RASHIN SO Complete Hausa Novel
Naja’atu ta amsa cikin k’aunar yayanta tace”nagode yah Hamid da irin d’awainiyar da kukeyi dani da yarana banda abinda zance muku saidai ince Allah ubangiji ya saka muku da mafificin Alkhairi, saboda irin taimakona da kukeyi da bada gudunmuwarku gareni tabbas da banidaku arayuwata da bansan yadda zata iya kasancewa ba”.
Hamid ya dubeta cikin kulawa yace”ki daina fad’ar wannan maganar k’anwata duk abinda ya sameki muma ya samemu, sannan duk irin k’unci da taskun da zaki fuskanta agidan Basheer karki kuskura ki nemi takardar saki da kanki saboda hakan bayada k’yau sannan raino da tarbiyar yaranki saike Naja’atu, ke kad’ai zaki iya azasu bisa turbar gaskiya da kuma tarbiyar data dace”.
“nagode yaya insha Allahu zanyi amfani da shawararka”.
“ba komai ai bari in tara miki keke napep ku wuce”.
“to yaya”.
Suna tsaye saiga mai keke napep ya gifto ta gabansu yah Hamid ya taresa sukayi jinga ya bashi kud’insa, su Naja’atu suka shiga cikin napep d’in suka zauna mai keke napep ya tadda napep d’in suka nufi unguwar da take aure.
Suna wucewa saiga Baffa ya iso wurin yah Hamid dake tsaye awaje yana ganin babansa ya fad’ad’a fuskarsa da fara’a sosai yace”sannu da zuwa Baffa”.
Baffa Zakari yace”yauwa Hamidu su waye na hango daga nesa sun shiga cikin napep ak’ofar gidan nan?”.
Hamid yayi murmushi yace”Baffa Naja’atu ce tazo gaisheka bakanan”.
Baffa ya kallesa cikin sakin fuska yace”madallah ta k’yauta bari in shiga cikin gidan”.
Hamid yace”to Baffa”.
Baffa Zakari ya shige cikin gidan yayinda yah Hamid ya nufi gidansa wurin matarsa Bilkisu.
********************
Baffa ya shigo cikin gidan ya taras da Anna ta share gidan tass tana zaune ita kad’ai cikin gidan, yana shigowa da sallama abakinsa Anna ta amsa masa fuska asake isowa wurinta yayi ya zauna, Anna ta mik’e tsaye ta shiga cikin d’akinta ta ciko masa kwano da abinci da ruwa masu sanyi kawowa tayi ta aje agabansa, Baffa ya wanke hannunsa yayi bismillah ya fara cin abinci cikin natsuwa yayinda Anna take zaune agefensa shiru, saida yaci ya k’oshi ya kawo ruwa masu sanyi ya jik’a mak’oshinsa sannan yayi gyashi yace”Alhmdulillahi ala kullin halin”.
Alokacin ne Anna tayi masa sannu da zuwa ya amsa mata cikin fara’a da walwalar fuska, kallonta yayi yace”naga fitar Naja’atu daga cikin gidan nan ina fatar ba yaji tayo ba?”.
Anna tayi ajiyar zuciya tace”a’a ba yaji tayi ba ai kasan matsalar bata wuce daga wurin mijinta Basheer da yake barinta itada yaranta da yunwa uwa uba babu ruwansa da ciwonsu, ni ban tab’a ganin irin wannan k’addararren aure ba irin wannan na Naja’atu!”.
Baffa ya jijjiga kai yace”to ya muka iya hak’uri kawai zaki dinga bata ta tsaya ta raini ‘ya’yanta domin idan ta rabuda mijinta batasan ko hannun wace irin mace zasu fad’a ba”………
_Share&Comments_.
~~Mugirat ce~~
[11/15, 12:40 PM] Mugiratmusa66: ????????????????????????
*RASHIN SO*
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????
*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION*®✍????
(Onward together).
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sis Najer’art*
_Free page._
*PAGE 2*
Anna ta gyad’a kanta alamar gamsuwa tace”haka ne maganarka maigida amma idan da babu ‘ya’ya atsakani mizai zaunar da ita gidansa tana ganin walak’anci da k’ask’anci arayuwarta, shiyasa kaga duk ta fice cikin kamanninta ta rame tayi bak’i kamar ba da jikinta da k’yawonta ya aureta ba, tabbas da munsan haka Basheer zai walak’anta rayuwar Naja’atu da tun farko bamu bashi aurenta ba, saboda yarinyar tana cikin wahala da k’uncin rayuwa atakure take zaune agidansa”.Baffa ya dubeta yace”sanin gaibu sai Allah Balira amma idan tayi hak’uri komai zai wuce da yardar Allah, nima ban tab’a zato ko tsammanin Basheer zai yiwa yarinyar nan rik’on sakainar kashi ba wannan ai cin amana ne kuma zalunci ne babba barin iyalinka da yunwa alhalin kanada abinda zaka iya d’aukar nauyinsu”.
