HAUSA NOVELRASHIN SO Complete Hausa Novel

RASHIN SO Complete Hausa Novel

Rik’e baki Anna tayi tana kallon Naja’atu tace”miye kuma abin kuka? Daga kawai nace ki koma gidan mijinki shine kike kuka Naja’atu nasan ko bance ki koma ba idan Baffanki ya dawo baxai tab’a barki ki zauna cikin gidan nan ba”.
“ki bari har ya dawo d’in Anna wallahi yah Basheer baya k’aunata kullum walak’anci yakeyimin tareda k’unsa min bak’in ciki da damuwa agidansa, yauma dukana yayi kalli jikina duk kwancin belt ne ya tsaneni ya tsani ya bud’e ido ya ganni ina farin ciki saidai bak’in ciki”.

Anna tace”banason k’arya yaushe ya bugeki!?”.

Naja’atu tace”wallahi ba k’arya nakeyi miki ba bari ki gani”.
“in gani d’in”.

Cire hijabinta tayi ta aje saman tabarma sannan ta kware jikinta ta nunawa mahaifiyarta, idanun Anna ya sauka ajikin Naja’atu wanda yayi rud’u rud’u jawur akan duka wani irin tururin b’acin rai da k’ololon bak’in ciki ya ziyarci zuciyarta, zuciyarta ta dinga k’una da tafasa cikin tsananin b’acin rai tace:yanzu duk Basheer ne yayi miki mugun duka haka kamar ya samu baiwa!? “.

Murmushin cin nasara Naja’atu tayi tareda marairaicewa tace”duk shine Anna”.
“Lallai ya tab’owa kansa jidali zaisan ya dokeki kuma ba zaki koma ba saimun k’watar miki ‘yancinki!”.

“ba yau ya fara dukana ba Anna ko ranar nan shida matarsa suka tara mana nida Rufaida sunata dukanmu”.

“eyehhh dole yayi miki haka saboda bayada albarka zai gane kurensa domin ni ba jaka na haifar masa ba bale ya dinga jibgarki yadda yaga dama, tashi ki shiga cikin d’aki kiyi wanka kici abinci”.

Naja’atu ta langwab’e kanta tace”idan Baffa ya dawo ina tsoron kada ya mayar dani gidansa”.

“bazai mayar dake ba ki kwantar da hankalinki ni nasan maganar dazan gaya masa, inyaso aje gidan iyayen Basheer agaya musu irin walak’anci da tozartaki da yakeyi akan Amaryarsa”.

“da kun k’yalesa Anna banason agayawa iyayensa “.

Harara Anna ta banka mata tace cikin kakkausar murya “dole susan abinda d’ansu yake aikatawa sarkin son miji bak’ya son asirinsa ya tonu ko miye nufinki?”.

Naja’atu ta b’ata fuska tace”sulhu ne banason ayi atsakaninmu na gaji da zaman gidansa Anna yah Basheer baya sona bayason ganin farin cikina rayuwata yake farauta idan na koma gidansa mutuwa zany!”.” Maganar shirme kikeyi baki duk mutuwa saboda duk wadda kikaga ta mutu to kwananta ne ya k’are Naja’atu, dole ayi sulhu tsakaninku ajawa Basheer kunne sai ki koma gidan mijinki saboda banga shegen namijin dazai aureki ba ya rik’a miki ‘ya’yanki ba “.Naja’atu ta zumb’ura baki tace”Anna bazaki fahimci halin da nake ciki ba? Ina cikin k’angin rayuwa da k’unci arayuwar aure! “.”Na fahimceki aurenki ne banason ya mutu kibar yaranki cikin wani hali su tashi alalace babu tarbiyar kirki”.”.Allah shike rayasu bani ba”.”Nasan da haka tun kafin in haifeki hak’uri zakiyi idan aka ja masa kunne ki koma gidan mijinki saboda ni bana fatar kiyi yawon d’aki “.Naja’atu ta mik’e tsaye tace “naji Anna”.”Kodai bakiji ba nadai gaya miki gaskiya “.Shigewa cikin d’akin mahaifiyarta tayi tana b’ata fuska kamar zata fashe da kukan takaici……….
[11/24, 3:15 PM] Mugiratmusa66: ????????????????????????
*RASHIN SO*
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION*®✍????
(Onward together).

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*

*Dedicated to*
*Sis Najer’art*

_Free page._

 

*PAGE 10*

 

