HAUSA NOVELRASHIN SO Complete Hausa Novel

RASHIN SO Complete Hausa Novel

*PAGE 1*

Hadari ne ya kankama sosai gari duk yayi duhu yayinda iska mai cikeda k’ura ta bayyana,giragizzai suka dinga shawagi a sararin samaniya can na tsinkayo wata mata rik’e da yara biyu d’aya goye abayanta d’ayar rik’e ahannunta tana ganin hadari ya taso da iska mai saka sanyi nan da nan ta samu rumfar kara ahanya ta shiga ciki, domin kada ruwan ya jik’ata tana shiga ciki ba’a dad’e ba kamar jiranta ake aka saki ruwa sosai kamar da bakin k’warya,k’aton icce ta hango cikin rumfar isa wurin iccen tayi ta zauna tareda banye zanen goyonta jan hannun ‘yarta tayi ta zaunar da ita kusa gareta, rungume d’anta Suhail tayi wanda bashida isassshiyar lafiya kwallar zallar takaici sai gangarowa sukeyi daga cikin idanunta da sukayi jajir akan yawan kuka, yarinyar ta jingina jikinta ga mahaifiyarta tana hamma alamar yunwa takeji tace”Ummi yunwa nakeji sosai”.
Mahaifiyarta ta kalleta cikin tausayawa tana sharar hawayenta afaikace tace”kiyi hak’uri Rufaida idan muka k’arasa gidan Baffa za kici abinci kinji”.
Rufaida ta girgiza kanta alamar to yayinda yunwa tana nan tana nuk’urk’usarta, mahaifiyar ta shafi jikin Suhail taji yayi matuk’ar zafi sosai akan zazzab’i dak’yar yake fitar da numfashin ciwo, hankalinta ya k’ara tashi ta dubi ruwan da akeyi sosai taga kamar yanzu aka fara yin ruwan, numfashin takaici ta sauke tace”Allah ubangiji yasa ad’auke ruwan da wuri”.
“Amin Ummi”.Inji Rufaida da take nishin yunwa.
Anjima ana tsuka ruwa kamar da bakin k’warya sannan daga baya aka tsagaita da yin ruwan, ganin an rage yin ruwan yasa Naja’atu ta mik’e tsaye ta goya Suhail abayanta ta kalli Rufaida tace”Rufaida tashi mu k’arasa gidan Baffa”.
Rufaida ta mik’e tsaye ta kasa magana takalminta data cire ak’afa ta sanya, tana gama sanyawa Naja’atu taja hannunta suka fice daga cikin rumfar kama hanyar gidan iyayenta tayi da k’afa suna tafiya shiru shiru domin kowacce daga cikinsu cikinta k’ugin yunwa kawai yakeyi.
Suna k’arasowa suka shiga cikin wani gida ginin jar k’asa suka shiga da sallama abakinsu, suna shiga suka iske Anna mahaifiyar Naja’atu zaune tana tankad’ar garin tuwo yayinda yayan Naja’atu Hamid yake zaune agefenta yana taya Anna fira, amsa sallamar yah Hamid yayi yayinda suka iso tsakiyar gidan Naja’atu ta durk’usa har k’asa ta gaida Anna da yah Hamid, amsa mata sukayi fuskarsu d’auke da annuri mik’ewa tsaye tayi ta shiga cikin d’akin ta d’auko tabarma suka zauna, alokacin ta banye zanen goyon Suhail ta rungume d’anta ajikinta yah Hamid ne ya dubeta cikin k’aunar ‘yar uwarsa yace”Naja’atu lafiya kika fito daga cikin ruwan nan mai sanyi keda yaranki?”.
Naja’atu ta langwab’e kanta cikin marairaicewa tace”yaya Suhail ne bashida lafiya tuntuni nayiwa babansa magana ko kallona baiyi ba, bale yacemin wani abu”.
Yah Hamid ya dubi Suhail cikin nazari yace”ayyah Allah ya bashi lafiya zazzab’i ne ke damunsa ko?”.
“eh yaya”.Inji Naja’atu cikin sanyin murya.
Anna dai kallon Naja’atu kawai takeyi cikin tausayawa akan halin da take fuskanta arayuwar aurenta mara dad’i, har azuciyarta batason ganin ‘yarta cikin k’unci da k’angin rayuwa to ya zatayi idan ba hak’uri domin komai ya samu bawa muk’addari ne daga Allah.
Yah Hamid ya mik’e tsaye yace”ok to kawosa in kaishi chemist ayi masa allura ahad’o masa magunguna”.
“to yaya”.Ta fad’a.
Tashi tsaye Naja’atu tayi ta mik’awa yah Hamid Suhail ahannunsa, ya d’aukesa yana amsarsa ya fice daga cikin gidan da sauri domin ya kaishi chemist.

