HAUSA NOVELRASHIN SO Complete Hausa Novel

RASHIN SO Complete Hausa Novel

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION*®✍????
(Onward together).

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*

*Dedicated to*
*Sis Najer’art*

_Free page._

*PAGE 9*

 

Suna isa bakin k’ofar gidan yah Hamid ya tsaya ya dubeta yace”ko akwai abinda kike buk’ata k’anwatah?”.Naja’atu ta langwab’e kanta da marairaice fuskarta kamar zatayi kuka cikin shagwab’a tace”komai kana iya k’ok’ari wurin yimin yayana aduniya banda iyayena banida kamarka, saboda yadda kake tausayina da kulawa dani tun ina k’ank’anuwa har zuwa girmana ubangiji Allah ya k’ara d’aukakamin kai d’an uwana”.Hak’ik’a yah Hamid yaji dad’in addu’ar da Naja’atu tayi masa har cikin zuciyarsa da b’argon jikinsa, murmushin dake k’ayartar da fuskarsa yayi tsantsar farin ciki ne shimfid’e afuskarsa yace”naji dad’in addu’arki gareni k’anwata karki damu muddin ina raye bake babu k’unci awannan duniyar”.Hawaye tausayin kanta ne suka zubo afuskarta tace”ina alfahari da kasancewarka yayana yah Hamid saboda kana k’ok’ari wurin jajircewa domin ganin kwantar mini da hankali da bani gudunmuwa arayuwa”.
Yah Hamid yasa hannunsa ya share mata hawayenta cikeda matuk’ar tausayi da k’auna yace”ki daina kuka Naja’atu domin banason ganin hawayenki arayuwata, tabbas da ba domin kashe aure bayada k’yau ba da nace ki kashe aurenki saboda ki fita cikin uk’uba da k’uncin rayuwa, amma ki k’ara hak’uri da juriya saboda komai da kike gani sai kayi hak’uri kake cimma nasara”.”Nasan da haka yah Hamid dama rayuwa ta gaji haka”.Cewar Naja’atu.
“zan wuce gida Allah ubangiji ya sada fuskokinmu da alkhairi”.
“Amin yah Hamid”.
Xai wuce kenan saiga yah Basheer ya parker mashin d’insa abakin k’ofar gidansa, ganinsa ne yasa yah Hamid ya dakata saboda su gaisa yah Basheer yana ganin Naja’atu da Hamid tsaye ya b’ata fuska yasha toka, isowa wurinsu yayi fuskar nan tasa amuturk’e kamar yaga mak’iyansa!Yana k’arasowa yah Hamid ya bashi hannu sukayi musabaha adak’ile yake kallon gefen Naja’atu, yah Hamid yi yayi kamar baiga chanjin yanayin fuskarsa ba yace”teacher ya d’alibbai”.
Ciki-ciki ya amsa mishi kamar bayaso yace”Alhmdulillahi”.
“masha Allah Allah ubangiji ya k’ara taimakawa”.
“Amin amin”.
“nizan wuce gida Basheer”.
“to yayi ka gaidasu Baffa sai munzo gaishesu”.
“OK zasuji”.
Suna kallon yah Hamid har ya b’acewa ganinsu shiga sukayi cikin gidan, suna isowa tsakiyar gidan yah Basheer ya kalli Naja’atu yace”kee tsaya bari wani sauri!”.
Naja’atu taja ta tsaya wuri d’aya isowa wurinta yayi gab da gab suna jin numfashin juna kallonta yayi sama da k’asa yace”uban wa ya baki izinin lek’awa waje!?”.
“yayana nayiwa rakiya”.Ta fad’a batare da ta waigoshi ba.
“da k’yau wato na fahimceki duk abinda bayada k’yau shi kike k’ok’arin yi ko Naja’atu?Ayau zakisan ke k’aramar ‘yar iska ce wlh”.
“ka daina kirana da ‘yar iska saboda wannan sunan bai dace dani ba”.
“xan iya kiranki da abinda yafi ‘yar iska ma!”.
“kaidai akeji”.
Harzuk’a yah Basheer yayi ya zare belt d’in dake k’ugunsa yana gama zarewa yasa k’afa ya shure Naja’atu ta fad’i k’asa d’immmmm, dinga watsa mata belt d’in yayi ajikinta ta ko’ina zafi da rad’ad’in duka ne ya ziyarci sassan jikinta da magudanar jininta kuka ta dingayi sosai tana kuwwa, saboda dukanta yakeyi kamar ya samu jaka bakin rai bakin fama shure-shure da birgima ta dingayi ak’asa,duk da kukanta da yakeji bai saka zuciyar yah Basheer yaji tausayinta ba dayaga ta damesa da kuka ya mare mata baki fas fass bakin ya fashe da jini, cigaba da dukanta yayi saida yaga ta galabaita numfashinta yana batun d’aukewa jikinta yayi rud’u rud’u akan kwancin bulala sannan ya k’yaleta cikin kakkausar murya yace”wato ke bakida d’abi’a saina lek’on mazan mutane ko? To in sake ganin kina lek’e-lek’e acikin gidana kuma ki tashi ki kwashe kayanki ki barmin gidana!”.
Yana gama maganarsa yaja k’afafunsa yayi wucewarsa zuwa d’akin Haseena, duk abinda yake faruwa a idanun Haseena ya faru saboda taga komai ataga take lek’onsu dad’i da farin ciki taji alokacin da taga yah Basheer yana dukan Naja’atu kamar ya samu jaka.
Naja’atu dake kwance ak’asa kuka kawai takeyi mai cikeda bak’in ciki da uk’ubar rayuwa, numfashin azaba kawai dake fitarwa dak’yar ta mik’e tsaye domin jikinta duk ciwo yakeyi mata da rad’ad’in duka shiga cikin d’akinta tayi ta d’auko akwatinta d’aya, goya Suhail tayi abayanta ta sakawa Rufaida riga suka fito daga cikin d’akin padlock ta sakawa d’akin sannan taja hannun Rufaida suka fice daga cikin gidan da sauri saboda tana tsoron kada yah Basheer ya sake dawowa ya jibgeta, suna fita waje suka samu mai keke napep jinga tayi dashi sannan suka shiga ciki tareda gaya masa sunan unguwar dazai kaisu..

