HAUSA NOVELRASHIN SO Complete Hausa Novel

RASHIN SO Complete Hausa Novel

Naja’atu ta saukar da numfashi sannu ahankali tace”kinyi k’ok’ari Allah ubangiji yayi miki albarka”.

Cikin jin dad’i Rufaida tace”amin Ummi”.Komawa wurin Suhail tayi suka cigaba da wasanninsu da guje-gujensu suna tsalle da dariye-dariye na k’urciya.
Tabarma Naja’atu ta shiga ta d’auko cikin d’aki ita kad’aice acikin gidan saisu Rufaida saboda Anna ta tafi biki gidan mak’wabta, zaunawa tayi ta d’auko arba’una hadith tana karantawa bata dad’e da fara karatu ba saiga sallamar Saliha ta shigo cikin gidan amsa mata Naja’atu tayi cikin sakin fuska da walwala sosai, k’arasowa tayi wurin Naja’atu tayi ta rungumeta cikin tsananin farin ciki da murnar ganin juna, sun jima k’ank’ame da juna sannan daga baya suka zare jikinsu ana juna Naja’atu ta sakar mata murmushi tace”Aminiya nayi matuk’ar kewarki”.
“nima nayi kewarki yaushe da rabon da muga juna”.
“gaskiya munyi wata uku rabon da muga juna yanzu dai d’an bani minti biyar ina zuwa”.Cewar Naja’atu alokacin ne ta tashi tsaye ta fad’a cikin d’akin Anna bata wani jima sosai da shiga d’akin ba sai gata ta fito da tire cikeda ruwan sanyi da abinci, kawowa tayi ta aje agabanta tana jifarta da murmushi tace”bismillah k’awata”.
Ruwa kawai Saliha ta d’auka tasha sannan ta aje kofin saman tire tace”Naja’atu kiyi hak’uri da rashin zuwana wurinki wallahi bansan Basheer ya koreki daga cikin gidansa ba, sai shekaranjiya Baban Rayyanu ke gayamin amma kwata kwata banji labari ko abakin kishiyarki ba bale a mak’wabta,waishin miye musabbabin abinda yasa ya koreki daga cikin gidansa Naja’atu ko kuwa rashin son da yake miki ne ya jawo haka!?”.
Kwallar zallar bak’in ciki ne ya cika mata idanu cikin d’acin rai da jimamin walak’ancin da Basheer yakeyi mata tace”babu abinda nayi masa Saliha sona ne bayayi azuciyarsa amma rashin son da yakeyimin bai tashi bayyana ba sai bayan ya auri Haseena, ina cikin matsananciyar damuwa da k’uncin rayuwa nidai arayuwata bansan abinda nake yiwa Basheer mara dad’i ba wanda ya zamo silar haddasa walak’anci da *RASHIN SO* atsakaninmu tun farkon aurenmu dashi yana mutuwar sona ina sonshi nima, yana matuk’ar tarairaiyata tareda nuna mini tsantsar *SOYAYYAR GASKIYA* wanda baki yayi kad’an ya kwatanta irin soyayyar da yake mini, amma yanzu bansan miyasa ya juyamin baya ba alokacin da nake buk’atar kulawa da taimakonsa!”.
Tana dasa aya hawaye masu rad’ad’i suka wanke mata fuska saboda wani irin rad’ad’in ciwo da zafi takeji aranta, ta rasa sukuni da walwala azuciyarta ta rasa waye zai wanke mata cuta da rad’ad’in dake mak’ale azuciyarta tabbas har gobe tana nadamar auren Basheer arayuwarta, saboda ya riga ya hargitsa zuciyarta da tarwatsa mata farin cikin rayuwarta.
Saliha ce ta sanya hannu ta share mata hawayenta cikeda matuk’ar tausayawa da jin d’aci azuciyarta, huci tayi mai tattare da damuwa tace”ki daina kuka Naja’atu nasan yadda kikeji azuciyarki babu dad’i amma inason ki sanyawa zuciyarki hak’uri da dangana, tabbas wata rana saidai ki bayar da labari wannan abin da yake faruwa dake jarabta ce Allah yakeyi miki domin ya gwada imaninki yaga ko zaki iya yin hak’uri”.
“nasan duk abinda ya sameni yana daga cikin jarabawar rayuwata sannan Allah baya jarabtar bawa abinda bazai iya hak’uri da dangana ba, hak’k’un komai zai wuce arayuwa kamar bai tab’a faruwa ba”.

