sai an siyo ba kuma a bar kuɗin,”Husna ta faɗa. “Banganeba wane kayan gidan za’a ɗiba?” Ibrahim ya tambayi Husna. “Kai Sweet Iro kamar ba da Hausa nake maka bayani ba? Muna da fulawa da Mai sai suger shine Mama ta ce a ɗiba ayi kawai,”Husna ta faɗa cikin shagwaɓa. “Yanzu ke wannan hidimar kika ɗora masu ba ki san yanayin da ake ciki ba?”Ibrahim ya faɗa. “Kai Sweet Irona ita fa ta ce a ɗiba wallahi ni bance mata ta bamu ba,rancen kuɗi kaɗai naje ta ban,”Husna ta faɗa tare da kishingiɗawa jikin katakon gado. “Allah ya so ki yarinya bake kika tambayeta ba da jikinki ya faɗa maku,”Ibrahim ya faɗa. “Naji dai tun da ban aikata ba sai a bi wani sarkin ba dai ni ba,”Husna ta faɗa ta na dariya. “To zan kwanta ban daɗe da dawowa daga masallaci ba,ke ɗaya za kiyi fanken ko har dasu Maryam?” Ibrahim ya tambayi Husna. “Eh ni da Maryam da Fadilane amma sai wurin ƙarfe sha biyu saboda mu gama da wuri,”Husna ta faɗa. “To shi kenan sai anjima ki kular man da kanki,”yana faɗin haka ya kashe wayarshi. Kallon wayar Husna ta yi ta na murmushi cikin ranta ta ce sweet Iro ba dai rigima ba,Allah ya barmu tare ta faɗa tare da kwanciya domin ita ma baccin take ji,aikuwa ta na kwanciya babu daɗewa bacci ya dauketa. Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 15* Sai wurin ƙarfe tara da ƴan mintuna sannan Husna ta tashi daga bacci,ta na tashi sharar ɗakinta ta fara yi sannan ta fito tsakar gida,sai da ta sharo ɗakin Mama sannan ta sharo wani ɗaki sai ta haɗa da tsakar gidan. Ta na ida sharar kayan wanke-wanke ta haɗa ta wanke,ta na gama wanke-wanke wanka ta shiga,ba ta daɗe a wurin wankan ba ta fito,yau jin ta take yi cikin walwala da annabawa,babu abin da ke mata daɗi a rai sai idan ta tuna yau za ta ga mutanen gidan ƴan amana,duk cikin gidan mutum huɗu ta sani a fuska daga Maryam, Ibrahim, Umar Sulluɓawa sai Abba. Kallo ɗaya za kai mata ka ga tarin farin cikin da take ciki,ko ayyukan ma yau cikin karsashi take gudanar dashi,shi ya sa ko Lokaci mai tsawo ba ta ɗauka ba ta kammala,ta na fitowa daga wanka doguwar riga kawai ta sanya. Ƙafafuwanta kawai ta shafa ma mai sai turare da ta fesa, kitchen ta shiga flaks ɗin ruwan zafi ta buɗe ta zuba dai-dai cikinta sannan ta rufe,wurin da kayan tea suke aje taje ta haɗa bread dake aje gefe da alama na ta ne ta ɗauka. Ɗakinta ta dawo ta zauna,ta na kalacin ta na tunanin yadda za ta haɗu da mutanen da take tsananin so a rayuwarta,da haka har ta kammala kalacin ta ɗauraye kayan da ta ɓata sannan ta maida komai inda yake. Agogo ta kalla ganin har sha ɗaya da rabi ya sanyata nufar store ɗinsu,fulawa ta auno tiya ukku cikin wata Babbar roba ta zuɓo fulawar,yis ta ɗauko tsakar gida ta dawo ta har ta zauna sai ta tuna da ta bata ɗauko gishiri ba sai ta koma,bayan ta ɗauko ta zauna cikin sauri ta ke kwaɓa fulawar cikin lokaci kaɗan ta gama kwaɓin,amma fa ta jigatu saboda kafaɗunta duk sun gaji. Bayan ta gama kwaɓin ta ja robar ta kaita saitin rana,dawowa ta yi domin ta gyara inda ta ɓata,ta na cikin gyaran wurin Mama ta fito daga ɗakinta ta ce, “Wai aikin me kike haka cikin gidan Husna tun ɗazun nake jin motsinki?” Ɗagowa ta yi daga duƙen da take ta ce,”Mama kin manta yau akwai aikin fanke shi ya sa na fito da wuri ga shi ma har na kwaɓa.” Cikin mamaki Mama ta ke bin Husna da kallo,Husnar da bata son aiki ko kaɗan,duk in za’a sanyata aiki a gidan ba ta yin shi cikin daɗin rai,dan in ma kana da zuciya baka sanya Husna aiki,dan ba ta yin shi sai Mama ta mata jan ido a lokacin zata yi shi,yau ga Husna ba tare da an sanyata ba ta na aiki,lalle dole a jinjina ma waɗannan mutanen. Dariya Husna ta yi ta ce,”Mama sai kallona kike!” “Ba dole na kalleki ba Husna wannan aiki da ki kayi cikin lokaci,”Mama ta faɗa ta na ɓoye mamakinta. “Kin ga yanzu Mama lokacin da su Maryam zasu zo ta tashi sai tuya kaɗai zamu fara yi,”Husna ta faɗa cikin fara’a. “Hakane Allah ya taimaka,”Mama ta faɗa ta na komawa ɗakinta saboda wayarta da ke ƙara. Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 16* Husna na ganin shigar Mama ɗakinta ita ma sai ta nufi na ta ɗakin,ta na shiga ɗakin kan doguwar kujerar dake ɗakinta ta zauna, hannu ta miƙa ta ɗauki fankaceciyar wayarta dake ajiye a gefen gado, agogon wayar ta kalla gani ta yi har ƙarfe goma sha ɗaya da ƴan mintuna. Data ta buɗe sannan ta shiga WhatsApp, saƙonni su kai ta shigowa a wayar sai da ta jira su ka gama shigowa sannan ta fara maida amsa. Group ɗinsu na ƴan amana ta shiga don duk yau ba ta shiga ba,mutane ta iske na fira sallama ta yi ita ma,cikin sauri Dabai ya ce,”yar halak kin ƙi ambato yanzu nake maganarki.” “Gulmata dai za ka ce kayi kawai Malam.” Cikin son ƙular da Dabai Husna tai maganar. “Ke matsalata da ke abin arziƙi bai karɓeki ba daga an ma damu dake sai kuma ki fara wulaƙanci!” Dabai ya faɗa cikin jin haushi. Dariya Husna ta kama yi saboda ta san ta fara ƙular da shi dan haka ta ce,”ai matsalar ba ka iya daina yi man magana idan kuma kana iyawa to daga yau kar ka ƙara.” “Ke ɗin ke bazan iya daina yi ma magana ba to ke wacece da har zan kasa daina yi maki magana dallah Malama matsa chan gefe ka da ma na maujeki!!”Dabai ya ƙarasa maganar cikin jin haushi. “Gaskiya Abdul Dabai Husna ta ga wurin baccinka” cikin son ƙara hayaƙa Dabai Mustapha Madina ya faɗa. “Ka kyaleta ai yau ta guji haɗuwarmu ni da ita,wai ma dan ta raina ni wai ban iya daina yi mata magana wallahi yarinyar nan kin ci abinci!!” cikin jin haushin Husna, Dabai ya ƙarasa maganar kamar zai yi kuka. “Ai ba ƙarya nayi ma shi ba Musty kuma a gabanshi na faɗa ba bayan idonshi ba…”Husna ta yi maganar cikin dariya da son ƙara cusama Dabai haushi. “Ban da lokacinki yarinya amma abu ɗaya zan faɗa maki shi ne ki guji haɗuwarmu idan anjima…” Cikin jin haushi Dabai ya yi maganar saboda da ma kowa yasan Dabai da saurin hayaƙa. “Gaskiyarki ɗiyata ai kowa ya san Dabai ba zai iya daina yi maki magana ba” Nana Aisha ta faɗa wadda zuwanta kenan cikin gidan ta yadda ana maganar kawai ta sanya baki. “Yauwa Momy faɗa masa dai kowa ya gane abin da yake nufi…”Husna ta faɗa ta na dariya saboda tasan yau ta kai Dabai ƙarshe. “Ke wannan Nana A’ishar ke kike sanya wannan Husna Husnar ta raina mutane hakanan kun kasa yi ma yarinya tarbiyyar girmama manyan…”Dabai ya faɗa. “Ina manyan suke ai ni ban ga manya a nan ba balle har na girmamawa…” Husna ta faɗa cikin sauri. “Ni ɗiyata nayi mata tarbiyya mai kyau kuma ni ban ga rainin da ta yi ma mutane ba,kawai dai nasan ɗiyata ba ta ɗaukar raini shine kawai abin da nasani.” Nana A’ishah ta faɗa. “Ke Husna ki kiyayeni duk nan gidan akwai wanda kika raina irina kuma zan ɗauki mataki wallahi!” Dabai ya faɗa cikin jin haushi. Sannan ya cigaba da magana,”ke nan wannan ita ce tarbiyyar da kike faɗin kin ba ta?to gaskiya ki chanza tarbiyya saboda nan dai kowa ya san babu.” “Ni ban da lokacinka na tafi in yi aikin gabana,kai kuma sai ka zauna ka tsare mana group ka da kuma a tafi yawo, Momyna sai anjima na tafi aiki zanyi,” Husna na faɗin haka ta fita daga group ɗin. Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 17* Husna na fita daga WhatsApp, contact ɗinta ta shiga lambar Maryam ta danna ma kira,bugu ɗaya ana biyu Maryam ta ɗauka,”My Husna kin ga har yanzu ba mu zo ba koh?” Maryam ta faɗa cikin fara’a. “Eh wallahi Anty Maryam kuma ga rana ta fara yi wai dan mu gama da wuri shi ya sa saboda nasan yanzu fulawar ma har ta tashi.” Husna ta faɗa. “To insha Allah My Husna gamu nan tafe Fadila nake jira ita ma kuma ta na kan hanya.” Maryam ta faɗa. “To shi ke nan sai kun zo Anty Maryam.” Husna ta faɗa tare da kashe wayar. Husna na kashe waya ta aje wayar a gefen ta,tsakar gida ta nufa dan duba halin da fulawar ke ciki,kamar yadda ta zata hakan ce ta kasance har ta tashi sosai,maidawa ta yi ta rufe,store ɗinsu ta nufa ta ɗauko murhu ta aje inda suke ajewa idan zasu yi sanwar murhu,gyara murhun ta yi tare da shirya itatuwa a ciki,kalanzir da ashana ta ɗauko ta na cikin buɗe galan ɗin kalanzir ɗin ta ji wayarta na ƙara,fasa zuba kalanzir ɗin ta yi ta rufe galan ɗin, ɗaki ta nufa cikin sauri amma duk da haka ta na shiga wayar na karawa. Wayar ta ɗauka dan duba wanda ya kirata,bisa hannun kujera ta zauna ta na duba wayar, Chairman ta gani ƙoƙarin kiranshi ta fara kafin ta kira sai ga kiran ya sake shigowa,ɗagawa ta yi tare da yin sallama. “Assalamu Alaikum Chairman ka tashi lafiya?” “Wa’alaikissalam lafiya lau Alhamdullih Husna kun fara aikin dai ko kin ga yanzu har ƙarfe sha biyu ta yi muna so zuwa ƙarfe biyu da wani abu azo a ɗauka kin san yanzu an maida addu’ar ƙarfe ukku kada kuma a makara,”Chairman ya faɗa cikin sanyin murya. “Kar ka damu Abba insha Allah ba zamu makara ba yanzu haka fulawar ta tashi,su Maryam kawai nake jira su ƙaraso kuma har wuta ma yanzu zan hura na fara kafin su iso,”Husna ta faɗa. “Yauwa Husna sannu da aiki idan aka haɗu sai a ba ki kuɗin kayan da kika kashe,yanzu nawa kika kashe?” Chairman ya faɗa. “A’a Abba ba sai an biya ba Mama ta bada duka kayan ta ce a bar kuɗin,”Husna ta gayama Abba. “Allah sarki Mama mun gode ƙwarai Allah ya saka da mafificin alkhairi ki ce muna godiya kafin mu zo,dan dole mu shigo Mu yi mata godiyar wannan hidima da muka ɗora mata…!”Chairman ya faɗa cikin tsananin farin ciki. “Bakomi Abba zan faɗa mata insha Allah sai kun zo ɗin bari naje na fara aikin chan kafin su ƙaraso saboda Fadila kaɗai ake kira.”Husna ta faɗa. “To shi ke nan Husna sannu da ƙoƙari gaskiya muna alfahari da shigowarki cikinmu,har abada ƴan amana baza su manta da karamcinki a garesu ba.” Abba ya faɗa cikin tsananin farin ciki. “Bakomi Abba ai zaman tare kenan ka kyautatama wanda kake tare da shi nima nagode da yabonku a gareni sai anjima.” Bata jira amsar Chairman ba ta kashe wayarta,tsakar gida ta fito dan cigaba da aikinta Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 18* Wuta Husna ta hura ta cigaba da suyar fanke,sai da ta soya ya kai rabi sannan ta jiyo sautin Fadila na sallama,hanyar zaure ta kalla tare da amsawa. “Wa’alaikissalam Fadilarmu!” Husna ta faɗa cikin murna. “Allah sarki Husna sannu da aiki,dan Allah kiyi haƙuri Husna mun barki da aiki sannu….!” Maryam ta faɗa cikin sigar lallashi. “Kai My Anty har kin sanya naji kunya…ni fa abin da yasa ki ka ga na fara saboda kin san halin Abba da zumuɗi har fa ya kirani wai an gama?” Husna ta faɗa tare da tsame fanken da ke cikin kasko. “Husna ke da wa ke magana?” Mama ta faɗa lokacin da take fitowa daga cikin ɗakinta. “Mama su Anty Maryam ne fa…!” Husna ta faɗa ta na nuna su Fadila dake tsaye bakin kofar zaure tun ɗazun,duk maganar da su ke da Husna da ma basu shigo ba. Da kallo Mama ta bi inda Husna ke nuna mata,su Maryam ta gani tsaye su na kallonta,ta buɗe baki ta ce. “Ke dai Husna na ga ranar da za kiyi hankali yanzu ki iya ki ce masu su shigo amma sai hakan ta gagareki sai dai ki tsaresu da labari tun kafin su shigo cikin gidan… Maryam ku shigo mana kun biye ma shirmen Husna kun yi tsaye,in ba yi hankalin ce maku ku shigo ba ai sai ku shigo ko!!” Mama ta ƙa ra sa faɗa ta na kallon su Maryam dake tsaye su na mata murmushi. “Kiyi haƙuri Mama shigowa zamu yi da ma…ina wuni Mama” Fadila ta faɗa tare da durƙusawa ta na gaida Mama. “Lafiya lau Fadila ya Mamarku?” Mama ta faɗa. Maryam ma durƙusawa ta yi ta ce,”Mama ina wuni ya gida ina su Auter?” Kallonta Mama ta yi ta ce,”lafiya lau Alhamdullih su Auter sun tafi Makaranta ya Hajiyarku?” Duƙar da kai Husna ta yi ta ce,”lafiya lau ta ke ta ce ma a gaisheku.” “Masha Allah muna,amsawa ku shigo daga ciki mana” Mama ta faɗa tare da komawa cikin ɗakinta saboda su samu damar sakewa. Mama na shiga ɗakinta su Fadila suka taho har inda Husna ke sanya fanke cikin kaskon dake kan wuta, Abaya Maryam ta ɗora saman igiyar shanyar dake ɗaure a tsakar gidan. “Kawo ki huta My Husna ai kin yi ƙoƙari har kin ku sa toyewa duka” Maryam ta faɗa tare da ƙoƙarin amsar abin da Husna ke tsame fanken. “Kai My Anty daga zuwanku ko hutawa ba zaku zauna ku yi ba….balle ku sha ruwa sai kawai ku kama aiki!” Husna ta faɗa tare da riƙe abin tsamar. “Haba Husna dan Allah ki sakar mata mu ƙarasa aikin nan ai kinyi ƙoƙari,mu ida wane kawai ya rage zamu yi saboda duk kin toya yafi rabi” Fadila ta faɗa tare da cire abayarta inda Maryam ta ɗora ta ta nan ita ma ta ɗora. Ganin sun dage akan sai ta bar masu ya sanya Husna ta sakar masu abin tsamar,abayoyinsu ta ƙwashe daga saman igiyar ta nufi ɗakinta dasu domin ta ajiye masu a chan nan waje kuma saboda ka da su ɗauki zafin rana. *PAGE 19* Husna na shiga ɗakinta saman doguwar kujerar ɗakin ta ɗora abayoyinsu bayan ta linke masu,fitowa ta yi ta nufi kitchen,filet ta ɗauka tare da shiga falon Mama ta ɗauko ruwa tare da kunun Aya ta ɗora a saman filet,tsakar gida inda suke ta dawo. “Ga ruwa ku sha Anty Maryam tun da kun ƙi bari mu huta!” Husna ta faɗa tare da jawo wata kujerar roba har gaban Fadila dake zaune gefen Maryam ta ɗora filet ɗin sama. “Sannu da ƙoƙari Husna” Anty Maryam ta faɗa ta na janye robar gabanta saboda ta cika. “Kai Anty Maryam wallahi har kun sanya na fara jin kunya wai meye abin yi man sannu har haka wannan abun fa duk yi wa kaine!” Husna ta faɗa tare da miƙewa ta na nufar kitchen. Da kallo su ka bita har ta shige cikin kitchen ɗin,sai da ta shige sannan suka maido kallon ga junansu Fadila ta ce,”gaskiya Husna na da ƙoƙari sosai.” “Eh wallahi shi ya sa su Abba ke yabonta sosai ke ba ma Abba ba duk wanda ke cikin group ɗin yana yabonta Allah dai ya bar zumunci kawai” Maryam ta faɗa tare da ɗaukar ledar ruwa ta na sha. “Ameen ya rabbi! Kin san wannan fanken kyauta take yin shi kuwa?” Fadila ta tambayi Maryam dake shan ruwa. Cikin zaro ido Maryam ta ce,”kyauta kuma Fadila? ba ance sai anje ba za’a haɗa mata kuɗin ba?” “Wallahi Sis mun yi waya da Chairman lokacin ina kan hanya yake faɗaman wai Mamarsu Husna ta bada kayan fanke ta ce a bar kuɗin” Fadila ta faɗa tare da gyarama Maryam kwandon da ake sanya fanken dan ya tsane kafin a sanya a roba. “Gaskiya Sis waɗannan mutanen na da kirki sosai dan wallahi wannan sayayyar fanken idan kuɗin ne zamu kashe sun fi dubu biyar amma gaskiya Allah yasa ka masu da mafificin alkhairi” Maryam ta faɗa cikin alamun jin daɗi saboda da ma aro kuɗi ta yi saboda ko da ance su bada kuɗin da aka haɗa. “Ke dai bari Sis wallahi zasu kai yadda kaya su kayi tsada yanzu,kuma wallahi yanzu da zan fito sai da na aro dubu ɗaya da ɗari biyar saboda ka da ace ka ba da kuɗi kuma ba ka dasu(saboda idan za’a yi wani abu wurin biki ko suna ko rasuwa officials ke haɗa kuɗi su yi abu). Fadila ta faɗa da iyakacin gaskiyarta. “Wallahi Sis kamar kin shiga cikin zuciyata ni ma sai da na aro kuɗin wurin Mama sannan na fito kin ga yanzu sai in maida mata kuɗinta,amma fa naji daɗi wallahi kuma Sis ita Husna kullum cikin hidimtawa ƴan amana take da kuɗinta da jikinta amma ita har yanzu ko naira ba’a taɓa kashe mata ba kuma bata taɓa nuna damuwa ba!” Maryam ta faɗa cikin sanyin murya. “Ke dai bari Sis gaskiya ta na ƙoƙari sosai kuma in kika lura ita kowa na ta ne babu ruwanta ban taɓa jin ta yi rigima da wani ba a cikin gidan ƴan amana ba tun da take amma….” Maganar Maryam ta datse ne saboda labulen ɗakin Mama da aka ɗaga,duk kallon kofar suke gaba ɗayansu da fatan babu wanda yaji me suke tattaunawa ba. Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 20* Mama ce ta fito hannunta ɗauke da filet da kofi da alama wanda ta yi amfani da shi ne da safe,cikin sauri Fadila taje da nufin ta karɓi kayan dake hannun Mamar. “Haba ki bar shi Fadila zan kai da kaina” Mama ta faɗa ta na murmushi. “A’a Mama ki kawo na kai dai” Fadila ta faɗa tare da riƙe filet ɗin. “To shi ke nan Fadila nagode Allah ya yi maku albarka.” Mama ta faɗa tare da sakar ma Fadila filet ɗin,dubanta ta maida wurin Maryam dake aiki ta juyo wurin Fadila da har ta kai kofar kitchen. “Ina Husna ta shigane ta sakar maku aikin kuma?” Mama ta tambaya tare da bin tsakar gidan da kallon ko za ta ga Husna. “Ta na kitchen!” Maryam ta faɗa ta na cigaba da aikinta. “Husna!” Mama ta ƙwalama Husna kira. “Na’am Mama gani” Husna ta fito cikin sauri da tawul a hannunta ta na tsane lema. “Me kike yi kitchen kika bar masu aiki?” Mama ta faɗa tare da tsare Husna da idanuwa. “Taliya na ɗora masu Mama kafin a ida tuyar nima na gama dafawa.” Husna ta faɗa tare da janye robar da aka cika da fanke gefe. “Yauwa kin yi tunani mai kyau nima da abin da zance maki kenan a nemar masu abin da zasu ci tunda kin yi wannan tunanin kuma shi ke nan je ki ci-gaba da aikin.” Mama ta faɗa ta na juyawa domin komawa cikin ɗakinta. Ganin Mama ta koma ɗakinta yasa Husna komawa wajen Anty Maryam,duba ƙullun fulawar ta yi ta kalli Anty Maryam ta ce, “Sannu Anty Maryam kin ma kusa ƙarasawa ba ri na ɗauko kular da za’a zuba fanken ciki na ɗauraye” Ta faɗa ta na komawa kitchen ɗin,bakin kofar shiga suka haɗe da Fadila dake ƙoƙarin fitowa,gefe Husna ta matsa ta ba Fadila hanya. Shigarta kitchen babu daɗewa ta fito da wata babbar kula ta ɗauraye ta sannan ta kife kular dan ta tsane. “Fadilarmu bari naje na duba sanwar kafin ku ƙarasa nima na gama.” Husna ta faɗa tare da nufar hanyar shiga kitchen ɗin. Har ta kusa shiga kitchen ɗin taji ƙarar wayarta,juyawa ta yi ta nufi ɗakinta,saman dressing mirror ta nufa saboda nan take jiyo ƙarar wayar. Fuskar wayar ta kalla ganin Iro ne yasa ta ɗauka ta ka ra a kunne tare da sallama. “Wa’alaikissalam yakike ya aikin?”Iro ya faɗa. “Lafiya lau Sweet Iro ga aiki nan har mun kusa ƙarasawa.” Ta faɗa ta na murmushi. “Allah ya shiryaki taɓa ganin aikin da ki kayi babu raki ba sai wannan!” Iro ya faɗa tare da gyara kwanciyar shi akan gado. “Sweet Iro nima har mamakin hakan nake yi kawai dai nasan hakan ya faru ne saboda ƴan group ɗin da nake so…!” Husna ta faɗa cikin dariya. “Yau dai hankalin ki zai kwanta tunda yau za ki ga kowa da kowa” Iro ya faɗa. “Eh wallahi har na ƙagara anjima ta yi!” Husna ta faɗa cikin nuna alamun ɗoki. “To sai anjima ɗin da ma na kira kine dan naji ya kike sai kun ida ɗin,”Iro ya faɗa. “To shi ke nan nagode ka kularman da kanka” Husna ta faɗa. “Insha Allah nima kiyi man alfarmar kulaman da kanki!” Iro ya faɗa cikin lallashi. “Ba ka da matsala sweet Iro sai kun zo” Husna ta faɗa tare da datse wayarta,cikin sauri ta nufi kitchen dan duba sanwar da ta ɗora. Cikin kitchen ɗin ta tadda Mama har ta sauke tukunyar,kallonta Mama ta yi ta ce,”ina kika shiga ki ka bar sanwar kan wuta ba dan Allah yasa na shigo ba da har sai taliyar dahe sosai.” “Ibrahim ya kirani yanzu kiyi haƙuri kawo na tsane taliyar…!” Husna ta faɗa tare da ƙoƙarin amsar tukunyar. Kallonta Mama ta yi ta ce,”ba ri na ƙarasa maki ki je ki shirya Hajiya ke son ganinki yanzu naso na faɗamata ta bari da daddare kije amma ta kafe akan yanzu take son ganinki!” Cikin sauri Husna ta saki ludayin dake hannunta…. Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 21* Cikin sarƙewar halshe Husna ta ce,”Ma…ma…kin…san fa in…da zanje kuma duk ba wannan ba ta ya zan iya faɗama su Abba bazan samu zuwa ba…?” Mama ta bi Husna da kallon tausayi ba dan komai ba sai dan yadda ta san Husna ta ƙwallafa ranta ga tafiya wurin gaisuwar nan,cikin dauriya ta ce,”Husna nayi bakin ƙoƙari na amma Hajiya ta kafe akan lalle sai kin je yanzu ta na son ganinki,kin san ban da ikon ja da maganar Hajiya saboda ba tsarata ba ce,kiyi haƙuri kiyi sauri ki shirya idan da rabo in kika je ko da a gidan gaisuwar ne sai ku haɗe.” Mama na kai wa nan ta juya ta na sake duba taliyar,saboda idan ta na kallon fuskar Husna tausayin Husnar ke ƙara shigarta. Husna ganin Mama ta juya mata baya ya sa ta fahimci babu wani taimako da za ta samu daga wurin Maman,dan haka jiki a saɓule ta juya tsakar gida inda su Maryam ke tuyar fanken ta nufa. Kallo ɗaya Fadila ta yi ma fuskar Husna ta fahimci ba ta cikin hayyacinta,da ƙafa Fadila ta zunguri Maryam wadda ba ta san abin da ke faruwa ba sai ƙoƙarin sauke kaskon daga kan wuta take yi, ɗagowa Maryam ta yi bayan ta juya man kaskon cikin wani kwano sai ta aje kaskon a gefe, Maryam ba ta sauke ke idanuwanta a ko ina ba sai akan fuskar Husna,cikin sauri Maryam ta ce,”My Husna lafiya kuwa na ga yanzu kika bar nan wurin lafiya lau amma yanzu da gani kina cikin damuwa meke faruwa ne?” Shiru Husna ta yi har sai da ta janyo jarka da suke zuba ruwa a ciki ta zauna sannan ta ce,”ina cikin matsala wallahi Anty Maryam…kakarmu ta kira yanzu wai ta na son ganina, Mama ta gayamata zanje gaisuwa idan na dawo sai naje kiran da ta ke man amma ta ce ita ba ta yarda ba yanzu take son ganina,ni wallahi na rasa yadda zan yi saboda yanzu da na ƙi zuwa Mama za ta ɗora ma laifin,ko ma ta ce Mama ta hanani zuwa.” Idanuwa su Fadila suka zuba ma fuskar Husna yadda kasan a kan fuskar ne zasu samu mafita,chan dai Fadila ta nisa tare da sauke gwauron numfashi ta ce,”Husna kar ki damu kije kiran da take maki ko dan ki fidda Mama daga zargi idan Allah yasa za ki je sai ki ga kinje ɗin idan ma ba kije ba haka Allah ya rubuta dan haka kar ki damu.” Fadila na yin shiru Maryam ta ce,”maganar ki haka take Sis ga ra taje ɗin dan rashin zuwan na ta yana iya haifar da matsala babba dan haka mafitar kawai ita ce kiyi haƙuri kije.” Girgiza kai Husna ta yi cikin raunin murya ta ce,”wallahi ban ji daɗin wannan kiran ba kuma Wallahi saboda Mama kaɗai zanje dan idan ban je ba abin akanta zai ƙare,wai duk burin da na ci yau amma Allah bai rubuta dani za’a je gaisuwar ba shi kenan Allah yasa haka shi yafi zama alkhairi.” “Ameen Husna sai haƙuri dan mu ma bamu ji daɗin rashin zuwan nan naki ba amma bakomi ai ga bikin Umma nan za’a yi kuma nasan shi kowa sai yaje.”Fadila ta faɗa cikin wani yanayi. “To shi kenan Allah ya kaimu ba ri in watsa ruwa sai na wuce,”Husna ta faɗa tare da miƙewa tsaye ta nufi ɗakinta. Da kallo su Fadila suka bi bayanta da shi har sai da ta shige ɗakinta. Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 23* Ƙanen mahaifin Husna ne Baba Abu ya shigo,cikin sauri Husna ta ƙarasa inda yake ta karɓi kayan hannunsa tare da yi masa sannu da zuwa,jawota Husna ya yi a jikinsa fuskarsa ɗauke da murmushi. “Ina ɗiyata za ta je ta sha ƙwalliya kamar za ta je gasar kyau?” Ya faɗa cikin salon tsokana,dariya Husna ta yi tare da jan mayafinta ta rufe fuska da shi. “Kai Baba ina ni ina zuwa gasar kyau ai da an koroni.” “No…no…kar ma ki fara wannan maganar ni yarinyata kyakkyawace za ta iya zuwa ko ina a yaba da kyawunta ai mu jininmu mai kyau ne a ko ina muna iya shiga…” Ya ƙarasa maganar ta re da kallonsu Fadila da ke tsaye suna kallonshi tun lokacin da ya shigo,mai da kallonshi ya yi wurin Husna ya ce. “Ɗiyata ƙawayenki ne wannan ko na ga ma kamar fita zaku yi?” “Eh…ƙawayena ne Baba,fanke muka yi da za’a kai gidan gaisuwa shine suka zo muka yi aikin har ma mun gama.” Husna ta faɗa tare da zuwa ta buɗe masa kular da aka cika da fanken. “Ina wuni Baba?” Maryam da Fadila suka haɗa baki wurin gaida Baba Abu,cikin fara’ar dake ɗauke akan fuskarsa(Kasancewar sa mutum mai fara’a da wuya ka ganshi babu fara’a a fuskarshi,shi ya sa yaran family ɗinsu ke ganin girmansa sosai dan ko da yaushe zai ga yaro to sai ya yi ƙoƙarin ganin yaro ya saki jiki da shi,kai har yaran unguwa basu da matsala da shi kowa dai Baba Abu.) “Ɗiyata miƙo man fanken nan na ɗan ci naji kun iya?” Ya faɗa tare da jawo kujera ya zauna akai,filet Husna ta nufi kitchen dan ta ɗauko,gane abin da take nufi yasa ya ce”ɗiyata ina kuma za kije ni da nace ki bani fanke.” “Filet zan ɗauko Baba na sanya maka.” Husna ta faɗa ba tare da ta juyo ba. “Kin ga dawo nan, miƙo man guda ɗaya ma ya isheni.” “Baba ɗaya kuma?ka bari a ɗauko a sanya maka dai.” Husna ta faɗa ta na sake nufar kitchen,saurin dakatar da ita ya yi,”idan dai ba za’a bani guda ɗayan da na nema ba to ki barshi nagode kin man rowa kuma.” “A’a Baba ba haka bane amma bari na baka wanda kake so ɗin.” Husna ta faɗa tare da nufar kular,jan kular ta yi har gabanshi ta ce,”Baba ka ɗauka to ga kular nan a gabanka.” “Wai Husna Muryar wa nake ji tun ɗazun cikin gidan nan?”Mama ta faɗa daga cikin ɗakinta. “Mama Baba Abu ne yazo.” Husna ta maida ma Mama amsa. “Baba Abu kuma! (da yake haka Maman ke kiranshi)Kai Husna kina fama da shiririta amma ki kawo shi ɗaki abu sai ya gagara sai dai ki tsare shi tsakar gida da magana Allah ya dai-dai ta maki tunaninki!” Mama ta faɗa cikin alamun faɗa, fitowa ta yi daga ɗakin ganinshi zaune da kular fanke a gabanshi yasa Mama ƙara cewa, “Yanzu Baba Abu kai ma sai ka biyema Husna kayi zaune anan?” Sai da ya kai fanken dake hannunshi a baki sannan ya yi Murmushi ya ce,”ba laifinta bane ni na zauna nan Hajiya…!” “Ka shigo daga ciki mana.” Mama ta faɗa ta na kallonshi, murmushi Baba Abu ya yi sannan ya miƙe tsaye,”da ma hanya ta biyo dani nan sai na ga kawai bari na shigo na ga Daughter.” Girgiza kai Mama ta yi dan tasan Baba Abu da ma akwai zumunci,”amma dai ai ka tsaya ka sha ruwa koh?” “Bar ruwan nan Hajiya akan hanya nake ina ma so na biya ta gidan Hajiya kaka daga nan.” Kafin kowa ya yi magana Husna ta ce,”lah…! Baba nima gidan Hajiya kaka zan je yanzu.” Cikin mamaki ya kalleta sai ya juya ya kalli abokanta. “Gidan Hajiya kaka kuma ba gaisuwa zaku je ba ko duk unguwa ɗaya ne?” Shiru ya ratsa wurin babu wanda ya ce komai,ganin haka yasa Baba Abu kallon Husna ya ce,”faɗaman meke faruwane?” Shiru Husna ta yi ta gagara furta komai sai gabanta dake ta faɗuwa. Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 22* Ajiyar zuciya Maryam ta sauke ta maido dubanta akan fuskar Fadila ta ce,”tsakani da Allah Husna ta ban tausayi, da gani dan bata da yadda za ta yi ne shi ya sa kawai za take kiran da kakarsu ke mata,kalli duk ya yadda ta zama kalar tausayi…” “Ai dole ta zama Sis kin ga yau kowa ya ci burin yaɗuwa da Husna dan ita ce babu wanda ya sani,kin ga tun da ta zo gidan ƴan amana ba’a yi wani taro ba,mu officials ne fa kawai muka sanya ta sanmu a fuska,amma kin ga Allah bai yadda ba!” Fadila ta faɗa fuskarta na nuna damuwa,dan har ga Allah ita ma taso ace yau anje gaisuwar nan tare da Husna amma sai ga yadda Allah ya tsara. “Allah sarki gaskiya abin ba daɗi dan ko jiya ina ji ta na jan Dabai,akan yau idan muka je salan ya ƙi zuwa da sauri ya karɓi jikkarta.” Maryam ta faɗa da iyakar gaskiyarta,dan Allah kaɗai yasan yadda kowa ya ci burin zuwa wurin gaisuwar ba dan komai ba sai dan yadda zasu yi zumunci sosai,sabbin zuwa kuma duk su haɗu da waɗanda basu sani ba. Tattaunawa suka rinƙa yi akan yadda gidan nasu na ƴan amana ke ta samun cigaba tunda aka sanya Husna a gidan,ko da ana magana a ciki amma zuwan Husna gidan gaskiya ya sanya yanzu mafi rinjayen members ɗin na fitowa ayi fira dasu,kowa na yabawa da ƙoƙarin da Husna ke yi a gidan,kowa janta wasa yake ga ƙarin abin da yafi burgesu da ita shine ta iya wasa sosai ba ta fushi. Sun ɗauki lokaci mai yawa suna tattaunawa,har Husna ta fito sanye da doguwar rigar material ja,mayafi da jakka da takalman ƙafarta duk baƙaƙe ta yi kyau sosai. Fuskarta kadaran kadahan ta ƙaraso wurinsu ta ce, Anty Maryam wai ba dai har an gama ba?” “Kai My Husna tun kafin ki shiga ɗaki fa aka gama ashe ba ki lura ba?”Maryam ta faɗa ta na kallon Husna. “Lah! Wallahi ban lura ba Anty Maryam ba ri na juye a kular da za’a sanya shi,sannunku da aiki” Husna ta faɗa tare da aje gyalenta bisa igiyar shanya ta ɗora jikkarta a kan jarka da ta tashi ɗazun,wurin da ta kife kular dan ta tsane taje ta ɗauko,fanken ta zuba har sai da ta cikata. Kallonsu Fadila ta yi ta ce,”Anty Maryam wannan ɗan kaɗan ɗin kuma ku sai ku ɗauke shi dan nasan idan ku kaje chan dai ba ci zaku yi ba.” Ta faɗa tare da karkata bakin robar dan su ga fanken da ta ragemasu. “Husna ba’a ba Mama fanken ba fa kuma kika juye.” Fadila ta faɗa tare da taso ta ƙaraso kusa da Husna. “Ke ba sai an ba Mama ba nasan ma ba zata karɓa ba.” Husna ta faɗa tare da aje robar hannunta ta nufi wani towel dake shanye kan igiyar ta goge hannunta da ya yi masƙin mai. “Gaskiya wannan ba magana ba ce Husna a kai mata dai.”Maryam ta faɗa. “Allah ku bar shi kawai ba sai an bata ba.”Husna ta faɗa tare da rataya gyalenta akai. “Sis ɗauki fanken nan ki kai ma Mama a ɗaki kyale Husna wane kalar ba za ta ci ba?” Husna ta buɗe baki ta yi magana ke nan aka yo sallama tare da shigowa,jin Muryar wanda ke sallamar ne ya sanya gaban Husna ya yi wata irin faɗuwa ta kasa amsa sallamar har ya shigo cikin gidan ta na bin shi da kallo. Amma ta kasa furta ko da kalma ɗaya ce. Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 24* “kiyi magana mana Husna lafiya dai koh?” Baba Abu ya faɗa fuskarshi da alamun damuwa. “Kyale shiriritar Husna Baba Abu wai fa Hajiya Kaka ke son ganinta shine take wannan abun,in ba dan rashin hankali ba meye abin damuwar?ai kamata ya yi ki gaggauta zuwa dan kiji kiran da ake ba wai ki tsaya shiririta ba!” Mama ta faɗa cikin faɗa dan ita ba ta ga abin damuwa a nan ba, murmushi Baba Abu ya yi tare da dafa kafaɗar Husna. “Kar ki damu ɗiyata kije kiran da Hajiya kaka ke maki saboda ba mu san dalilin kiran ba kiyi haƙuri kin ji ɗiyata!” Baba Abu ya faɗa cikin sigar lallashi,share mata hawayen da suka fara zubo mata a fuska Baba Abu ya yi. “zo muje sai na kai ki ma da kaina kinji ɗiyata…!” Baba Abu ya faɗa cikin sanyin murya,kallon ƙawayen Husna ya yi sai ya maida dubanshi gareta ya ce”tare da ƙawayenki zamu je?” Wasu sabbin hawayen suka sake zuɓo ma Husna a fuska, girgiza kai ta yi. “A’a…ba…tare zamu ba ni kaɗai zan…je su gidan gaisuwar zasu tafi…!” Husna ta faɗa cikin muryar kuka, girgiza kai Baba Abu ya yi dan sai yanzu ya fahimci inda kukan na Husna ya nufa dan haka sai ya kwantar da murya ya ce. “Kiyi haƙuri ɗiyata idan muka je kika ji kiran da Hajiya kaka ke maki sai ki wuce chan gidan gaisuwar kin ji ko kar ki damu…!” Jinjina kai Husna ta yi ba tare da ta ce komai ba,har Mama ta buɗe baki ta yi magana ƙarar wayar Fadila ta katse mata maganar,gaba ɗaya kallon inda Fadilar take su kayi,daga wayar Fadila ta yi ganin su Chairman ne. “Gamu kofar gidan.” Daga chan cikin wayar ta ji murya Chairman ya faɗa. “To shi kenan gamu nan.” Fadila ta faɗa tare da kashe wayar, kallon Husna ta yi ta ce,”ga ma su Chairman nan sun zo.” Shiru Husna ta yi sai ajiyar zuciya kawai da take yi,ganin haka yasa Mama ta ce,”Fadila ki ce masu su shigo su ɗauki kular da kansu dan wannan kayan sun maku nauyi sai dai su zo su ɗauka.” “To Mama bari na sanar masu.” Fadila ta faɗa tare da ɗaukar abayarta ta sanya,wajen ta nufa,babu daɗewa sai ga ta ita dasu Chairman su ukku ne, Chairman, Ibrahim,Baban gida har ƙasa suka duƙa suka gaida Baba Abu da Mama. “Mama mun gode ƙwarai Allah ya yi maku sakayya da gidan aljannah mun ga abin arziƙi mun gode Allah ya ƙara buɗi na alkhairi.” Baban gida ya faɗa kanshi a ƙasa, murmushi Mama ta yi ta ce,”Baba komai nima nagode.” “Muke da godiya Mama Allah ya ƙara girma muna godiya sosai.” Ibrahim ya faɗa cikin jin kunyar Mama,kafin Mama ta yi magana Chairman ya ce,”gaskiya muna godiya da wannan hidima da ake damu tabbas mun san mun haɗu da ɗiyar da ta fito daga gidan karamci babu abin da zamu ce sai dai Allah ya yi sakayya da gidan aljannah.” “Ameen nagode ƙwarai da addu’ar ku, kar ku damu ai Ɗa duk na kowane yadda zan ma Husna abu haka kuma zan maku dan haka ku daina yi man godiya,fatana dai duk inda ku ka tsinci kanku ku kasance masu tare mutuncinku.” Mama ta faɗa fuskarta da murmushi,su ma sunkuyar da kai ƙasa suka yi amma kana hango murmushin dake kwance akan fuskarsa. “Insha Allah zamu kasance masu kiyayewa muna godiya ƙwarai da gaske.” Suka haɗa baki wurin faɗa dan matar ta ƙara ƙima a idanuwansu,nan ne suka gane inda Husna ta gado halinta. “Ku tashi ku tafi lokaci na ƙurewa yamma ta kawo jiki sai dai kuyi haƙuri Husna bazata samu zuwa ba kakarsu ke kiranta amma wani lokacin insha Allah zata je kuyi haƙuri…!” Mama ta faɗa cikin lallashi,daga inda take ta na hango yadda fuskarsu ta chanza amma dai hakan nan suka daure. “To Mama mun gode,bakomi wata ranar sai taje ai wani abun yafi gaban wani hakan ma muna godiya.” “Ku yi haƙuri ita ma ba taso hakan ta faru ba amma insha Allah gaba zata halarta,ga kular nan gabanku ku ɗauka Allah ya kiyaye hanya.” Baba Abu ya faɗa wanda tunda ga gaisuwar da ya amsa bai sake magana ba, miƙewa gaba ɗayansu suka yi,mutum biyu suka ɗauki kular sauran su ka bisu a baya. Baba Abu ma miƙewa ya yi ya ce,”to Hajiya mu ma zamu wuce sai mun dawo.” Ya faɗa tare da kama hannun Husna suka nufi hanyar fita daga gidan. “Allah ya kiyaye hanya to a gaidasu Baby da Mamansu.” Mama ta faɗa cikin ɗan ɗaga murya saboda har sun fice daga gidan,ko da suka fita har su Chairman sun shiga Mota sun tada,hannu kawai ta ɗaga masu suna haɗa ido da Iro ta kashe ma shi ido ɗaya,sai kuma suka saki murmushi a tare,mota suka shiga nan Baba Abu ya tada suka wuce. 08105217201 Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 25* Tafiyar minti goma sha biyar ta kai su unguwarsu Hajiya Kaka, ƙofar gida Baba Abu ya yi parking ɗin motarsa, Husna ta fara fitowa daga cikin motar. Cikin gidan Hajiya Kaka ta shiga da sallama,tsakar gidan babu kowa sai daga cikin ɗaki ta jiyo muryar Hajiya Kaka na amsa mata sallama,kai tsaye ɗakin ta nufa. “Wai neman me kike man da har kika hanani rawar gaban hantsina yau ko dai tafiyar ce tazo?” Husna ta faɗa lokacin da ta ke shiga cikin ɗakin Hajiya Kaka,a zaune ta iske Hajiya Kaka cikin shirin fita dan har mayafi ta yafa ma jikinta. “Dallah chan ai da tafiya ta zanyi tun yaushe na kira uwarki nace ta turoman ke amma sai yanzu kika gadamar zuwa….da ma gidan Hajiya Falmata zanje shi ya sa nayi kiranki saura kaɗan nayi tafiya ta!” Hajiya Kaka ta faɗa cikin nuna alamun ƙosawa da zaman da ta yi. Cikin sauri Husna ta ƙarasa ta rungume Hajiya Kaka ta ce,”haba ai ke ba ma kin fara wannan ɗanyen aikin ba na tafiya ki bar ni ka ga tsohuwa mai ran ƙarfe uwar gidan Alhaji Musa.” Husna ta ƙarasa faɗa ta na gyarama Hajiya Kaka zaman mayafinta,wanda rungumar da ta yi mata ya sanya ya ɗan zame. Ture hannunta Hajiya Kaka ta yi ta miƙe tsaye ta na gyara riƙon yar ƙaramar jikkar hannunta,babu komai cikin jikkar sai yar ƙaramar wayarta da goro sai kuwa ƴan kuɗaɗenta. “Za ki wuce mu tafi ko sai kin ƙara ɓataman lokaci gaskiya wannan mijinki yana tare da aiki,ace Mace duk inda za kaje da ita sai ta ɓata maka lokaci Allah ya kyauta Mali dai!” Hajiya Kaka ta faɗa tare da tilla goronta a baki,fita daga ɗakin ta yi ta tsaya tsakar gidan tare da ƙwalama wadda ke ma ta aikace-aikace kira. “Ramatu!” “Na’am Hajiya gani na ɗan kewayane ina ta sauri na fito tun da naji muryar Husna ta shigo.” Ramatu ta faɗa lokacin da ta fito daga kewayensu hannunta riƙe da buta,bisa wani katako ta ɗora butar da alama anyi shine saboda ajiyarta dan ga butoci nan da yawa aje. “Manta da wanchan mai shiriritar da yanzu na daɗe da dawowa amma kin ga har yamma ta yi ban tafi ba kuma Wallahi ban son tafiyar yammacin nan,ki ɗora tuwon alkamar da yawa saboda yau muna da baƙi anjima.” “Ke da Husna ai ba’a shiga tsakaninku Hajiya idan mutum ya shiga sai yaji kunya,insha Allah zan yi kamar yadda ki ka umarta kafin ku dawo ma insha Allah na kammala, Allah ya maido ku lafiya.” Ramatu ta faɗa ta na murmushi,dan ta gama sanin halin Hajiya Kaka ba’a shiga tsakaninsu da Husna,yanzu sun sanya ka sha kunya idan ka shiga tsakaninsu kuma Hajiya Kaka ba ta iya tafiya unguwa dole sai da Husna dan duk cikin jikokinta Husna ta fi shiga jikinta. “Haba Baba Ramatu ai ni yau wannan tsohuwar ta ɓataman shirina,ina ƴan group ɗin ƴan amana da nake ba ki labari?to yau da zamu haɗu dasu amma wannan tsohuwar ta ɓataman shirina ai ni dai gaskiya ba’a dubaman ba!” Husna ta faɗa lokacin da take fitowa daga cikin ɗakin Hajiya Kaka. “Mtssss! Haka ma za ki faɗa? ba dan nasan kina son zuwa gidan Hajiya Falmata ba ai da babu abin da zai sanya na tsaya jiranki amma ko yanzu kina iya tafiyarki…tun da ke dama abin arziƙi bai karɓeki ba!” Hajiya Kaka ta faɗa ta na hura hanji alamar ta shaƙa,gyaran murya Baba Abu ya yi wanda ya daɗe a tsaye yana sauraren dramar Hajiya Kaka da Husna wanda inda sabo duk sun saba da jinta,juyawa gaba ɗayansu suka yi dan ganin wanda ya yi gyaran muryar. Sai lokacin Husna ta tuna da tare suka zo,ida shigowa ya yi har ƙasa ya tsugunna ya gaida Hajiya Kaka,ita kuma Ramatu ta gaidashi saboda ya girmeta. “Hajiya ku taho sai na aje ku tunda hanyar nayi.” Baba Abu ya faɗa har lokacin kanshi na duƙe a ƙasa. “Daga zuwanka sai kuma ka juya ka shiga mana ko ruwa ka sha.” Hajiya Kaka ta faɗa ta na nufar ɗakinta,dakatar da ita Baba Abu ya yi ya ce,”A’a Hajiya ai tare da Husna muka zo yanzu kuma daga nan gida na wuce da ma na biyone na gaidaki.” “Amma wannan yarinya akwai sakarai amma ba ta sanar dani ba tare ku ka zo,kai ni dai wannan yarinya na ga ranar da zata yi hankali!” Hajiya Kaka ta faɗa cikin jimami,dariya Husna ta saki ta ce,”haba Hajiya Kaka duk hankalin da ake faɗar ina dashi amma ke ba ki gani ba tab gaskiya idanuwanki sun kwana biyu!” “Ki bani idanuwan ubanki sai na rinƙa gani dasu Husna!”Hajiya Kaka ta faɗa cikin fushi. Ganin ta fara hassala ya sa Baba Abu yi ma Husna nuni akan ta fita waje,shi kuma ya samu da kyar ya lallashi Hajiya Kaka suka fito dan da har ta ce ta fasa tafiyar in dai da Husna za’a je(sai ka ce ba ita ta kira Husnar ba). Shi dai Baba Abu haƙuri ya ba Hajiya Kaka har ya samu lallaɓata sai da ya kai su ƙofar gidan Hajiya Falmata ya ajesu,sai da ya ga shigarsu sannan ya juya motarshi ya yi gaba yana dariyar dramar Hajiya Kaka da Husna. 