HAUSA NOVELRASHIN ADALCI Complete Hausa

RASHIN ADALCI Complete Hausa

“Mu yi sauri gaskiya ni Allah so nake naje gida da wuri akwai inda zanje”,inji Mieynart.

“Kun tsaya kuna ta surutu da yanzu mun yi nisa a tafiyar mu”,inji Sadam

Jerawa su kayi gaba ɗayansu su na tafiya,fira suke yi nan Husna ke sanar dasu yadda su kayi da ƴan group ɗin su,cikin sigar jan faɗa Sadam ya kalli Husna ya ce,”gaskiya Husna ƴan group ɗinku su na da kirki”.

Cikin jin daɗin yabon da aka masu ta ce,”dan ma ba ka cikin group ɗin Allah da sai kaji kamar ai ta zama idan ana fira”.

“Gaskiya Husna har naji ina son shiga group ɗin nan saboda na ga wacce wainar ake toyawa”,inji Sadam.

Cikin matsanancin jin daɗi Husna ta dakata da tafiyar da take ta ce,”dagaske kana son shiga na bada lambar wayarka a sanya ka a group ɗin”.

Murmushi Sadam ya yi saboda ganin yadda Husna ta ɗauki maganar da muhimmanci ya ce,”wasa nake maki Husna kin san ni bana son shiga cikin kowane group saboda matsalolin da ke faruwa a ciki”.

Tun kafin ya ƙarasa maganarshi Husna ke girgiza kai sannan ta ce,”wallahi su ba haka suke ba duk wanda ya zauna dasu zai so gobe ma ya zauna dasu su na da mutunci sosai Babban daɗin guda kuma shine sun san darajar mutane ban taɓa ganin sun wulaƙanta wani ba dan haka in dai kana son shiga wallahi na bada lambarka kawai idan aka sanya ka sai kaji daɗin zama dasu fiye ma da yadda nake faɗa maka”.

Dariya Sadam ya yi sannan ya ce,”kar ki damu Husna tun da kina ciki ai zan rinƙa jin labarin su hakan ma yana sanyani nishaɗi aminiyar”,ya juya wurin Mieynart da ke ta faman ɓoye dariyarta dan ka da Husna ta gani amma ka sa ɓoyuwa dariyar ta yi har sai da ta saketa a fili.

Harararta Husna ta yi ta ce,”kin dai ji haushin gulma wallahi yanzu meye abin dariya anan toh?”.
Girgiza kai Mieynart ta yi tare da haɗiye dariyar da take yi sannan ta harari Husna ta ce,”dan kin ga ina dariya shikenan kuma babu da wanda nake sai ke kenan ko Hajiyata?”.

Bugu Husna ta kai ma Mieynart ta ce,”idan ba dani kike ba to da wa kike nan in ba ni dake magana ba kuma ai nasan akan me kike man dariya banza ai ban ce ki bada lambarki a sanya ki ba bare ki kama yi man wannan banzar dariyar ta ki”, Husna ta ƙarasa faɗa a hassale.

Ganin yadda Husna ta hassala ya sanya Mieynart ta haɗiye dariyarta lokaci guda,matsowa ta yi kusa da Husna sannan ta da fa ma Husna kafaɗa ta ce,”meye abin fushi kuma Ƙawata daga magana amma tunda ba ki so shikenan na yi shiru”.

Sadam ma matsowa ya yi inda suke shima tare da ƙoƙarin haɗiye ta shi dariyar ya ce,”gaskiya Mieynart ba ki kyauta ba meye abin dariya nan bayan ma ba dake ake maganar ba dan dai k…”,saurin dakatawa da maganar shi ya yi saboda wata dariya da ta taho ma shi ya yi,dan lura da yadda Husna ke ta ƙara murtuke fuska.

“Nagode maku sosai ni dai ku ka maida mahaukaciyar ƙarfi da yaji ko dan kun ga ina baku labari shine har abin ya zama abin tsokana ko bakomi nagaode laifinane da nake gayamaku duk wani abu da ya danganceni”,ta ida faɗar maganar a matuƙar hassale.

Jinin jikinsu su ka sha saboda ganin yadda take maganar acikin fushi,dan haka sai suka koma bata haƙuri,ko saurarensu Husna ba ta yi ba ta cigaba da tafiya.

Bayanta su ka biyo babu mai magana a tsakanin su saboda ganin yadda Husna ta hassala,nan wurin Bus stop su ka tsaya dan jiran Bus.

 

*Hussy Saniey*.????
*____________________________________*

*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*RASHIN ADALCI 2021*

 

*NA*

*HUSSY SANIEY*

PAGE 6

Shiru zaman ya kasance a tsakaninsu,babu wanda ke da ƙwarin guiwar yin wata fira,zaman minti goma sai ga Bus ta zo,su na shiga cikin Bus ɗin Husna ta chanza kujerar zama,da kallo su ka bi ta dashi saboda abin da bai taɓa faruwa a tsakaninsu ba,duk rintsi wuri ɗaya suke zama amma yau ga shi Husna ta raba masu wurin zama.
Husna na kallon yadda su ke bin ta da kallo, ɗauke kanta ta yi kamar ba ta san suna yi ba,a haka tafiyar ta kasance babu daɗi,kowa da abin da yake saƙawa a cikin zuciyarsa.
Ko da aka zo inda suke sauka,Bus na tsayawa Husna ce farkon fita,bayanta su Mieynart suka bi,lokacin da suka fito har ta tsaida Keke napep.
Ji ta yi an riƙe mata Abaya ta baya,juyowa ta yi suka haɗa idanuwa da Mieynart,ɗaure fuska Husna ta ƙara yi ta ce,”sakeni zan wuce!”

