HAUSA NOVELRASHIN SO Complete Hausa Novel

RASHIN SO Complete Hausa Novel

Murmushi yah Basheer ya sakar mata yace”karki damu babyna dama inason in gaya miki wata magana”.
Haseena ta kallesa cikin farin ciki tace”ina saurarenka mijina”.

“su Alhaji ne suka kirani akan inzo gida sunason magana dani, ina zuwa Alhaji da hajiya suka rufeni da fad’a akan cewa nak’i mayarda Naja’atu d’akinta dak’yar na samu na basu hak’uri tareda yi musu alk’awarin zan maidata d’akinta, sannan daga baya suka hak’ura Alhaji ya bani kwana biyu rak inje in mayarda Naja’atu d’akinta shin ke wace irin shawara zaki bani in maidata gidana ko in k’yaleta ta k’arasa can gidansu!? “.Murmushin dake bayyana hak’ora Haseena tayi tace”abinda yafi dacewa shine ka mayarda matarka nima ina goyon bayan haka mijina, saboda kada bakin mutane yayi maka yawa kasan mutane akwai sa idanu da shiga cikin lamarin da bai shafesu ba”………
[11/27, 1:47 PM] Mugiratmusa66: ????????????????????????
*RASHIN SO*
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION*®✍????
(Onward together).

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*

*Dedicated to*
*Sis Najer’art*

_Free page._

*PAGE 17*

Basheer ya gyad’a kansa alamar ya gamsu da bayaninta yace”zanje gidansu gobe in bada hak’uri ta dawo amma saboda darajarki da bin umurnin iyayena kawai zan mayarda ita gidana, amma idan basu ba saidai ta tabbata gidansu saboda babu d’igon sonta araina”.Haseena tace”kadai daure idan kaje karka nuna k’iyayya da rashin sonta agaban idanun iyayenta, domin kasan baxa suji dad’in haka ba”.”Zan kwatanta in gani ko xan iya babyna”.”Ya kamata kam gaskiya ka iya siyasar zamantakewa da mutane”.Basheer ya kalleta yace”kar kiji komai zanyi yadda kikace”.

