RASHIN SO Complete Hausa Novel

Malam Haliru ya fice daga cikin office d’in yayinda yah Basheer ya kammala had’a komai nasa yabarsu a office d’in, jawo k’ofar yayi ya kulle direct inda ya parker mashin d’insa ya nufa acikin filin school d’in, yana isa wurin mashin d’in ya sanya makulli ya tadda mashin tareda ficewa daga cikin makarantar ya nufi hanyar zuwa gidansu cikin fad’uwar gaba da tsinkewar zuciya gabansa sai d’ar d’ar d’ar yakeyi masa, daurewa ne kawai yakeyi saboda su iyaye komai rashin kirkinsu ba’a tab’a chanzasu.
____________________
Yah Basheer yana isa wurin parking lot ya parker mashin d’insa tareda zare key d’insa ya nufi cikin tsakiyar parlourn kai tsaye, yana shiga ya taradda ba kowa cikin parlourn masauki yayi kansa asaman cushion d’in dake malale acikin parlourn, kunna TV show yayi ya fara kallo can bada dad’ewa ba ya tsinkayo muryar iyayensa suna tattaunawa da takun tafiyarsu suna nufo cikin parlourn ,suna k’arasowa cikin parlourn suka zazzauna saman cushion yah Basheer ya gaidasu suka amsa fuska ad’aure tamau tun nan jikinsa ya k’ara yin sanyi sosai, wani irin kallo suke jifarsa dashi mai d’auke da ma’anoni masu yawa Alhaji Tasi’u ne yayi gyaran murya tareda sauke nannauyar numfashin takaici yace”Basheer wato tun wata uku da suka wuce da nace kaje gidansu Naja’atu ka basu hak’uri ka mayarda matarka,ashe baka tafi ba saboda ka rainani bakasan darajana ba akan mi zan baka umurni kak’i bin umurnina!?.
Cikin fargaba da karayar zuciya yah Basheer ya noce kansa a k’asa yana kallon carpet d’in dayake shimfid’e cikin parlourn yace”ba laifina bane Alhaji akasi aka samu ayyuka sunyimin yawa shiyasa kaga banje ba amma badason raina nak’i zuw……”.
Tsawar da Alhaji ya daka masa ne yasa ya kasa k’arasa maganarsa cikin takaici yace”karka kuskura ka k’ara sharamin k’aryarka Basheer idan banda kana k’aton mak’aryaci har tsawon wata uku kace baka samu damar keb’e kwana guda rak kaje bikon matarka ba,wannan maganartaka bata ko kawo kallo ba saboda k’arya ne”.
Basheer ya marairaice fuska yace”kayi hak’uri Alhaji gobe zanje”.
“babu wani hak’urin da zaka bani ka riga ka watsamin k’asa a idanu ka nunamin ban isa dakai ba Basheer, saboda haka na baka kwana biyu kaje ka mayarda matarka idan ba haka ba zanyi mummunan sab’a maka kaji dai abinda na gaya maka!”.
Basheer ya kalli gefen hajiya Hannatu yana rok’onta ta cikin idanu akan ta saka bakinta cikin maganar, hajiya tayi biris dashi tayi kamar dai bata fahimci inda ya dosa ba, sassauta murya yayi kamar na k’warai cikin nadama yace”bazanyi ma kwana biyu banje bikonta ba Alhaji ka yafemin nasan nayi kuskure abaya”.
Alhaji ya tsura masa idanu yana kallonsa na wani lokaci can dai ya kauda kansa yace”babu komai ya riga ya wuce”.
“nagode sosai Alhaji Allah ubangiji ya k’ara girma”.
“Amin”.
Alokacin ne hajiya Hannatu tace”Basheer idan ka mayarda Naja’atu ka daure ka dinga kwatanta adalci atsakaninsu banason na koma jin labarin cewa kana fifita wata akan wata, sannan kayi iya bakin k’ok’arinka wurin ganin ka b’oye soyayyar wadda kafi k’auna azuciyarka domin gidanka ya samu zaman lafiya da kwanciyar hankali”.
Basheer ya gyad’a kansa yace”da yardar Allah zanyi amfani da shawarar da kuke bani iyayena”.
Atare sukace”Allah ubangiji yasa ka gama da duniya lafiya”.
“Amin ya rabbi”.
Tashi tsaye yayi yace”ni zan wuce gida”.
“ka gaida Haseena”.Inji hajiya Hannatu.
“zan gaya mata insha Allahu”.Yana k’arasa maganarsa ya fice da sauri daga cikin parlourn ya nufi inda ya parker mashin d’insa ya zuwa yahau saman mashin d’insa ya fice daga cikin gidan da masifaffen gudu.