Naja’atu tana shigewa cikin d’akin Anna Rufaida da Suhail suka tashi sukabi bayanta, tana cire tufafinta saigasu sun shigo d’aura zane tayi ajikinta ganinsu Suhail sun shigo yasa ta kalli Rufaida tace”ku zauna har nayi wanka idan na fito sai kije kiyi wanka keda k’anenki”.Rufaida ta shagwab’e fuskarta tace”to Ummi”.Suhail dai kallon Naja’atu kawai yakeyi yana dariya sosai ita kuma bata lura ba fitowa tayi awaje wurin Anna dake zaune tace”Anna akwai sabulun wanka?”.”Eh diba cikin wata bak’ar leda ad’aki”.”To”.Kawai tace ta juya ta komo cikin d’akin dube-dube ta kamayi Rufaida tana tayata har suka gano inda ledar take aje cikin d’akin, suna ganin ledar Naja’atu tasa hannu ta d’auki sabulu d’aya Rufaida ta koma ta zauna wurin k’anenta .
Fitowa Naja’atu tayi ta d’auki bokiti ta jawo ruwa arijiya da guga ta cika bokitinta ta fad’a cikin toilet d’in dake cikin gidan, ta jima tana gurza ko’ina ajikinta sannan ta d’oraye jikinta tareda d’auro alwala ta fito daga cikin d’akin, koda ta fito bataga Anna awaje ba kutsa kanta tayi cikin d’akin ta iske Anna kwance saman gadon k’arfe na da, jawo ‘yar k’aramar jikkarta tayi ta ciro mai da kayan kwalliya shafe jikinta tayi da mayuka masu k’amshi ta shafa powder kallon Rufaida tayi alokacin ne take k’ok’arin saka rigarta tace”tashi kuje kuyi wanka idan kuka gama sai insa muku abinci kuci”.
Rufaida tace”to”.Mik’ewa tsaye tayi ta cire tufafinta sannan ta cirewa Suhail nashi jan hannunsa tayi ta nufi toilet, suna zuwa sukaga bokiti wayam babu ruwa dayake taga rijiya ce kuma bata iya jan ruwa arijiya ba kuma gugar tayi mata girma direct wurin randa ta nufa da bokiti ahannunta cika bokitin tayi da ruwa, tana cikawa ta shiga cikin d’akin ta tsaya kusaga k’ofa tace”Ummi na d’ebi ruwa aranda bana iya kaisu toilet”.
“kije gani nan zuwa inkai miki”.Fad’ar Naja’atu da ta kammala shiryawa cikin atamfarta light blue.
Juyawa kawai Rufaida tayi ta dawo wurin Suhail Naja’atu bata dad’e ba tazo ta d’auki bokiti da ruwa takai musu cikin toilet d’in, tana ajewa ta fito ta koma d’akin addu’ar shiga cikin toilet Rufaida ta karanta sannan taja hannun Suhail suka shiga ciki, shi ta fara yiwa wanka daga k’arshe tayiwa kanta suna kammala wankan ta jawo hannunsa suka fito daga cikin toilet d’in, d’aki suka shiga Naja’atu ta shafa musu manshafi yiwa Rufaida kwalliya tayi mai k’yau sannan ta ciro musu kayansu cikin akwati ta sanya musu, abinci taje ta d’ebo musu aplate d’aya da ruwa ta kawo ta dire agabansu komawa tayi ta d’ebo nata abinci da ruwa akofi sannan ta dawo ta zauna tareda lank’washe k’afafunta ta fara cin abincinta atsanake, sun jima suna ci Anna dai sai kallonsu takeyi daga baya Naja’atu taji ta k’oshi d’auke plates d’in tayi duka biyu dayake suma sunci sun k’oshi, fitowa tayi ta nufi wurin wanke-wanke ta wankesu sannan ta maidasu a inda ta d’aukosu..
**********************
Tana adana plates d’in ta koma cikin d’aki ta kishingid’a saman babbar cushion d’in ita kad’aice acikin d’akin mahaifiyarta, tuni Anna dasu Rufaida barci yayi awon gaba dasu yayinda Naja’atu tayi zugum ita kad’ai babu abokin fira tayi shiru ta fad’a cikin duniyar tunani saiga sallamar Baffa Zakari ya shigo cikin d’akin kai tsaye hannunsa rik’e sandar arake da ledar kayan marmari Naja’atu ta amsa masa sallamarsa tareda mik’ewa tsaye ta amshi kayan dake hannunsa, yi masa sannu da zuwa tayi ya amsa mata fuska asake yace”ankawo mana ziyara ne?”.
Naja’atu ta gyad’a kanta tace”eh Baffa”.
Shigowa yayi tsakiyar d’akin ya zauna saman gadon da Anna take barci, Naja’atu ta aje araken da ledar marmari saman kujera yayinda Baffa ya tayarda Anna daga barci yace”tashi barcin ya isa hakanan”.
Firgigit! Anna ta falka daga barci sannan ta tashi zaune cikin yanayin wadda barci bai isheta ba tana lumshe idanu tana bud’ewa tace”maigida ka dawo ashe ban sani ba ina nan ina barci”.
Baffa yayi murmushi yace”sarkin barci kike Balira bak’ya gajiya”.
“ba’a gajiya da barci bari in kawo maka abincinka”.
“to Anna”.