08105217201 Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 26* Sun daɗe a gidan Hajiya Falmata sosai sai gab da magrib suka baro gidan,akan hanya Husna sai mita take ma Hajiya Kaka akan daɗewar da suka yi dan ita gidansu take son ƙwana,banza Hajiya Kaka ta yi da ita ko ƙala ta ƙi ce mata har suka iso gida. Suna shigowa masallacin ƙofar gidan Hajiya Kaka ana kiran sallah,saboda haka su na shiga gidan basu zauna ba, alwalla suka hau ƙoƙarin yi. Bayan an gama sallar magrib Husna ta miƙe ta ce gida za ta tafi,nan fa Hajiya Kaka ta rinƙa faɗa akan babu inda za taje saboda dare ya yi,duk ƙoƙarin da Husna ta yi na san ganin ta tafi gida hakan ba ta samu ba,dole ta haƙura ta kwana a gidan,gari na wayewa wurin ƙarfe goma kuma ta ce gidansu za ta tafi,duk faɗan da Hajiya Kaka ke yi na ta zauna ta yi kalaci ƙin kulata Husna ta yi,dole Hajiya Kaka ta sanya mata idanuwa ta tafi. Ta na zuwa gida ta iske Mama zaune akan sallaya ta gama sallar walha,kallo ɗaya Mama ta yi mata ta ɗauke kanta,dan ta san wannan kaɗan ne daga aikin Husna,zai yi wuya taje wani wuri ta ƙwana idan kuwa har ta kama dole ta ƙwana ɗin to tun da safe za ta baro wurin. Ganin Mama na lazimi yasa ta nufi kitchen dan wata muguwar yunwa take ji,ba ta samu komai ba dan haka ta ɗora ruwan zafi Lipton da kayan ƙamshi ta sanya ta na tsaye har ya tafasa ta juye a kofi, ɗakin Mama ta dawo har lokacin Mama bata tashi daga inda ta isketa ba,gefe ta aje kofin ta koma kitchen ta ɗauko kayan shayi ta koma ɗakin Mama. Da kallo Mama ta ke bin ta har ta kammala haɗa shayin ta soma sha,sai da ta gama komai sannan ta ƙwashe ta maida su kitchen ɗin,kai tsaye ɗakin Mama ta komo Lokacin Mama ke naɗe sallayar,dan haka ta samu wuri ta zauna ta ce, “Mama ina ƙwana?” “Yanzu Husna ba za ki daina halinki ba ace ki ƙwana wuri amma tunda safe ki baro shi ko karyawa ba ki tsaya kin yi ba salan ki ja man zagi?” Mama ta faɗa ranta a ɗan ɓace,ta san dole sai Hajiya Kaka ta yi faɗan fitowar Husna ko karyawa ba ta tsaya ta yi ba. “Mama ni fa lokacin ban jin yunwa.” Husna ta faɗa ta na turo baki gaba,hannu Mama ta sanya ta doke bakin ta ce,”kin ci gidanku kina nufin daga gidan Hajiya Kaka zuwa nan gidan ne har kika ji yunwa Allah dai ya shiryaki tun da kin dawo gidan sai ki ɗauki abin da za ki ɗauka a cikinsa!” “Mama wai ina su Abba da Awu ban gansu ba?” Husna ta faɗa dan son kore maganar tahowarta daga gidan Hajiya Kaka. “Abba ya tafi makaranta,Awu kuma ya fita waje bai dai yi nisa ba dan bai daɗe da fita ba wani abu zasu yi maki ne?” Mama ta ƙarasa maganar da tambayar Husna. Girgiza kai Husna ta yi ta ce,”babu abin da zasu man na dai ga ban gansu bane shine kawai na tambayesu… Mama Baba tun ɗazun ya fita?” “Eh tun wurin ƙarfe tara ya fita bai je gidan Hajiya Kaka bane?” Mama ta amsa ma Husna. “Eh bai je ba har na baro gidan ƙila sai anjima zai je ko kuma bayan tahowata ya isa.” “A’a sai dai idan bari ya yi sai da marece ya je amma inda chan ya nufa ai da ya iske ki tunda tun ɗazun ya fita.” “To Allah ya maidoshi lafiya bari naje na ɗan ƙwanta Mama bacci nake ji…su Abba sun ce a ƙara yi maki godiya.” Husna ta faɗa lokacin har ta miƙe tsaye. “Kin samu zuwa gidan gaisuwar kuwa jiyan?” Mama ta tambayi Husna. “A’a banje ba,gidan Hajiya Falmata na raka Hajiya Kaka kuma bamu baro gidan ba sai magrib, lokacin naso na taho gida Hajiya Kaka ta hana.” Husna ta faɗa ta na nufar hanyar fita daga ɗakin. “Yanzu ai ga shi kin dawo gidan sai hankalinki ya kwanta.” Mama ta faɗa ta na zama akan kujera. Murmushi Husna ta yi ba tare da tace komai ba ta fita daga ɗakin,kai tsaye ɗakinta ta nufa. Girgiza kai Mama ta yi bayan tafiyar Husna,dan inda sabo ya kamata ace kowa ya saba dan zai yi wuya ka ga Husna taje wuri ta ƙwana,ƙallafar gida gareta ko wuri taje ta rinƙa faɗin a tashi a tafi gida tun ta na ƙarama. 08105217201 Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 29* “Haba Husna gaskiya ba za ki ɗauki wannan ba saboda ya yi maki girma da yawa kin kuwa san nawa ake decoration balle ga harda wasu kyauta kuma kin ɗauka gaskiya A’a ba za’a yi haka ba.” Chairman ya faɗa dan dagaske yake abun da Husna ta ɗauka ya yi yawa duba da ba aiki take ba kuma ba ta sana’a. “Ni ma dai haka na gani gaskiya a chanza mata wani.” Hadiza Muhammad ta faɗa dan duk wanda zai faɗi gaskiya ya san wannan ai ya yi yawa. “A’a zan iya ba sai an chanza man ba.” Husna ta faɗa dan ita dai ta san za ta iya abin da ta faɗa. “Wallahi sai an chanza shi kin ji ma na rantse ni na ɗauki decoration ɗin ke sai ki kawo Dj ɗin dan gaskiya wannan aikin mazane babu yadda za’a yi mu bar maki ke kaɗai.” Sulluɓawa ya faɗa saboda yasan halin Husna idan ta kafe akan abu shi ya sa ya yi saurin rantsuwa dan ma ta saki tun da wuri. “Yauwa Sulluɓawa ka kyauta gaskiya abin da kayi.” Chairman ya faɗa,dan ya ji daɗin abin da Sulluɓawa ya yi har kullum ƴan group suna alfahari da Sulluɓawa dan bai jin ƙyashin kashe kuɗi. “Maganar kyautar da za’a ba amarya kuma mun yi magana da Zee Abba ta nuna ta na son bada gudunmawa to yanzu sai na ce ta siyo mana agogo sai aka a sanya hoton amaryar kawai mun gama wannan maganar Husna mun gode Allah yasa ka da alkhairi.” Ibrahim ya faɗa dan shi kanshi abin da yasa farko bai yi magana ba saboda ka da ace dan Husna ce shi ya sa zai ce a chanza amma yaji daɗin yadda komai yazo cikin sauƙi. “Amma gaskiya ban ji daɗin abin da ku kai man ba wallahi,ai ni nace zan iya ba sai a sanyaman ido ba a gani amma shi ne kai Sulluɓawa har da saurin rantsuwa…!” Husna ta faɗa dan gaskiya taso a barta ta yi decoration ɗin wurin dan da kanta taso yi. “Malama mun gama wannan maganar kuma shi kenan sai dai a tari gaba kawai Allah yasa ka ma kowa da alkhairi Allah ya ƙara haɗa kawunnan mu.” Muhammad Daura ya faɗa,dan kullum yana yaba ma yan group ɗin nan akan jajircewarsu akan duk abin da ya taso a cikin group ɗin ana haɗa ƙarfi da ƙarfi ayi maganin abin. “To zan kawo Dj kamar yadda ku ka buƙata amma wallahi sai na haɗo da mai hoto dan Allah kar ku ce A’a kun dai ji na rantse koh?” Husna ta faɗa dan gaskiya ta na son wannan partyn ya bada kala sosai kowa,duk wanda yazo ya ji daɗin wurin. “Babu matsala ki kawo muna godiya sosai.” Maryam da ta ji daɗin mai hoton da za’a kawo shi ya sa ta riga kowa amsawa dan gaskiya su sun manta da wani hoto ma sai yanzu da Husna ta yi maganar babu abin da zasu iya ce ma Husna sai dai addu’ar gamawa da iyayenta lafiya. “Yauwa kuma duk wanda yasan abin da zai kawo ba mai lalacewa bane muna buƙatar abin tun saura ƙwana ukku partyn.” Husna ta faɗi dan ba ta son a samu matsala ko kaɗan. “Eh gaskiya kin yi maganar da nake son yi yanzu dan Allah ayi ƙoƙarin yin abun cikin lokaci.” Chairman ya faɗa dan kowa yasan Chairman akwai zumuɗi akan abu,duk in za’a yi abu to fa Chairman ya rinƙa kiran wayar mutum kenan har sai an gama. “Matan za ka faɗamawa dan sune masu shirita.” Dabai ya faɗi cikin son tsokano matan ai kuwa ya ci nasara,dan gaba ɗaya suka taso ma shi. “Kai wa ya kai ka daɗewa ma ko tafiya za’a yi sai ka ɓatama mutane lokaci!” Zulaihat ta faɗa dan sun taɓa tafiya da Dabai aikuwa sun daɗe suna kiranshi. “Yauwa zulaihat faɗamasa dai!” Husna ta faɗa duk da bata cikin group ɗin lokacin da aka yi tafiyar. “Dillah Malama ware! Kin ma san lokacin da aka yi?” Dabai ya tambayi Husna. “Eh kin san lokacin Husna.” Zulaihat ta faɗa dan son tarema Husna. “Yauwa zulaihat faɗa masa dai ai shi ma ya san na san lokacin.” Husna ta faɗa ta na dariya. “Malama ki ma mutane shiru wai waya kasa dake ne ma?” Dabai ya tambayi Husna. “Malam ban da lokacin ka.” Husna ta faɗi. “Yauwa Husna sannu da ƙoƙari ba ri mu ware tunda an gama sai mu koma bacci.” Chairman ya faɗa dan bacci yake ji sosai. “To shi kenan Chairman namu na ƴan amana,wai ya jikin Fauzee Kabir?” Husna ta amsa ma Chairman. “Da sauƙi duk da dai tun shekaran jiya rabon da mu yi magana da ita amma zuwa anjima zan kirata.” Chairman ya faɗa yana sauka. “Allah ya bata lafiya.” Husna ta faɗa tare da komawa chan Main group ɗinsu na ƴan amana. 08105217201 Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 27* Bayan shigar Husna ɗakinta kai tsaye saman gado ta ƙwanta,wayarta ta jawo ta buɗe data dan gaskiya ta yi missing ɗin chat dan jiya gidan Hajiya Kaka ba ta hau ba babu network har ta yi bacci. Minti goma ta bada har sai da saƙonni suka gama shigowa,duk wanda ya mata magana ta rinƙa ba amsa har ta kammala da masu yi mata magana private, group ɗinsu na ƴan amana officials ta ga saƙonni da yawa,sanin ba’a fira a ciki sai idan magana mai muhimmanci ce yasa ta yi saurin shiga ciki. Tun da ga magana ta farko ta fara bi har taje ƙarshe,an yi magana akan yadda za’a gabatar da bikin Umma ɗaya daga cikin offials ɗin gidan,bikin saura ƙwana ashirin da sun so jiya idan aka haɗu a gidan gaisuwa sai su yi maganar amma hakan ba ta samu ba. Yanzu dai an aje magana akan anjima zasu yi maganar lokacin kowa na nan,dubawa ta yi ta ga ai kowa na online sai ta yi sallama a gidan. “Assalamu Alaikum ykk fatan kuna lafiya na ga tattaunawar da ku kayi gaskiya abin ya yi kyau sosai Allah ya ƙara haɗa kanmu,ni dai abin da zance akan haka na ce me zai hana ga bikin mu ma mu haɗa mata party na ƴan amana sai ta gayyato wasu daga cikin ƙawayenta amma ya ku ke gani?” Ko minti biyar da yin maganar ba’a yi ba sai ga Ibrahim ya yi magana. “Gaskiya kin yi magana mai kyau Husna idan aka yi hakan nasan za ta ji daɗi sosai.” “Yauwa Ibrahim ni ma haka nake tunani amma ba ri sauran su zo sai muji abin da zasu faɗa.” “Gaskiya ne mutunniyata gaskiya shawararki ta yi ina goyon bayanki ɗari bisa ɗari.” Dabai ya faɗa wanda tun da aka fara maganar sai yanzu ya sanya baki. “Yauwah ƙanwata hakan ma shawarace mai kyau.” Muhammad Daura ya faɗa. Nan fa duk wanda yazo sai ya yi na’am da wannan shawarar,ganin haka yasa Chairman ya ce,”to wani hanzari ba gudu ba yanzu ya ku ke ganin zamu ɓilloma al’amarin party ɗin yadda zai ƙayatar?” “Ni a ganina tunda mu tara ne offials mai zai hana kowa ya ɗauki nauyin wani abu sai mu ga abin da ya rage ko ya ku ka gani.” Husna ta faɗa da addu’ar Allah ya sanya shawararta ta samu karɓuwa. “Yauwa Husna hakan ma dai-dai ne.” Maryam ta faɗa. “Eh gaskiya ayi hakan kawai zai fi.” “To shi kenan yanzu waɗanne abubuwa ku ke ganin ana buƙata a wurin?” Dabai ya faɗa. “Ni abin da nake ganin muna buƙata sune;snacks, drink’s,ruwa,take away,dj, venue, decoration,kamar waɗannan sune manyan abubuwan da muke buƙata a yanzu!” Hadiza Muhammad ta faɗa,ita ma tunda aka fara maganar ba ta ce komai ba sai yanzu. “Yauwa Kakata kuma ya kamata ayi tags a ba kowa dan gudun idan an haɗu ka da ai ta tambayar juna wanene Wannan amma idan aka ba mutum da sunanshi sai ya liƙa tunda ƙarami za’a yi.” Husna ta faɗa. “Yauwa amarya ma ya kamata a bata kyautar wani abu wanda za ta rinƙa tunawa da ƴan amana idan ta kallah.” Chairman ya faɗa. “Gaskiya ne mutanena shawarwarin ku duk sun yi gaskiya kun yi ƙoƙari Allah ya bar zumunci.” Sulluɓawa ya faɗa wanda zuwanshi kenan gidan yanzu. “Kuma gaskiya muna so mu yi amfani da tables dan haka idan san samune venue ɗin da za’a samu ya kasance harabace inda zamu yi shi saboda mun fi jin daɗi,kuma ya kamata a yanka chake ko ya ku ka gani.” Husna ta faɗa,ta na gyara kwanciyarta. “Yauwa PRO ta mu gaskiya aikin ki na kyau.” Chairman ya yi maganar har cikin ranshi yana jin daɗin yadda Husna ke basu goyon baya da shawarwari masu kyau. “To yanzu sai kowa ya ɗauki abin da zai kawo,ko da yake ga Chairman nan ya faɗa ma kowa abin da zai kawo kawai.”Husna ta yi tambayar dan ganin kowa ya hallara. “A’a gaskiya wannan aikin na kine PRO raba mana kawai.” Chairman ya faɗa saboda yasan za ta yi abin da ya kamata. “A’a gaskiya ga manya nan su zaɓa mana dan ni dai ban iya komai ba nan.” Husna ta faɗa da iyakar gaskiyarta. “A’a gaskiya tun da ance ki zaɓa kawai ki zaɓa.” Maryam ta faɗa,nan fa kowa ya kama dole Husna ta raba ma kowa abin da zai kawo,shiru ta yi ta na tunanin yadda za ta iya irin wannan aikin. “Ke muke jira Hajiya.”Ibrahim ya faɗa saboda yasan yanzu ta na chan ta na zare idanuwa,nan fa kuma aka yi chaaa akan ta fito ta raba ta ba kowa nasa, ƙara tsurewa Husna ta yi. 08105217201 Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 28* “Kowa ya matso to zan raba.” Husna ta faɗa cikin ƙarfin hali,zuciyarta sai faman bugawa take dan ita dai ba ta san me za ta ba mutane ba. “Zaaaa…PRO ta mu fara kawai kowa na kallonki.” Sulluɓawa ya faɗa dan ya lura kamar ƙarfin haline take yi. “Zan fara ta kan Chairman.” Husna ta faɗa cikin tsoro dan har ga Allah ta rasa abin da za ta yi. “Muna saurarenki.” Iro ya faɗa yana dariya daga inda yake zaune. Bin Iro private Husna ta yi,”dan Allah Sweet Iro faɗaman yanda zanyi Allah kaina ya kulle” Husna ta faɗa kamar za ta yi kuka. “Haba daina ma ka da aji ai mana dariya,na yadda dake Sweet Husnata nasan za ki iya dan haka raba ma kowa na shi,kin ga yanzu idan na faɗa maki to ranar da irin haka ta faru ban kusa dake fa dan haka kiyi haƙuri kiyi abin da ya dace kin ji ko Tawan nasan za ki iya.” Iro ya faɗa cikin lallashi, shagwaɓewa Husna ta yi ta ce,”to zan yi man na yau kawai dan Allah.” “A’a Sweet Husnata nima ina so naga yanayin abin da za ki yi idan kinyi ba dai-dai ba zan gyara maki,muje ki cigaba kin ji ko Tawan.” jinjina kai Husna ta yi ta ɗan samu ƙwarin guiwa dan haka ta gyara kwanciyarta, group ta koma ta fara magana. “Chairman muna buƙatar motocin da zamu yi amfani dasu wurin mayar da mutane gida fatan babu matsala?” Tafa mata Muhammad Daura ya yi,sai ga su Sulluɓawa su ma suna tafa mata, Iro kuma jinjina ya yi mata. “Da gani dai ɗan achaɓa za ki hawo shi ya sa kike neman motar komawa gida.” Dabai ya faɗa cikin tsokana, emoji mai alamar murguɗa baki ta tura ma shi. “Gareka Sectary (Iro shine Sectary)” “Insha Allah Babu wata matsala za’a kawo.” Chairman ya faɗa yana dariya,dan bai yi tunanin abin da za ta ce ya kawo ba kenan. “Yauwa muna godiya, Sectary ko ba ka kusa?” “Ina jinki Hajiya faɗi.” Ibrahim ya faɗa. “Yauwa duk kajin da za’a ci a wurin mun ɗora maka wannan nauyin da zirga-zirgar abin hawa na karɓo kaya daga hannun waɗanda suka ɗauki nauyi.” “Komai zan yi shi yanda ake so insha Allah.” Iro ya faɗa yana dariya. “Gaskiyane PRO aikin ki na tafiya yadda ake so muna jinjina.” Wannan karon Sulluɓawa da Maryam suka faɗa a tare,har ana yi masu dariya. “Yauwa muna godiya,gareka Treasurer (Sulluɓawa)” “Ma’am faɗi na aikata abin da kike so Hajiya da girman kujerarki.” Sulluɓawa ya faɗa yana jiran jin mai za’a ce ya kawo. “Yauwa muna buƙatar Dj mai Mc daga gareka.” Husna ta faɗa cikin ranta ta na addu’ar Allah yasa ta yi abin da ya kamata. “Insha Allah kun samu Hajiya.” “Yauwa sai kai Shehu (Muhammad Daura take nufi).” “Ina jinki ƙanwar Shehu mekike so?” “Muna buƙatar ruwa katon goma a wurinka.” “Insha Allah zan kawo kamar yadda aka buƙata.”Muhammad Daura ya faɗa. “Yauwa mun gode Allah yasa ka da alkhairi.” “Gareka Welfare 1(Abdul Dabai)” “Ina jinki ƴar yarinya.” Dabai ya faɗa yana dariya dan yasan ya tsokanota dan bata san yana ce mata yarinya. “Mtssss…! Chan ma ga yarinya,muna buƙatar Venue a wurinka da tables ɗin zama.” “Angama yarinya za’a samu insha Allah.” “Yauwa mun gode yaro!” Husna ta faɗa dan ta san shi ma ya tsani ace ma shi yaro. “Yauwa gareki Welfare 2(Maryam)” “Ina jinki My Husna.” “Yauwa muna buƙatar lemu katon goma a wurinki.” “Insha Allah za’a samu.” Maryam ta faɗa. “Yauwa mun gode,kai nayi tuya zan manta da albasa ina Kakata?” “Gani kusa dake Jikata me kikeso a wurina?” “Yauwa My Kakus Cake muke so mai kyau a wurinki.” “Insha Allah za’a samu.” “Yauwa mun gode,wai ina Xulaihah ki fito mana ki karɓa.” “Gani nan kusa Husna ke nake saurare.” Zulaihat ta faɗa dan babu ma wanda ya lura da zuwanta sai yanzu,dan ita in dai ba abu mai muhimmanci ake ba baka cika ganinta ba. “Yauwa matso snacks muke so a wurinki,samosa hamsin, spring grill hamsin,daugnut hamsin.” “Insha Allah zan kawo Allah ya shige mana gaba.” “Ameen nagode,ina Mustapha Madina gareka.” “Gani Hajiya Husna.” Mustapha ya faɗa dan lokacin da yazo ana magana shi ya sa bai ce komai ba ya tsaya yana saurare. “Yauwa kai muna son kai mana Tags guda talatin da biyar dan duka members ɗin group ɗin iyakarmu kenan sai ka haɗo mana da ledar take away guda ɗari,sai tishu da robali fatan babu matsala.” Husna ta faɗa gabanta na faɗuwa, Allah dai yasa ta raba dai-dai. “Babu matsala Hajiya insha Allah zan kawo.” Mustapha Madina ya faɗa yana jin daɗin ba’a ba shi abubuwa masu wahala ba. “Yauwa mun gode yanzu sai ni kuma,insha Allah zan ɗauki nauyin decoration da kyautar da za’a ba amarya.” Lokaci guda kowa ya zaro idanuwa saboda jin uban aikin da Husna ta ɗaukar ma kanta. 08105217201 Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 31* “Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un Fauzee!! Hasbunallahu wai dagaske ne?” Kawai sai ta fashe da wani matsanancin kuka,wanda har sai da saurin ya kai kunnen Mama da ke ɗakinta zaune,ji ta yi kamar kunnuwanta na jiyo mata kukan Husna ba ta tabbatar ba sai da ta ƙara saurarawa lokacin ta tabbatar. Cikin sauri Mama ta iso ɗakin,halin da ta iske Husna ciki shi ya sanya gabanta ya yi wata irin faɗuwa,cikin rawar jiki Mama ta riƙe kafaɗun Husna ta juyo da ita su na fuskantar juna. “Lafiya Husna meke faruwa?” Sautin muryar Mama ne ya daki dodon kunnuwan Husna, faɗawa Husna ta yi a jikin Mama ta saki wani wahalallan kuka. “Dan Allah Husna ki natsu ki faɗaman meke faruwa!” Mama ta furta cikin sanyin murya,amma ina Husna ba ta san ta na yi ba,kuka Husna ke yi mai ban tausayi cikin kuka ta ke faɗar. “Fauzee Kabir innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!!” Abin da kawai take mai-maita wa kenan a bakinta,lallashinta Mama ke yi amma kamar ƙara zugata take yi,sun ɗauki lokaci mai tsawo a haka. Ɗagowa Husna ta yi ta kalli Mama ta ce,”Mama Fauzee Kabir ta rasu Mama!kai innalillahi wa’inna ilaihirraji’un Mama babu Fauzee shi kenan ta tafi ta barmu Mama!!” Ta faɗa tare da sake durƙushewa ƙasa ta na kuka,ita kanta Mama sai da bugun zuciyarta ya chanza dan kowa ya san irin amintar da ke tsakanin Husna da Fauzee Kabir. Kuka Husna ke yi kamar ranta zai fita, Mama ta ka sa rarrashinta saboda ita kanta mutuwar ta daketa,dole Husna ta yi kuka saboda akwai shaƙuwa mai ƙarfi a tsakaninsu. “Mama dagaske Fauzee ta mutu?” Husna ta tsurama Mama idanuwa tamkar a fuskar Maman za ta ga amsar tambayarta. “Husna ke wa ya faɗa maki Fauzee ta rasu?” Mama ta tambayi Husna cikin sanyin murya. “Mama…a group… Umma ta sanar kuma kin…san ƴar uwarsu Fauzee ce ba ri ma ki gani.” Husna ta faɗa tare da jawo wayarta da ta yi ratsa-ratsa, kunna wayar ta yi sai da ta jira ta gama loading sannan ta shiga WhatsApp, group ɗinsu ta shiga nan fa ta ƙara tabbatarwa dan mutane sai kuka ake. Miƙa ma Mama wayar ta yi ta ce,”ki duba Mama ki gani dagaske ne gobe za’a yi jana’izarta da safe… Mama shi kenan mun rabu ni da Fauzee… innalillahi wa’inna ilaihirraji’un Mama!!” Husna ta ida maganar ta na sakin wani irin kuka mai tsuma zuciya,babu abin da ke mata yawo akai irin yadda suka yi rayuwa ita da Fauzee,amma yanzu duk ya zama tarihi kenan,abin da yafi ɗaure mata kai ko shekaran jiya sai da ta kira Fauzee amma ba ta ɗaga ba,ita kuma sai ba ta sake kira ba ashe shi kenan babu sauran magana a tsakaninsu. “Husna kiyi haƙuri bari na kira wayar Mamanta dan mu tabbatar.” Mama na maganar ta na latsa wayarta,cikin Sa’a ta shiga bugu ɗaya ana biyun aka ɗaga,daga yanda ta ji muryar Maman Fauzee jikin Mama ya yi sanyi. “Assalamu Alaikum ina wuni Maman Husna?” Maman Fauzee ta faɗa cikin muryarta da ko fita sosai ba ta yi. “Wa’alaikissalam Maman Fauzee yanzu Husna ke faɗaman wani al’amari da babu daɗin ji.” Maman Husna ta faɗa cikin sanyin murya. Murmushin ƙarfin hali Maman Fauzee ta yi ta ce,”to ya za’a yi da al’amarin Ubangiji ai sai dai mu yi godiya a gareshi amma Fauzee ta amsa kiran mahaliccinta gata nan kwance a gaba amma babu rai!” Maman Fauzee ta ƙarasa maganar hawaye na zubowa a saman fuskarta,hannu ta sanya ta share ta cigaba da magana. “Ina ganin abin tamkar mafarki Maman Husna amma nasan gaskene bazan iya chanza ƙaddarar Allah ba.” Mama ta ja numfashi cikin ƙarfin hali ta ce,”hakane Maman Fauzee kiyi haƙuri addu’a kawai Fauzee ke buƙata a yanzu, Allah yasa kwanciya hutuce agareta!” “Ameen Maman Husna nagode kwarai ga mutane chan sun zo bari naje wurinsu.” Maman Fauzee ta faɗa tare da kashe wayarta. Jikin Husna ya yi sanyi sosai,ta ƙara tabbatarwa duniya ba wurin zama ba ce,yanzu shi kenan babu Fauzee har ta zama tarihi a cikin duniya kenan lalle rayuwa abin tsoroce. Mama ta daɗe ta na lallashin Husna,har sai da ta ga zuciyarta ta ɗan yi sanyi,ruwa mai sanyi Mama ta je ta kawo ma Husna ta sha, ƙara yi mata nasiha Mama ta yi da nuna mata muhimmancin haƙuri da babu wani abu da Fauzee ke buƙata sai addu’a. Ganin Husna ta ɗan samu natsuwa yasa Mama ta koma ɗakinta,bayan fitar Mama shiru Husna ta yi ta na tuna rayuwarsu ita da Fauzee. Fauzee ita ce lokacin da aka sanyata a gidan ƴan amana ta fara yi mata barka da zuwa gidan tun daga lokacin suka saba sosai. Lumshe idanuwanta ta yi kamar a mafarki ta fara tariyar rayuwarsu da Fauzee, ɗaya bayan ɗaya ta fara tuna rayuwarsu. 