********************
Haseena na hango cikin kitchen tana kichaniyar had’a dinner friedrice ce take k’ok’arin girkawa, k’amshin girkin duk ya gauraye sassan cikin gidan gaba d’aya yayinda ta saka wak’a awayarta sai aiki takeyi tana kad’a k’ugu da karkad’a jikinta cikin salo da k’warewa, ta jima da fara girkinta yana dahuwa ta juye abincin cikin babbar kula ta rufe blender ta d’auko ta had’a musu pineapple juice tana kammala komai ta d’auki kular da drink d’in ta aza saman tire direct d’akinta ta nufa da abincin ta ajiye.
Tana ajewa ta fad’a bathroom domin tayi wanka ta d’an jima sosai tana gurza sassan jikinta, sannan daga baya ta fito daga cikin toilet d’in ta samu ta zauna kayan kwalliya ta jawo ta shafe fuskarta da powder ta kawo eyeshadow, mascara,eyeliner duk ta shafa afuskarta sannan ta mik’e tsaye ta ciro lace d’inta black da purple colour ta sanya turarenta ta d’auko ta feshe jikinta dashi, tana gamawa ta dawo ta zauna tana dannar phone d’inta tana murmushin farin ciki, ganin tayi zaman ya isheta dole ta jawo pillow ta kishingid’a samansa tana danne-danne awayarta tana murmushi, ta dad’e tana zaune ita kad’ai saiga sallamar yah Basheer ya shigo cikin d’akin ko amsawa batayi ba domin ita addini bai dameta ba.
Shigowa yayi ya tunkari wurinta k’amshin turarenta ya daki hancinsa ya lumshe idanu ya bud’e yana isa wurinta ya rungomota ta baya yace”baby babu ko sannu da zuwa”.
Tashi zaune tayi tana shagwab’e fuskarta da marairaicewa tace”sorry mijina i miss you so much”.Ta k’ara mannewa ajikinsa saukar da numfashi yayi cikin wani irin yanayi yace”nima nayi kewar rashinki akusa dani babyna”.
Shafar gashin jikinsa tayi tana wani langwab’ewa akan makirci tace”nayi farin cikin dawowarka gida mijina saboda rashinka akusa dani babbar illa ne”.
“idan bana tare dake ji nakeyi kamar in haukace Haseena k’aunarki ba k’aramar kamu tayi mini azuciya ba tabbas kece rayuwata”.
Wani irin dad’i da farin ciki taji ya wanzu cikin zuciyarta yana shawagi asassan jikinta kallon soyayya take jifarsa dashi murmushi k’unshe afuskarta tace”nima soyayyarka ta mamaye zuciyata banda *ABUNDA NAKE SO* fiye dakai, yanzu dai tashi muje kayi wanka kaci abinci domin kada in cikaka da surutu alhalin kana tareda yunwa”.
Peck yayi mata afuska saboda yaji dad’in kalamanta har cikin zuciyarsa da jininsa, mik’ewa yayi tsaye itama ta tashi cire masa tufafi ta farayi sai kallonta yakeyi yana murmushi harta gama cirewa towel ta mik’o masa ya d’aura ya shiga cikin toilet, gyare-gyare tayi tareda k’ara shefe room d’inta da turarurka masu shegen k’amshi.
Saida ta k’ara gyara zanen shimfid’ar gadon sannan ta zauna tana jiran fitowarsa, bai wani dad’e ba saigashi ya fito daga cikin toilet d’in tashi tsaye tayi ta isa wurinsa ta fara goge masa sauran ruwan dake jikinsa, bayan ta goge ta d’auko lotions d’insa ta shafe masa jiki ta d’auko masa jalabiyarsa blue colour ta sanya masa, jan hannunsa tayi ta xaunar dashi saman carpet k’arami data shimfid’a masa tiren abincin ta kawo ta aje agabansa, bud’e kula tayi ta zuba musu abinci aplate d’aya d’aukar spoon d’aya tayi ta bashi d’aya suka fara cin abincin cikin natsuwa da kwanciyar hankali.
Bakajin motsin komai saina spoon d’insu ci sukeyi atsanake babu mai magana,sun jima suna ci daga k’arshe sukaji sun k’oshi kowa ya cire hannunsa tareda aje spoon cikin plate, tattara kayayyakin Haseena tayi ta fice daga cikin room d’in ta nufi kitchen ta wawwankesu.
Tana kammala wankewa ta sanya kular da tiren cikin kwandon kwanoni, d’oraye hannunta tayi ta nufi wurin yah Basheer dake zaune zurum babu abokin fira,tana shiga ta isa wurinsa tana murmushi tace”mijina yi hak’uri na barka kai d’aya cikin d’aki”.