Anna ta bintsire baki kamar zatayi kuka tace”cin,amana ne mana ita Amaryarsa daya auro wata guda daya wuce ba tace har k’unshin ledar nama yake shigowa da ita ba yana ba Amaryar, adole shi gashi yayi sabon aure ‘yata ko itada yaranta ko ohoo saidai yunwa ta kashesu Allah dai baya kwana baya angaje shi zai yiwa Naja’atu sakayyar zaluncin da yakeyi mata wlh! “.
Baffa yace”Balira hak’uri zamuyi da irin abubuwan da Naja’atu take fuskanta agidan mijinta marasa dad’i alal hak’ik’a wata rana za taci ribar hak’urinta saboda mai hak’uri baya tab’a tab’ewa arayuwa”.
“to maigida Allah ubangiji ya musanya mata da mafi Alkhairi arayuwarta ya kuma yaye mata bak’in cikin rayuwa”.
“Amin ya rabbi Balira addu’ar daya kamata ki dinga yi mata kenan”.
“ai ina yawan tayata da addu’a maigida”.
“hakan yanada k’yau bari in shiga ciki in watsa ruwa masu d’umi”.
“to maigida”.
Yana kai k’arshen kalamansa ya tashi tsaye ya shige cikin d’akinsa yayinda yabar Anna zaune tayi tagumi tana tunanin halin da Naja’atu take ciki..
*********************
Keke napep d’in da Naja’atu ta shiga bai ajeta ko’ina ba sai a k’ofar gidan mijinta, yana parker napep d’in suka fito daga ciki mai napep yaja keke napep d’insa ya k’ara gaba, jan hannun Rufaida tayi suka shiga cikin gidan da baya za’a kirasa da gidan talaka ba kuma ba za’a ce masa mai kud’i ba gwargwado yanada rufin asiri saboda gidan ginin zamani ne anyi plaster da shafe duka gidan da painting k’ofa ce amaimakon get abakin gidan, tana shiga cikin tsakiyar gidan tayi kicib’us da Basheer dazai fita daga gidan ai yana ganinta yaja birki ya tsaya fuskarsa amurtuk’e cikin rashin annuri ya kalleta yace”Naja’atu daga ina kika fito awannan lokaci!?”.
Naja’atu tace”kaji ka da wata tambaya Abban Suhail dazan fita saida na gaya maka gidanmu zanje ziyara kuma da kanka ka bani izni na fita”.
Basheer ya harareta yace”ohh na tuna shine tun safe da kika tafi baki tashi dawowa ba sai yanzu da marece tayi, waike wace irin yarinya ce mara jin magana wato ke tafi gidanku kina shiga mak’wabta kina zagina keda k’awayenki ko!?To wallahi bazan d’auki wannan sakarci ba salon kija mini zagi agari!”.
Naja’atu ta duk’ar da kanta ak’asa tace cikin takaicin maganarsa”yaushe ka tab’a jina da kunnenka ina zaginka yah Basheer? Ko kuwa wani sharri da k’azafin da ka saba yimin ne zakayimin daga zuwa ziyara sai kace ina zuwa gida-gida ina zaginka!”.
“nasan zaki iya zagina saboda ba tarbiya kika gada ba agidanku”.
“niba yah Basheer dama bakasan banida tarbiya ba saida kayi sabon aure? Ai tun kafin ka aureni banida tarbiya sani ne bakayi ba ka aurowa kanka mara tarbiya”.
“naga alama shiyasa na fad’i haka”.
“gaskiya kam kanada fahimta sosai”.
Bata k’ara sauraren abinda zai fito daga bakinsa ba taja hannun Rufaida suka shige cikin d’akinta suka barshi atsaye, da yaga tayi wucewarta dole ya juya ya shiga d’akin Amaryarsa Haseena.
Yana shiga ya isketa zaune ta aza k’afarta d’aya saman d’aya tana taunar chewgam k’asss k’ass k’ass kawai ke tashi idan tayi k’wai, ganinsa yasa tayi murmushin dake k’ara narkar dashi cikin kogin soyayyarta tace”darling har ka dawo amma baka fita ba ko?”.
Yah Basheer ya k’araso wurinta tareda cire tufafinsa ya koma dagashi sai singlet da guntun wando ya zauna yace”ban fita ba Hasee baby ina shirin fita dai naci karo da Naja’atu ashe sai yanzu taga damar dawowa cikin gidan nan, bayan agabana ta fita tun safe”.