“tabbas haka ne Naja’atu Allah ubangiji ya k’yautata k’arshenmu, ina Anna taje ne tunda nazo banji maganarta ba?”.

Murmushin da baikai zuci ba tayi tace”ta tafin gidan mak’wabta biki tunda safe dagani sai yara kawai ne cikin gida”.
“Allah sarki idan ta dawo ina gaisheta”.
“zataji Aminiyata”.
Saliha ta kalleta cikin tausayawa tace”Basheer d’in yazo wurinki ne biko ko har yanzu baizo ba?”.
Naja’atu ta bintsire baki tace”hmmm ina zaizo kuwa shida yakeda Haseena kuma kinsan niba *MATAR SO* bace wadda ake so da k’auna ai ita ake biyowa biko, nida bayaso baya k’auna taya kike tunanin zai biyoni dama sakina yayi da yanzu nayi idda na samu wani mijin aure, wata k’ila in samu sassauci da jin d’adin rayuwar aure idan na k’ara gaba”.
“kidai cigaba da hak’uri komai zai yi dai-dai kuma duk abinda yafi zama alkhairi a rayuwarki Allah ubangiji ya tabbatar miki dashi Naja’atu, ya kuma kauda duk wata fitina arayuwarki ya musanya miki da wanda yafi alkhairi”.

“Amin Saliha ina Rayyanu yake?”.

“Rayyanu shida Shamsiya suna gidan iyayen Salisu sunje yi musu kwana biyu acan”.

“Ayyah idan kinje gida ki shafamin kan ‘ya’yana”.
“OK zanyi”.
Firarsu suka cigaba dayi cikin kwanciyar hankali da natsuwa Saliha ta mik’e tsaye tana niyar zuwa gida, saiga Anna ta kutso kai har cikin gidan da sallama amsa mata sukayi cikin girmamawa, Saliha ta duk’a ta gaisheta Anna ta amsa mata fuskarta asake cikin walwala sun gaggaisa sannan Saliha tayi musu sai wata rana ta nufi hanyar fita daga cikin gidan Naja’atu ta jawo mayafinta ta yafa tayi mata rakiya har bakin k’ofar gidansu, anan ma saida sukayi fira kamar kada su rabuda juna sannan ak’arshe Naja’atu ta tara mata keke napep sukayi jinga dashi ta biyasa kud’insa,Saliha ta shiga cikin napep d’in ta zauna mai keke napep ya tadda napep d’insa ya fice hannu Naja’atu ta d’aga tanayi mata bye bye ???? har saida taga b’acewar napep d’in sannan ta juya ta koma cikin gidansu cikeda matuk’ar farin ciki da sanyin zuciya.

*******************

Acikin wani madaidaicin office na hango Basheer zaune saman kujera yana wasu rubuce -rubuce atakardu,aiki yakeyi cikin himma da k’warewa kansa noce yake ak’asa ya mayarda hankalinsa kacokam akan abinda yakeyi can saiga sallamar Malam Haliru abokinsa ya shigo cikin office d’in kai tsaye, yana isowa yaja kujera ya zauna yace”sannu da aiki Basheer tun d’azu nakeson shigowa wurinka amma aiki ya b’oyeni”.

Basheer ya aje biron dake hannunsa ya d’ago kansa yace”yauwa abokina gani ina saurarenka”.

