RASHIN SO Complete Hausa Novel
“ni bazan iya ba kema nasan b’acin rai ne yasa kika fad’i haka kinsha yimin nasiha akan inyi biyayya ga mijina domin aljannata tana k’ark’ashin tafin k’afafunsa Anna, komai yakeyi mini na zalunci na barshi ga Allah mad’aukakin sarki shi yasan hukuncin da zaiyi atsakaninmu, sannan abubuwan da suke faruwa tsakanina dashi zaman tare ne”.
Kalaman Naja’atu ya sanya zuciyar mahaifiyarta ta ragu akan b’acin rai da tsantsar bak’in cikin da take cikinsa, jikinta ne yayi sanyi lak’was wani irin abu ne ke yawo acikin ilahirin jikinta da zuciyarta kallon k’aunar ‘yarta tayi ta saki nannauyar ajiyar zuciya tace”Allah yayi miki albarka Naja’atu kin tunatar dani abinda na manta alokacin da b’acin rai da k’unar zuciya ya rufe mini idanu, alal hak’ik’a ke yarinyar kirki ce ina alfaharin kasancewarki d’iya agareni saboda kinada hak’uri da hangen nesa saboda haka idan aka sulhunta atsakaninki da mijinki ki cigaba da hak’uri tabbas komai zai wuce kamar ba’a tab’a yinsa ba arayuwa”.
Naja’atu ta amsa da to duk dayake har cikin zuciyarta batason ta k’ara komawa gidan yah Basheer saboda irin walak’anci da taskun da yakeyi mata ya isheta, batada yadda zatayi ne da ta saki kanta ta huta da fitinar rayuwa saboda idan tana gidansa ji takeyi tamkar tana kwana saman k’aya ne ji take tamkar tana rayuwa gidan tarmani ne suna cizonta, babu wani farin ciki da take tsinta agidansa sai b’acin rai da bak’in cikin rayuwa kullum cin amanarta yakeyi rabon daya kwana d’akinta ya kuma bata hak’k’inta na auratayya harta manta, ganin ta fad’a duniyar tunani yasa Anna ta dafa kafad’arta tayi firgigit ta dawo cikin hayyacinta kallonta tayi tace”kee lafiyarki k’alau kuwa mi kike tunani haka?”.
Naja’atu tace”babu abinda nake tunani Anna”.
Anna ta jijjiga kanta alamar bata yarda ba tace”ki daina saka damuwa da yawan tunani aranki kada ki jawa kanki wani ciwo”.
“na daina Anna”.
“yafi miki Naja’atu”.Anna tana rufe bakinta saiga yah Hamid ya shigo cikin gidan wurin Naja’atu ya nufa ya zauna yana kallon fuskarta yace”Anna mi ya kawo Naja’atu gidan nan yanzu? “.Anna tayi murmushin takaici tace”mijinta ya korota agidansa!.”………
[11/25, 4:01 PM] Mugiratmusa66: ????????????????????????
*RASHIN SO*
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????
*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION*®✍????
(Onward together).
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sis Najer’art*
_Free page._
*PAGE 11*
“What!?”.Cewar yah Hamid saboda maganar ya soki k’ahon zuciyarsa wani irin d’aci da k’ololon bak’in ciki ne ya tokare ak’irjinsa gumi ne ya tsattsafo ajikinsa nan da nan batare da b’ata lokaci ba, cikin yanayin damuwa da b’acin rai yace”Anna mi tayi masa ne har ya korota!?”.Anna ta kalli gefen Naja’atu tace”tambayeta mana kaji ta bakinta saboda wak’a abakin mai ita tafi dad’i”.Yah Hamid ya mayarda idanunsa akan Naja’atu da take sharar kwallar zallar bak’in ciki yace”k’anwata mi ya had’aki da mijinki har ya koroki!?”.Naja’atu tana hawaye ta kwashe labarin fad’ansu da yah Basheer ta gaya masa, komai ta sanar masa kamar yadda ta gayawasu Baffa har k’arshe babu abinda ta rage ko ta k’ara acikin labarinta.
Tana kai aya yah Hamid yaji wani irin d’aci da rad’ad’in bak’in ciki azuciyarsa idanunsa suka bayyanar da tsananin damuwa da bak’in ciki, kallo d’aya zakayi masa ka hango zafi da k’unar abinda yah Basheer yayiwa ‘yar uwarsa jijiyoyin kansa suka tashi rud’u rud’u idanunsa suka chanza colour zuwa jajir danne abinda yakeyi azuciyarsa yace”Anna yanzu irin wannan rik’on sakainar kashin Basheer yakeyiwa Naja’atu, saboda nakai mata ziyara zai kamata ya jibgeta son ranshi tabbas zaiyi nadamar abinda ya aikatawa k’anwata Anna!”.
Anna taja dogon numfashi tace”sai hak’uri Hamidu abin dai babu dad’i gaskiya kam amma Basheer bai gaji halin mahaifinsa ba”.
“nasan komai sai anyi hak’uri amma ya kamata ace an takawa Basheer birki saboda walak’anci da zaluncin da yakeyiwa Naja’atu yayi over”.
“ai Baffanka ya nufi gidan mahaifinsa domin su tattauna akan maganarsu saboda asan yadda za’a b’ullowa al’amarin”.
Yah Hamid ya mik’e tsaye zumbur kamar an tsikaresa yace”Allah ubangiji ya daidaita al’amarinsu nizan wuce zuwa gidana”.