08105217201 Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 30* Fira Husna da Abdul Mai kasuwa ke yi sosai sai tsokanarta yake ita kuma ta na biye ma shi. Ko kaɗan ba ta san Iro na online ɗin ba saboda ya sha yi mata magana akan Abdul. “Hajiya wannan firar ta isa haka nan ki sauka!” Saƙon Iro ne da ya shigo mata ta private yanzu,murmushi ta yi dan ta gane abin da yasa ya ce mata haka. “Ƴallabai ba ka ga fira nake da mutane ba?” Ta faɗa ta na danne dariyar da ke taso mata. “Fira ko zance?” Ibrahim ya faɗa cikin kishi,dan ya tsani ya ga ta na magana da Abdul mai kasuwa saboda tsohon saurin Husna ne. “Fira dai ƴallabai.” Husna ta ba shi amsa ta na dariya. “To na ce a daina ta dan gaskiya bazan ɗauka ba!!” Ya faɗa cikin tsantsan kishi. “To ƴallabai yanzu me kake so ayi?” Husna ta faɗa saboda ta ga ranshi ya ɓaci. “Ki sauka haka nan!” Ya faɗa cikin ba da umarni. “Kai kuma sai ka tsaya amma ni ka koreni?” Husna ta faɗa cikin jinjina ƙarfin hali irin na Iro. “Ni na faɗa maki?” Iro ya tambayi Husna. Kafin ta ba shi amsa sai ta ga kiranshi ya shigo cikin ƙaramar wayarta, ɗauka ta yi cikin dariya ta ce,”kai Sweet Iro kishinka ya yi yawa.” “Babu wani kishi da ya yi yawa.” Ibrahim ya faɗa yana dariya shi ma. “Yanzu in ba kishi ba meye wannan muna cikin fira kazo ka hana?” Husna ta faɗa ta na murmushi. “Dan kin raina ni ma a gabana kike fira da shi?” Ibrahim ya faɗa da iyakar gaskiyarshi. “Babu wani raini Sweet Iro ya man magana ta ya zan yi shiru na kyaleshi?” “Ko ba ki shiru ba amma kuna gaisawa ai sai ki kyaleshi,ko da yake tsohuwar zuma ta motsa ai!” Iro ya ida maganar cikin kishi. “Aikuwa dai ka san da tsohuwar zuma ake magani!” Husna ta faɗa cikin jin haushi saboda ba tun yau ba take faɗa ma shi ya daina yi mata haka ba. “Ta ya zan manta Hajiya ai shi ne ma dalilin da yasa na tambaya.” Ibrahim ya faɗa yana dariya. “Hakan da kayi ya yi kyau haka ake so ai!” Husna na faɗin haka ta kashe wayarta,kiranta Ibrahim ya yi amma ta ƙi ɗagawa,wasa-wasa sai da ya yi mata kira goma lokacin ta ɗauka ta na kumbura fuska. “Lafiya kake takuraman?” Ta faɗa cikin ɗaure fuska kamar yana gabanta. “Ke dan ki raina ni shi ne za ki kasheman waya kuma ina kiranki amma ki ƙi ɗagaman kira!” Shi ma ya faɗa cikin jin haushi. “Amma so nawa ina gayamaka ka daina yi man maganar Abdul?” Husna ta faɗi kamar za ta yi kuka. “Kina tunanin zan daina bayan na ga yanzu sai shishshige maki ya ke yi!!” Muryarshi kawai za ta tabbatar maka da tsantsan kishin dake ranshi. “Ni dai idan ya yi man magana zan ma amsa shi.” Husna ta faɗa da iyakar gaskiyarta dan wallahi in dai Abdul ya mata magana ba za ta yi shiru ba,dan wannan ma ai wulaƙanci ne. “Zan yi maganin abun da kaina,ki turoman lambar Baba Abu zan yi magana da shi akai kuɗin nan kawai yanzu bayan sallar an sanya bikin!!” Ibrahim ya faɗa cikin jin haushi. “Kai Sweet Iro tun yanzu? Gaskiya a bari sai bayan sallar an kawo kuɗin.” Husna ta faɗi kamar za ta yi kuka. “Saboda ba ki sona koh? Kallonki kawai nake yarinya duk abin da kike yi yanzu,inda Abdul me ai da ba ki ce ba yanzu ba!” Yana faɗin haka ya kashe wayarshi gaba ɗaya,ko da Husna ta kira sai ta ji ta switch off dole ta haƙura,shiru ta yi ta na tunani ganin babu mafita yasa ta nufi ɗakin Mama. Zaune ta tadda Mama ta na yankan farce,shiga ta yi cikin ɗakin ta amshi abin yankan ta zauna ta cigaba da yanke ma Mama farcen, nan take sanar da Mama yadda suka yi da Iro. Faɗa Mama ta rinƙa yi ma ta akan abin da ta aikata. Haƙuri ta ba Mama akan hakan hakan ba za ta ƙara faruwa ba,kuma za ta bashi haƙuri. Sai da ta kammala ma Mama gyaran sannan ta koma ɗakinta,wayarta ta jawo ta sake kiran wayarshi har lokacin kashe take dan haka sai kawai ta tura ma shi text na ban haƙuri tare da lambar Baba Abu. Tun lokacin da Husna ta sauka daga online ba ta sake hawa ba sai dare wurin ƙarfe takwas,har lokacin kuma basu yi waya da Ibrahim ba. Ta na hawa online har ta tafi inbox ɗin shi dan ta yi ma shi magana sai ta ga ana salati cikin group ɗin ƴan amana,cikin sauri ta shiga group ɗin saƙonnin ta fara dubawa gabanta na faɗuwa,ka sa jurewa ta yi sai kawai ta yi ƙasa gaba ɗaya abin da ta yi tozali da shine yasa ta sakin wayarta ƙasa ta fashe. 08105217201 Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 32* TUNA BAYA A ranar wata talata da misalin ƙarfe tara na dare, Husna ta hau WhatsApp sai ta ga wata ƙawarta Umma ta sanyata a wani group mai suna ƴan amana,shiga group ɗin ta yi ta yi sallama. “Assalamu Alaikum yakuke fatan kuna lafiya,sunana Asma’u amma an fi kirana da Husna fatan zan samu karɓuwa a gareku.” Babu daɗewa sai ga wata mai suna Fauzee ta amsa mata. “Oyoyo Husna mun ji daɗin zuwanki gidanmu insha Allah za ki samu karɓuwa.” Murmushi Husna ta yi dan ta ji daɗin yadda aka karɓeta. “Masha Allah nima naji daɗin zuwana tun da ga shi har na samu ƙawa.” “Haba ƙawata ai ba ki kaini jin daɗi ba duk gidan nan ban da Ƙawa amma yanzu ga shi Allah ya kawoman ke gaskiya naji daɗi dole yau a zo a ɗan yi celebration.” Fauzee ta faɗa cikin alamun jin daɗi,dan lokaci ɗaya ta ji Husna ta ƙwanta mata a rai,dan haka ta cigaba da magana. “Ƙawata dan Allah turo hotonki na gani nima ba ri na turo maki nawa.” Fauzee Kabir ta faɗa ta na ƙoƙarin shiga gallery ɗin wayarta. “To shi kenan nima ga shi nan zan turo maki ƙawata.” Husna ta faɗa ta na mamakin yadda lokaci ɗaya sabo ke neman shiga tsakaninsu,dan ita ko group ba ta taɓa shiga ba wannan shi ne shigarta group na farko a duniyar WhatsApp. Hoton ta tura haɗe da faɗin,”ƙawata ga hoton nan.” Bayan minti biyu da tura hoton sai ga Fauzee ma ta turo na ta, buɗewa Husna ta yi a fili ta furta masha Allah saboda ba ƙarya Fauzee ta yi kyau. “Masha Allah ƙawata irin wannan kyan gaskiya na samu kyakkyawar ƙawa!” Fauzee Kabir ta faɗa cikin jin daɗi dan dagaske ba ƙarya Husna ta yi mata kyau duk da kasancewarta baƙa amma baƙin mai kyau ne. “Kai ƙawata kin sanya naji kunya ina kyan a nan?” Husna ta faɗa ta na murmushi kamar Fauzee Kabir na a gabanta. “Haba ƙawata da gaske kin yi kyau.” Fauzee ta faɗa cikin tabbatar ma da Husna ta yi kyau. “To nagode ƙawata amma dai kin fi ni kyau.” Husna ta faɗa da iyakar gaskiyarta. “Haba ƙawata ta ina nafi ki kyan gaskiya ke ba ki ma san kyau ba.” Fauzee Kabir ta faɗa ta na dariya saboda so take firarsu ta yi tsayi. “Haba ƙawata ga ma zagina ke fa farace kuma kin san farar mace alkyabbar mata dan kowa ya san na kin fini kyau.” Husna ta faɗa saboda ita dai ta san Fauzee Kabir ta fita kyau sosai. “Malama kin fa dameta da magana ki barta ta huta mana,baƙuwa sannu da zuwa muna maki barka da kasancewar ki a gidan ƴan amana.” Wani ya yi maganar wanda ta ga sunanshi ya sanya Ibrahim Muhammad. “Kai kuma ina ruwanka Iroro daga zuwanka za ka wani sako mana baki!” Fauzee Kabir ta faɗa cikin tsokana. “Nagode kwarai nima naji daɗin kasancewata a cikinku.” Husna ta faɗa ta na murmushi saboda har ga Allah ta lura mutanen gidan su na da kirki. “Ke zan sanya ayi maki ɗaukar amarya idan ba ki kiyayeni ba, baƙuwa bakomi mu ma mun ji daɗi sai dai kiyayi wannan yarinyar dan bata girmama manyanta shi ya sa zamu tillata ta taga dan haka ka da ki biye mata.” Ibrahim ya faɗa cikin son tunzura Fauzee Kabir. “Ƙawata kyaleshi ka da ki biye abin da yake faɗa kin ga abin da nake gayamaki ƴan gidan nan sun takuraman sai yanzu da ki kazo gaskiya naji daɗi ni ma na samu mai tare man ko Darling?” Fauzee ta faɗa cikin alamun a tausayamata. “Kar ki damu My Fauzee daga yau zan rinƙa tare maki kin ji koh.” Husna ta faɗa ta na dariyar dramar Fauzee da Ibrahim. “Kar ki yadda da abin da take faɗa Sweet Husna.” Ibrahim ya faɗa dan ya tunzura Fauzee. “Danƙari! Wai sweet jama’a kun ji wani nai man suna koh? My Husna kar ki biyema duk abin da zai faɗi a hankali za ki gane irin takurar da ake man.” Fauzee Kabir ta faɗa cikin sigar zama kalar ban tausayi. “Kalleta kamar wata salaha!” Ibrahim ya faɗa cikin dariya. “Gaskiya ka fara takurama Ƙawata ban son haka!” Husna ta faɗa ma Ibrahim ta na ɗaure fuska. “Ni ka ga tafiya ta sai dai kayi da wata ba dai ni ba!” Fauzee Kabir ta faɗa tare da sauka daga online. “Sweet Husna kar ki shiga cikin wannan maganar ki kyaleta.” Ibrahim ya faɗa yana dariya. “Ni dai gaskiya ban ji daɗi ba yanzu ka ga ka korar man ƙawa.” Husna ta faɗa saboda da gasken ba ta ji daɗin tafiyar Fauzee ba. “Kyale wannan yarinyar za ta dawone ai.” Ibrahim ya faɗa yana dariya saboda ganin yadda Husna ta damu. “Ni ma tafiya zan yi sai da safe bacci nake ji.” Husna ta faɗa saboda sai ta ji duk group ɗin ya isheta. “Saboda tafiyar waccan yarinyar shi ne za ki tafi?” Ibrahim ya tambayi Husna saboda ya ga da gaske tafiyar za ta yi. “A’a ba saboda haka bane bacci nake ji sai da safe.” Husna na faɗin haka ko amsar Ibrahim ba ta tsaya jira ba ta kashe data,har ta kwanta kuma sai ta ji babu daɗi yanda ko sallama basu yi da Fauzee ba,da wannan tunanin bacci ya yi gaba da ita. 08105217201 Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 33* Washe gari gaba ɗaya Husna ba ta samu zama ba dan haka sai ba ta samu hawa WhatsApp ba,da marece wurin ƙarfe huɗu sai ga kira ya shigo wayarta,ko da ta duba baƙuwar lamba ta gani kamar ba za ta ɗaga ba sai kuma ta ɗaga. “Ko dai kina tsoron a saceki ne?” Wata murya mai cike da barkwanci ta jiyo a cikin kunnenta,ɗan jim ta yi domin ta na so ta gane mai magana, jin ta yi shiru yasa daga chan bangaren aka ƙa ra sakin dariya,”Oh Ni! Fauzee ashe haka ƙawata take da tsoro,idan kina haka ta y zan yi tunanin za ki rinƙa tareman faɗa idan na jawo?” Sai yanzu Husna ta gane mai magana dan haka ta yi murmushi tare da ƙara dafe wayar a kunnenta,”ba tsoro naji ba Ƙawata na dai tsaya ne dan na gane mai magana amma ba dan wani abu ba.” “Kai Ƙawata ke dai kawai kin ji tsorone kar ki wani damu ni ce,yakike yau na ga ba ki hau WhatsApp ba shi ne nayi tunanin na kira ki naji ko lafiya Allah yasa dai ban takura maki ba?” Fauzee Kabir ta faɗa ta na murmushi dan ita Allah ya yi ta irin mutanen nan ne masu fara’a. “Allah sarki Ƙawata lafiya lau yau dai na ɗan yi busy ne shi yasa ki ka ji shiru da ma zuwa anjima nake tunanin hawa.” “Allah sarki sannu ya kike?” Fauzee Kabir ta faɗa cikin nuna kulawa, saƙonta kuwa yaje inda aka tura shi dan Husna ba ƙaramin daɗi ta ji ba da kiran da Fauzee ta yi mata,dan haka ta ƙawata fuskarta da murmushi tamkar suna ganin juna. “Lafiya lau Ƙawata fatan ke ma kina lafiya? gaskiya bazan iya ɓoye maki ba naji daɗin kiran nan da ki kayi man sosai wallahi nagode Allah ya bar zumunci.” “Haba…haba! meye abin godiyar dan Allah ki ma yi shiru…yanzu kenan idan da ni ce ban hau ba ke baza ki iya kirana ba?” Fauzee Kabir ta faɗa ta na ɗan ɗaga sauti, girgiza kai Husna ta yi kamar ta na gaban Fauzee ta ce,”haba ƙawata da gudu zan kira ki kuwa.” “Yauwa yanzu naji batu mai daɗi Ƙawata.” Fauzee Kabir ta faɗa ta na dariya,ita ma Husna murmushi ta yi ta gyara zaman ta dan ta ji daɗi. “Ai ni na manta ma fushi nake da ke shi ne jiya kika gudu muna cikin magana.” “Ke wallahi bacci naji sosai jiyan shi ne kawai dalili amma kiyi haƙuri.” Fauzee ta faɗa cikin sanyin murya. “Nayi tunanin saboda zuwan Ibrahim kika gudu!” Husna ta faɗa dan ita abun da ta yi tunani kenan. “Tab! Wai kina nufin Iro lalle ai wallahi ba dan shi na tafi ba,ke Iro fa bai da matsala dan kin ji ina faɗin ya takuraman?wasa nake ma shi yana da hankali kuma ya na da daɗin zama sosai ke ma nasan nan gaba za ki gane haka.” Fauzee ta faɗa ta na dariya dan ita da gaske dariya Husna ta bata da ta ce saboda Iro ta gudu. “Allah sarki nima na lura yana da kirki.” Husna ta faɗa cikin sanyin murya. “Eh gaskiya yana da hankali dan ni kin ga abokin saurayina ne,amma gaskiya muna wasa da shi sosai bai da matsala wallahi ke ma nasan za kiji daɗin zama da shi sosai.” Fauzee Kabir ta faɗa ta na murmushi dan har lokacin dariyar ba ta saketa ba. “Ai da ma za ki ga wani ya iya mu’amala da mutane.” Husna ta faɗa dan ba ta san komai game da group ɗin ba,tun da ita jiyane aka sanyata. “Eh hakane gaskiya to shi ma bai da matsala, Husna wane gari kike?” Fauzee ta juya akalar maganar ta zuwa ga tambaya. “Katsina nake ke fa?” Husna ta faɗa a taƙaice. “Wayyyoooooo Ƙawata mun samu ban-banci ni Kaduna nake,gaskiya naso ace Kaduna kike da cikin satin nan sai mun haɗu,amma kin ga yawancin ƴan group ɗin duk ƴan nan Katsina ne,kun rinƙa haɗuwa ana zumunci!” “Da ma ana haɗuwa ne yan group ɗin?” Husna ta tambayi Fauzee saboda ita dai ba ta san ana haka ba. “Sosaima duk sallah ƴan group ɗin na haɗa partyn sallah haka kuma idan wani abu ya samu wani suna zuwa!” Fauzee ta faɗi cikin farin ciki,mamaki sosai Husna ta rinƙa yi,ganin Fauzee ta ɗan damu akan rashin kasancewar su gari ɗaya yasa Husna jin ƙaunarta a cikin ranta. “Kai ban so haka ba nima naso ace Kadunar nake amma bakomi wata rana sai ki ga mun haɗu.” Cikin kulawa Husna ta faɗi dan ta lura yanayin Fauzee ya ɗan chanza. “Hakane kuma ai insha Allah wata rana zamu haɗu,ke ka da na cika ki da surutu da yawa,amma dan Allah da kin gama abin da kike ki hau saboda ban san na sake hawa na ga ke ba ki hau ba sai anjima.” Fauzee ta faɗa ta na dariya saboda ta ji daɗin firar da suka yi da Husna “To shi kenan insha Allah da na ida zan hau sai anjima.” Husna na faɗin haka ta kashe wayarta,shiru ta yi ta na mamakin yadda har sabo ya fara shiga tsakaninsu. 08105217201 Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 34* Husna na katse wayar mamakin kirkin Fauzee take ta yi daga haɗuwa group amma kalli kalar mutuncin da ta yi mata,gaskiyar Umma (wadda ta sanyata a group ɗin)da ta ce duk masu hankali ta sanya a group ɗinta. Ɗakin Mama Husna ta shiga,zaune ta iske Mama na linkin kayan wanki,gefen Mama ta samu wuri ta zauna,wasu kayan ta ɗauka ta fara linkewa ita ma. Ɗagowa ta yi ta ga Mama sai kallonta ta ke yi, murmushi Husna ta yi dan ganin yadda Mama ke bin ta da kallo. “Kai Mama kamar na chanza maki sai kallona kike!” Husna ta faɗa tare da ɗaukar kayan da Mama ta linke,wadrop ta buɗe ta fara ƙoƙarin sanya kayan ciki. “Gani na yi kin shigo sai murmushi kike ke ɗaya ko dai ta samu ne? Mama ta faɗa ba tare da ta kalli inda Husna ta ke ba,rigar da ta linke ta aje a gefenta,wata ta ɗauka ta na linkewa. “Mama wallahi wani mutunci aka yi man wanda nake ta mamakinshi.” Husna ta faɗa bayan ta saka kayan da ta ɗauka cikin wadrop. “Mutuncin kuma Husna wa ya yi maki toh?” Juyowa Mama ta yi ta na kallon Husna tare da tsayawa da linkin kallabin da ke hannunta. “Mama shekaran jiya ba na faɗa maki mun haɗu da Umma a gidan Kadarko ba?” Husna ta faɗa ita ma tare da maido hankalinta gaba ɗaya akan Mama. Jinjina kai Mama ta yi ta ce,”eh kin faɗa meyafaru kuma.” “To ranar ne take faɗaman za ta sanyani a group ɗinta mai suna ƴan amana,da har na ce mata a’a sai ta ce ai group ɗin duk masu hankali ne a ciki,to jiya da daddare bayan naje zan kwanta sai na hau WhatsApp,ina dubawa kuwa sai na ga ta sanyani a group ɗin,sai ga shi kuwa na tabbatar da maganarta wallahi Mama mutanen na da kirki sosai.” Husna ta faɗa ta na zama gefen gadon Mama,sai ya kasance su na fuskantar juna ita da Mama. “Kai Husna cikin daren jiya kaɗai har kin tabbatar da su na da kirki?” Mama ta faɗi ta na cigaba da linke kayanta. “Allah Mama su na da kirki sosai kin san me yasa na ce haka Mama?” Husna ta faɗa ta na kishingiɗawa jikin katakon gado, fuskarta ɗauke da murmushi wanda kallo ɗaya za ka yi mata kasan ta na cikin farin ciki. “A’a sai kin faɗa Husna ina saurarenki.” Mama ta faɗa ita ma fuskarta da murmushin saboda ganin ɗiyarta mace ƙwalli ɗaya tal(Husna ita kaɗai ce mace a gidansu sauran duk mazane) a duniya ta na cikin farin ciki. “Mama ba ri na faɗamaki dan ki tabbatar ke ma.” Husna ta faɗa ta na dariya ganin yadda Mama ke murmushi ita ma. “Ina jinki.” Mama ta faɗi har lokacin akwai murmushi a fuskarta. “Mama jiya bayan na ga group ɗin sai na shiga nayi sallama,da yin sallamata ba’a ɗauki wani tsawon lokaci ba sai ga wata Fauzee Kabir ta amsa man,nan muka ɗan yi magana da ita,ta na nunaman yadda ta ji daɗin zuwana a gidan,wai ta samu ƙawa saboda gidan ba ta da Ƙawa,kin san wani abu Mama?” Husna ta faɗa ta na kallon Mama. Girgiza kai Mama ta yi fuskarta cike da murmushi,dan ta ƙosa Husna ta ida faɗa mata labarin. “Yauwa Mama yanzu kuwa zan faɗa maku.” Husna ta faɗa tare da tashi daga kishingiɗawar da ta yi ta koma zaune,ba tare da ta jira Mama ta yi magana ba ta cigaba da maganarta. “Muna cikin magana da Fauzee Kabir ta na faɗaman irin yadda ta ji daɗin zuwana gidan dan duk takura mata ake babu mai tare mata,sai kuwa ga wani shi kuma sunanshi Ibrahim Muhammad, Mama ya na zuwa shi