RASHIN SO Complete Hausa Novel

Naja’atu tana k’ulla kayayyakin miya wand’anda take siyarwa Rufaida tana zaune kusa gareta tana tayata, Suhail kuwa yana zagayar filin d’akin da gudu yana k’iriniya saiga shigowar yah Basheer kai tsaye cikin d’akinta babu ko sallama Haseena tana biye abayansa, jin motsin shigowarsa yasa ta d’ago idanunta da sauri idanunta suka fad’a cikin nasu cikin zullumi da fargaba tace”lafiya Abban Suhail kuka shigomin cikin d’aki kai tsaye?”.
Basheer yayi mata mugun kallo mai d’auke da tsana da rashin sonta yace”dama kinada d’aki acikin gidan nan?”.
Haseena tayi charab tace”gaya mata dai farin cikina”.Tace tana bankawa Naja’atu harara.
Ganin yadda suka had’e mata kai yasa gaban Naja’atu ya fad’i rasssss zuciyarta ta girgiza hankalinta ya d’unguma sosai, zuciyarta ta nasa mata ba alkhairi bane ya kawosu cikin d’akinta ba cikin k’arfin hali tace”Abban Suhail naji banida d’aki acikin gidanka to miye nayi kuma saboda nasan ni bana rabo da laifi?”.
Basheer yace”bakima san laifinki ba kenan!”.
“gaskiya ban sani ba”.
“mi Haseena tayi miki kawai don ta aiki ‘yarki shine zakice bata zuwa ki dinga zaginta kawai domin son zuciya da raini irin naki!?”.
Mamaki da takaici ne ya bayyana afuskarta tareda bak’in ciki, agaskiya ta sarawa Haseena wurin iya tsara k’arya da makirci haka b’oye damuwarta tayi tace”Haseenar ce ta gaya maka na zageta?”.
“ita ta gayamin nasan kuma batayimin k’arya!”.
Naja’atu tayi murmushin takaici ta kalli gefen da Haseena take tsaye tana yamutsa fuska kamar taga kashi tace”ke Amarya kece kika gayawa mijinki na zageki yaushe na zageki akan zaki aiki Rufaida?”.
Haseena tayi mata kallon walak’anci tace”banason rainin wayo ni zaki tambaya lokacin da kika zageni saboda kina mahaukaciya bak’ar makira!”.
Basheer ya hasala yace”k’yaleni da ita babyna Naja’atu ayau zakisan kin zagi matata saina nuna miki ke k’aramar shegiya ce”.
Naja’atu ta girgiza kanta tace”kafi kowa sanin niba shegiya bace Basheer!”.
Haseena ta dubesa tace”mijina kanajin fa tana zaginka”.
Rufaida dake zaune kusaga mahaifiyarta harta fara hawayen tausayin kansu saboda ganin yadda lokaci guda Abbanta da kishiyar Umminta sun tarawa Naja’atu, su kuma ko kula da Rufaida basuyi ba.
“ni kike zagi Naja’atu lallai bakida mutunci dama keba d’iyar mutanen k’warai bace!.
K’ala Naja’atu bata sake cewa ba saboda abin yafi k’arfin tunaninta da zuciyarta tagumi tayi tana kallon ikon rabbi.
Ganin tayi shiru yasa suka dinga zaginta da iyayenta sai abinda suka mance abakinsu, itadai saurarensu kawai takeyi har suka gaji sukayi shiru yah Basheer ya kalli gefenta yaga Rufaida zaune tana hawaye daka mata rikitaccen tsawa yayi yace”keee dan uwarki! Zo nan”.
Naja’atu tace”mi zatayi maka?”.
“ki rufemin bakinki babu ruwanki!”.
“da ruwana saboda ‘yata ce”.
“to idan kin isa ki hana tazo wurina!”.
Basheer ya sake dakawa Rufaida tsawa ai kuwa cikin firgici da tsananin tsoro ta iso gaban mahaifinta ta gurfana ak’asa jikinta sai mazari yakeyi can ya bud’i baki yace”ke saboda bakida tarbiya har matata ce zata kiraki ta aikeki kice baki zuwa!”.
Rufaida duk ta gama rud’ewa akan yanayin yadda mahaifinta keyi mata muryarta tana rawa tace”walla..hi… Abba… bata.. ai….keni…ba”.
Cikin hargowa da k’arfi yace”matartawa zatayi miki k’arya ne?”.
Girgiza kanta tayi alamar eh mana ai kuwa idanun Basheer suka rufe kunnuwansa suka toshe baiyi wata wata ba ya kwasheta da gigitattun maruka guda biyu wad’anda asanadiyar haka saida taga taurari ta saki gigitacciyar k’ara da kuwwa ta fad’i k’asa gwafff kaji kanta ya bugi sumuntin dake cikin d’akin! Haka ne ya basu damar shida Haseena suka rufeta da matsanancin duka ko’ina ajikinta kamar rayuwarta suke nema!.