*********************

Yah Basheer yana shiga cikin d’akin Haseena ta shek’o da gudu ta fad’a ajikinsa cikin murna tace”sannu da zuwa mijina”.
D’adi yaji har azuciyarsa ganin irin tarbar daya samu awurinta yace”yauwa babyna hop kin tanadamin abinci mai dad’i sosai”.
“bakada matsala indai ta wannan b’angare ne”.
“ina godiya da nuna soyayya Hasee baby”.
“karka damu kafi k’arfin komai awajena bari kayi wanka kaci abinci”.
“ehmm babyna”.
Cire masa tufafinsa tayi itama ta cire nata d’aura towel sukayi atare, hannunsu mak’ale suka fad’a cikin bathroom tare sukeyin wanka idan ya cud’ata ta cud’ashi haka suka cigaba dayi har saida suka kammala wankan suka fito daga cikin toilet d’in, zaunawa sukayi saman gado suna shafawa junansu lotions yah Basheer sai shafar boobs d’inta yakeyi yana liliyawa kamar ya samu minti, ganin haka ne yasa ta sakar masa jikinta tana wani langwab’ewa shi kuma sai k’ara manneta yakeyi ajikinsa, kwantar da ita yayi rigiggine ya fara kissing d’inta yana shafar jikinta ko’ina, ganin sun fara zaucewa yasa naja k’afafuna na k’ara gaba domin in basu damar da zasu adana sirrinsu.

____________________

Naja’atu keke napep ya sauketa ak’ofar gidansu ta fitar da akwatinta da Rufaida, biyansa kud’insa tayi shi kuma yaja napep d’insa ya k’ara gaba tusa Rufaida tayi agaba hannunta d’aya yana jan akwati, da sallama abakinta ta shiga cikin tsakiyar gidansu Anna dake cikin d’aki ta fito da saurinta tareda amsa mata sallama, kallon mamaki takeyiwa Naja’atu ganinta rik’e da akwati ahannunta isowa wurin mahaifiyarta tayi tareda zaunawa saman tabarmar dake shimfid’e awaje, Anna tana ganin Naja’atu ta zauna itama ta k’araso wurinta ta zauna tace”Naja’atu lafiya na ganki da akwati ahannu?”.
Banye zanen goyon Suhail tayi ta mayardashi saman k’afafunta tace”Anna yah Basheer ne yace inbar masa gidansa”.
Anna ta bugi k’irji da k’arfi! Tsantsar damuwa da fargaba ne ya bayyana k’arara afuskarta tace”kibar masa gidansa yace Naja’atu sakinki yayi ne ?”.
Naja’atu ta had’iye wani abu mai d’aci a mak’oshinta tace”a’a ba saki na yayi ba koroni yayi daga cikin gidansa! “.
Anna ta mik’e tsaye zumbur kamar wadda aka tsikara tace”wato ba sakinki yayi ba kice dai yaji kikayo Naja’atu! To tashi d’auki akwatinki kamar yadda kikazo ki koma gidan mijinki salin alin, ke idan banda kina sakaryar yarinya haka kawai zakiyo yaji wannan ai rashin sanin darajar aure ne! “.

Idanun Naja’atu suka cicciko da ruwan hawaye ganin Anna zata iya tilastata ta koma shiyasa nan da nan ta fara kuka tace”dan Allah Anna kiyi hak’uri kada ki tilastamin in koma gidan yah Basheer wallahi dukana yakeyi so yake ya kasheni kowa ya huta! “.Tace tana hawaye harda shasshekarta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button