ma sai ya fara nuna yadda yaji daɗin zuwana gidan,amma Mama kin ga yadda yake jan Fauzee wasa har sai da ta gudu,gaskiya Mama su na da kirki sosai jiya kaɗai Mama amma na ga ya ba da ƙoƙarinsu.” Husna ta ida faɗar maganar fuskarta ɗauke da murmushi,zuru ta yi ma Mama ta na jiran jin abin da Mamar za ta faɗa. Gyara zamanta Mama ta yi ta na kallon Husna,nisawa ta yi sannan ta ce,”Husna ban hana ki mu’amala da mutane ba amma Husna ki rinƙa kiyayewa kin san zamani ya chanza yanzu ba’a yadda da mutane sosai.” “Hakane Mama kin san ina bakin ƙoƙarina wurin kiyayewa amma insha Allah zan ƙara, ɗazun Fauzee Kabir ta kirani wai ta ga duk yau ban hau online ba.” Husna ta ƙarasa maganar fara’ar da ke fuskarta na raguwa. Ganin haka yasa Mama sakin murmushi dan ta kwantar ma Husna da hankali sai ta ce,”Allah sarki gaskiya ta na da kirki Allah ya yi mana jagora Allah ya tsaremanaku a duk inda ku ke,ku ma sai ku ƙara tsare mutuncin kanku.” Mama na faɗar haka ta cigaba da linkin kayanta,ganin kamar Husna ta shiga damuwa yasa Mama ta rinƙa jan ta da fira har sai da ta ga ta saki jikinta sun cigaba da aikinsu. Su na aikin suna fira har suka ida,sai lokacin Husna ta yi ma Mama sallama ta koma ɗakinta 08105217201 Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 36* “Na amince da me?” Husna ta faɗa cikin sauri dan sai yanzu ta gane katoɓarar da ta yi tun farko na amincewa da abin da zai faɗa. Dariya Ibrahim ya rinƙa yi har da ƙyaƙyatawa dan ya lura da Husna ta ji tsoro “Meye na saurin magana Hajiya ki bari na faɗa mana dan kin san dai ba ki isa ba dai ki ƙi amincewa!” Girgiza kai kawai Husna ta yi cikin shan ƙamshi irin kar ya raina ta ɗin nan ta ce,”ina jinka faɗi!” “Yauwa jaruma haka nake son ji.” Ya faɗa dan ya lura ƙarfin haline kawai yasa ta maganar. “Faɗi kawai Malam ina son kwantawa dare ya yi.” Husna ta faɗa tare da ɗaure fuska tamkar a gabanshi take. “Kwantar da hankalinki ba wani abu bane kawai so nake daga yau ki rinƙa kirana da Sweet Ibrahim kin ga ni ma da Sweet nake kiranki wannan shi ne kawai sharaɗin!” Ibrahim ya faɗa yana dariya dan yasan ya gama wana ta,shi kanshi ya rasa dalilin da yasa yake so ta rinƙa kiranshi da haka,duk da jiyane ya santa amma hakanan yake jin ta har cikin ranshi. “Kin yi shiru Malama ke nake saurare kin dai san ba ki isa ki ƙi amincewa ba dan haka ko a gaban waye haka za ki rinƙa kirana da shi.” Ya sake faɗa ganin ta yi shiru duk da kuma ya ga ta duba maganar ta shi. “To shi kenan na amince amma kai ma kar ka sake takurama Ƙawata.” Husna ta faɗa ta na murmushi dan ba ta yi tunanin abin da zai faɗa ba kenan. “To kin ga idan ki kayi haka to kin wanke ƙawarki.” “Ba damuwa na amince bacci nake ji zan kwanta.” Husna ta faɗa ta na hamma dan da gasken baccin take ji,dan ita ba ma’abociyar chat ɗin tsakar dare ba ce duk rintsi ba ta wuce ƙarfe sha ɗaya amma yanzu har sha biyu ta yi. “To shi kenan ki yi bacci mai daɗi.” Ibrahim ya faɗa cikin jin daɗin firar da suka yi,ji yake kamar sun shekara da sanin juna. “To nagode sai da safe.” Husna na faɗar haka ta kashe datarta ta kwanta,babu daɗewa bacci ya yi awon gaba da ita. Tun da Husna ta kwanta ko sau ɗaya ba ta farka daga baccin ba,duk da kasancewar ta na yawan tashi shan ruwa cikin dare amma yau ko sau ɗaya ba ta tashi ba,hakan ya farune har da gajiyar da ta yi. Chan cikin bacci ta ji wayarta da ta sanya ƙarƙashin fillo ta na vibration,ko idanuwanta ba ta buɗe ba ta shiga laluben wayar,cikin sa’a kuwa ta jawota ko duba sunan waye ba ta yi ba ta kanga wayar a kunne. “Hajiya ki tashi ki yi sallah ka da lokacinta ya wuce kina ta bacci.” Wata baƙuwar murya ta ji ta faɗa,dan ita dai a iya saninta ba ta san wani mai irin wannan muryar ba. “Hajiya ko baccin bai isheki ba?” Aka sake faɗa daga chan bangaren. Cikin muryar bacci Husna ta ce,”wacce sallah kuma yanzu?” “Sallar Asuba ko kin yi?” Janye wayar Husna ta yi daga kunnenta dan so take ta gane wake magana,ita dai babu wanda ya taɓa kiranta da asuba bare ta yi tunanin ko shi ne,ganin lambace babu suna ya sanya ta maida wayar a kunne. “To shi kenan na tashi yanzu zan yi.” Ta faɗa ta na ƙoƙarin tashi daga kwancen da take. “Yauwa ya kamata dai nima ga liman nan zai ta da Sallah sai anjima.” Yana faɗin haka ya kashe wayarshi. Tsurama wayar Husna idanuwa ta yi cikin ranta ta na mamakin waye wannan ya kirata,dan ita har a lokacin ba ta gane ko waye ba. Kallon agogon da ke manne a bangon ɗakinta ta yi,ganin lokacin sallah ya yi yasa ta miƙewa ta nufi toilet,cikin ranta ta na godema ko ma waye ya tada ta dan tasan da ƙila yau sai ta makara wurin yin sallah,ko kuma idan masallacin ƙofar gidansu an tada sallar ta ji. Cikin ranta ta na ƙara jinjina irin baccin da ta yi yau,dan ita zai yi wuya ta kwanta ba ta farka ba. Da waɗannan tunane-tunanen ta yi alwallah ta fito,abin sallah ta shimfiɗa ta kabbara sallah. 08105217201 Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 35* Da misalin ƙarfe goma na dare Husna ta gama duk wani abu da ya zame mata al’ada,sai lokacin Husna ta samu zarafin buɗe Data, WhatsApp ta shiga sai da ta yi jira na ƴan mintoci saboda saƙonnin dake shigowa,bayan gama shigowar saƙonnin kai tsaye group ɗin ƴan amana ta shiga,nan ta iske dai babu wata magana mai yawa,firar duk Fauzee Kabir da Ibrahim Muhammad ne suka ɗan yi wasa,sai kuma maganganun wasu mutane da ta gani,dubawa ta yi ta ga Fauzee Kabir ba ta online dan ha sai ba ta ce komai ba ta fita daga cikin group ɗin. Hankalinta ta mayar wurin chat da take yi da mutane a private,ta na cikin chat ɗin ne wani saƙo ya shigo mata, ba ta samu damar dubawa ba Saboda maganar da take yi da wata ƙawarta,bayan minti biyar da shigowar saƙon aka sake turo wani. Dan haka ta yanke shawarar dubawa,ta na buɗe saƙon sai ta ga sallama ce aka fara yi mata daga baya kuma aka turo mata wai ta tafi taje ta kwanta. Mamaki ya kamata dan haka ta duba sunan wanda ya turo mata saƙon ganin ko waye ya sanyata yin murmushi. Kafin ta samu damar ba da amsa wani ya ƙara shigowa,”Hajiya da ma ke matsoraciyace ashe?” Ita dariya ma ya bata,dan haka sai ta tura emojin nan na dariya sai ta ce,”meye abin da zan ji ma tsoron toh?” “Ga shi kin ji tsoron kuwa,idan kuma ba tsoro kika ji ba faɗaman me ya hana ki amsa sallamata?” “Haba dai ni babu tsoron da naji,wai wake magana ne?” Husna ta yi tambayar duk da ta gane ko waye tun da har group ɗin da suka haɗu sai da ta duba ta gani. “Kam ina nufin ba ki ma gane da wa kike magana ba?” Ya faɗa duk da yasan basu taɓa chat ba kuma ba ta da lambarshi,amma ai yana tunanin ta na iya duba sunanshi da kuma daga inda suka haɗu. “Ta ya zan gane bayan bansan ko waye ba?” Husna ta mayar masa da tambayar da ya yi mata ta na murmushi. “Hmmm! Kai Sweet Husna ka da dai wannan yarinyar ta fara koyamaki halinta?” Ya faɗa da tabbacin yanzu za ta gane ko waye shi. “Wacce yarinya kenan?” Husna ta faɗa ta na dariya dan ta fahimci wa ya ke nufi, ɗayan gefen kuma ta na mamakin sunan da yake kiranta da shi. “Fauzee Kabir mana dan naga yanzu ta zama ƙawarki.” Ya faɗa dan yasan ya zuwa yanzu ta gama gane daga inda yake. “Gaskiya kana takurama Ƙawata!” Husna ta yi maganar cikin son tsokano shi. “Yarinyar ce ta raina manyanta shi yasa nake takura mata.” Shi ma ya maida mata amsa yana murmushi tamkar a gabanta yake. “A’a gaskiya ka daina takurama Ƙawata ko da yake bansaniba ko ku kalar taku salan soyayyar kenan?” Husna ta faɗa duk da Fauzee Kabir ta faɗa mata abokin saurayinta ne,hakanan ta ji ta na son jin abin da zai faɗa ma ta shi ma. “Ke waye saurayin na ta gaskiya Sweet Husna ba dan ke ki kayi wannan maganar ba da na ɗauki mataki mai tsauri!” Ibrahim Muhammad ya faɗa yana dariya dan ya lura ita ma Husnar ta iya wasa. “To ba gaskiya na faɗa ba ai da anga wannan salon naku ansan na masoyane.” Husna ta faɗa cike da barkwanci. “Ke da gaske ba budurwata ba ce asalima yarinyar abokina ce kuma yana nan a cikin group ɗin,ke ma za ki san shi sunanshi Sardauna amma an fi kiranshi da Abba.” Ibrahim ya faɗa cikin son ta yadda da abin da yake faɗa. “Allah sarki! Allah ya barsu tare,to gaskiya ka daina takuramata ka ga jiya ma muna cikin fira ka zo ka korar man ita!” Husna ta faɗa da alamun damuwa a tare da ita. “To tun da naga kin damu zan daina takuramata amma sai da sharaɗi ɗaya idan kin amince babu matsala?” Ya faɗa yana dariya dan shi kaɗai yasan wane tarko zai ɗana mata. Ba tare da damuwar komai ba Husna ta ce,”ina jinka faɗi kawai na aikata.” “Kin tabbata za ki aikata?” Ibrahim ya tambayi Husna fuskarshi ɗauke da murmushin mugunta. “Me kake ji ma wani ɗar kawai ka faɗa na aika.” Husna ta faɗa cikin nuna irin ta kai ɗin nan. “Kin tabbata ka da sai na faɗa kuma ki zo ki ce a’a dan bazan yadda ba?” “Kar ka ji komai kawai ka faɗi ni kuma na aikata?” Husna ta sake tabbatar ma shi da maganarta. “Ba aikatawa za kiyi ba kawai amincewa za kiyi?” Ya faɗa yana dariya dan yasan ya sanya mata tarko da baza ta iya bijirema buƙatar shi ba. “Kar ka wani damu faɗa na amince,sai wani zagaye-zagaye kake yi ko kana shakkar ƙawance mune?” Husna ta faɗa ita a dole ga mai ƙawa. “A’a bana shakka yanzu dai za ki tabbatar man da abin da kika faɗa,dan haka so nake ki amince da…. 08105217201 Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 37* Bayan Husna ta dawo daga gaidosu Mama,kan gado ta koma domin ta samu ta rage baccin da ke idanuwanta,har bacci ya fara daukarta ta ji wayarta ta fara vibration, tsaki ta yi dan baccine a idanuwanta sosai,ko da ta ɗauki wayar lambar da aka kira ɗazun ce ta sake gani. Shiru ta yi ta na tunanin ko za ta iya gane wake da wannan lambar,ganin kiran na niyyar tsinkewa ba ta tuna komai ba yasa ta yanke shawarar ɗauka. “Assalamu Alaikum fatan kin yi sallah lafiya?” Runtse idanuwanta ta yi lokacin da muryar mutumin ta do ki dodon kunnenta,har cikin ranta ta ji maganar dan ba ƙarya in dai fannin muryane nan dai Allah ya ba shi ita,sai dai fatan ya yi amfani da ita ta hanyar da al’umma zasu amfane. “Ko baccin ki ke har yanzu.” Maganar da ya sake yi ce ta maidota cikin hankalinta,ajiyar zuciya ta sauke wadda har sai da ya jiyo sautinta a cikin kunnuwanshi. “Kai Sweet Husna haka ki ke da nauyin bacci da ma” Muryarshi ta do ki majiyar kunnuwanta a karo na ukku,dan haka ta yi ƙarfin halin sauke wani gwauron numfashi,dan sai yanzu ta gane da wanda take magana,muskutawa ta yi ta gyara kwanciyarta. “Eh yanzu na koma,ba wani nauyin bacci gajiyace wallahi ga jiya ka hanani bacci da wuri,ni ban taɓa kai ƙarfe sha biyu a online ba sai jiya da ka tsareni,ka ga kuwa ai dole nayi ramuwar baccin?” Ta faɗa cikin muryar da ka ji kasan bacci da gajiya sun gama yi ma wanda ya kasance ma mallakinta rubdugu. Murmushi ya yi wanda har sai da ta jiyo sautin fitarshi a kunnuwanta ya ce,”kai Sweet Husna Kar dai ki faɗaman ke ragguwace” Ya ida maganar cikin salon tsokana. Ɓata fuska Husna ta yi tamkar yana kallonta ta ce,”Allah ni ba ragguwa ba ce,dan dai kawai ba ka san aikin da nayi ba a jiya da baka faɗi haka ba.” Cikin kwantar da murya ya ce,”wasa nake maki Sweet Husna ya zan yi na ce maki ragguwa bayan nasan ke jarumace.” Ya ƙarasa maganar cikin yanayi na mai son yin dariya amma kuma ya ƙi barin dariyar fitowa. “Yauwa Sweet Iro!” Husna ta faɗa cikin fara’a wadda har sai da ya gane. “Ɗan sake faɗar sunan da ki ka faɗi yanzu!!” Ya faɗa dan a bazata sunan yazo ma shi,duk da shi yace ta rinƙa kiranshi da shi amma bai yi tunanin za ta faɗa ba,gaskiya ya ji daɗin sunan sosai. “A’a ba sai na ƙara faɗi ba ai ka ji abin da na ce.” Husna ta faɗa ta na turo bakinta gaba cikin alamun jin kunya,dan ita kanta sai da ta faɗa lokacin kuma wata kunya ta lulluɓeta. “Dan Allah ki sake faɗa kin ji Sweet Husna sau ɗaya kawai za ki sake!” Ya faɗa cikin sanyin murya da kuma lallashi. “Sweet Iro!” Ta faɗa ta na rufe idanuwanta sai kuma ta dage bakinta kamar wadda ba ta so faɗa ba. “Kai gaskiya ban taɓa jin wanda ya kirani ba na ji kiran ya ratsa man ɓargo ba irin wannan kiran da ki kayi man ba,nagode kwarai sweet Husnata,sai dai wani abu guda kuma ki daina kirana da Iro dan waccan yarinyar kaɗai ta sanya man shi.” Ya faɗa cikin jin daɗi dan jin shi yake wani nishaɗi na shigarshi ta kowacce gaba dake a jikinshi,dan haka ya sake bajewa akan gadonshi dan ya ji daɗin firar. “A’a ni dai da Iro zan rinƙa kiranka,ita kuma ai da Iroro take kiranka ka ga akwai banbanci kenan koh?” Husna ta yi maganar cikin shagwaɓa dan ba ƙarya ita kanta ta na jin daɗin wannan yanayin da take ciki. “Eh akwai banbanci sosai,amma me yasa ba za ki kirani da Ibrahim ɗina ba?” Ya faɗa yana ƙara jawo bargon da yake gefenshi,lulluɓewa ya yi har kan jikinshi. “Na fi jin daɗin sunan ai.” Husna ta faɗa a takaice,ita kanta ba ta san me yasa take son kiranshi da Iro ba. “To ki daina gaskiya.” Ya faɗa yana murmushi. “A’a bazan iya dainawa ba ina jin daɗin sunan.” Husna ta faɗa ta na sakin dariya ƙasa-ƙasa. “To shi kenan ki cigaba da faɗa in dai hakan zai sanyaki cikin farin ciki na amince ki rinƙa kira.” Ibrahim ya faɗa cikin wata irin murya wadda shi kanshi bai san yana da ita ba,ai kuwa muryarshi ta yi tasiri wurin Husna dan har tsakar kai take jin maganganun shi. “Ko dai da gaske ba ka so ina kiranka da shi na daina?” Husna ta faɗa cikin sanyin murya. “A’a ina so ki cigaba da kirana da shi tunda kina so nima naji ya man daɗi sosai ina godiya!” Ibrahim ya faɗa cikin wani yanayi mai wuyar fassarawa,shi kanshi ba zai iya gane a yanayin da yake ba kawai dai yasan yana cikin wani shauƙine. “To shi kenan zan rinƙa kiranka da Sweet Iro.” Husna ta faɗa ta na sakin hamma,jin hammarta ya ankarer da Ibrahim bacci take ji. “To shi kenan Nagode ki kwanta kiyi bacci nima zan ɗan kwanta zuwa anjima sai na fita shago.” Ya faɗa ba dan ya gaji da firar ba sai dai kawai yanda ya ji ta na hammane yasa dole zai haƙura. “To sai anjima nagode kwarai Allah yasa ka da alkhairi.” Husna na faɗar haka ba ta tsaya jiran jin abin da zai faɗa ba ta kashe wayarta,rufe idanuwanta ta yi da addu’ar bacci ya yi gaba da ita. 08205217201 Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 38* Tun daga wannan ranar Husna da Ibrahim su ka yi wani irin sabo mai ban mamaki,wanda ya kai duk in ɗaya ya hau online to ɗayan ko ya hau ba zai yi chat ba,zai ji babu daɗi har sai ɗayan yazo,duk ƴan gidansu Ibrahim sun san Husna haka ita ma gidansu an san Ibrahim. Group ɗin ƴan amana group ne wanda ya haɗa mutane waɗanda suka san darajar kansu,shi yasa lokaci ɗaya Husna ta zama tauraruwa a cikin gidan,dan duk ranar da ba ta hau online da wuri ba an rinƙa jajenta kenan daga ƙarshe har sai an samu wani ya kirata,duk mutanen gidan suna girmama junansu ba kin gwargwado,shi yasa Husna ta yi sabo dasu sosai,ko a gida Husna ba ta da labarin ba dawa sai na ƴan amana. Fauzee Kabir kuwa ita ce babbar ƙawar Husna a cikin group ɗin,sai Maryam Hassan wadda suke yawan gaisawa a cikin group ɗin. A hankali shaƙuwar da ke tsakanin Ibrahim da Husna ta rikiɗe ta zama soyayya,duk ƴan group ɗin kowa yasan da wannan soyayyar,dan haka kowa yake masu fatan alkhairi,mutane da yawa su na addu’a akan Allah ya ɗorar da wannan soyayya,dan yanzu dai Husna da Fauzee kowa yana burin su auri samarinsu na gidan,a cewarsu wai ayi komai tuwona mai na. Amincin da ke tsakanin Fauzee da Husna ya kai har iyayensu suka haɗa,duk da ba gari ɗaya su ke ba amma su na gaisawa sosai. Wata rana aka yi wani baƙo a cikin group ɗin ƴan amana mai suna Abdullahi amma Abdul ake kiranshi. Abdul mutum ne mai dizgi da son nuna shi wani ne,hakan yasa wata rana su kayi rigima da Fauzee Kabir a cikin gidan, wannan rigimar ita ta ɗaga hankalin kowa da ke gidan,inda Fauzee ta yi zuciya ta bar magana a gidan ƴan amana. Nan ne fa aka rigima mai girma ta ɓarke a tsakaninsu inda wasu ke cewa sai dai a fidda Abdul daga gidan,nan wasu kuma su ka nuna ba su yadda ba. Wannan abu shi ya kawo saɓani sosai,dalilin wannan rigimarce har aka samu matsala tsakanin Husna da Ibrahim,sai kuma gidan ya ida rikicewa inda Husna ta yi iƙirarin rabuwa da Ibrahim. An sha rikici sosai da ƙyar Umma(wadda ta buɗe group ɗin)ta samu ta shawo kan matsalar ta hanyar cire Abdul daga gidan. Wannan hukuncin ne yasa hankalin mutane ya kwanta,amma dai Husna da Ibrahim basu shirya ba,dan tsakaninsu kowa na taƙama da zuciya. Wannan rabuwar da su kayi ne ya sanya Abdul Mai kasuwa yazo ya nuna yana son Husna,ba ta sonshi amma dan ta ba Ibrahim haushi sai ta amsa ma shi,nan fa aka fara buga soyayya a private. Wani lokaci har a group su kan ɗan yi magana amma dai ba wata ta soyayya ba,sanin abin duniya ba ya ɓoyuwa yasa maganar soyayyar Husna da mai kasuwa ta fasu cikin gidan kowa ya ji,nan ma sai aka fara rigima wasu na ganin cin amana ne,rigimar ba ta yi tsawo ba aka kwantar da ita inda Abdul mai kasuwa ya ƙaryata akan cewa shi ba soyayya suke da Husna ba. Wannan magana da ya yi ita ce ta sanya Husna ta fusata ta yi rantsuwa akan sun gama soyayya,wannan shi ne dalilin rabuwar Husna da Abdul mai kasuwa. Bayan rabuwar Husna da Abdul mai kasuwa sai kuma Ibrahim ya sake dawowa,bai je kai tsaye ba amma idan ana magana a group yana ƙoƙarin sanya Husna,idan kuma ita ke magana yana sanya baki da haka dai ya samu ya shawo kanta da ƙyar,shi ma sai da wasu daga cikin ƴan group ɗin suka sanya baki babu yadda Husna za ta yi dole ta haƙura suka dawo da soyayyarsu. A chan bayan fage kuma ashe Maryam Hassan bala’in son Ibrahim take babu wanda ya sani sai shi da ya gane,ko wasa ake a group idan Husna da Fauzee su na yi ma shi to Maryam ita ke kare ma shi tana cewa Broz ba haka yake ba,babu wanda hankalinshi ya kai akan abin da take yi duk kowa ya ɗauka saboda ta na kiranshi Yayanta shi yasa. Daga baya Sardauna ya fahimci halin da ake ciki,yaso fahimtar da Maryam amma bai san ta inda zai fara ba saboda bata fito fili ta nuna ba. 08105217201 Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 40* DAWOWA LABARI Ajiyar zuciya Husna ta yi lokacin da ta gama tuna rayuwarsu ta baya ita da Fauzee,wasu hawaye masu ɗumine suka wanke mata fuska,ganin abin take tamkar a mafarki wai shi kenan Fauzee ta yi tafiya mai nisan zango,tafiyar da duk wanda ya yi ta ya tafi kenan babu ranar dawowa. Kukane ya ci karfinta duk yadda taso danneshi amma ya ƙi dannuwa,kanta ta sanya a tsakanin cibiyoyinta ta saki kukan mai tsuma zuciyar mai sauraro,ta daɗe ta na kukan dan ba ta san iya adadin lokacin da ta ɗauka ta na kukan ba. Ta na cikin wannan yanayin ta lura da wayarta sai haske take kawowa,ka sa ɗaukar wayar ta yi har sai da aka rinƙa kira kamar ba za a daina ba,cikin sanyin jiki ta ja jikinta zuwa inda take hango hasken wayar. Fuskar wayar ta kalla ganin wanda ke kira yasa ta ɗauka,ta na jiyo lokacin da ya sauke ajiyar zuciya,sun ɗauki sama da sakan talatin babu wanda ya iya faɗar komai,chan dai ta yi ƙarfin halin furta. “Ina wuni?” Cikin dashashshiyar muryarta