HAUSA NOVELRASHIN SO Complete Hausa Novel

RASHIN SO Complete Hausa Novel

“zanyi tunanin ranar data dace inje inyi bikonta Hasee baby”.
“yadda kikeso haka zanyi baby”.
Cigaba da firarsu sukayi cikin walwala da annashuwa mara misaltuwa daga baya Haseena ta mik’e tsaye ta shiga cikin kitchen ta d’auko musu abinci da plates da lemun kwakwa, tire ta kawo ta aje agabansa itama ta zauna k’asa sanya musu abincin cikin plate d’aya tareda saka musu lemun kwakwa akofi guda biyu, fara ci sukayi atsanake babu abinda kakejin yana k’ara sai TV.

********************

Yah Hamid yake sanya shaddarsa fara ya kawo turare ya feshe jikinsa dashi Bilkisu tana tsaye tana tayasa sanya kayansa, hula da takalmi ta ciro masa cikin drower kawo masa tayi tace”Abban Hassan wannan kwalliyar sai ina?”.

Kallonta yayi ya sakar mata murmushi yace”rumfarsu Baffa zanje in gaidashi my billy”.
Bilkisu tayi fari da idanunta cikin nishad’i tace”yanzu duk wannan had’add’iyar kwalliyar ta zuwa wurin Baffa ne?”.

Hamid yace”daga wurinsa zan biya in gaidasu Anna”.
“ka gaidamin dasu please”.
“sak’onki zai isa wurinsu”.
Yana rufe bakinsa ya fice daga cikin d’akin yayinda yabar Bilkisu tana gyare-gyare.

********************
Baffa Zakari suna zaune cikin rumfa suna magana shida Malam Buba yayinda mutane sai shigowa sukeyi turururu suna siyen kayan miya da itace, daga k’arshe da suka tsagaita da shigowa alokacin ne Malam Buba ya dubi Baffa yace “Zakari yaron nan surukinka bayada kirki ko kad’an arayuwarsa ban tab’a tsammanin zai iya kallon k’wayar idanunka yaci maka mutunci ba”.
Baffa yace”ai inda kake zaton yaron nan ya wuce saboda yadda yake walak’anta rayuwar Naja’atu da barinta da yunwa itada ‘ya’yanta abin sai ya baka tausayi, ni kaina nayi dana sanin bashi auren d’iyata domin bai dace da rayuwarta ba yanzu ma maganar da mukeyi dakai ya korota daga gidansa tana nan gidana zaune kuma har yanzu bai biyota ba”.
Malam Buba ya girgiza kai cikin jimami da bak’in cikin rayuwa yace”banji dad’in wannan lamari ba Zakari shawarar dazan baka shine idan har yazo biko ku barshi ya tafi da matarsa ko domin darajar ‘ya’yansa sannan mahaifinsa Alhaji Tasi’u mutumen kirki ne bayada wata matsala arayuwarsa “.
“bazan hanashi zuwa da matarsa ba idan yazo aini bana fatar in zamo silar kashe mata aure Buba, sai dai inyi mata addu’ar Allah ubangiji ya daidaita atsakaninsu”.

Malam Buba ya kalli Baffa cikin tausayawa da tsantsar damuwa yasan Baffa mutum ne mai sauk’in kai da tsananin hak’uri da kawaici akan dukkan abinda yake fuskanta, bayada rik’o azuciyarsa sannan yana saurin hucewa idan abu ya b’ata masa rai dafa kafad’arsa yayi yace” hak’ik’a Zakari kanada zuciyar k’warai kai mutum ne mai saurin manta sharri da rik’o da alkhairi Allah ubangiji yayi mana jagora acikin lamurranmu”.
“Amin ya aka iya zaman duniya ma gaba d’ayansa sai mutum yayi hak’uri yake kaiwa ga nasara”.”maganarka hak’k’un ce Zakari “.Malam Buba yana rufe bakinsa suka hango yah Hamid tafe saman mashin d’insa yana isowa ya sauka saman mashin d’in tareda parkersa agaban rumfar, direct ya nufi cikin rumfar da sallama abakinsa amsa masa sallamarsa sukayi cikin walwala duk’awa yayi har k’asa ya gaidasu suka amsa masa…….
[11/27, 1:47 PM] Mugiratmusa66: ????????????????????????
*RASHIN SO*
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION*®✍????
(Onward together).