Anna ta tashi tsaye ta d’auko masa kwanon abincinsa da ruwa akofi kawowa tayi ta aje agabansa, wanke hannunsa Baffa yayi yayi bismillah ya fara cin abinci cikin natsuwa ci yakeyi atsanake har ya kammala yasha ruwa ya dubi Anna yace”Balira agaskiya wannan abincin yayi dad’i sosai Allah ubangiji yayi miki albarka”.
Murmushin dake bayyana hak’ora Anna tayi tace”amin maigida ina son in sanar maka wani abu”.
Baffa ya tattara hankalinsa da natsuwarsa ya mayar kacokam wurin Anna ajiyar numfashi yayi yace”ki fad’a Balira ina jinki”.
Yak’e tayi ta duk’ar da kanta ak’asa tace”Basheer ne ya koro Naja’atu daga gidansa ba ziyara ta kawo mana ba”.
Gaban Baffa ya fad’i rasssss zuciyarsa ta tsinke! Tattaro dauriya yayi yace”miya had’asu ne har yasa ya korota!?”.
Anna ta mayarda kallonta wurin Naja’atu dake zaune hawayen takaici suna shatata afuskarta tace”saika tambayeta abinda ya had’asu muji daga bakinta”.
Baffa yayi huci mai tattare da d’acin rai yace”Naja’atu ki dubi girman Allah ki gaya mana gaskiyar abinda ya had’aki da mijinki kada ki gayamin abinda ba gaskiya bane”.
Naja’atu ta bud’i baki cikin sanyin murya da tsananin bak’in ciki tace”Baffa yah Basheer ne ya kamani ya jibgeni adalilin yah Hamid yazo wurina nayi masa rakiya bakin k’ofar gidansa, muna tsaye shi yana waje ni ina daga cikin gidan muna magana bamu dad’e da tsayuwa ba saiga yah Basheer ya parker mashin d’insa suka gaisa da yah Hamid……….. “.Labarin komai ta sanar musu harda taron dangin da yayi mata shida matarsa Haseena saida ta gaya musu, da ranar tana dahuwar macaroni ya zuba mata k’asa aciki da ranar da Haseena ta fasawa Rufaida kanta itada Suhail duk saida ta kwashe komai ta gaya musu.
Daga Baffa har Anna duk jikinsu yayi sanyi akan wannan labarin da Naja’atu ta basu mai tattare da d’acin rai da bak’in ciki,kallo d’aya zakayi musu ka hango tashin hankali da tsananin b’acin rai kwance cikin idanunsu sunyi shiru dukansu saboda maganar ta daki zuk’atansu, kowane daga cikinsu da abinda yake sak’awa aransa Anna akan d’acin rai ta noce kanta a k’asa kwallar zallar takaici sai zubowa takeyi afuskarta tana sa hannunta tana sharewa da wayo-wayo, Baffa ne ya d’ago kansa ya kalli Naja’atu yace”yanzu duk wad’annan abubuwan marasa k’yau Basheer ne yakeyi miki su?”.
Naja’atu tace”Allah Baffa duk shine yakeyimin abubuwa marasa dad’i tareda k’unsamin bak’in ciki “.
Baffa yayi huci mai tattare da d’acin rai da tafasar zuciya yace”ba komai akwai Allah ku barni dashi zanyi magana da mahaifinsa Alhaji Tasi’u domin mu gano bakin zaren”.
Anna tace”to maigida amma abinda Basheer yakeyiwa yarinyar nan yayi yawa gaskiya, ace bai mayar da ita abakin komai ba saboda ya raina mata hankali!Wannan wace irin rayuwar aure ce sai kace garesa aka fara yin Amarya?Wannan cin amana ne da zalunci kuma tabbas sai *AMANA* taci Basheer domin ya cutar da rayuwar Naja’atu”.
Baffa yayi shiru tareda yin tagumi cikin damuwa yace”ki daina fad’ar haka Balira kinsan har yanzu akwai aure atsakaninsu kuma tsakanin mata da miji sai Allah, ki dinga bata shawara akan ta cigaba da hak’uri domin mai hak’uri yakan dafa dutse har yasha romonsa “.
Anna tace”har kullum ina kan bata hak’uri amma bayada wata k’wakk’waran hujja ko dalilin dazai sa ya dinga jibgarmin ‘ya ba kamar jaka wannan ai rashin imani da tsoron Allah ne ! Ko saboda yaga kamar idan suka samu matsala ana sulhuntasu shiyasa yake neman ya kashemin yarinya!”.
Baffa ya mik’e tsaye ya sanya takalminsa yace”Allah ya huci zuciyarki Balira yanzu dai bari inje wurin Alhaji Tasi’u in gaya masa abinda yake faruwa”.Yana rufe bakinsa yaja k’afafunsa ya fice daga cikin gidan Anna ta d’aga murya da k’arfi ta yadda Baffa zai iya jiyota tace”ka gayawa Alhaji Tasi’u ya jawa shegen d’ansa kunne akan ya kiyaye daga dukan ‘yata saboda ba jakar uwarsa bace kota ubansa! Idan bai daina wallahi wata rana sai nayi k’ararsa wurin ‘yan sanda… “.
Naja’atu tayi charab tace”kiyi hak’uri ki daina d’aga murya sosai Anna mak’wabta da mazan dake wucewa suna jinki kina banbami”.
“dallah rufamin bakinka! Sakaryar yarinya kawai ke idan banda kina wawuya ki zauna namiji yana jibgarki abanza baki turesa ya fad’i k’asa ya halaka ki huta da bak’in azzalumi maciyi amana! “.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button