da ba ta fita sosai saboda kukan da take yi. “Husna kuka ki ke yi koh?” Shi ma ya faɗa cikin tashi muryar da babu komai sai zallar damuwa. “Ta ya kake tambayata kuka nake bayan kasan dole nayi ko zan samu sassauci akan halin da nake ciki, da ma Fauzee ta faɗaman wannan ciwon mutuwa za ta yi ashe kuwa da gaske take!” Husna ta faɗa hawaye na sake wanke mata fuska,dan ba ta da ikon hanasu zuba. Jim Ibrahim ya yi dan shi kanshi yana cikin yanayi na ruɗu wanda da zai samu dama shi ma da kukan zai yi. “Husna ba mu da ikon chanza ƙaddarar da Allah ya ɗoramana,lokacin da ya ba mu Fauzee mun ji daɗi mun yi murna,yanzu kuma da ya karɓeta ya kamata mu yi mata addu’a dan ita kaɗai tafi buƙata a garemu!” Ibrahim ya ida maganar tamkar zai yi kukan shi ma amma saboda ƙarfin hali ya daure,dan shi kanshi ya san sun yi rashi sosai,ya yi wani irin sabo da Fauzee dan tun zuwanta gidan shaƙuwa mai girma ta shiga tsakaninsu. “Nima ina so na daina kukan Sweet Iro amma wallahi hawayen sun ƙi tsayawa.” Husna ta faɗa tare da sakin wani mahaukacin kuka,duk idan ta tuna ta rasa Fauzee hankalinta na tashi sosai. Runtse idanuwana Ibrahim ya yi dan shi kaɗai ya san halin da yake ciki,shi kanshi da zai samu mai rarrashin shi so yake,amma ya zama dole gareshi akan ya samu ya lallashi Husna. Dan haka cikin sanyin murya wanda damuwace ta haifar masa da shi ya ce,”ashe bazamu iya rungumar duk abin da Allah ya ɗoramana ba,kar ki manta Husna yana daga cikin cikar mumuni shine yarda da ƙaddara mai kyau ko akasinta,dan me mu bazamu yi koyi da abin da addininmu ya koyar damu ba, Husna mutuwa dolece inda Fauzee ta tafi mu ma dole a chan zamu je,kiyi haƙuri ki yi alwalla ki ɗauki alƙur’ani ki karanta mata suratul Rahman har da Yasin kin ji ko Tawan!!” Ya faɗa cikin wani yanayi dan sautin kukanta dake shiga kunnuwanshi yana ƙara rikitashi. “Yanzu shi kenan da gaske na rasa aminiyatace?” Husna ta faɗa tare da fashewa da kuka. “Ki yi haƙuri haka Allah ya tsara,mu kasance masu karɓar ƙaddara a duk yanda ta zo mana.” Ibrahim ya faɗa cikin sanyin murya. “To na karɓi wannan ƙaddarar Allah ya jiƙanki Fauzee!” Husna ta faɗa ta na share hawayen dake zuba akan fuskarta. “Yauwa Tawan je kiyi alwalla ki zo ki ɗauki qur’ani ki karanta,insha Allah za ki ji sauƙi saboda shi qur’ani warakane.” Ibrahim ya faɗa cikin sigar lallashi. “To shi kenan zanyi insha Allah.” Husna ta faɗa ta na ƙoƙarin danne kukan dake taso mata amma ina ta makara dole ta sake shi,shiru Ibrahim ya yi dan ya kula Husna ta na cikin yanayin da bai kamata a hana ta kukan ba,duba da ganin kukan na ta ba irin wanda aka haramta bane mai kururuwa,sai da ta ɗauki lokaci mai tsawo kafin ya samu ya shawo kanta da ƙyar. Sai da ya tabbatar ta ɗan samu natsuwa sannan ya kashe wayarshi,yana kashewa ya fara neman masu motar da zasu yi tafiya a cikinta,dan su na so ranar sadaka suje Kaduna su yi ma iyayen Fauzee gaisuwa. Bayan Ibrahim ya kashe wayarshi nan Husna ta miƙe ta je ta ɗauro alwalla,inda ta tashi ta dawo qur’ani ta ɗauka ta fara karatu. Nan fa mutane su kai ta kiranta wayata saboda sanin yadda suka shaƙu da Fauzee, wannan kiran da ake mata shi ne ya maido mata da kukanta baya,dole Mama ta zo ta tafi da ita ɗakinta. 08105217201 Hussy Saniey.???? Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/LmbGi3TbkTF2sUurNrJ8zZ *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 41* Husna ba ta taɓa cin karo da dare mai tsayi a rayuwarta kamar daren yau ba,ta yi kuka har idanuwanta suka daina zubar da ruwa,daga ƙarshe sai miƙewa ta yi ta kabbara sallah,da nafilfili ta raya wannan daren. Husna na gama sallar asuba ta hau WhatsApp,ta san mutuwa ɗaya ce kuma ba’a wasa da ita amma har yanzu ganin abun take kamar mafarki take,ta na fatan ta tashi daga wannan mummunan mafarkin,sai dai shigarta group ɗin ƴan amana yasa ta ida tabbatar ma da kanta ba mafarki take ba, hawayene ke ta sintiri akan fuskarta,yanzu shi kenan Fauzee ta yi tafiyar da babu ranar dawowa. Kallon hotunan Fauzee da aka turo take yi ta na tuna rayuwarsu,duk in ta kalli hotunan babu abin da ke tada mata hankali irin idan ta ga an sanya RIP,duk in ta kalli waɗannan kalmomin suna matuƙar ta da mata hankali,fita ta yi ta koma private ta rinƙa bin chat ɗinsu ta na dubawa,hawaye kuwa tamkar an buɗe lalataccen famfo haka suke zuba. Jin kanta na mata wata irin sarawa yasa ta miƙe ta na layi tamkar wadda ta sha wani abu, haɗa hanya ta rinƙa yi,saura kaɗan su yi karo da Mama dake ƙoƙarin shigowa hannunta riƙe da kofi,ganin yadda Husna ke laluben hanya yasa ta kama hannunta,maido ta cikin ɗakin ta yi sai ta zaunar da ita. “Husna ina za ki je haka bayan kin san ba ki da lafiya?” Mama ta yi maganar ta na ƙare ma Husna kallo,ganin yadda duk ta zabge a cikin dare guda amma ramar da ta yi har ta fito. “Kaina…ke…ciwo nake so naje ɗakina na kwanta.” Husna ta faɗa tamkar mai koyon magana,dan muryar ta yi ƙasa da yawa sai ka saurara sosai ka ke jin abin da take faɗa. “To shi kenan gama shan shayin nan sai ki sha magani ki kwanta.” Mama ta yi maganar tare da ɗauko kofin da ta shigo da shi. Girgiza kai Husna ta yi,”Mama bazan iya sha ba bakina ɗaci gareshi amma bani maganin sai na sha,kaina kamar zai ɓare biyu nake ji.” Husna ta ƙarasa maganar ta na yamutsa fuskarta. “Ki yi haƙuri Husna ki daure ki sha shayin sai ki sha maganin kin ga ko jiya ba ki ci komai ba haka nan ki ka kwanta.” Mama ta yi maganar ta na kai ma Husna kofin a baki,babu yanda Husna ta iya dole ta buɗe bakinta,sau biyu ta kurɓi shayin ta janye kanta,ƙa ra kai mata kofin a baki Mama ta yi sai ta girgiza kanta alamar ya isheta. “Ki daure ki sha Husna sai ki sha magani kin ga babu komai a cikin ki!” Mama ta faɗa cikin sanyin murya,dan ba ƙaramin tausayin Husna take ji ba,kallo ɗaya za kai ma fuskar Husna ka yi saurin ɗauke kanka,dan duk ta kumbura ga idanuwanta sun yi shishshige ciki,duk da kasancewar Husna baƙa amma sai da fuskarta ta yi ja. “Mama na ƙoshi ki bani maganin dan Allah!” Husna ta faɗa wasu hawaye na sake zubowa akan fuskarta,hannu ta sa cikin sauri ta goge dan gudun ka da Mama ta gani amma ta makara saboda idanuwan Mama akan ta su ke tun ɗazun. “Husna bazan fasa yi maki nasiha ba,duk musulmin ƙwarai an san shi da karɓar ƙaddara ko wacce iri ce,a yanzu kuka babu abin da zai chanza Husna, Allah ya riga da ya yanke abin da yake dai-dai a garemu sai dai mu bi da addu’a kawai, Allah shi yafi mu sanin dai-dai a rayuwarmu,lokacin da ya haɗa ku bai yi shawara da kowa ba haka lokacin da ya karɓeta bai yi shawara da kowa ba,a yau Husna ko ke Allah ya buƙata babu tsumi babu dabara dole sai kin tafi,dan haka kuka ba naki bane addu’a kaɗai Fauzee ke buƙata daga gareki,dan haka kiyi haƙuri ki daina wannan kukan kin ji Husnata!” Mama ta faɗa cikin sigar lallashi. “Zan daina Mama insha Allah kuma zan ta yi Mama Fauzee addu’a dan nuna soyayya ta a gareta.” Husna ta faɗa da muryarta wadda kuka ya disasheta. “Yauwa ɗiyar albarka karɓi shayin ki shanye sai ki sha maganin ki kwanta insha Allah kan zai sauka.” Mama ta yi maganar cikin karayar zuciya,ta san ɗiyarta ta yi sabo da Fauzee sosai,duk wanda ke tare da Husna sai yasan Fauzee duk da kasancewar su ba’a gari ɗaya ba amma akwai shaƙuwa mai girma a tsakaninsu,ganin yanda Mama ta shiga damuwa yasa Husna ɗaukar kofin shayin ta ɗaga,ba ta sauke kofin ba sai da ta shanye shi tsab,duk da ba ta jin daɗin shi akan halshenta amma haka ta daure, miƙa hannu ta yi ta karɓi magani,shi ma nan take ta shanye shi,hakan ya ma Mama daɗi kuwa sosai,dan haka ta kama hannun Husna ta mai da ta akan gadonta. Taimaka ma Husna ta yi har sai da ta kwanta,bargo Mama ta yafa ma Husna a jikinta dan ta san Husna ba ta iya bacci sai ta lulluɓe,sai da Mama ta tabbatar Husna ta ji daɗin kwanciyar sannan ta fita ta baro mata ɗakin. Shiru Husna ta yi kamar ta na bacci, waya take son yi amma babu hali tun da ta ga lokacin da Mama ta fita da wayar,dan haka ta lumshe idanuwanta kamar ta na bacci. 08105217201 Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 39* A kwana a tashi asarar mai rai, a haka aka cigaba da rayuwa a group ɗin tamkar babu wata rigima da ta taɓa faruwa. Mutane sun samu natsuwa sosai,dan komai ya wuce ba kamar ɓangaren Husna da Ibrahim soyayya suke mai ban mamaki,har lokacin Husna duka mutum ukku ta sa ni a cikin group ɗin a fuska, Ibrahim, Sardauna,sai Abu Abdul Rahman. Kwatsam wata rana sai ga Sardauna ya sanyo wata Hadiza Muhammad a gidan(kasancewar shi ma admin ne,da ma admin ukku ne a gidan shi da Maryam Hassan da Umma.)mutane sun mata barka da zuwa an karɓeta kamar yadda aka saba karɓar baƙi a gidan. Ita ma sun yi sabo da Husna sosai dan Kakus Husna ke kiranta da shi,ita kuma ta na kiran Husna da jikata. Bayan kwana biyu da sanyo Hadiza Muhammad sai Sardauna ya bata admin,nan fa Umma ta ce ba ta yarda ba,dan ga tsaffin members nan ba’a basu admin ba dan haka ba za’a ba Hadiza Muhammad ba. Nan fa Abba ya ce shi kuma ba zai cire Hadiza Muhammad daga admin ba, wannan furuci na Sardauna shi ne ya tada rigima sosai a gidan,daga ƙarshe ma sai Umma ta fita daga gidan. Wannan fita da Umma ta yi shine buɗewar kofofin matsala a gidan,an yi ƙoƙari ƙwarai da gaske wurin ganin Umma ta dawo gidan amma ta yi rantsuwa ta gama zama a gidan. Har taro aka yi da duka Officials ɗin gidan amma aka ka sa samun damar shawo kan Umma dan har cire Hadiza Muhammad ɗin aka yi daga admin amma dai babu biyan buƙata,wannan haɗuwa da aka yi ita ce ta sanya Husna ta san offials ɗin gidan,amma ban dasu ba ta san sauran members ɗin gidan ba. Dole aka haƙura aka kyaleta ba dan rai na so ba, group ɗin sai da ya yi tamkar zai mutu cikin ikon Allah kuma da taimakon Husna da Fauzee sai ga shi ya tashi. Duk da Umma ta fita daga gidan idan aka yi wani abu da ya danganci ƴan group ɗin ta na zuwa. Yanzu ma ko hidimar bikin da ake a gidan ƴan amana bikin ummar ne yazo shi ne suke tunanin gudummawar da zasu ba ta,dan Umma ta na da kirki sosai wannan dai matsalar da aka samu ce kawai. Fauzee na da ciwon zuciya da ma yana tashi lokaci bayan lokaci,dan akwai lokacin da aka kwantar da ita asibitin Shika ƴan amana sun so zuwa amma Allah bai yadda ba. Wayar Husna da Fauzee ta ƙarshe saura ƙwana biyu ta rasu,wata rana da misalin ƙarfe sha ɗaya na dare su na chat sai Fauzee ta ce, “Wallahi Husna ji nake kamar ciwon nan ba zai bar ni ba dan ni kaɗai nasan abin da nake ji.” Cikin wasa Husna ta ce,”ki ce mu shirya cin wake da shinkafa?” Fuskantar da Fauzee ta yi wasa Husna ta ɗauki maganarta yasa ta ce, “Hmmm! Husna ba wasa nake ba wallahi yanzu fa ina asibiti kuma ko bacci ban iyawa Husna kirjina ke ciwo kamar zan mutu!” Ta faɗa cikin karaya dan ta sadaƙas da rayuwa. Cikin zaro idanuwa Husna ta ce,”innalillahi Fauzee amma ki kayi shiru ba ki faɗaman ba?” Cikin tashin hankali Husna ta yi maganar. “Banso hankalinki ya tashi yanzu haka ina asibiti ina faɗa maki ne yanzu saboda bansaniba ko wannan ce maganarmu ta ƙarshe!” Fauzee ta faɗa ta na ciye leɓenta na ƙasa. “Kiyi haƙuri insha Allah za ki samu lafiya Ƙawata tun da kina asibiti likitoci kuma na kula da ke.” Husna ta faɗa cikin karfafawa Fauzee guiwa. “Husna asibiti babu abin da zasu iya yi man a halin da nake ciki yanzu,sai asarar kuɗi da ake yi dan nasan mutuwa zan yi wannan ciwon ba zai bar ni ba!” Fauzee ta faɗa tare da dafe kirji ta na jin yadda numfashinta ke sarƙewa. “Wannan wacce kalar maganace Fauzee?cuta ai ba mutuwa ba ce,mai lafiya nawa ki ka ji ya mutu ya bar mara lafiya dan haka ki daina wannan maganar ma!” Husna ta faɗa ta na share hawayen da suka cika mata idanuwa,dan maganar Fauzee ta karya mata da zuciya. “Wallahi Husna da gaske nake ina ji a jikina mutuwa zan yi dan Allah ki yafeman lokacin da labarin mutuwata ya riske ki,ni dai nasan tawa ta ƙare na yafema kowa dan Allah ki roƙarman gafarar mutane.” Kalaman Fauzee ba ƙaramin tsoratar da Husna su kayi ba dan haka sai kawai ta kira Fauzee a waya. Yanda muryar Fauzee ke fita kawai ya sanya Husna ta fashe da kuka,nan fa Fauzee ta yi ta lallashinta,sun tattauna maganganu masu yawa daga ƙarshe kuma su kayi sallama saboda zuwan wani likita ya ce ma Fauzee ta kwanta dan ta na buƙatar hutu,washe gari kuma gaba ɗaya wayar Fauzee a kashe take,daga haka kuma basu ƙara magana ba sai dai da wannan mummunan labarin ya isketa. 08105217201 Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 44* Ruwa masu sanyi Mama ta zuba ma Husna a fuska,ruwan na sauka akan fuskarta,ajiyar zuciya mai ƙarfi ta yi, buɗe idanuwanta ta yi tana ƙarema rufin ɗakin kallo. “Sannu Husna.” Muryar Mama ta do ki dodon kunnenta,a hankali ta maido dubanta akan fuskar Mama,kallo ɗaya ta yi ma fuskar Mama ta ɗauke kanta,dan ba ƙaramin tausayin Mama ba ne ya ratsata, lumshe idanuwanta ta yi a hankali ta ce,”Mama ki yi haƙuri dan Allah wallahi na ka sa jurewa ne shi yasa kike ganin kamar ban jin maganarki amma insha Allah na maki alƙawari daga yanzu na daina kukan nan.” Ta ida maganarta ba ta san lokacin da wasu hawaye masu ɗumi suka wanke mata fuska ba, murmushin ƙarfin hali Mama ta yi. “Ki ɗauki ƙaddara Husna,da ma haka rayuwa take sai ki ga yau kin rayu da wani gobe kuma da waninsa za ki rayu.” Tashi Husna ta yi daga kwancen da take,kallon Mama ta yi duk sai ta ga ma Mamar duk ta fa ɗa. “Hakane Mama kuma na karɓi wannan ƙaddarar da hannu bibbiyu insha Allah,sai dai alfarma ɗaya nake so ki yi man Mama,dan Allah ka da ki ce A’a.” Kallon ƴan sakanni Mama ta yi ma Husna,sai kuma ta saki murmushi. “Faɗi abin da kike so in dai bai fi ƙarfina ba zan maki shi insha Allah.” Gyara zama Husna ta yi tare da riƙo hannun Mama,kallon fuskar Mama Husna ta yi tare da ƙara narke fuska,yanda ta yi kallo ɗaya za ka yi mata ta baka tausayi. “Mama dan Allah ki taimakeni kamar yanda Allah ya taimakeka,idan za’a gaisuwa ki roƙar man Baba ya barni naje ka da ku hanani dan Allah Mama, wallahi Mama ina so na haɗu da iyayen Fauzee tun da ita Allah bai ƙaddara haɗuwa ta da ita ba.” Ta ƙarasa maganar cikin yanayi na mai son yin kuka,dafa kafaɗarta Mama ta yi ganin yanda ta koma kalar tausayi,dan haka sai Mama ta sakar mata wani murmushi mai kwantar da hankali. “Ba zamu hana ki zuwa ba Husna,sai dai mu yi fatan Allah ya kai ku lafiya ya dawo mana daku lafiya,yaushe ne zaku yi tafiyar?” Duk da tana cikin wani hali amma sai da ta ji daɗin barinta da aka yi,dan har sai da fuskarta ta gaza ɓoyewa. “Ibrahim dai ya faɗa man ranar sadaka za a je amma dai zan ƙara tambayarshi sai naji.” “Yauwa Husna ni dai abin da nake so dake dan Allah ki sanya ma ranki dauriya,idan kika aikata haka zamu kasance cikin jin daɗi.” Mama ta yi maganar tana ƙoƙarin tashi daga zaunen da take. “Insha Allah Mama ba zan kuma ba,ai kin gama man komai tun da kika bar ni zuwa Kaduna.” Husna ta yi maganar kamar ba ita bace ta suma yanzu ba,har cikin ran Mama ta ji daɗin yanda Husna ta saki jikinta,nasiha ta ƙara yi mata sosai,sai da Mama ta tabbatar Husna ta yi laushi sosai,lokacin ta fita daga ɗakin ta bar ta zaune. Shiru Husna ta yi tana jinjina wannan rayuwar a cikin ranta,dole ƴan magana ke ce wa ba gidan zama ba ce duniya,yanzu kamar ba a yi Fauzee ba a duniya,sai dai a bi ta da addu’a kawai,lalle rayuwa ba ta da tabbas. Ta ɗauki tsawon lokaci ta na wannan tunanin,ganin babu abin da yake ƙara mata sai damuwa yasa ta jawo wayarta,kai tsaye gidan ƴan amana ta shiga,yanzu ma dai babu wata fira,dan haka ta fito, Ibrahim ta kira dan ta ji yanda tafiyar za ta kasance,sun daɗe sosai suna tattaunawa akan yanda za a yi tafiyar,inda daga ƙarshe aka samu matsaya. Ranar sadaka suna gama sallar asuba suka fito daga gidajensu,in da suka yi zasu haɗu chan kuwa suka haɗun,su gomane zasu yi tafiyar,da yake motar babba ce sai ta ɗaukesu babu ɓata lokaci suka hau hanya,cikin ikon Allah ƙarfe biyu a gidansu Fauzee ta yi masu. Duk da gidan cike yake da mutane kasancewar ranar akai sadaka,hakan bai hana su samu tarba mai kyau daga wurin iyayen Fauzee ba,gaskiya iyayen Fauzee sun ya ba da kirkin mutanen sosai,duk da sun san ƴarsu ba za ta yi tarayya da mutane marasa mutunci ba,nan fa aka dasa sabon kuka saboda labarin da Maman Fauzee ke basu na yanda akai rasuwar,sun yi kuka sosai ji suke tamkar yanzu ne abin ke faruwa,daga ƙarshe suka ba zukatansu haƙuri,an yi doguwar addu’a akan Allah ya sanyaya makwancin Fauzee,ana yin sallar la’asar kuma suka yi shirin komawa gida,nan fa dauriyar Maman Fauzee ta ƙare,dan rungume Husna ta yi tana kuka mai cin rai,ganin kukan da Maman Fauzee ke yi duk sai jikinsu ya yi sanyi, da ƙyar aka raba Husna da Maman Fauzee,har suka shiga Mota Husna na kuka. Yan da ƴan cikin Motar ke ƙoƙarin jan Husna da magana yasa tun tana sharewa har sai da ta saki jikinta,basu suka shigo garin Katsina ba sai ƙarfe takwas na dare,har ƙofar gida aka kai kowa. Husna na shiga gida ta zauna nan fa ta fara basu labarin kirkin iyayen Fauzee, Mama ta ji daɗi sosai har ta kira Maman Fauzee tai mata godiya,nan take nuna mata ai an zama ɗaya. 08205217201 Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 43* Taso ƙwarai da gaske wayarta ta kasance tare da ita,amma ga shi Mama ta hana ta wayarta,har hawaye sai da ta yi na jin haushi,ta na wannan tuƙuburin bacci mai nauyi ya yi awon gaba da ita,dan harda maganin bacci Mama ta haɗa mata,aikuwa nan ma ta yi baccin mai nauyi dan ko da la’asar da ƙyar Mama ta tada ta,ko da ta gama sallar ma nan kan darduma ta yi bacci. Ba ita ta farka ba sai wurin ƙarfe shidda da ƴan mintoci,aikuwa ta ji jikinta ya mata daɗi sosai,wanka ta sake yi da ruwa mai ɗumi,nan ma ba ta shafa mai ga jikinta ba,sai ta nufi tsakar gida ta zauna inda Mama ke yanka alayyahu, rinƙa haɗa ma Mama ta yi da haka har suka gama,ganin ta ɗan saki jikinta yasa Mama ta bata wayarta tare da mata gargaɗin ka da ta ganta ta na kuka,babu musu ta amince,sai bayan ta gama sallar isha’i sannan ta buɗe data. Sakonni ta iske na masu yi mata ta’aziyya sosai,a hankali ta rinƙa bi tana amsawa har ta gama,sai ta shiga group ɗin ƴan amana,tun safe har yanzu babu wata magana mai yawa da aka yi, ƴar maganar ma dai gaisuwa ce suka yi ma junansu. Sallama ta yi tare da yi masu ta’aziyya,nan aka fito ana amsawa ashe duk suna kusa amma jimami yasa kowa ya yi shiru. Fita ta yi daga group ɗin saboda wani tunani da yazo mata a rai,wurin lambobinta ta shiga nan ta tsaya a wurin lambar Fauzee,sai kawai ta ji hawaye sun zuɓo mata,ba tare da ta damu da ta gogeba ta danna kira,sai da ta kira sau biyu kafin a ɗaga jin muryar Maman Fauzee yasa ta ƙara tabbatar ma kanta babu Fauzee a wannan duniyar. Katse mata tunani maganar Maman Fauzee ta yi,”ɗiyata ya jikinki? ɗazun mun yi waya da Mamanki take faɗaman ba ki da lafiya.” Kamar wadda aka ta da daga bacci haka Husna ta firgita,nan ta kama inda-inda. “Ma…ma…da… sauƙi!” Husna ta yi maganar da muryarta da ko fita sosai ba ta yi,dan