RASHIN SO Complete Hausa Novel

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION*®✍????
(Onward together).
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sis Najer’art*
_Free page._
*PAGE 14*
Ganin Basheer ya kafe yana turjewa akan Malam Buba ya bari ya isa wurin Baffa ya dakesa dole wasu dattijawa guda biyu sukazo suka b’anb’aresa ajikin Malam Buba, jan hannunsa sukayi suka fitar dashi daga cikin rumfar mutane sai kallonsa sukeyi suna Allah wadaran da hali irin Basheer tareda tsine masa albarka!.
Baffa tsaye yake k’yam kunya tayi masa yawa cikin zuciyarsa, Malam Buba ne ya juyo yacewa mutane”lafiya kuka tsaya kuna kallonmu? Kowa ya watse ya kama gabansa!”.Mutanen dake cike bakin rumfar sukayi fara watsewa sufsufsuf kamar munafukai, haka suka cigaba da watsewa kowa yayi tafiyarsa inda zaije.
Ganin sun watse yasa Malam Buba ya sauke gwauron numfashi ya kalli Baffa yace”kayi hak’uri Zakari da abinda wannan yaron yayi maka saboda gaskiya bai nuna tarbiya ba!”.
Wani irin tururin d’aci rai da bak’in ciki ne ya gauraye sassan jikinsa da zuciyarsa rad’ad’i da k’una kawai zuciyarsa keyi! Ya rasa abinda yakeyi masa dad’i aduniya saboda tunda ya taso arayuwarsa tun k’urciya zuwa tsufansa ba’a samun wanda yaci masa mutunci ya tozartashi gaban mutane ba sai Basheer, tsantsar nadama da dana sani ne ya shimfid’u asaman fuskarsa tabbas yayi nadamar aurawa Basheer ‘yarsa Naja’atu!.
Nannauyar ajiyar zuciya mai tattare da d’acin rai yayi yace”ba komai Buba k’urciya ce ke damunsa wata rana sai labari”.
Malam Buba yayi murmushi mai bayyanar da d’acin rai yace”Allah ubangiji ya shiryeshi”.
“Amin Buba”.
Zazzaunawa sukayi saman teburin katako kowane daga cikinsu ya cigaba saida kayan sana’arsa, mutane suka dinga shigowa suna saye idan wancan ya fita sai wannan ya shigo haka dai suka cigaba da gudanar da harakokin sana’arsu cikin natsuwa.
__________________
Baffa Zakari bai koma gida ba sai kusan bayan sallar la’asar yana shiga cikin gida ya iske Anna tana ba awakinta dussa, yayinda Naja’atu take girka tuwon garin masara da miyar d’anye kub’ewa cikin kitchen azaune gefe Rufaida ce da Suhail suke yin wasar k’asa.
Sallamar Baffa ne yasa suka shek’a da gudu suka rungumesa dak’yar ya jayesu ajikinsa yaja hannunsu suka zazzauna saman tabarma, Anna tana lura da shigowarsa ta fito daga cikin awaki ta nufi randar ruwa ta d’ebo masa ruwa akofi, tana k’arasowa wurinsa tayi masa sannu da zuwa ya amsa mata cikin sakin fuska ruwan ta bashi yasha sannan ta zauna kusa gareshi tace”ya gajiyar hanya maigida?”.
“ba gajiya Balira”.
Shiru yayi bai sake magana yana sak’e sak’e acikin zuciyarsa can yaja numfashi cikin jimami da yanayin damuwa yace”ban tab’a tozarta ba irin yau Balira ashe yaron nan ba k’aramin mara mutunci bane ban tabbata ba sai yau”.
Naja’atu dake cikin kitchen dumm taji gabanta ya fad’i zuciyarta ta tsinke domin tana jiyo firar da Baffa yakeyi da Anna.
Anna ta kallesa cikin zullumi tace”ban fahimci inda maganarka ta dosa ba waye bayada mutunci sannan kuma ya tozartarka cikin jama’a!?”.
Baffa yayi hucin takaici ya kwashe labarin komai ya gaya mata irin tijarar da Basheer yayi masa akasuwa, yanayin bak’in ciki da takaicin rayuwa ne ya shimfid’u afuskokinsu Anna itada Naja’atu saboda abinda yayiwa Baffa akasuwa ya k’ona musu rai matuk’a.
Tsantsar damuwa da tsananin takaici ne shimfid’e afuskar Anna jijjiga kanta kawai takeyi cikin alhini can tace”maigida agaskiya wannan yaron bayada hankali ban tab’a tsammanin zai iya yi maka rashin mutunci da tozarci atsakar kasuwa ba, saboda haka kawai araba aurensa da Naja’atu kowa ya tsaya matsayinsa!”.