Malam Haliru ya musk’uta tareda gyara zamansa yace”ya kamata ka mayarda Naja’atu d’akinta hakanan saboda kaga ai tasha zama gidansu sosai”.
Yah Basheer yayi yak’e tareda hamma alamar ya gaji sosai yace”saboda mi zakace in mayar da ita gidana bayan kasan aduniya babu wadda na tsana irinta! Idan ina ganinta ji nakeyi kamar in dab’awa kaina wuk’a azuciya”.

Malam Haliru yaja dogon numfashi yace “yanzu kuwa zan gaya maka dalilin dayasa nace ka mayarda matarka kawo kunnenka kaji “.Basheer ya tara kunnensa adaidai bakin Haliru yana gaya masa wad’ansu irin maganganun wanda koni banji abinda suke fad’a ba balantana in sanar muku………
[11/27, 1:47 PM] Mugiratmusa66: ????????????????????????
*RASHIN SO*
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION*®✍????
(Onward together).

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*

*Dedicated to*
*Sis Najer’art*

_Free page._

 

*PAGE 16*

 

Sun jima suna maganganu akunne sannan daga k’arshe yah Basheer ya jaye kunnensa sunata k’yalk’yalar dariyar kamar bazasu daina ba, can suka tsagaita da dariyarsu yah Basheer ya kallesa yace”Haliru bakada sauk’i ashe wannan maganganu haka sai kace mai k’wak’walwar computer”.”Nifa da kake ganina banida wasa cikin dukkan lamarina”.Basheer yayi dariya yace”ai daga gani kam bakada wasa”.Malam Haliru yace”kayi hak’uri ka tabbatar da ka mayarda matarka a d’akinta kasan lamarin mata sai hak’uri da juriya”.Basheer yace”da yardar Allah zanyi k’ok’ari wurin ganin naje gidansu biko aiko iyayena basusan ban maida Naja’atu d’akinta ba, saboda tun watanni uku da suka wuce Alhaji ya kirani yayimin fad’a akan in mayarda ita d’akinta na nuna masa zan maidata amma daga baya na share da maganar domin alokacin ina cikin zafi da rad’ad’in abin gaskiya”.”Ya zakayi daurewa kawai zakayi ka maidata d……. “.Ringing d’in wayar Basheer ya katsewa Haliru hanzari dole yaja bakinsa ya tsuke Basheer ya d’auko phone d’insa dake saman teburin tareda danna receiving call yace”ina wuni Alhaji? “.
Tsawa naji an daka masa cikin wayar Alhaji Tasi’u yace”dakata banason gaisuwarka ka rik’e abarka!”.
Jikin Basheer ya d’auki rawa yace”Alhaji lafiya mi nayi maka!?”.
“wato bakasan laifin da kayi mini ba idan kanason kaji laifinka to ka iskoni gidana amma ka sani nafi k’arfin ka mayardani dattijon banza wlh! “.
“to.. to.. Alhaji ganinan zuwa yanzu Allah ya baka hak’uri”.
“bana buk’atar bayar da hak’urinka Basheer abinda nakeso kawai kazo ka sameni gida!”.
“zanzo yanzu nan”.Alhaji Tasi’u ya katse wayar ahasale cikin haushin Basheer.
Basheer ya saukar da numfashi tareda mayarda kallonsa wurin Haliru yace”Haliru Alhaji ne ke nemana agida ina ganin yanzu zan rufe office d’ina inje inji dalilin dayasa yake nemana”.
Haliru yace”ina ganin kamar baya wuce maganarka da Naja’atu da kak’i mayarda ita gidanka”.
Basheer ya jijjiga kansa alamar gamsuwa yace”nima fa haka nake tunani idan kuwa haka ne nasan zansha fad’a wurinsu Alhaji akan tsinanniyar yarinyar nan”.
“akanta ma ne saidai ka toshe kunnuwanka daga sauraren wasu maganganu saboda su iyayenka ne babu yadda zakayi dasu sai hak’uri”.
“gaskiyarka bari in had’a kayayyakina in wuce”.
Haliru ya mik’e tsaye yace”to ba matsala nizan wuce sai mun had’u amajalisarmu”.
“OK friend”.Cewar Basheer.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button