HAUSA NOVELRASHIN SO Complete Hausa Novel

RASHIN SO Complete Hausa Novel

____________________

Koda yah Basheer ya koma gidansa bai iske Nasiru ba saboda har sun gama masha’arsu Haseena ta bashi kud’i dubu talatin domin ya ajiye mata awurinsa yayi tafiyarsa, bai fahimci abinda Haseena ta aikata ba daya dawo tambayarsa tayi dalilin dayasa mahaifinsa ya kirasa bai b’oye mata komai ba ya kwashe labarin nasihar da sukayi masa ya gaya mata, taji wani irin d’aci azuciyarta amma bata nuna masa ko azahiri ba tace”yanzu kana nufin mayar da ita gidanka zakayi?”.
“eh mana zan mayar da ita amma ba yanzu ba saita dad’e gidansu”.
Haseena ta saukar da numfashi tace”baka tsoron kada iyayenka suji labarin bakaje gidansu Naja’atu ba ka basu hak’uri”.
Yah Basheer ya kalli k’wayar idonta yace”bakisan yadda na tsani Naja’atu ba azuciyata kwata kwata banason zamanta agidana, ko iyayena sunji nasan yadda zan k’ara lallab’asu in basu hak’uri saboda yayanta Hamid yayimini mugun walak’anci a cikin office d’ina”.
Waro idanunta tayi ta rik’e baki tace”darling mi ya had’aka da Hamid kuma?”.
“office d’ina ya shigo yanata zagina harda taramin jama’a ana kallonsu, abin dai babu k’yawon gani Haseena”.
Haseena ta yamutsa fuska cikin munafurci da zugi tace”amma Hamid ya raina maka da wayo taya zai iskoka har cikin office d’inka ya nemi ya yaga maka rigar mutunci ya dace ka tashi tsaye ka d’auki mummunan mataki akansa! “.
“ai bazan tab’a k’yalesa ba tsohon munafikin ubansa zan gayawa abinda yayi mini yaja masa kunne! “.

“tabbas ya kamata kaje ka sami ubansa kace ya jawa shegen d’ansa kunne idan ba haka ba duk abinda da kayi masa to taurin kansa yaja masa”.

“sai gobe zan iskoshi wurin sayar da itacensa”.
Haseena ta k’yalk’yale da dariyar k’eta tace”shi Zakarin faskaren itace yakeyi dashi yake ciyar uwar Naja’atu ashe k’aton matsiyaci ne! “.
“auu dama baki sani ba ban baki labari ba ai ubanta k’aton talaka ne bai aje komai ba sai tsiya, lokacin da akayi aurena da Naja’atu ko gidan shiga baya dashi akan talauci kamar kusun masallaci”.
Haseena ta karkace baki tace”irinsu matsiyatan nan idan suka samu wuri sunfi kowa gadara da jin kai”.
Basheer yace”sudai suka sani idan domin nine su rik’e d’iyarsu banaso”.
“ai gara ka mayar da matarka ko domin saboda ‘ya’yanka kasan ni ba ‘yar rainon ‘ya’ya bace! “.

Basheer ya jawota ya rungumeta ajikinsa yace”na sani baby so nake ta gane akwai banbamci tsakanin gidansu da zama gidana”.
“kuma kanada gaskiyarka mijina”.

*********************

Baffa Zakari ya dawo gida bayan yaje wurin Alhaji Tasi’u ya gaya masa duk abinda ake ciki, isko Anna yayi tana daka aturmi tana ganinsa ta aje tab’arya sannu ahankali k’asa ta shimfid’awa Baffa tabarma ya zauna itama ta zauna tace”maigida har ka dawo?”.
“na dawo Balira”.
Anna ta dubesa tace”ka samu damar ganawa da Alhaji tareda gaya masa irin rashin mutunci da tozarcin da d’ansa yake yiwa Naja’atu?”.
Baffa Zakari yace”na sanar masa duk abubuwan da suke faruwa babu abinda na b’oye masa karkiso kiga yadda Alhaji ya nuna tsantsar b’acin ransa da bak’in ciki afili, hmmm Alhaji yanada kirki yasan darajar d’an Adam arayuwa duk da yanada rufin asiri baisa ya dinga walak’anta mutane ba, amma tir da halin Basheer albasa bata biyo halin ruwa ba!”.

Anna tace”Allah yayi wadaran naka ya lalace ai Basheer yayi nisa bayajin kira Allah ubangiji ya shiryeshi”.
“Amin ina Naja’atu taje ne naji banji motsinta ba itada yaranta?”.
Anna ta kishigid’a bayanta ga bango tace “suna cikin d’aki suna fira”.
“Allah sarki bari inje wurin sana’ata”.Cewar Baffa ya tashi tsaye yana gyara rigarsa.
“Allah ya bada kasuwa saika dawo”.
“Amin Balira”.
Ficewa yayi daga cikin gidansa ya nufi rumfar da yake zama yana sayar da itacen abinci, koda ya isa ya iske rumfar cikeda abokan sana’arsa da mutane anata firarraki da dariye dariye tsoma bakinsa yayi aka cigaba da firar dashi tareda gudanar da tsabtacciyar sana’arsu.