Anna ta dubi Naja’atu tace”kwana nawa yayi bayada lafiya Naja’atu?”.
“kwanansa biyar Anna babansa ko damuwa baiyi da rashin lafiyarsa ba”.
Anna tace cikin jimami da bak’in ciki”hmm wannan auren naki ya isheni abin yak’i ci yak’i cinyewa tuntuni Naja’atu, agaskiya bakiyi dacen samun miji nagari ba!”.
Naja’atu ta duk’ar da kanta ak’asa kwalla taff cike cikin idanunta tana sharewa cikin yanayin damuwa tace”ni kaina Anna wannan auren na Basheer ya isheni!Aure yana yiyuwa da yunwa ga rashin sutura wannan wace irin k’addara ce mai k’unshe da bak’in ciki da tarin damuwa!?”.
Anna ta girgiza kanta fargaba da damuwa ne shimfid’e afuskarta tace”ki k’ara hak’uri tabbas komai lokaci ne duk abinda Basheer yakeyi miki na cutarwa Allah yana sama yana kallonsa shi zaiyi miki sakayya!”.
Rufaida ganin an k’yaleta ba’a bata abinci ba yasa ta bud’i baki dak’yar tace”Anna yunwa fa nakeji tun d’azu”.
“A’a Rufaida kika k’iyin magana tuntuni sai yanzu Naja’atu tashi shiga kitchen ki d’ebo muku abinci kuci, nasan kema yunwa kikeji tunda Basheer ya zama azzalumi sakaran namiji”.
Naja’atu tayi yak’e tace”to Anna”.
Mik’ewa tsaye tayi ta shiga cikin kitchen kwano ta wanko ta sanyo musu dafukan taliya cikin kwanon ta fito daga cikin kitchen d’in, kai tsaye ta nufi wurinsu Anna ta zauna tana zaunawa Rufaida ta kalli Umminta tace”Ummi baki d’ebo mana ruwa ba”.
“je ki d’ebo ruwan”.Fad’ar Naja’atu.
“to”.Tace tana yamutsar fuskarta.
Tashi tsaye tayi ta nufi wurin tulun ruwa kofin dake cikin tulun ruwan ta cikoshi da ruwa, sannan ta iso wurin mahaifiyarta ta zauna ta lank’washe k’afafunta domin taji dad’in cin abincin, tana zama suka wanke hannayensu suka fara cin abincin kamar yau ne suka fara cin abinci mai yawa isasshe musamman Rufaida da take k’aramar yarinya batada jimirin yunwa, ci sukeyi sosai saida sukaji cikinsu ya d’auka sannan Naja’atu tabar mata sauran ta iyar da cinyewa.

Anna tana ganin sun kammala cin abincin tace”idan baku k’oshi ba kije ki k’aro”.
Rufaida ta gyad’a kanta tace”Anna na k’oshi sosai gaskiya”.
“haka nakeson ji”.
Tashi tsaye Anna tayi ta shiga cikin d’akinta ta jima aciki ta d’auko babbar leda cikeda kayan abinci,tana fitowa ta mik’awa Naja’atu ledar ahannunta tace”ga wannan idan kika koma gidan mijinki ki dinga amfani dashi idan ya k’are ki bugo waya ki sanarmin sai in aiko yayanki Hamid ya kawo miki wani, sannan dan Allah ki daure ki daina saka damuwa azuciyarki saboda kinsan babanki baxai tab’a barin ki kashe aurenki ba, ki cigaba da hak’uri komai na duniya yanada iyaka tabbas anan gaba kad’an za kici ribar hak’urinki”.
Naja’atu tayi murmushin dake k’ayartar da fuskarta tace”zan jure da yardar Allah Anna”.
Tana rufe bakinta saiga sallamar yah Hamid ya shigo da Suhail d’auke ahannunsa, yana isowa ya mik’awa Naja’atu d’anta ta amsa sannan ya dubeta yace”anyi masa allurar Allah ubangiji ya bashi lafiya ga maganin zazzab’i da paracetamol ki dinga bashi yana sha, da sannu sannu zai samu waraka”.Ledar maganin dake hannunsa ya mik’a mata ta amsa tace”Amin yaya nagode sosai Allah ubangiji ya k’ara bud’i na Alkhairi”.
“Amin amin”.
Alokacin ne Anna tace”to tashi kiyi sauri ki koma gidan mijinki kafin Baffanki ya dawo ya taras dake”.

Naja’atu tace”Anna”.Tashi tsaye tayi ta goya Suhail abayanta sannan ta yafa mayafinta ledar da Anna ta bata yah Hamid ya rik’e mata ahannunsa, jan hannun Rufaida tayi zasu wuce ta waigo tace”idan Baffa ya dawo ina gaidashi”.

Anna ta gyara zamanta tareda rufe garin tuwonta cikin k’warya tace”zaiji asauka lafiya”.

“Allah ya yarda”.Cewar Naja’atu.

Hanyar fita daga cikin gidan suka nufa yayinda suka jera itada yah Hamid atare, suna isa bakin k’ofar sukaja suka tsaya yah Hamid ya ciro kud’i daga cikin aljihunsa yace”ga kud’i ki sayi sabulun wanki dana wanka k’anwata”.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button