Naja’atu tana ganin suna neman kashe mata d’iya tayi kukan kura ta fad’a cikinsu, shiga tsakiyarsu tayi ta rungume d’iyarta tana hawaye duk bugun da sukeyi saidai ya sauka ajikinta, duk da sunga uwar ce hakan baisa suka daina dukanta ba saida suka gaji suna haki da nishin gajiya sannan sukaja suka tsaya turus suna kallon jikin Naja’atu da Rufaida wanda asanadiyar duka duk yayi jajir da chanza kala zad tausayi sosai.
Yah Basheer ya mak’ale hannun Haseena acikin nasa yace”gobema ki sake zagin matata ki gani abinda zaiyi miki sai yafi wannan muni arayuwa!”.
Naja’atu ko ta d’aga kai ta kallesu batayi ba bale suji dad’i cikin zafi da rad’ad’in dukan da suka yiwa Rufaida tace”ba komai duk abinda kakeyi ka cigaba Allah yana ganinka!Kuma dukan da kuka yiwa Rufaida bada wani laifi ba sai Allah ya isar mata domin bata yafe ba!”.
“ai Allah isasshe ne tunda ya k’addari uwarki da ubanki suka haifeki!”.
“jahilar banza wadda batasan ciwon kanta ba shiyasa bakida farin jinin ga miji”.
Basheer ya tsotsi bakin Haseena yace”share banza babyna muje d’aki mu kwanta”.
Kwanto masa ajiki Haseena tayi tana wani mak’ale masa ajikinsa cikin yanga tace”ok muje in baka dad’i kasha saika k’oshi mijina”.
“Allah kuwa babyna”.
“da gaske nake farin cikina”.
Tattare hannun rigarsa yayi ya sunkuceta sai k’yalk’yalar dariya sukeyi suna murna yayinda sukabar Naja’atu zaune da Rufaida suna rusa uban kuka mai k’unshe da bak’in ciki da takaicin rayuwa, shasshekar kukan Rufaida kawai kakeji yana tashi alokacin ne Naja’atu ta jawota ta rungumeta tareda bubbuga bayanta alamar lallashinta, ayinin ranar sun kasance cikin tsananin b’acin rai da tsantsar damuwa k’unshewa sukayi cikin d’aki akan tsananin bak’in ciki .
********************
Da rana Naja’atu tana surfen hatsin kunu acikin turmi bayan ta gama ta wanke hatsin tareda jik’ashi cikin roba, zata shige cikin d’akinta kenan taji muryar yayanta Hamid yana sallama jikinta yana mazari akan murna da tsantsar farin ciki ta juyo ta amsa mishi murmushi k’unshe afuskarta, shigowa yayi har cikin gidan rik’e da babbar leda ahannunsa yana isowa wurinta ta gaidashi fuska asake ya amsa mata, jagora tayi masa har cikin parlourn suka zazzauna saman kujera yayinda Naja’atu ta mik’e ta d’ebo masa ruwa akofi masu sanyi, saida yasha ruwan sannan yayi ajiyar zuciya itace ta fara ce masa”yaya yasu Anna da Aunty Bilkisu ina fatar duk suna cikin k’oshin lafiya”.
Murmushi ya sakar mata yace”lafiyarsu k’alau suna gaisheki”.
“ina amsawa”.
Yah Hamid ya kalleta cikin k’auna da tausayawa yace”ya maigidanki da fatar baya takura miki sannan ga wannan kayayyakin sawa ne kiyi amfani dasu”.Ledar daya shigo da ita ya nuna mata.
Wani abu ta had’iye mak’wat azuciyarta mai d’aci cikin yanayin damuwa tace”ya rage takuramin yaya”.
Yah Hamid ya girgiza kai saka hannu yayi cikin aljihunsa ya ciro kud’i masu yawa ya mik’a mata yace”ga wannan ki samu sana’a kiyi kinji k’anwata nasan bak’ya jin dad’in zama agidan Basheer, amma kiyi hak’uri dukkan tsanani yana tare da sauk’i komai yayi farko yanada k’arshe da yardar Allah”.
Kwallar zallar takaici ne ya zubo afuskarta ta saka hannu ta share tace”nagode,yaya insha Allahu zan cigaba da hak’urin duk walak’ancin da yakeyi mini”.
“haka nakeson ji ki d’auka duk abinda yake faruwa dake *K’ADDARA CE* tabbas wata rana zaki tsinci kanki cikin rayuwar farin ciki domin aduniya babu abinda yake dawwama farin ciki ko bak’in ciki kowane daga cikinsu zaka iya riskar kanka acikinsu “.Murmushin da baikai zuci ba tayi tace”maganarka gaskiya ce yaya aini na yarda da k’addarata wlh babu komai, komai yayi zafi maganinsa Allah sannan haka duniyar take tun fil’azal”.
“nizan wuce gida Naja’atu Allah ya fitar dake cikin yanayin damuwa ya juyarda zuciyarki daga cikin bak’in ciki zuwa farin ciki sosai, kuma duk mai biyarki da sharri Allah ubangiji ya mayar masa da sharrinsa saman wuyansa “.Amin yah Hamid ka mik’a sak’on gaisuwata gasu Anna”.”zasuji da yardar Allah “.Fitowa yayi daga cikin room d’in itama tabi bayansa domin tayi masa rakiya………
[11/24, 3:15 PM] Mugiratmusa66: ????????????????????????
*RASHIN SO*
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????