HAUSA NOVELRASHIN ADALCI Complete Hausa

RASHIN ADALCI Complete Hausa

Murmushi Mama ta yi cikin ranta ta na ƙara jinjina irin wannan soyayya da ƴarta ke ma waɗannan mutane,duk abin da ya dangancesu ta na ba shi muhimmanci sosai,dama ta yi mamakin abin da ya fiddo Husna yanzu dan haka ta ce,”ai muna da fulawa da mai a gidan nan kuma jiya an kawo suga dan haka idan dai fulawar tiya ukku za ta isheku sai ki ɗiba kawai.”

Cikin farin cikin da ya kasa ɓoyuwa ta ce,”Nagode kwarai Mama Allah yasa ka da mafificin alkhairi Allah ya ƙara buɗi na alkhairi.”
“Ameen ya Allah sai ki tashi kije ki kwanta ko yau ba ki komawa baccin?”Mama ta faɗa tare da miƙewa tsaye ta na linke sallaya.
“Zan koma Mama anjima Maryam da Fadila za su zo tare zamu yi aikin dasu,”Husna dake miƙewa tsaye ta faɗa ta na kallon Mama.
“To shi ke nan Allah ya kawosu lafiya,”daga haka Mama ta nufi wadrop ta saka sallaya.

Ganin haka yasa Husna fita ta koma ɗakinta wayarta da ke kan gado ta ɗauka,kira biyar ta gani ta na dubawa ta ga Iro ne,dama ta yi tunanin shine saboda yau bai tada ita sallah ba(haka suke yi cikinsu duk wanda ya riga tashi shi ke tada ɗaya).
Murmushi ta yi cikin ranta ta ce yau akwai chakwakiya kenan tsakanin ta da Iro.

 

Hussy Saniey.????
*RASHIN ADALCI 2021*

*NA*

*HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*PAGE 14*

Kira ta danna masa bugu ɗaya ya ɗauka,ko sallamar da take bai amsa ba ya fara tambayar ta,”lafiya kike?ina kika shigane ina ta kira ba ki ɗagaba fatan dai kina lafiya?” Ya ƙarasa faɗa cikin alamun damuwa.

Wani ƙasaitaccen murmushi ta ƙawata fuskarta da shi sannan ta ce,”kai Sweet Irona irin wannan ruɗewa haka…?”
“Malama ki amsa man tambaya!…”ya faɗa cikin fushi.
Dariya ta sa ki cikin jin daɗi ta ce,”kwantar da hankalinka babu abin da ke damuna kuma bani da wata matsala,naje ɗakin Mamane na bar wayata nan ɗakina.”

Wata wawuyar ajiyar zuciya Ibrahim ya saki,wadda har sai da Husna na jiyota,cikin shan mur tamkar wanda yake a gabanta ya ce,
“Amma wannan wane irin zamane kika yi a chan daga zuwa ki gaisheta sai ki nemi wuri kiyi zaune ko aiki ta sanyaki?”

Dariya Husna ta yi wadda har sai da ya jiyo sautin dariyar sannan ta ce,”A’a na tsaya mun yi maganar fanken da za’a yi idan anjima a kai gidan rasuwa…”

“Ke aka sanya kiyi fanken?” Bai bari ta ƙarasa faɗar maganarta ba ya jefa mata tambayar da ta sanyata yin shiru.
“Eh mun yi magana da Abba jiya bayan mun gama waya da kai,” ta faɗa cikin sanyin murya.
“Amma kin san ke za kiyi fanken har muka gama waya baki sanar dani ba!” Ya faɗa cikin alamun fushi.

Kwantar da muryarta ta yi fiye da farko ta ce,”Sweet Iro na faɗa maka sai bayan mun gama waya da kai sannan mu kayi magana da Abba.”
“To yaushe ya kawo maki kayan yin fanken ko sai anjima?” Yana faɗin haka ya yi shiru yana jiran amsar da za ta ba shi.

“A’a ya ce nayi daga baya za’a ban kuɗin saboda yanzu asusu babu kuɗi, kuma lokaci ya ƙure ba’a yi maganar nawa zamu haɗa ba sai daga baya za’a yi maganar,”ta faɗa cikin sanyin murya.

“Ke ina kika samu kuɗin da za kiyi hidimar dasu bayan ko jiya ba ki da kuɗi?” Ya faɗa cikin sauri.
“Abin da yasa naje wurin Mama kenan dan ta araman to sai kuma ma ta ce a ɗebi kayan gida ayi dasu ba sai an siyo ba kuma a bar kuɗin,”Husna ta faɗa.

