HAUSA NOVELRASHIN SO Complete Hausa Novel

RASHIN SO Complete Hausa Novel

“tashi muje muyi wankan tsarki”.
Tashi sukayi kusan tare yah Basheer ya fara shiga yayi wankan tsarki sannan ya fito Haseena ta shiga tayo, koda tazo har ta iskeshi ya sanya shaddarsa fara ya kawo turare ya sake feshe jikinsa batace masa komai ba ta d’auko doguwar rigarta bak’a mai adon flowers light blue colour ta sanya, kallonta yayi yana murmushi yace mata”baby ni zan fita kasuwa”.
Haseena tace”mi zaka siyo akasuwa?”.
Ya bud’i baki zaiyi mata magana kenan sai sukaji wayarsa tana ruri alamar ana kiransa awaya, sanya hannu yayi cikin aljihunsa ya zaro phone d’in tareda dibin screen d’in wayar yaga sunan mahaifinsa b’aro b’aro receiving call yayi ya kara wayar akunnensa yace”Alhaji ina wuni”.
Ab’angaren Alhaji Tasi’u yace”lafiya k’alau Basheer kana ina?”.
“ina gida Alhaji”.
“kazo gidana yanzu yanzun nan ka sameni akwai muhimmiyar maganar da zamuyi”.
“ba matsala gani nan zuwa yanzu”.
“OK sai kazo ina jiranka”.
“to Alhaji ka gaida hajiya”.
“zataji da yardar Allah”.Alhaji Tasi’u ya katse wayar da kansa.

Basheer yana k’arasa wayar ya kalli Haseena dake tsaye k’yam ta tsura masa idanu babu ko k’iftawa, ce mata yayi”baby na fasa zuwa kasuwa gidanmu zanje yanzu Alhaji ya kirani yace yanason ganina agidansa”.
Haseena ta rungume hannunta saman k’irjinta tace”ba damuwa amma karka dad’e sosai mijina domin kasan ni kad’aice acikin gidan nan”.
“bazan dad’e ba kinji”.Inji yah Basheer.
“Allah ubangiji ya kaika lafiya ka dawo lafiya”.
Yah Basheer ya mannata a k’irjinsa yayi mata kiss abaki yace”amin”.
Jayeta yayi ajikinsa ya fice daga cikin d’akinta alokacin ne Haseena tayi huci mai tattare da d’acin rai tace”nasan kiran da akeyi masa baya wuce akan maganar Naja’atu lallai babansa bayada hankali, bari dai in jira ya dawo ya gayamin dalilin dayasa munafikin mahaifinsa ya kirasa indai ni sukewa zangon k’asa zama daram agidan Basheer! “.
Tana kai k’arshen maganarta ta nufi wurin mirror ta d’auki phone d’inta ta kira nombar da suke magana d’azu lokacin da Basheer yazo dole ta katse wayar, nombar tana shiga yayi receiving call d’inta magana sukeyi naji tace masa yayi sauri yazo mijinta ya fita ad’ayan b’angaren yace mata to gashinan zuwa.
Turare ta k’ara feshe jikinta dasu masu k’amshi da narkar da zuciya wata riga ce ta d’auko ta sanya wadda da ita da babu duk d’aya saboda surar jikinta gaba d’aya afili take musamman boob’s d’inta da suke tantsa tantsa kamar su faso daga cikin riga.
Zaunawa tayi saman gado tana danne-dannen phone d’inta can taji ana knocking d’in k’ofar parlour tashi tayi da sauri ta isa wurin k’ofar ta bud’e, tsohon saurayinta ta gani Nasiru atsaye wanda abokaninsa suke kira da Nas ganinsa yasa ta fad’ad’a fuskarta da murmushi tace”Nas ina maka barka da zuwa gidana”.
Wani irin malalacin murmushi yayi mata yace”ina godiya my ‘Haseena”.
Gefen ta jaye ta bashi hanya ya shigo cikin tsakiyar parlourn yayinda ta rufe k’ofar parlour ta nufi wurinsa, saman kujera yayiwa kansa masauki yayinda ya tsurawa k’yakk’yawar halittar jikinta da idanu sai had’iyar miyau yakeyi kamar tsohon maye ita kuma sai girgiza k’ugu takeyi tana bank’are nonuwanta direct room d’inta ta wuce shi kuma sai binta yakeyi da kallo yana raya wasu abubuwa da dama cikin ransa, bata jima ba ta fito da tire d’auke ahannunta cikeda kayan mak’ulashe gabansa ta kawo ta dire ruwa kawai ya zuba yasha Haseena kallonsa tayi tace “Nas kaci wani abu mana ruwa kawai kasha fa”.