ba dan Maman Fauzee ta saurara sosai da ba ta jin mai Husna ke faɗa. Tausayin yarinyar ya kama Maman Fauzee ta ce,”kiyi haƙuri ɗiyata,mu ma dole haƙuri muka yi wanda ya ba mu Fauzee ya karɓe kayanshi dan ya fi mu sonta, addu’a kaɗai zamu bi ta da ita,dan muma zaman jiran tamu mutuwar muke koyi haƙuri da ma haka rayuwa take wata ran akwai mu wata rana kuma za’a wayi gari babu mu kin ga dai alama akan ƙawarki dan haka sai dai mu yi fatan samun kyakkyawan ƙarshen.” Mama Fauzee ta ida maganarta tare da share hawayen da suka zuɓo mata akan fuskarta,dan ita kaɗai ta san halin da take ciki,ta na yin ƙarfin haline kawai dan mutane su samu natsuwa,dan ta lura ba ƙaramin bugu mutuwar Fauzee ta yi ma mutane ba. “To shi kenan Mama insha Allah zan kasance mai yi mata addu’a duk da dai nayi to zan ƙara,naji ma ƴan amana na maganar zamu zo nan Kaduna.” Husna ta faɗa a hankali,dan Maman wannan karon ba ta ji mai Husna ta faɗa ba sai da ta ƙara maimaita mata. “Eh sun faɗaman da muka yi waya dasu,dan har ma Baban gida yazo ɗazun da shi aka yi jana’iza.” Mama ta faɗa ta na danne wani abu da ke taso mata. “Allah sarki ashe yazo Allah ya ba shi lada ita kuma Allah ya jaddada rahamarshi a gareta!” Ta ƙarasa maganar tare da fashewa da kuka,dan ta kasa daurewa duk ƙoƙarin da tayi amma ta kasa. Ita ma Maman Fauzee hawayen ne suka zuɓo mata dan ɗiyarta take tunawa,zaman Babansu Fauzee a kusa da ita yasa ta share hawayenta,cikin ƙarfin hali ta ce,”Ameen Husna ki kwanta kiyi bacci kin ga baki da lafiya gobe mun yi magana.” “To Mama nagode Allah ya bada haƙurin rashi sai anjima.” Husna na faɗar haka kuka mai ƙarfi ya kwacemata,dan Maman Fauzee na jin kukan ita ma hawayen suka sake zuɓo mata,kuka sosai Husna ta yi,dan ji take kamar yanzu aka faɗi mata rasuwar. Tunawa da Sardauna da Husna ta yi yasa ta tsaida kukanta,kiran wayarshi ta yi kamar ba zai ɗaga ba chan kuma aka ɗaga,daga yanda ta ji muryarshi ta san shi ma kukan yake,nan fa ta kasa magana kawai ta kashe wayarta ta na sakin kuka mai ban tausayi,wai yanzu babu Fauzee a cikin wannan duniyar,maganar da tafi juyawa a ranta kenan,jin ta na kuka ta kashe wayarta yasa Sardauna tura ma Ibrahim text akan ya lallashi Husna. Shi Ibrahim bai ma san Husna ta karɓi wayarta ba,dan ya kira ya kai sau biyar sai dai Mama ke ɗagawa shi yasa ya jinkirta da kiran da yake faman yi mata. Kiranta ya yi ta na kallo amma ta kasa ɗagawa saboda kukan da take dan ko ta ɗaga baza ta iya magana ba,nan fa numfashinta ya fara sama kamar mai cutar numfashi,hakan ya yi dai-dai da shigowar Mama ɗakin dan ta dubata ta ji ta shiru tunda ta shigo ɗakin,kafin Mama ta ƙaraso inda take har ta faɗo daga saman gado,cikin sauri Mama ta isa inda take,kasa ɗagata Mama ta yi sai dai ta kama hannunta, dai-dai saitin agogon hannunta ta taɓa amma sai taji babu motsi,saman hancin Husna Mama ta kai hannunta amma nan ma babu numfashi. 08105217201 Hussy Saniey.???? Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/LmbGi3TbkTF2sUurNrJ8zZ *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 42* Ƙarfin maganin da Husna ta sha,ga baccin da ba ta samu yi ba a daren jiya yasa ko minti biyar da kwanciya ba ta yi ba bacci ya yi awon gaba da ita. Ko da Mama ta leƙo dubata ta ga bacci take sai ta gyara mata bargo,da za ta fita har sai da ta ja mata kyauren ɗakin saboda ta san Husna in ta na bacci ba ta son hasken,aikuwa ta yi bacci mai nauyi dan ba ita ta farka ba sai wurin ƙarfe ɗaya da rabi,shi ma kun san jiki da jini duk lokacin da ka saba sallah da ya yi cikin ikon Allah ko kana baccine sai ka tashi. Da addu’a a bakinta ta farka,kallon ɗakin take yi kamar yau ta fara ganinshi,sai lokacin ta tuna da a ɗakin Mama take,agogon dake manne a jikin gado ta kalla,ganin yanda lokaci ya ja yasa ta tashi daga kwanciyar da take,ta mamakin baccin da ta yi take yi,tunaninta ya yanke ganin haske ya haske mata idanuwa har sai da ta runtse idanuwanta,ganin haka yasa Mama sakin labulen ɗakin ta shigo ciki. “Kin tashi ashe? da ma shigowa nayi na tada ki kiyi sallah dan har an kira yanzu kin ji sun tada sallah,” Mama ta faɗa tare da kai hannu jikin Husna,jin babu zafi a jikin yasa ta yi murmushi ta ce,”Alhamdullih jikin ma babu zafi yanzu ga ruwa chan na haɗa maki kije kiyi wanka dan ki ji ƙarfin jikinki.” “To Mama.” Husna ta faɗa ta na yaye bargon dake jikinta,saukowa ta yi daga kan gadon ta fara tafiya a hankali,har ta nufi hanyar fita daga ɗakin Mama ta ce,”Husna ki shiga toilet ɗin nan ɗakin dan ciki ma na haɗa maki ruwan.” “To Mama amma bari na ɗauko kayana.” Husna ta yi maganar cikin muryarta da har yanzu ba ta fita sosai. “Je kiyi wankan bari na ɗauko maki kayana.” Mama ta faɗa ta na fita daga ɗakin. Bayanta Husna ta bi da kallo har cikin ranta ta na jin tausayin mahaifiyarta,duk lokacin da Husna ba ta lafiya ko ta na cikin damuwa Mama sai ta fita shiga wani hali,shi yasa lokutta da dama take ƙoƙari ƙwarai wurin danne damuwarta,jin motsin Mama na ta fito daga ɗakinta yasa cikin sauri Husna ta shige toilet,har sai da Mama ta ji kamar ƙarar rufe ƙofar dan haka ta kalli ƙofar amma jin ƙarar ruwan da Husna ta taɓa sai ta yi tunanin ko kunnuwanta ne suka ji mata haka,da ma Husna ta taɓa ruwan ne saboda ta kauda ma Mama tunanin yanzu ta shigo kuma ta samu nasara. Ba ta wani jima sosai a toilet ɗin ba ta fito,ta ji daɗin jikinta sosai dan jin ta take wani sakarai,gefen gado ta iske kayanta da Mama ta ɗauko mata,jin gyaran muryar da liman ya yi na shirin ta da Sallah yasa ta saurin sanya kayan,ko mai ba ta shafa ba sai turare da ta ɗauka ta sanya ma jikinta,jin an tada sallah yasa ta shimfiɗa darduma ta kabbara sallah ita ma. Ko da aka gama sallah ba ta tashi daga inda take zaune ba,sai ma ta jingina bayanta da katakon gado,lumshe idanuwanta ta yi ta na tunanin halin da take ciki,duk da tasan yanzu an daɗe da kai Fauzee maƙwancinta amma har yanzu kamar wasa take ganin abun,hawaye ta ji na sauka akan fuskarta,ka sa tsaida su ta yi dan haka ta barsu suna zuba,jin motsin Mama ta nufo ɗakin yasa ta yi saurin goge hawayen fuskarta. Mahaifiya ba wasa ba,kallo ɗaya tai ma fuskar Husna ta san ta yi kuka,dan haka ta zauna kusa ta ita,ta rinƙa yi ma Husna nasiha da nuna mata illar kukan da take yi,sun daɗe Mama na mata nasiha,har sai da Mama ta tabbatar yarinyarta ta samu natsuwa sannan ta miƙe tsaye ta nufi fita daga ɗakin. “Ba ri na kawo maki abinci kin ji koh?” “Mama dan Allah ki bar abincin ki bani ruwan shayi kaɗai ma ya isa!” Husna ta yi maganar kamar za ta fasa kuka,dan har ga Allah ba ta jin bakinta zai iya tauna wani abu a yanzu. “A’a Husna ki daure dai ki ci abinci yaushe shayi zai iya riƙe maku ciki.” Mama ta faɗa tare da juyowa ta kalli Husna. “Mama ki dai bani shayin zan fi iya shan shi dan bakina ɗaci yake man!” Husna ta faɗa tare da marairacewa,dan Mama ta ji tausayin ta,haƙarta kuwa ta cimma ruwa dan Mama ta kuwa ji tausayin na ta,dan haka ba tare da Mama ta sake faɗin komai ba ta juya ta fita,babu daɗewa sai ga Mama ta dawo da kofi da filet riƙe a hannunta. Sai da ta aje kofin da filet ɗin sannan Husna ta ga ashe wainar ƙwai ce,tura mata kayan gabanta Mama ta yi tare da tsareta da idanuwa. Ganin babu wasa a fuskarta yasa Husna jan kofin shayin da yaji madara ta kai bakinta,duk da shayin ya mata daɗi a baki amma sai ta ji bata sha’awar shan shi, ɗagowa ta yi ta kalli Mama ganin yadda fuskarta take a ɗaure yasa ta sunkuyar da kai, wainar ƙwan ta jawo ta fara cusama cikinta har ta cinye ƙwan ta kuma shanye shayin ba ta sake gigin kallon Mama ba. Babu wanda ya yi magana sai Mama da ta ɓallo magani ta miƙo mata,babu musu ta karɓa ta kora da ruwa,ganin Mama ta tattare kayan ta na niyyar fita yasa ta ƙara narke fuskarta. “Mama wayata fa dan Allah.” Ba tare da Mama ta tsaya saurarenta ba ta fita daga ɗakin,wasu hawaye masu ɗumine suka wanke mata fuska. Sake jingina bayanta da gado ta yi ta lumshe idanuwanta,dan gaskiya ba ta so haka ba,wayarta take so dan tana son amfani da ita. 08105217201 Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 45* A kwana a tashi asarar mai rai,ga shi har an samu kimanin wata biyu da rasuwar Fauzee,kowa ya sa ki jikinsa an koma rayuwa kamar da,sai idan an yi wani abu za ka ji an ce Allah ya jiƙan Fauzee,a haka bikin Umma ya rage saura ƙwana ukku a yau ne kuma ƴan amana zasu gabatar da partynsu. Yau tun da safe Husna da duk ma wani mai hannu da tsaki a cikin group ɗin bai samu zama ba,basu nan basu chan suna ƙoƙarin ganin komai ya tafi akan tsari,cikin ikon Allah kuma sai komai yana tafiya yanda suka tsara sai dai ƴan abubuwan da ba za a rasa ba,cikin ikon Allah kuwa sai ga shi zuwa ƙarfe ukku har an gama decoration ɗin wurin. Sai da suka ga komai ya yi yanda suke so,sannan mazan suka tafi gida dan su yi wanka,idan suka dawo sai matan su tafi su ma,duk wani abu da aka tanada na ci ko sha sai da su Husna suka tabbatar ya zauna a wurinshi, ƙarfe huɗu dai-dai mai Dj yazo inda aka tanadar masa ya aje kayanshi. Huɗu da minti goma sha biyar mazan suka dawo,nan su Maryam suka bi Husna gidansu a chan zasu yi wanka(gidansu Husna yafi kusa da inda za a yi partyn,shi yasa suka kai kayansu chan.) Ko da suka je gidansu Husna basu zauna ba, Fadila ita ce ta fara shiga wankan,kafin ta fito Husna ta yi masu turaren kayan,ta na fitowa Maryam ta shiga,kaya kawai Fadila ta sanya ta zauna Husna ta fara yi mata ƙwalliya, shaf-shaf ta gama mata,ganin Maryam ba ta fito ba yasa Husna nufa toilet ɗin Mama ta shiga na ta wankan a chan,kusan a tare suka fito ita da Maryam, sallar la’asar suka fara yi sannan Maryam ta zauna ita ma,cikin ƙwarewar aiki Husna ta gama ma Maryam ƙwalliyarta. Nan fa kira ya fara shigowa wayar Husna,ganin mai kiran yasa Husna yin murmushi ta kalli su Maryam ta ce,”Mu yi sauri mu fita ga amarya chan fa na jirana.” Husna ta faɗa lokacin da ta ida ɗaura ma Maryam kallabi,Masha Allah sun yi kyau sosai,kamar jira ake Husna ta zauna gaban madubi sai ga kira ya fara shigowa wayarta. “Anty Maryam ku zo mu tafi kawai dan ba zasu kyaleni ba in ba zuwa nayi ba.” Ta faɗa tana gyara akwatin kayan ƙwalliyar,sai da ta gama maida kayan ciki sannan ta rufe. “Ke ba ki ƙwalliyar ba Husna,dan Allah ki zauna kiyi sai mu tafi.” Maryam ta faɗa tana ƙoƙarin riƙe akwatin kayan ƙwalliyar,murmushi Husna ta yi ta ce,”Anty Maryam ki bari mu tafi idan naje nayi ma amarya sai nima nayi a chan ɗin,kin ga amarya tafi ni buƙatar ƙwalliyar.” Husna ta yi maganar tare da bubbuga bayan Anty Maryam, murmushi kwance akan fuskarta. “Wai zaman me kuke a ɗaki har yanzu baku fito ba?” Muryar Mama dake tsaye bakin ƙofar ɗakin,suka tsinkaya a cikin kunnuwansu, murmushi Husna ta ƙara yi ta ce,”wai Mama dole sai nayi ƙwalliya kafin mu tafi bayan ga amarya chan na jirana.” Labulen ɗakin Mama ta riƙe ta ce,”Aa ba za a yi haka ba,ku je dai ayi ma amaryar ina fatan dai kin gama ma su Fadila ƙwalliyar?” “Na gama masu Mama.” Husna ta faɗa tare da yafa gyalenta, akwatin ta ɗauka ta fito tsakar gida,ganin haka su Maryam su ma suka biyo ta wajen,kallonsu Mama ta yi ta ce,”Masha Allah kun yi kyau sosai, Allah ya kawo mazaje na gari,ku yi sauri ku tafi har biyar saura minti goma.” “Innalillahi mun makara wallahi ƙarfe biyar da aka sanya za a fara,Anty Maryam ku yi sauri mu wuce,ina ganin kawai ku wuce wurin partyn dan ku kula da wurin,ni kuma na taho tare da amarya idan mun gam…” Kiran da ya shigo a wayarta ne ya hana ta ƙarasa maganar ta,ganin mai kiran yasa ta ɗauka tare da nufar hanyar waje,hannu kawai ta ɗaga ma su Maryam alamar sai sun haɗu chan, Ibrahim ne ke kiranta ɗagawa ta yi tare da sallama. “Amincin Allah ya tabbata a gareka masoyi.” “Tare da ke gimbiya,yau gaba ɗaya kin manta dani koh?” Ya faɗa dan ya tsokaneta, murmushi ta yi har yana jiyo sautin shi ta ce,”haba Malam yau gaba ɗaya duk muna tare shi ne za ka faɗi haka?” Shi ma dariyar ya yi,”kina ina haka naji kamar kina tafiya?” Ibrahim ya faɗa yana dariya. “Gani na fito zan tafi yi ma amarya ƙwalliya.” Ta faɗa tare da ɗagama wani mai keke napep hannu. “Okay kiyi sauri dan Allah kin ga lokaci na ƙurewa,amma ban yadda ba ke kiyi ma fuskar ki ƙwalliya ba.” Ya ƙarasa maganar shi cikin kishi,sanin abin da yake nufi yasa ta yin murmushi ta ce,”ƴallabai ban yi ba dama.” “Yauwa Tawan shi yasa nake ƙara sonki,a kullum kina girmama abin da nake so,kina ƙoƙarin kiyaye abin da bana so, Allah ya kauda idon mahassada akanmu, Allah ya tsareman ke sai kin iso.” Yana fadar haka ya datse wayarshi bai tsaya jin amsarta ba. “Hajiya ina zan kai ki?” Muryar mai keke napep ce ta daki dodon kunnenta,saurin dawowa hayyacinta ta yi nan ta faɗa masa,tare da shiga suka tafi. 08105217201 Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 46* Mintina ƙalilan suka kai su ƙofar gidansu Umma,ko da ta sallami mai keke napep gidan ta shiga,tana zuwa babu ɓata lokaci ta fara yi ma amarya ƙwalliya,sun ɗauki lokaci ana ƙwalliyar,kowa dai yasan yanda shirin amarya yake,dan haka sai biyar da minti goma sha biyar suka gama,gamawarsu babu daɗewa aka zo ɗaukarsu,ko da suka isa wurin da ake partyn har da rabi ta yi,gaskiya wurin ya ƙawatu sosai. Cikin tsari aka shiga da amarya wurin,sai da aka kai amarya kan kujerarta sannan mai dije ya saki kiɗa. Su Husna ko zama basu samu yi ba saboda yawan mutane,suna kai da komowa ganin komai ya tafi yanda aka tsara,duk wanda yazo wurin suna ƙoƙarin ganin ya ji daɗin wurin, Alhamdullih komai ya tafi dai-dai dan mutane sun yaba ƙwarai da karamcin mutanen gidan ƴan amana,ba kamar Husna da kowa ke burin haɗuwa da ita,aikuwa an yi wasa da dariya kamar ka da a rabu,saboda magana har sai da muryar Husna ta shaƙe. Su Husna basu samu natsuwa ba har sai da aka tashi,lokacin ana ta kiran sallar magrib,mutane aka fara jigilar ɗauka,sai da aka kai kowa gida lokacin ne su Husna suka fara shirin tafiya nasu gidan,lokacin har an shiga sallar isha’i, kayayyakin da aka yi amfani dasu ne suka rinƙa fiddowa,kowa na ɗaukar kayan da ya zuɓo abin da ya kawo,ganin ba a rage komai ba yasa Chairman ce wa, “Wai Husna ina namu kason ne?” Ya yi maganar yana buɗe kular da ke gabanshi,dariya kowa ya yi sannan Husna ta ce,”Malam ni ban ɗibi komai ba.” Kowa idanuwa ya zuba mata,dan sai da aka ce ta ɗiba ta aje wanda zasu ci idan an gama,ganin kallon da kowa ke mata yasa ta katse masu shirun. “Kai da har na ɗiba kuma mutane suka rinƙa zuwa babu abin da za a basu,shi yasa ni kuma na ɗauki wanda na aje na basu.” “Amma yarinyar nan kin gama damu wallahi,nan wata baƙar yunwa nake ji duk yau ban ci komai ba,nan niyyata na samu abin da kika aje mana na ci.” Dabai yai maganar yana harararta,ganin haka yasa ta yin dariya ta ce,”To su acici Mala’ikun tauna ni ban ake komai ba duka na rabar!” Kafin Dabai ya yi magana sai Abu Abdul Rahman ya rigashi,”Ustaziya dan Allah ki miƙo mana ko mun cinye mu ƙara gaba.” Kallonshi ta yi sai kawai ta kama dariya ganin yadda duk suka yi zaman ci,”wallahi ni ban rage komai ba kuma ku tambayi Anty Maryam ku ji.” Husna ta faɗa tana ƙara sakin dariya,duk maida kallonsu suka yi kan Maryam dake tsaye,ganin suna kallonta yasa Maryam ce wa,”Da gaske Husna ke yi ba a rage komai ba wallahi.” “Amma dai gaskiya kun gama damu wallahi,yanzu duk kayan da aka ci amma ace ban damu? Da nasani da tun ana ci zan karɓi nawa!” Ibrahim ya faɗa da iyakar gaskiyarshi,kallonshi Husna ta yi suna haɗa idanuwa sai ta kashe ma shi ido guda, ɗaure fuska ya yi tare da ɗauke kanshi. “Da wannan zaman da mun san abin da ya kamata kawai, wallahi yunwa nake ji kamar an sace man yan hanjina nake ji.” Sulluɓawa ya faɗa dan shi tun da aka fara maganar bai yi magana ba,kowa shiru ya yi yana tunanin abin da ya kamata,ganin babu wanda ya ce komai sai Husna ta ce,”akwai abinci gidanmu ko muje chan sai aci?” Ta ida maganar tana murmushi,dan ta san da gaske yunwar suke ji,ita kanta yunwar ke damunta dan duk yau sau ɗaya ta ci abinci,nan take suka yarda da shawararta dan ita kaɗai ce mafita a garesu,nan fa suka shiga Mota aka ta da,basu tsaya a ko ina ba sai kofar gidansu Husna,dan babu nisa sosai a tsakani,fitowa suka yi daga cikin motar gaba ɗayansu,matan suka fara shiga cikin gidan,bayan minti biyar sai ga Maryam ta fito kiransu,cikin gidan suka shiga. Falon Babansu Husna aka sauke mazan,kular abinci ce a gabansu sai ta miya,ko da suka aje ma Mazan komai da zasu buƙata sai su ka wuce ɗakin Husna inda su ma chan zasu ci abinci su, kasancewar kowa yunwa yake ji sai ba ka jin hayaniyar komai sai ƙarar cokulla. Basu bar gidansu Husna ba sai goma saura,nan fa suka yi sallama da Husna,inda aka wuce dasu Maryam dan kusan hanyarsu ɗaya. Husna na komawa gida nan fa ta tattare komai da aka ɓata, kitchen ta kai su ta wuce ɗakin Mama,nan ta zauna tana ba Mama labarin yanda komai ya gudana,sun daɗe suna tattaunawa sannan Husna ta yi ma Mama sallama ta nufi ɗakinta. Wanka ta shiga ba ta daɗe ba ta fito,rigar bacci kawai ta sanya ta hau kan gado,har ta gama addu’oin kwanciya bacci,tana shirin kwanciya sai ga kiran Ibrahim ya shigo, ɗauka ta yi tana gyara kwanciyarta, kasancewar duk a gajiye suke sai firar ba ta yi nisa ba suka yi sallama,kwanciya ta gyara babu daɗewa bacci ya ɗauketa. 