“Amin Hamidu ka gaida Bilkisu dasu Hassan”.
“zasuji insha Allahu Naja’atu kiyi hak’uri kinji dukan tsanani yana tare da sauk’i”.
Naja’atu ta kallesa idanunta duk sun kumbura akan fitar da kwalla tace”to yah Hamid babu komai ai”.
Hamid ya fice daga cikin gidan da saurinsa yayinda zuciyarsa ke zugi da rad’ad’in ciwo, yana fitowa daga cikin gidan yahau mashin d’insa ya nufi gidansa.
Baiyi doguwar tafiya ba ya iso bakin k’ofar gidansa parker mashin d’insa yayi agaban gidansa ya sauka, yana sauka ya zare makullin mashin d’insa ya sanya key d’insa acikin aljihunsa shiga yayi cikin gidansa, yana isowa tsakiyar gidan ya hango Bilkisu tana sharar tsakar filin gidan tana kwashe sharar da sanyawa cikin kwandon shara jin takun tafiyar mijinta ne yasa ta d’ago idanunta fuskarta d’auke da annuri tace”Baban Hassan sannu da zuwa”.
“yauwa Bilkisu”.Cewar yah Hamid.
Da sauri Bilkisu ta shimfid’a masa tabarma yana isowa ya zauna saman tabarmar data shimfid’a, yana zama Bilkisu ta shiga cikin d’akinta ta kawo masa ruwa da abincinsa agabansa kallonta yayi tareda yin huci mai zafi yace”da kinbar abincin nan”.
Bilkisu tayi turus da wik’i wik’i da idanu tace”akan mi Baban Hassan miye ya b’ata maka rai?”.
Yah Hamid ya saukar da ajiyar zuciya yace”kedai Basheer ne yake walak’antamin rayuwar k’anwa”.
Zama Bilkisu tayi kusa garesa tace”subahanillah!Taya hakan ya faru?”.Kwashe labarin komai yayi ya gaya mata duk irin abubuwan da suke faruwa arayuwar auren Naja’atu har yakai k’arshe.
Yana gaya mata irin abubuwan da suke faruwa Bilkisu ta saki salati imani da mamaki ne suka bayyana k’arara akan fuskarta shiru tayi tana jimami tace”wannan abin gaskiya baiyi dad’i ba Basheer bai k’yautawa Naja’atu ba, abubuwan da yakeyi basuda k’yawo ko addinin musulunci”.
Hamid yaja gwauron numfashi yace”raina mutane ne yayi amma da sannu zan koya masa hankali wlh saboda yaron nan bayada mutunci ko kad’an arayuwarsa”.
“hak’uri zaku cigaba da bata *RAYUWA CE* wata rana sai labari”.
Tashi tsaye yayi ya maida takalminsa ak’afarsa ya dubi Bilkisu yace”ina zuwa zanje shago in dawo”.
Bilkisu ta linke tabarma tace”Allah ya kiyaye hanya”.
“Amin amin Bilkisu”.Yana k’arasa maganarsa ya fice daga cikin gidan da sauri fitowa yayi awaje yahau saman mashin d’insa, tadda mashin d’in yayi ya k’ara gaba.
____________________
Baffa Zakari yana isa bakin get d’in gidan Alhaji Tasi’u yaja yayi tsaye abakin k’ofar get d’in, sallama ya dinga dokawa da k’arfi maigadi ne yazo ya lek’o ta tagar k’ofa ganin Baffa Zakari ne atsaye yasa yazo da sauri ya bud’e k’ofar gidan yace”Baffa Zakari kaine abakin get d’in gidan nan?”.
Baffa yace”nine Malam Isa barka da yau”.
“barka dai ya iyalinka”.
“k’alau suke Alhaji Tasi’u yana cikin gidan nan kuwa?”.
Malam Isa yace”yana ciki”.
“kayimin sallama dashi”.
“to Baffa Zakari”.K’arasa maganarsa keda wuya ya juya ya shige cikin gidan anjima kad’an saiga Alhaji Tasi’u ya fito daga cikin gidan ya nufi wurin Baffa Zakari fuskarsa ayalwace yana isowa sukayi musabaha da juna, cikin girmamawa sukayi gaishe-gaishe atsakaninsu sun jima suna tattaunawa sannan Baffa Zakari ya kawo labarin walak’anci da k’ask’ancin da Basheer yakeyiwa Naja’atu, Alhaji Tasi’u ya nuna matuk’ar b’acin ransa afili ya dinga fad’a kamar yaga Basheer agabansa anan dai yaba Baffa Zakari hak’uri tareda nuna masa da yardar Allah zaiyi masa fad’a yaja masa kunne, sun dad’e suna maida martanin magana sannan daga k’arshe Baffa Zakari da Alhaji Tasi’u sukayi sallama da juna, Baffa ya nufi hanyar kasuwa yayinda Alhaji Tasi’u ya shige cikin gidansa, yana isa tsakiyar parlourn gidan ya iske mahaifiyar Basheer zaune saman cushion hajiya Hannatu, isowa wurinta yayi ya zauna sannan ya fara kwararo mata labarin abinda yake faruwa agidan Basheer itama hajiya Hannatu bataji dad’in abinda Basheer yayi ba ko kad’an azuciyarta, wani irin d’aci da rad’ad’i ne takeji azuciyarta tattaunawa suka cigaba dayi itada Alhaji akan yadda zasu b’ullowa al’amarin gidan Basheer tareda ja mishi kunne akan abinda yake aikatawa babu k’yawo.