Nas yayi mata wani irin kallo idanunsa sunyi jajir jaraba ce kwance cikin k’wayar idonsa dak’yar ya bud’i baki yace “k’oshi nake Haseena banida yunwar abinci gani nazo ki gayamin dalilin dayasa kike yawan damuna da kira kullum ?”.
Haseena ta taso daga inda take ko’ina ajikinta sai rawa yakeyi kujerar da Nas yake zaune ta zauna tace”yi hak’uri Nas karkayi fushi dani yanzu dai gayamin nawa kakeso in baka? “Nasiru ya musk’uta yace “niba kud’i nake ra’ayi ba kanki kawai zaki bani in kauda k’ishirwata”.
Haseena tace”ok mu shiga cikin d’aki in baka muradin zuciyarka”.

Atare suka mik’e tsaye suka shige cikin d’akinta yayinda Haseena itace ta jagorancesa har saman shimfid’ar mijinta, cire tufafinsu sukayi sunata aikata masha’arsu acikin gidan yah Basheer.

**********************

Hajiya Hannatu itada Alhaji Tasi’u suna zaune saman cushion suna sauraren labaren duniya saiga sallamar yah Basheer ya shigo cikin tsakiyar parlourn duk’awa yayi har k’asa ya gaida iyayensa suka amsa masa fuskarsu d’auke da annuri, tashi tsaye yayi ya samu wuri k’asan carpet yana zama Alhaji Tasi’u ya dubesa atsanake cikin karantarsa yace”Basheer”.”Na’am Alhaji”.”Kasan dalilin dayasa na kiraka “.”A’a Alhaji gaskiya ban sani ba “.Alhaji ya sauke gwauron numfashi yace”shekaranjiya wani labari ya riskeni wanda banji dad’insa ba kwata kwata bai dace ace kaine kake aikata irin wad’annan abubuwan ba marasa k’yawo sosai, bakason idan ‘ya’yanka suka taso suyi koyi da k’yawawan halayenka kaji tsoron Allah ka daina cutar da rayuwar Naja’atu! “.

Basheer ya d’ago kansa da sauri yace “k’arata ta kawo muku nifa babu abinda nakeyi mata na cutarwa, duk wanda ya gaya muku ina musgunawa rayuwar Naja’atu k’arya yakeyi wlh”.”Kai Basheer yiwa mutane shiru azzalumi mara tsoron Allah! Baffa Zakarin ne zaiyi maka k’arya? “.Basheer ya b’ata fuska kamar zaiyi kuka yace”Hajiya shi wa nene da baya k’arya? Idan har rabani yakeson yayi da d’iyarsa aiba sai ya bini da k’azafi ba ko ta lalama zai iya cewa in sakar masa d’iya! “.Muguwar harara hajiya Hannatu tayi masa tace”sannu isasshe gara daka nuna mana halinka afili Basheer tun yanzu kaje ka saketa d’in wawan banza! “.”Yanxu hajiya akan wata banzar yarinya kike zagina? “.”Na zageka Basheer saboda na fahimci bakada halayyar k’warai ko kad’an arayuwarka! “.Basheer yaji zafi har cikin zuciyarsa kallon mahaifinsa yayi yace “Alhaji kanajin yadda take zagina kamar ba itace ta haifeni ba! “…………..
[11/25, 4:01 PM] Mugiratmusa66: ????????????????????????
*RASHIN SO*
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION*®✍????
(Onward together).