____________________

*BAYAN KWANA BIYAR*

Da Basheer ya kori Naja’atu daga cikin gidansa saiya zamana cin amarcinsa yakeyi da Haseena babu kama hannun yaro, soyayya da tsantsar kulawa suke nunawa junansu fiye da misali babu ne kawai basa ci agidansu saboda duk abinda Haseena takeso jikin Basheer yana rawa har sai ya nemo mata shi ya kawo mata sannan hankalinsa zai kwanta, soyayya da k’aunar Haseena ta riga tayi masa mugun kamu azuciya ya fad’a cikin kogin soyayyarta sai nitso yakeyi acikinsa, ganin Basheer ya mutu sonta shiyasa take juyashi son ranta kamar yadda ake juya waina atanda, tareda shimfid’a izzar mulkinta agidansa duk abinda ta bashi umurni tace yayi shi yakeyi wanda ta hanesa dayi bazaiyi ba, domin yana matuk’ar gudun fushinta da b’acin ranta idan akwai abinda ya tsana bai wuce yaga Haseenarsa ba cikin damuwa ko bak’in ciki shiyasa yake iya bakin k’ok’arinsa wurin bata kulawa da tarairaiyarta kamar k’wai.
Baffa Zakari yana zaune cikin rumfarsa yana saida itace yayinda abokinsa Malam Buba yake zaune agefensa yana saida kayan miya, mutane d’ai d’aya sai shiga sukeyi suna sayen kayan miya ko itace can saiga yah Basheer ya parker mashin d’insa kusa ga rumfar saida ya bari mutanen sun gama sayan itace da kayan miya, sannan ya sauko saman machine d’insa ya nufi rumfar Baffa gadan gadan babu alamun fara’a afuskarsa yana zuwa babu ko sallama yace”tsoho wurinka nazo! “.

Jin magana daga sama yasa Baffa ya d’ago kansa da sauri idanunsa suka fad’a cikin na yah Basheer yace”a’aaa Basheer kaine arumfata sannu da z…….. “.
Bai bari ya k’arasa maganarsa ba ya tari numfashinsa yace”kai dakata tsohon munafiki! Bashi ya kawoni cikin k’azamar rumfarka ba”.
Imani da mamaki suka yiwa Baffa yawa yayi tsaye k’yam yana kallon rashin mutunci da tijara irinta d’an zamani, cikin sanyin jiki ya nuni kansa yace “Basheer kana cikin hayyacinka kuwa nine bak’in munafiki!?”.
“ance maka bak’in munafiki wanda baiyiwa shegiyar d’iyarsa tarbiya ba! “.
Malam Buba baiso sanya bakinsa cikin lamarin da amma ganin yadda Basheer keson tozarta abokinsa yasa ya taso daga inda yake yace “d’an samari lafiya mi Zakari yayi maka ne da zakazo tsakar kasuwa ka aza masa tijara da cin mutunci!?”.
Basheer ya juyo ya wurgawa Malam Buba uban harara yace”babu ruwanka Malam saboda haka ka rufemin bakinka!”.
Malam Buba yayi mamakin rashin kunyar Basheer k’ara isowa wurin Baffa yayi ya dafa kafad’arsa cikin jimami yace”Zakari ina ka jajibo mana wannan fitsararren yaro?”.
Cikin mutuwar jiki Baffa yace “mijin Naja’atu ne Buba”.

Yah Basheer ya zaburo da k’arfi kamar zai daki Baffa Malam Buba ya shiga tsakaninsu, Basheer ya dinga zabure zabure yana cewa “daka barni naci mutuncin tsohon banzan nan! Saboda yana bak’in munafiki yaje har gidan iyayena ya kwashe k’arya da gaskiya ya gaya musu yace ina cutar da d’iyarsa, to idan ina cin amanarta ka rik’e ‘yarka mana banaso! Sannan daga k’arshe ya turomin wawan d’ansa Hamid ya iskoni har cikin office d’ina yana zagina da dukana kamar jaki, saboda haka ayau saina d’auki fansar dukana da d’anka yayi ajikinka!”.

Malam Buba yace”kayi hak’uri ai Zakari uba yake agareka”.
“bazanyi ba ka jaye ka bani wuri ko in d’ungujeka ka fad’i k’asa! “.Mutane jin hayaniya tana tashi yasa suka taru mak’il sukayi cincirido suna kallon diramar da akeyi………
[11/25, 4:01 PM] Mugiratmusa66: ????????????????????????
*RASHIN SO*
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button