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*

*Dedicated to*
*Sis Najer’art*

_Free page._

*PAGE 15*

 

Hamid ya tashi tsaye ya isa wurin mahaifinsa yana isa Baffa Zakari ya tambayesa akan wane dalili zaije har cikin office d’in Basheer yaci masa mutunci?.Yah Hamid ya kama wani kame-kame yana kakkaucewa yana cewa shi baici masa mutunci ba, magana kawai yayi masa akan ya daina walak’anta rayuwar Naja’atu Baffa Zakari yayi masa nasiha da maganganu masu sanyaya zuciyar mai sauraro tareda nuna masa kada ya kuskura ya sake zuwa office d’in Basheer koda wasa, ya nuna masa matuk’ar b’acin ransa dayi masa kashedi akan babushi babu Basheer, dayake yah Hamid nagartaccen mutum ne yaba mahaifinsa hak’uri tareda yi masa alk’awarin bazai k’ara takawa office d’insa ba, Baffa yaji dad’in yadda ya nuna nadamarsa afili domin yasan d’ansa yanada tarbiya da halin dattako dazai wuce ya d’auko dubu ishirin yaba Baffa, alal hak’ik’a Baffa yaji dad’in wannan k’yautar matuk’a saka masa albarka ya dingayi har saida yah Hamid ya fice daga cikin rumfar, isa wurin Malam Buba yayi ya ciri dubu biyar daga cikin kud’in ya bashi shima yayi godiya matuk’a tareda k’ara sakawa yah Hamid albarka, tabbas d’an kirki na kowa ne d’an banza kuwa na iyayen da suka haifeshi ne haka dai suka zauna suna yabon halayyarsa da kuma yadda yake k’ok’ari wurin taimakawa mahaifinsa tabbas halayyar Hamid abar koyi ce da sha’awa, saboda mutum ne mai taimakawa mahaifinsa da tsantsar tausayinsu baya cewa iyalinsa kawai zai taimakawa yasan kima da darajar iyayensa.

___________________

*BAYAN WATA HUD’U*

Naja’atu ta cigaba da zama gidansu itada yaranta yah Basheer har yanzu bai biyota ba kuma iyayensa basuda labarin cewa bai mayarda Naja’atu d’akinta ba, haka take zaune da iyayenta cikin kwanciyar hankali da kulawa domin Baffa yana k’ok’ari wurin ganin ya farantawa Naja’atu da yaranta duk abinda suke buk’ata wanda baifi k’arfinsa ba gwargwado yana yi musu, itama Anna ba’a barta abaya ba wurin k’yautatawa Naja’atu yah Hamid ma kusan kullum yana wurin k’anwarsa suna fira yana d’ebe mata kewar rashin miji nagari, Naja’atu ta samu walwala da annashuwa nan da nan ta chanza tayi k’yawo fatarta ta k’ara haske da shek’i ,kallo d’aya zakayi mata ka gane ta samu natsuwa da jin dad’in rayuwa domin agidansu babu mai takura mata ko hantararta.
Kowa sonta yakeyi babu mai tsamgwamarta tareda nuna mata *RASHIN SO*.

Naja’atu ce ta kammala wanke kayansu Rufaida yayinda su kuma suke guje-guje da wasanni itada Suhail,yaran sunfi sakewa da jin dad’i agidan Baffa Zakari saboda kowa sonsu yakeyi tareda nuna musu tsantsar k’auna da soyayyar gaskiya, shiyasa suma sukayi k’iba suka k’ara haske, Rufaida da take zuwa school Naja’atu mai mashin ta d’auka mata wanda zai rik’a kaita yana dawowa da ita, shi kuma Suhail sai wata shekarar zata sakashi aschool.
Bayan ta gama wankin ta shanya kayan asaman igiyar shanya, sannan ta shiga cikin d’aki ta d’auko tsintsiya ta fara share tsakar gidan cikin tsabta da natsuwa, cigaba da sharar tayi harta kammala ta kwashe sharar data tule awuri d’aya ta saka cikin kwandon shara, kiran Rufaida tayi tace”zo kikai sharar abola”.
Rufaida ta shek’o da gudu tazo wurinta tace”to Ummi yaushe zaki koma wurin Abbana?”.
Naja’atu ta harareta tareda had’iye wani abu mai d’aci a mak’oshinta tace”dallah ban sani ba! Banason surutun banza da yofi”.
Rufaida tace”Ummi tambayarki kawai nayi”.
“ki d’auki sharar kije ki zubar kada ki b’atamin rai yanzu in faffasa miki jiki da bulala”.
Rufaida ta marairaice fuskarta tace”kiyi Ummi Allah ya huci zuciyarki”.Tana rufe bakinta ta d’auki kwandon sharar ta nufi waje wurin bola,bata jima ba ta dawo cikin gidan ta aje kwandon sharar atsakiyar gida kallon mahaifiyarta tayi tace”Ummi na zubar”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button