“Banganeba wane kayan gidan za’a ɗiba?” Ibrahim ya tambayi Husna.
“Kai Sweet Iro kamar ba da Hausa nake maka bayani ba? Muna da fulawa da Mai sai suger shine Mama ta ce a ɗiba ayi kawai,”Husna ta faɗa cikin shagwaɓa.
“Yanzu ke wannan hidimar kika ɗora masu ba ki san yanayin da ake ciki ba?”Ibrahim ya faɗa.
“Kai Sweet Irona ita fa ta ce a ɗiba wallahi ni bance mata ta bamu ba,rancen kuɗi kaɗai naje ta ban,”Husna ta faɗa tare da kishingiɗawa jikin katakon gado.

“Allah ya so ki yarinya bake kika tambayeta ba da jikinki ya faɗa maku,”Ibrahim ya faɗa.
“Naji dai tun da ban aikata ba sai a bi wani sarkin ba dai ni ba,”Husna ta faɗa ta na dariya.
“To zan kwanta ban daɗe da dawowa daga masallaci ba,ke ɗaya za kiyi fanken ko har dasu Maryam?” Ibrahim ya tambayi Husna.

“Eh ni da Maryam da Fadilane amma sai wurin ƙarfe sha biyu saboda mu gama da wuri,”Husna ta faɗa.
“To shi kenan sai anjima ki kular man da kanki,”yana faɗin haka ya kashe wayarshi.

Kallon wayar Husna ta yi ta na murmushi cikin ranta ta ce sweet Iro ba dai rigima ba,Allah ya barmu tare ta faɗa tare da kwanciya domin ita ma baccin take ji,aikuwa ta na kwanciya babu daɗewa bacci ya dauketa.

Hussy Saniey.????
*RASHIN ADALCI 2021*

*NA*

*HUSSY SANIEY*

*____________________________________*

*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*????????

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

 

*PAGE 15*

Sai wurin ƙarfe tara da ƴan mintuna sannan Husna ta tashi daga bacci,ta na tashi sharar ɗakinta ta fara yi sannan ta fito tsakar gida,sai da ta sharo ɗakin Mama sannan ta sharo wani ɗaki sai ta haɗa da tsakar gidan.

Ta na ida sharar kayan wanke-wanke ta haɗa ta wanke,ta na gama wanke-wanke wanka ta shiga,ba ta daɗe a wurin wankan ba ta fito,yau jin ta take yi cikin walwala da annabawa,babu abin da ke mata daɗi a rai sai idan ta tuna yau za ta ga mutanen gidan ƴan amana,duk cikin gidan mutum huɗu ta sani a fuska daga Maryam, Ibrahim, Umar Sulluɓawa sai Abba.

Kallo ɗaya za kai mata ka ga tarin farin cikin da take ciki,ko ayyukan ma yau cikin karsashi take gudanar dashi,shi ya sa ko Lokaci mai tsawo ba ta ɗauka ba ta kammala,ta na fitowa daga wanka doguwar riga kawai ta sanya.

Ƙafafuwanta kawai ta shafa ma mai sai turare da ta fesa, kitchen ta shiga flaks ɗin ruwan zafi ta buɗe ta zuba dai-dai cikinta sannan ta rufe,wurin da kayan tea suke aje taje ta haɗa bread dake aje gefe da alama na ta ne ta ɗauka.

Ɗakinta ta dawo ta zauna,ta na kalacin ta na tunanin yadda za ta haɗu da mutanen da take tsananin so a rayuwarta,da haka har ta kammala kalacin ta ɗauraye kayan da ta ɓata sannan ta maida komai inda yake.

Agogo ta kalla ganin har sha ɗaya da rabi ya sanyata nufar store ɗinsu,fulawa ta auno tiya ukku cikin wata Babbar roba ta zuɓo fulawar,yis ta ɗauko tsakar gida ta dawo ta har ta zauna sai ta tuna da ta bata ɗauko gishiri ba sai ta koma,bayan ta ɗauko ta zauna cikin sauri ta ke kwaɓa fulawar cikin lokaci kaɗan ta gama kwaɓin,amma fa ta jigatu saboda kafaɗunta duk sun gaji.

Bayan ta gama kwaɓin ta ja robar ta kaita saitin rana,dawowa ta yi domin ta gyara inda ta ɓata,ta na cikin gyaran wurin Mama ta fito daga ɗakinta ta ce,
“Wai aikin me kike haka cikin gidan Husna tun ɗazun nake jin motsinki?”

Ɗagowa ta yi daga duƙen da take ta ce,”Mama kin manta yau akwai aikin fanke shi ya sa na fito da wuri ga shi ma har na kwaɓa.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button