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*

*Dedicated to*
*Sis Najer’art*

_Free page._

*PAGE 13*

 

Alhaji Tasi’u ya katse masa hanzari yace”kul!Kada in sake jin wannan mummunan maganar ta fito daga cikin bakinka Basheer mahaifiyarka ce ya zamo dole ta gaya maka gaskiya komai d’acinta,kuma Baffa Zakari baya tab’a yi maka k’arya saboda haka ka gyara zamantakewar rayuwar gidanka ka daina nuna bambanci atsakanin matanka shi aure da kake gani *AMANA* ne tsakanin mata da miji duk wanda ya zalunci d’aya sai amana taci shi, kaji tsoron Allah ka guji ranar nadama domin ubangiji baya tab’a yafe hak’k’in wani akan wani duka matanka Naja’atu da Haseena ya dace ka dinga kwatanta adalci atsakaninsu, duk dayake bazaka iya daidaita so da k’auna atsakaninsu ba kayi iya bakin k’ok’arinka wurin ganin ka tseratar da kanka daga shiga wutar jahannama!”.Duk’ar da kansa k’asa yayi yana jijjiga kansa kamar nasihar da Babansa yakeyi masa tana shigarsa, hajiya Hannatu itama shiru tayi tana sauraren wa’azin dake fitowa daga cikin bakin mijinta.
Ya k’ara da cewa”bai kamata ace baka bata ci, sha, sutura, kula da ‘ya’yanka kaidai babu wadda ka sani sai Haseena gwargwado kanada kud’in da kake iya d’aukar nauyinsu, amma ace kayi biris ka k’yaleta itada yaranta saidai idan cin mutunci ne da duka nan ka k’ware waishin jakar gidanku ce ko kuwa baiwarka ce!?”.
Hajiya ta gyad’a kanta tace”gaya masa dai Alhaji abubuwan da Basheer yakeyi sunyi yawa sosai! Miyasa bakada zuciyar tausayi ‘ya’yanka da Naja’atu ace basu tab’a jin dad’inka ba? Ahaka kakeson yaran su tashi suji tausayinka ko su k’aunaceka rayuwarka tanada gyara Basheer idan baka gyara halayyarka tabbas wata rana zakayi nadamar abinda kakeyiwa Naja’atu da ‘ya’yanta, ni ban tab’a ganin *RASHIN SO* irin wannan ba da toshewar basira! “.
Alhaji Tasi’u ya dubesa yace”Basheer ka gayamin mi yake damunka anya kana cikin hayyacinka!?”.Basheer yaji wani irin d’aci da k’ololon bak’in ciki ya tokare masa ak’irji saboda shi arayuwarsa ya tsani atisashi agaba anayi masa fad’a, ya k’udurta azuciyarsa ko an maida Naja’atu agidansa saiya d’auki fansar dukan da yayanta Hamid yayi masa!.
B’oye b’acin ransa yayi agabansu Alhaji murmushin da baikai zuci ba yayi yace”babu abinda yake damuna Alhaji ku gafarceni nasan nayi kuskure amma da yardar Allah irin haka bazai sake faruwa ba”.
Daga Alhaji Tasi’u har hajiya Hannatu suji dad’in maganarsa sosai har cikin ransu, farin ciki da murna ne ya shimfid’u asaman fuskokinsu k’arara cikin walwala Alhaji Tasi’u yace”komai ya wuce Basheer yanzu abinda ya rage maka ka samu lokaci kaje gidan iyayen Naja’atu ka basu kuma ka mayarda ita d’akinta”.
“zan saka rana inje gidansu Alhaji karku damu”.Cewar Basheer.
“ba matsala dama mutum duka mai kuskure ne Allah yayi maka albarka”.Inji Alhaji Tasi’u.
“Amin Alhaji”.
Hajiya Hannatu ta gyara zamanta tace”ka k’ara hak’uri da juriya akan zamantakewar rayuwar aurenka Basheer sannan mu mata da kake ganinmu da hankalinku da tunaninku ba d’aya bane da namu, ita mace an halitta ne da awazar namiji shiyasa Allah ya d’aukakaku akanmu ba’a tab’a had’a hankalin namiji da mace ba Basheer saboda haka na rok’eka dan girman Allah ka dinga hak’uri da iyalinka, duka-duka idan kana duba da la’akari duniyar nan guda nawa take?Da sannu sannu za’a wayi gari duk babu mu cikinta mun mutu mun koma wurin muhalinccinmu daga mu sai abinda muka shuka zamu taras cikin kabarinmu! “.
“ba komai hajiya zanyi k’ok’ari in gyara kuskurena”.
Alhaji Tasi’u yace”zaka iya tafiya ba matsala”.
Basheer ya mik’e tsaye cikin ladabi kamar na k’warai yace”na barku lafiya”.Yana rufe bakinsa ya fice daga cikin parlourn da sauri yabar iyayensa suna tattaunawa akan lamarin gidansa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button