Murmushi Mieynart ta yi,”Husna ban taɓa ganin haka a wurinki ba saboda haka kiyi haƙuri hakan bazata ƙara faruwa ba insha Allah.”
Girgiza kai Husna ta yi ta ce,”bakomi ya wuce sai Allah ya kaimu gobe.”
Kafin Mieynart ta ce wani abu har Husna ta shige cikin keke napep ɗin,ta na shiga mai keke napep yaja suka tafi,sai da suka ɓace sannan Mieynart ta kalli Sadam ta ce,”tun da nake da Husna ba ta taɓa nunaman taji haushin abu ba irin yau,gsky bansan wannan wace irin ƙauna ba ce take ma waɗannan bayin Allah ba.”
Cikin mamaki Sadam ya ce,”ni kaina abin nan ya matuƙar ɗaure man kai,wai Husna ce ta iya nuna mana ɓacin ranta saboda mun kushe wasu!”
Mieynart ta riƙe haba ta ce,”abin da yafi ɗaure man kan kenan,fatana dai Allah ya sanya yadda take son su haka su ma suke mata irin wannan son.”
Gyara tsayuwa Sadam ya yi tare da ɗaga ma wani mai mashin hannu,duban shi ya maido ga Mieynart ya ce,”ameen dan gaskiya abin ya ban mamaki sosai.”
Tsayuwar mai mashin gabansu shi ya hana Mieynart magana, Sadam ya kalli Mieynart dake tsaye amma da gani kasan ba ta cikin yanayi mai daɗi ya ce,”Mieynart idan naje gida zamu yi waya akan wannan case ɗin kar ki damu kinji koh?”
Numfashi Mieynart ta sauke ta ce,”Sadam dagaske hankali na ya tashi saboda Husna duk yadda kake ganinta ba ta da haƙuri to wallahi ta na da kawaici ba abu kaɗan ke sanyawa ta nuna ɓacin ranta ba.”
Hawan mashin Sadam ya yi sai da ya zauna sosai sannan ya ce,”kar ki damu Mieynart zamu yi magana idan na koma gida ai dole mu tabbatar Husna ta sauko daga fushin nan saboda wallahi yau ban ji daɗin yadda muka rabu ba.”
Gyara riƙon jikka Mieynart ta yi ta ce,”nima abin da yafi ɗaga man hankali kenan amma insha Allah idan ta kama har gida zan taddata sai na bata haƙurin kaje idan mun koma mun yi waya sai anjima Allah ya kiyaye hanya.”
Littafin da ke hannun shi ya ɗora bisa cinya,ya kalli Mieynart ya ce,”ki bari idan naje gidan duk yadda ta kama sai ayi kawai kinji kin ga napep chan kije ki hau ki gaida Mama.”
Bayan wucewar Sadam babu daɗewa ta samu Keke napep,ta tafi gidansu lokacin har an kusa fara kiran sallar magrib.
**************
Husna na isa ƙofar gidansu,mai Keke napep ɗin ta sallama sannan ta shiga cikin gidansu,da sallama ta shiga,Mama na zaune ta na ɗaurin kunun Aya,kallo ɗaya Mama ta yi ma Husna ta san akwai matsala a tattare da Husnar.
Ganin irin kallon da Mama ke bin ta da shi ya sanya Husna washe baki ta ce,”Mama sannu da aiki na dawo.”
Cikin kallon tuhuma Mama ta ce,”yauwa lafiyar ki ƙlau kuwa Husna! kin ga yadda kika yi?”
Cikin ƙoƙarin ɓoye damuwarta, Husna ta yafa ma fuskarta murmushin ƙarfin hali ta ce,”lafiya lau nake Mama kawai tsabar gajiyace kawai ta maidani haka kamar marar lafiya amma lafiya lau nake babu wani abu Mama.”
Ba dan Mama ta yadda ba ta ce,”ki je ki ɗan watsa ruwa ki zo ki ci abinci nasan dai kina jin yunwa?”
Murmushi Husna ta ɗan yi duk don son ɓoye damuwarta ta ce,”zan dai watsa ruwa Mama amma ba na jin yunwa na ci abinci a makaranta Mieynart ta zo mana da shi.”
Kallonta kawai Mama ta tsaya tana yi saboda zai yi wuya Husna ta dawo daga makaranta ba ta ci abinci ba,wani lokacin har janta ake ace an manta ba’a aje mata abincin ba,ganin irin kallon da Mama ke bin ta da shi ya sanya kawai ta shige ɗaki,dan tsab Mama na iya gano abin da take ƙoƙarin ɓoyewa,kuma ko kaɗan bata san hakan ta kasance.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button