08105217201 Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 48* Washe gari Husna ba ta samu damar hawa WhatsApp ba sai da marece,tana hawa kai tsaye gidan ƴan amana ta shiga,nan ta ga an yi tagging ɗinta,dubawa ta yi sai ta ga Chairman ne yake kiranta,amsawa ta yi cikin sa a kuwa yana online sai ya maido mata da amsa. “Chairman irin wannan kira haka ko ta samu ne?” Husna ta faɗa tare da amfani da emojin dariya,ko sakon goma ba a yi ba sai ga amsa Chairman ya maido mata da ita. “Lafiya lau farin cikin ƴan amana dama so nake na faɗamaki Sakwara nake son ci.” “Ba ka da matsala in dai Sakwara ce,yanzu ba mu da doya amma idan aka kawomana zan yi maka.” Husna ta faɗa tare da gyara kwanciyar ta,babu jimawa Chairman ya sake maido mata da amsa. “To shi kenan Husna dama nasan ke kaɗai ce mai mutuncin da za ta iya yi man.” Dariya Husna ta yi ta ce,”ba ruwana Chairman in dai ni ce to insha Allah za ka ci Sakwara.” “Chairman idan an yi maka Sakwarar ina ci,” Anty Maryam ta faɗa,sai yanzu Husna ta san Maryam ɗin na online. “Ha ba yarinya ba ki cinta,amma dai zan ba ki siɗin ƙwano.” Chairman ya yi maganar yana dariya,kafin ta ba shi amsa sai ga Ibrahim ya yi sallama,mamaki ya kama Husna da ma yana online amma ta ma shi magana bai amsa ta ba,dama yau ta kirashi da safe yana waya da ya gama kuma bai kirata ba,kasancewarta a busy yasa ba ta damu ba,kuma ta san in dai ya gani zai kira,dan haka da ta ga bai kira ba sai ta yi tunanin ko wani abu yake, ƙarar shigowar saƙon da Chairman ya turo ne yasa ta maido hankalinta akan chat ɗin. “Kai Sectary ya daga jin an yi maganar Sakwara har ka fito?” Chairman ya faɗa tare da yin dariya. “Zuwa ya yi domin a yammashi shi ma,kar ka damu idan aka kawo za a baka.” Maryam ta yi maganar,babu daɗewa sai ga amsa Ibrahim ya turo da ita,”A’a ni ban ci sai dai idan ke za ki yi man to zan ci.” “Kar ka damu zan maka Sakwarar mai daɗi kuwa.” Maryam ta faɗa, sosai mamaki ya kama Husna na wannan maganar da ake yi,sai ta danne ba ta ce komai ba,ganin ranta ma zai ɓaci sai kawai ta sauka daga online ɗin,amma zuciyarta fal tunanin abin da ya faru,haka dai ta share komai daga cikin zuciyarta,ba ta sake hawa ba sai wurin ƙarfe goma sha ɗaya na dare,ko da ta shiga group ɗin sai ta ga ana ta maganar Sakwara,abin ya matuƙar tsaya ma ta a rai,kyalewa kawai ta yi,har lokacin kuma Ibrahim bai kirata ba,dubawa ta yi kuma ta ganshi yana online,dan haka sai ta yi ma shi sallama,ya buɗe ya duba amma sai bai maido mata da reply ba,ganin haka sai ta kyaleshi kawai ta sauka,rufe datarta ta yi ta kwanta. Washe gari da safe wurin ƙarfe goma na safiya ta sake hawa online,ko da ta shiga gidan ƴan amana sai ta ga Chairman na ƙwalama ta kira,ko da ta duba lokacin da ya kirata ɗin sai ta ga ƙarfe ɗaya da rabi,ranta ya ɓaci sosai sai ta ce,”Akwai matsalane kake kirana tsakar dare?” Cikin sa a kuwa yana online ɗin sai ya maido mata da amsa,”lafiya lau wai Sakwarar nake maki tuni ka da ki manta.” Chairman ya faɗa. Ran Husna ya ɓaci sosai dan yanzu ta tabbatar akwai abin da ke faruwa,dan haka sai ta maida ma shi da martani. “Na fasa yin Sakwarar ka kai kuɗi ka siyo!” Husna ta faɗa ranta a ɓace,amsa ya maido mata ya ce,”a’a Husna ba mun yi haka da ke ba.” Shiru Husna ta yi ba ta ce ma shi komai ba,sai ta fara tunanin meye matsalar,nan take tunanin ko dai sun yi magana da Zarah shi ne suka ji haushi,dan haka sai ta yanke shawarar kiran Zarah,tana kira ringing ukku Zarah ta ɗauka. “Assalamu Alaikum Zarah yakike ya gida?” Husna ta faɗa a hankali,daga chan ɓangaren Zarah ta amsa mata da,”lafiya lau Husna.” “Zarah dan Allah tambayarki zan yi,kin masu Chairman maganar nan kuwa?” Husna ta yi maganar cikin sanyin murya. “Eh na kirasu na ce masu Nagode da abin da suke yi man,” Zarah ta yi maganar a hankali. “Okay! Su ya suka ce maki?” Husna ta tambayi Zarah. “Babu abin da suka ce,ni kuma na kashe wayata lafiya dai koh?” Zarah ta tambayi Husna, girgiza kai Husna ta yi tamkar Zarah na ganinta sai ta ce,”babu komai kawai dai na ga ana man wasu abubuwane wanda gaskiya ba zan jura ba.” “Wane abubuwa kenan?” Zarah ta tambaya. “Ke share kawai Zarah sai anjima nagode.” Husna tana faɗar haka ta kashe wayarta,duk da haka dai abin ya ƙi barin zuciyar Husna. 08105217201 Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 47* A haka aka gama bikin Umma,sai dai fatan zaman lafiya tsakanin ango da amarya,bayan bikin Umma da sati ɗaya aka shirya zuwa gidanta cin cin-cin da dubulan. Ranar asabar da misalin ƙarfe huɗu na marece suka je gidan,sun samu tarba mai kyau daga wurin ango,inda yai masu jagora har cikin gidan,nan dai aka gaisa cikin girmama juna,bayan gama gaisuwar nan fa aka gabatar masu da abinci, abincine mai rai da lafiya. Fried rice da Cus-cus aka dafa masu,sai farfesu naman kaza,ga haɗaɗɗen zoɓo da ka tanadar masu,nan fa suka ci suka sha. Fira aka ɗora da ita,nan fa aka shiririce basu baro gidan ba sai da aka fara kiran sallar magrib,sun yaba ƙwarai da irin tarbar da suka samu a wurin Umma,inda kowa ya taho da ledarshi cike da dubulan. A kwana a tashi a haka dai ake ta gudanar da rayuwar,yau fari gobe baƙi,a wannan tsakanin abubuwa da yawa sun faru ciki kuwa harda sabbin mutanen da aka kawo gidan ƴan amana,bayan waɗanda aka yi ma aure,dan bayan bikin Umma sai da aka yi bikin mutum biyu,Asiya da Zulaihat kuma duk sai da ƴan amana suka haɗa masu party ga bikinsu. Ana haka wayar Husna ta samu matsala,dan haka ta daina chat har lokacin kuma idan wani abu ya faru a gidan ƴan amana tana zuwa,cikin wannan lokacin ne aka sanya bikinta da Ibrahim,sa bikin da ya girgiza mutane dan basu yi tsammanin soyayyar gaske ake yi ba,duk dai an ɗauka iyakarta cikin gidan ƴan amana. Nan fa mutane suka rinƙa fitowa suna nuna murnarsu,wasu kuma baƙin cikine fal ransu,sanya bikin da sati guda aka yi Asharalle, ƴan amana sun nuna ba jinta sosai a wannan wurin,dan su zuba kuɗi kamar ba gobe,a nan ne Husna ta ga baƙin fuskokin da aka sanya bayan daina chat ɗinta (har lokacin ba ta koma yin chat ba). Yin Asharalle da ƙwana biyu matar Sulluɓawa ta haihu,ranar suna daga islamiyya Chairman ya ɗauki Husna suka tafi,akan hanya aka biya aka ɗauki wata sabuwar member mai suna Zarah,nan suka rinƙa fira da Husna kamar ba yau ce ranar da suka fara haɗuwa ba. Su Maryam aka biya aka ɗauka,nan fa Husna ta ɗan lura da Maryam ta chanza mata, Husna ba ta kawo komai a ranta ba,ko da ta tambayi Maryam lafiya sai ta ce mata bata jin daɗine,dan haka sai ta yi mata addu’ar samun lafiya,amma abin da ya ba Husna mamaki sai ta ga lafiya lau take magana da sauran mutane,sai ta kyale kawai dan ta yadda akan Maryam ba ta da lafiyar. Akan hanyarsu ta dawowane ana fira nan Husna ta ji ashe Chairman da Zarah har soyayya suka yi,amma yanzu sun rabu,bayan an sauke Maryam a gidansu ne Zarah ke ba Husna labarin abin da ya haɗasu,sai Zarah ta ce Husna ta yi masu Shari’a, Chairman ma ya yarda da wannan abun da Zarah ta yi,ita kuma Husna nan fa duk inda taji mutum ya yi ba dai-dai sai ta faɗa masa,basu rabu ba har sai da Husna ta maida wannan soyayyar. Nan fa Zarah da Husna suka zama ƙawaye, Chairman ya ji daɗin wannan sulhu da Husna ta yi masu sosai,nan suka koma soyayya shi da Zarah, kasancewar shi da Zarah duk basu da haƙuri sai kuma suka sake samun saɓani fiye da na farkon. Wata rana yaron Abu Abdul Rahman bai da lafiya zasu je ganinshi,akan hanya nan take jin labarin rabuwar a bakin Chairman da Maryam,inda Maryam ke faɗin akan wannan saɓanin Zarah sai zarya take a gidansu wai ta sasanta su,shi kuma Chairman na faɗin Zarah ba ta da kamun kai duk ta liƙe ma shi,ko da Husna ta ji maganar ta yi yawa sai take nuna masu hakan bai dace ba su daina,ba a shiga faɗan masoya nan fa Maryam ta ɗaure fuska, Husna ba ta damu ba saboda zuwa yanzu ta saba da chanjin da Maryam ke nuna mata,ta yi tambayar akan abin da ya faru kuma har ta gaji,nan Chairman ke faɗar da gaske Zarah ta liƙe ma shi,sai Husna ta ce,”aikuwa Chairman da zan ba Zarah shawara ta ji da nace ta rabu da kai!” Dan Husna ta ji haushin yanda ake muzanta Zarah a cikin mutane,duk da ba a gabanta bane amma dai kowa ya san Zarah. “Da kuwa har kyauta sai nayi maki.” Chairman ya faɗa dan bai yi tunanin Husna da gaske za ta iya gayama Zarah ba. “Insha Allah kuwa sai na faɗa mata.” Husna ta faɗa cikin jin haushi,Ahaka aka yi wannan tafiyar dai babu daɗi. Bayan wasu kwanaki Ibrahim ya sai ma Husna waya,dan haka ta koma yin chat,wata rana da daddare sai ga Zarah ta yi ma Husna sallama,nan suka gaisa tare da tambayar bayan saduwa,nan ne Zarah ke faɗama Husna ai sun rabu da Chairman, Husna ba ta nuna ta san sun rabun ba sai ta yi mata jaje,nan Zarah ke nuna mata Chairman sai bibiyarta yake yi,sai Husna ta ce,”Zarah da zan ba ki shawara ki ji da nace ki rabu da Abba,tun da dai tarayyar ku ta ƙi yiwuwa.” Sai Zarah take ce wa,”Husna ai na rabu da Chairman shi ne dai ya liƙeman kullum sai ya man magana.” “Zarah wannan rayuwar ba ta yiwuwa a haka,an rasa gane mai gaskiya a tsakaninku,shi ya ce ke kike liƙe ma shi ke kuma kin ce shi yake liƙe maki.” Husna ta faɗa dan ita Husna ba ruwanta da ɓoye-ɓoye,kai tsaye take abu. “Wallahi ƙarya ne amma ke waya faɗa maki?” Zarah ta tambayi Husna, Husna kuma ta amsa mata da Chairman ya faɗa,kuma da gaske yake tun da har gidansu Maryam Zarar na zuwa akan ta sasanta su. “Na shiga ukku ƙarya ne wallahi ban taɓa yi ma kowa magana ba akan tsakanina da Chairman ba,Amma sai nayi masu magana dan ƙarya suke man.” Zarah ta faɗa dan dagaske ba ta taɓa zuwa gidansu Maryam ba,ita kuma Husna ta ce,”to shi kenan kina iya yi masu maganar dan ni dai su suka faɗaman.” “Zan kuwa yi masu Nagode.” Zarah ta faɗa. “Bakomi Zarah ke dai idan ma kina liƙe ma shin ki daina,saboda ke macece kuma Mace da kunya aka santa.” Husna ta faɗa,nan suka yi sallama ita da Zarah. 08105217201 Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 49* Da daddare wurin ƙarfe goma Husna na chat,kawai sai ta ga Chairman ya kira sunanta a gidan ƴan amana,shiga ta yi tare da amsawa sai ya ce mata,”Husna wai ina Sakwara ta ne?” Ran Husna ya kai kololuwar ɓaci ta ce,”Chairman ban yi ka je ka kai kuɗinka ka siya mana ka fa dameni!” “Ke fa ba ki da kunya wallahi Husna,” Chairman ya faɗa,a wannan lokacin ita ma Husna ranta a ɓace yake sai ta ce,”eh ba kai ƙarya ba,ban san kunya ba amma idan kaje kasuwa sai ka siyoman!” “Aikuwa yanzu za ki ji ta in dai kunya ce,” Chairman ya faɗa, Husna ba ta yi sanya ba wurin maida ma shi da martani ba dan haka sai ta ce,”insha Allah babu kunyar da zan ji dan ban aikata abin jin kunyar ba.” “Ibrahim, Maryam, Husna ku fito ina da tambaya,menene hukuncin maci amana? Mu ci gaba da zama da shi ko mu koreshi?” Chairman ya faɗa,kafin kowa ya yi magana sai Husna ta riga ba shi amsa ta ce,”in dai an tabbatar da cin amana ya yi tabbas zama da shi bai da amfani!” “Yauwa yanzu kuwa kowa zai ga maciya amanar gidan nan,dan haka muna ba kowa haƙuri dan mun san zamu ɓata ma wani rai,” Chairman ya faɗa,sai Husna ta ce,”amma koma waye idan aka gabatar da shi ya kamata a ba shi ikon kare kanshi.” “Wannan maciya amana,macijiya ba kowa ba ce face Husna tsohuwar PRO ta gidan ƴan amana,ba mu yi wannan abun da niyyar ƙage ba har sai da muka tabbatar ta hanyar manyan hujjoji,duk wanda yake so ya tabbatar kuma zai iya tuntubar Maryam Ɗan Ali.” Wannan shi ne doguwar wasiƙar da Anty Maryam ta turo,wata irin faɗuwar gaba ce ta riski Husna,ku san sakin wayarta ta yi tare da salati mai ƙarfi,ko ina na jikinta rawa yake,magana take so ta yi amma ta gagara yin typing ɗin,dan dole ta danna voice da muryarta dake cike da tashin hankali. “Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un…Allahumma ajirni fi…musibati wa’akalibni khairan minha…me na aikata da zafi da na chanchanci a jefeni da wannan miyagun kalmomin?” Husna ta yi maganar cikin tsantsan tashin hankali,kafin ta sake yin wata maganar sai ta ga record ɗin Chairman ya shigo,dan haka sai ta duba ga abin da ya ce,”ba mu da lokacin sauraren duk wasu kalamai naki na borin kunya,yanzu zamu fitar da ke dan yanzu ba ki da gurbin zama a cikin gidan nan, Husna ko lahira ban fatan Allah ya sake haɗa mu dake,nayi danasanin saninki a rayuwata.” Kafin ta ba shi amsa har an yi removing ɗinta daga gidan ƴan amana,zuwa wannan lokacin hawaye sun daɗe suna zarya akan fuskarta, babban tashin hankalinta shi ne akwai mutanen dake ganinta da mutunci sosai amma ta san ya zuwa yanzu mutuncinta ya daɗe da zubewa a fuskarsu,sai tunani take na son lalabo laifin da ta aikata,ita dai ta san babu wani abu da ta yi idan ma akwai to bai wuce magana da Zarah ba,idan kuma wannan ce ai ya kamata a bata dama domin ta kare kanta,kuka take har da shessheka,wata dubara ce ta faɗo mata a rai,cikin sauri ta danna kiran Chairman amma har sau biyar bai ɗaga ba,kuma tana ganinshi a online ɗin,nan fa ta bi Anty Maryam private tana tambayarta abin da ta aikata,sai Maryam ta ce,” Husna kin ci amanarmu,kin sanyani cikin tashin hankalin da ban taɓa shiga cikin shi ba,nayi kuka sosai amma babu abin da zan ce maki sai kije Allah ya isa!” “Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!! Dan Allah Anty Maryam ki faɗaman me na aikata maku da zafi haka?” Husna ta faɗa wasu sabbin hawaye na sake kwaranya akan fuskarta, Maryam ta sake maido mata amsa da cewa,”har ma kina da bakin tambayata? To bari na turomaki sai ki gani.” Nan Maryam ta turomata da screen shot ɗin chat ɗinsu da Zarah,har ma da wayar da suka yi da marece,amma abin da ya bata mamaki shi ne yanda babu maganar Zarah sai maganarta kawai,nan fa hankalinta ya ƙara tashi,nan mutane suka rinƙa yi mata magana akan ba za su yarda ba sai sun bi mata haƙƙinta,zuwa wannan lokacin Husna wani ciwon kai mai tsanani ya dirar mata, hankalinta bai ƙara tashi ba sai da aka turo mata screen shot ɗin maganganun da mutane suka yi bayan fitarta,nan ta ga wasu na nuna rashin amincewa akan abin da aka mata,wasu kuma na ba da goyon baya,babban abin da ya ƙara ta da mata da hankali sai mummunan raddin da Ibrahim ya yi,kuka Husna ta yi shi a wannan daren har hawayenta suka ƙafe,yanda ta ga dare haka ta ga rana,duk da ƙoƙarin Abdul Dabai da Abdul Mai kasuwa,da wasu daga cikin ƴan group ɗin,ta ga ƙauna sosai a wannan daren har ma da wurin mutanen da ba ta magana dasu a cikin gidan,amma suna bayanta tunda duk maganar da aka yi a group suna turo mata ta san duk abin da ke faruwa,ta yi mamaki sosai yanda har wannan lokacin Ibrahim bai mata magana ba. 08105217201 Hussy Saniey.???? *RASHIN ADALCI 2021* *NA* *HUSSY SANIEY* *____________________________________* *????????AINUWA ????RITER’S✍????* *????SSOCIATION????????* “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???????? https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association *____________________________________* *PAGE 50* Lokacin da gari ya waye, Husna ko idanuwanta ba ta iya buɗewa saboda tsabar kukan da ta sha,ga kanta na wani irin yi mata a zaɓaɓɓen ciwo,rikicine mai yawa ya tashi a gidan ƴan amana dan sun nuna basu yarda ba akan hukuncin da aka yanke ma Husna ba. In da su kuma offials ɗin suka yi shiru suka kyale kowa,ganin hakan bai hana members magana ba dole suka sanya admins suka rufe gidan,wurin ƙarfe goma na safe dole aka sada Husna asibiti saboda yanda numfashinta ke sarƙewa, hankalin ahalinta ya tashi sosai dan likita ya sanar dasu damuwace tai mata yawa,nan aka tsare Husna akan ta faɗi abin da ke damunta amma sai ta nuna ita ba ta da damuwar komai,dole ba dan an so ba aka kyaleta. A haka Husna ta gama jinyar jikinta a gadon asibiti,ko a lokacin damuwa ce fal ranta,tana daurewane saboda iyayenta,saboda zuwan wasu daga cikin gidan ƴan amana ganinta shi ne ya hana a gane matsalata samu dasu,har lokacin kuma Ibrahim bai kirata ba,sai a bakin Dabai ne take jin wai Ibrahim soyayya suke shi da Maryam, wannan labarin sai da ya kusa maida Husna akan gadon asibiti,bayan ƙwana biyu da jin wannan maganar, Ibrahim ya turo mata da saƙon fasa bikinsu,in da yake sanar da ita ya yafe duk kayan da aka kawo. Nan fa hankalin Husna yai mummunan tashi,ta shiga damuwa sosai wanda kallo ɗaya za kai mata ka tausaya mata,ko magana sai dole take yin ta,ita har gobe ta rasa gane dalilin da yasa suka aikata mata haka,in akan maganar da suka yi da Zarah ne ai da amincewar Chairman ta yi ma Zarah magana,iyayen Husna sun tsareta akan ta sanar dasu abin da ya haɗata da Ibrahim amsa ɗaya take basu shi ne ba ta sani ba,shi ma ko da aka tuntuɓeshi sai ya ce ba komai,jin haka yasa iyayen Husna hassala suka kyaleshi. A haka Husna ta ɗauki komai ta fauwalama Allah,har lokacin kullum sai ta yi kuka dan ita dai ba ta ga abin da ta aikata ba,wata rana suna magana da Dabai nan take fadamasa ita fa sai ta gano dalilin da yasa suka aikata mata haka,nan yake ɗaukar mata alƙawari akan sai ya gano mata koma miye,bayan ƙwana biyar da yin maganarsu sai ga shi kuwa ya gano dalilin,ashe saboda Maryam na son Ibrahim shi yasa ita da Chairman suka aikata haka dan su raba Husna da Ibrahim ɗin, girgiza kai kawai Husna ta yi ba ta sake cewa komai ba,sai dai cikin ranta take ce wa,”da sun sani da basu zubar man da mutuncina ba,amma bakomi akwai Allah.” Wannan fitar da Husna da aka yi daga cikin gidan ƴan amana,sai mutane da yawa suka fita daga gidan dan zuwa yanzu kowa yasan dalilin Chairman da Maryam na aikata ma Husna haka,rayukan mutane ya ɓaci sosai dan haka su kai ta fita, waɗanda suka zauna kuma sai suka daina magana,ganin haka yasa Chairman ya sanya offials suka kawo masu sabbin members,haka kuwa aka yi nan aka cika gidan da mutane masu yawa. Bayan wata huɗu,komai ya faru a wannan watannin a gidan ƴan amana,ciki kuwa har da rabuwar soyayyar Maryam da Ibrahim,in da sabbin members ɗin da suka kawo basu magana,nan fa suka ciresu aka sake sabon zubi,nan ma dai ƴar gidan jiyan,dan haka suka yanke shawarar maido tsaffin members ɗin gidan,dan haka suka shirya zuwa har gida suna ba tsaffin members haƙuri,ko da suka zo gidansu Husna sun ba ta haƙuri sosai har sai da zuciyarta ta yi sanyi,in da ta amince za ta koma gidan,amma cikin ranta ta yi niyyar sake fita,haka dai aka maida Husna cikin gidan ƴan amana,amma tamkar babu ita cikin gidan saboda ba ta magana ko kaɗan,nan aka sake yi mata magana akan rashin maganarta,nan take sanar dasu za ta ci-gaba,haka kuwa aka yi ta kan yi sallama har ma wani lokaci ta ɗan yi labari da wanda ke kusa,har lokacin kuma basu magana da Ibrahim da Maryam amma idan ta yi sallama suna amsawa,komawarta da sati biyu ta sake barin gidan saboda zamanta na tuna mata da abubuwan da suka faru,har yanzu ta kasa manta yanda abubuwan suka kasance,duk lokacin da ta kallesu tana jin zafi a ranta,dan haka ta fita daga gidan, wannan fitar da ta yi ce fa, Chairman ya bi ta yake bata haƙuri da sanar da ita ba laifinshi bane,kuma ya aikata hakan ne saboda Maryam amma ta yi haƙuri,nan ta nuna ma shi babu komai,amma dai gaskiya ba za ta sake zama a gidan ba,ta dai masu alƙawari duk in za su yi wata hidima aka gayyaceta za ta je,ba dan sun so ba kuwa suka amince. Bayan wasu watanni aka tashi bikin wata A’isha,nan ƴan amana suka gayyaci Husna zuwa bikin babu musu kuwa ta amince,har gida aka zo aka ɗauketa,ko da zuwansu kuwa irin mutanen da ta gani cikin gidan ƴan amana sai da ta yi hawaye,saboda gidan ya lalace duk ƴan bariki aka tara cikin gidan,iskanci dai kala-kala ake yi a gidan yanzu,sai dai kawai ta bisu da addu’ar shiriya, Wata uku da zuwanta bikin kuma aka yi bikinta, ƴan amana sun zo har suka kawo mata kyauta,amma dai duk wanda ya sansu a da ya ga ƴan group ɗin a yanzu sai ya yi hawaye,saboda babu mutanen kirki sosai a gidan,duk wanda Husna ta sani a gidan yanzu babu shi a ciki,daga Chairman sai Maryam kaɗai ne a cikin tsaffin members ɗin gidan,ita kanta Maryam ɗin ta yi laushi sosai,tun tana kunyar haɗa ido da Husna har dai ta saki jikinta saboda yanda Husna ke janta a jiki,bayan mutane sun watsene Maryam ta samu kebewa da Husna,nan take roƙon Husna gafara akan abubuwan da ta aikata mata,nan Husna ke nuna mata ba komi ai Bawa bai wuce ƙaddararsa,kuma Ibrahim Allah ya rubuta da ma ba mijinta bane,ga shi yanzu ta samu wani har ta yi aurenta,ita ma yana mata addu’ar Allah ya kawo mata miji ta yi aurenta,kuka Maryam ta fashe da shi tare da yi ma Husna godiya,shiru Husna ta yi bayan tafiyar Maryam,babu abin da take tunani sai abubuwan da suka faru a baya,amma ita dai babu abin da za ta ce da Allah sai godiya. TAMMAT BI HAMDILILLAHI!!! Post navigation [ad_2]