Baffa Zakari yace cikin jimami”ba za’ayi haka ba Balira shi aure da kike gani rai dashi babu wanda yasan lokacin k’arewarsa sai ubangiji, sannan abinda duk Basheer yayimin na walak’anci yaje duniya ce tana iya da kowane shege kuma zata koya masa hankali”.
Anna ba haka taso ba har cikin ranta taso ya amince da shawarar data bashi na araba auren, amma ya kasa fahimtarta cikin sauk’i danne abinda yake cikin zuciyarta tayi tace” babu komai Allah ya sawwak’a”.
“amin”.Yace zuciyar nan tasa cunkushe da bak’in ciki da d’acin rai sai sak’a da warwara zuciyarsa keyi.
Naja’atu ce ta fito daga cikin kitchen cikin b’acin rai da tsantsar damuwa akan tozarcin da Basheer yayiwa mahaifinta, bata tab’a zaton rashin imaninsa ya wuce nan ba sai yanzu bata tab’a tsammanin zai iya ciwa mahaifinta mutunci ba sai yanzu data tabbatar, ashe *RASHIN SO* da k’iyayyar da yakeyi mata ta wuce tunaninta da hasashenta tabbas Basheer ya cika mara mutunci wanda baisan halacci da amana ba, hawaye masu zafi suka dinga shatata afuskarta tana sharewa cikin yanayin damuwar data b’oye azuciyarta ta iso wurin iyayenta ta duk’a har k’asa ta gaidasu cikin kunya amsa mata sukayi cikin sakin fuska.
Alokacin ne Baffa ya dubeta yace”Naja’atu Allah ubangiji yayi miki albarka ki cigaba da hak’uri kinji komai yayi tsanani sauk’insa yana nan tafe, idan mijinki yazo biko ki daure ki bishi ba komai halin rayuwa ne wata rana zaki tsinci kanki cikin rayuwar farin ciki”.
Kwallar zallar takaici ne ya zubo afuskarta tayi sauri ta share cikin tausayin iyayenta tace”Baffa zan bi dukkan umurninka saboda nasan duk abinda ya faru dani yana daga cikin kundin k’addarata “.
Baffa yace”haka nakeson ji ubangiji ya cireki daga cikin rayuwar bak’in ciki”.
Anna da Naja’atu sukace”Amin”.
Naja’atu ta tashi daga tsugunne ta fad’a cikin d’akin Anna ta shiga ta kwanta saman gadon mahaifiyarta, hawaye masu rad’ad’i sai shatata sukeyi asaman k’yakk’yawar fuskarta wani irin k’ololon bak’in ciki da takaicin Basheer ya dinga taso mata a k’irji, ta rasa sukuni da walwala agidan Basheer yanzu bayan ta koma gidan iyayenta akan baya sonta shine ya iske mahaifinta har kasuwa yaci masa mutunci, wannan wane irin masifa da rayuwa ce mai cikeda tashin hankali da rikicewar rayuwa!.
Juye-juye ta dingayi saman gado damuwa cunkushe azuciyarta babu inda zata saka rayuwarta taji sanyi a duniya, shiru tayi tana maganganun zuci da sak’e sak’en zuciya yayinda hawayenta suka cigaba da gangarowa daga cikin k’wayar idanunta kallo d’aya zakayi mata ka gano tana cikin k’unci da tsananin damuwa.
___________________
Haseena ce zaune saman k’afafunsa daga su sai kayan shan iska, yah Basheer sai wani shige mata yakeyi cikin jiki yana kissing d’in sassan jikinta ita kuma sai wani langwab’ewa takeyi ajikinsa kamar jaririya tace”farin cikina”.
“Na’am babyna”.
Haseena ta narke fuskarta tace”kaga Baffan Naja’atu ka gaya masa cin mutuncin da Hamid yayi maka?”.
Basheer ya shafi fuskarta cikin so yace”na iskoshi acan shagon rumfarsa nayi masa kashedi akan d’ansa yazo yaci mini mutunci har cikin office d’ina”.
“gara da kayi masa haka domin ni da kake ganina nan na tsani raini da walak’anci shiyasa kaga ban faye shiga cikin sha’anin mutane ba”.
Basheer ya maidata saman kujera gab da gab dashi suna shak’ar k’amshin turaren juna yace”ai saina nuna masa shi k’aramin d’an iska zan mayarda Naja’atu in cigaba da gana mata azaba da uk’uba iri iri daban daban acikin gidan nan, babu wani mai k’watarta ahannuna sai Allah! “.
Haseena ta kauda kanta gefe tace”shawararka tayi habibi kasa ranar da zaka mayar da ita”.