__________________

Washegari da safe misalin k’arfe tara na safe Naja’atu ta tashi ta share tsakar gidan tas, sannan taje wurin rijiya da gugar jan ruwa ta fara jidar ruwa tana sakawa cikin randunar dake jere agefen tsakiyar gida, cigaba da jidar ruwa takeyi harta gama cika randunar gaba d’aya shiga cikin tayi ta had’a wuta tayi amurhu ta aza tukunya saman murhu ruwa ta d’ebo abucket ta sanya cikin tukunyar dake saman murhu.
Tana sanya ruwa ta rufe tukunyar da murfinta direct cikin d’aki ta nufa ta tayardasu Rufaida da barci tayi musu wanka, ta saka musu kayansu k’ullun kunu ta d’auko da bucket mai murfi ta nufi kitchen dasu ahannunta, acan ta dama kunu ta d’auko ta kawo ta dire cikin d’akin alokacin ne Anna ta tashi tana goge bakinta da aswaki, gaida mahaifiyarta tayi ta amsa mata fuskarta asake suna magana saiga Baffa ya aiko yaro da ledar k’osai da kayan miya ahannu, yana shigowa ya gaida Anna ta amsa ya mik’a mata ledodin ya fice daga cikin gidan.
Yana ficewa Anna ta kirasu Rufaida suka shek’o da gudu suka zazzauna saman tabarma, kowane aka sanya mishi kunu tareda basa k’osai suka fara karyawa sun jima suna shan kunun sannan kowa ya k’oshi Naja’atu ta had’a kofunan ta wankesu ta adana a ma’ajinsu.
Fad’awa bathroom tayi domin tayi wanka ta jima tana wanka daga k’arshe ta fito daga cikin toilet d’aure da zane ajikinta,wurin jikkar data sanya kayan kwalliyarta ta nufa bud’e zip tayi ta ciro powder da lipstick kawai ta shafa afuskarta sannan ta ciro atamfarta brown colour da ash ta sanya ajikinta,d’inkin yayi mata d’as ajiki tareda bayyana tsantsar k’yawon halittarta fatarta sai shek’i takeyi tayi luwai-luwai da ita alamar kwanciyar hankali da hutu sun ratsata, turare ta fesa ajikinta sannan ta nufi wurin mahaifiyarta dake waje zaune tana kallon awakinta da kajinta dake ta zagayar filin gida suna kiwo.
Tana zaunawa gab da Anna mahaifiyarta ta kalleta cikin farin cikin ganin yadda Naja’atu ta chanza cikin lokaci k’alilan akan ta samu natsuwa da kwanciyar hankali, ita Naja’atu kuwa ganin kallon da Anna keyi mata yasa taji kunya ta duk’ar da kanta ak’asa tana wasa da kwaliyar rigarta, ganin abinda Naja’atu yasa tayi murmushi tace”yau kuma kunyata akeji Naja’atu hmmm wai tsohon labari kenan”.
Naja’atu ta sanya tafin hannunta dayasha zanen flowers masu k’yau ta rufe fuskarta tace”Anna kunyarki nakeji sosai ayau saboda naga kinamin kallon k’urilla”.
Anna ta sake kallonta tace”naga kinyi k’yawo sosai kin chanza alamun kin samu natsuwa”.
“kayy ki daina fasamin kai ina wani k’yawo anan?”.
“naji yanzu dai tashi ki aza abincin rana kafin Baffanki ya dawo daga kasuwa”.
Naja’atu ta langwab’e kanta cikin sagarci tace”to Anna bari in tashi inje in girka abincin rana”.
“OK”.Inji Anna.
Naja’atu ta mik’e tsaye ta nufi kitchen shinkafa ta fara dafawa, sannan tayi jajjagen kayan miya ta had’a miyar tumatur taji kifi k’amshin girkinta sai bugarwa Anna hanci yakeyi, tana kammala girkin ta juye abincin cikin kula babba d’aukar kular tayi ta nufi d’aki da ita ta aje.
Komawa wurin mahaifiyarta ta aza kanta saman cinyoyin Anna ita kuma sai shafar tsorayen gashinta takeyi suna fira,sallamar yah Basheer da abokinsa Haliru ta katse musu magana yayinda Baffa Zakari yake gabansu shine ya basu iznin shigowa har tsakiyar gidan, jin muryar Basheer yasa gaban Naja’atu ya fad’i zuciyarta ta tsinke cikin zullumi da fargabar komawa gidansa ta jaye kanta saman cinyoyin Anna ta murtuk’e fuskarta babu alamar fara’a, isowa sukayi har kusaga su Naja’atu Baffa ya dubeta yace”Naja’atu tashi ki k’aro tabarma wannan bata isarmu zama gaba d’ayanmu”.
Su Basheer tsura mata idanu sukayi suna kallon yadda ta chanza ko k’iftawa basayi, zumb’ura baki tayi ta mik’e tsaye ba domin ranta yaso ba sai dai saboda ta cika umurnin mahaifinta, cikin d’akin ta shiga ta d’auko tabarma ta yafa gyalenta saman kafad’arta tana isowa wurinsu ta duk’a ta shimfid’a musu tabarmar suka zazzauna.
Suna zama yah Basheer ya bud’e baki dak’yar bada son ransa ba yace”Baffa dama munzo ne mu baku hak’uri akan abinda ya faru tsakanina da Naja’atu,nasan nayi kuskure abinda nayi ban k’yauta dan Allah kuyi hak’uri ku yafemin, Naja’atu ki yafemin duk d’an Adam ajizine hakan bazai sake faruwa ba”.
Haliru yace”ayi hak’uri Baffa Basheer da kansa ya gayamin abinda yake faruwa kuma nace masa bai k’yauta ba nayi masa nasiha akan ya gyara halayyarsa, domin banason mutumen da yake walak’anta matarsa ta farko”.
Daga Baffa har Anna sun kashe kunne suna sauraren abinda yake fitowa daga cikin bakinsu, Naja’atu dai wani irin k’ololon bak’in ciki da takaici ne ke taso mata azuciyarta cikin damuwa domin tasan ko ta koma mai hali bazai fasa halinsa domin hali zanen dutse ne barinsa saidai mutuwa, kwallar zallar d’acin rai da bak’in ciki ne suka cicciko mata cikin idanunta sharewa ta dingayi a b’oye domin batason iyayenta sun fahimci tana cikin matsananciyar tashin hankali da damuwa, tafi son tayi musu biyayya tareda sanyasu cikin farin ciki na har abada.
Sai asannan Baffa Zakari yayi gyaran murya cikin karamci da dattako yace”Basheer ba komai duk abinda ya faru sharrin shed’an ne saidai aguji gaba sannan nasihar da zanyi maka shine kaji tsoron Allah duk abinda kakeyi a b’oye kasan cewa idan mu bama ganinka, to Allah yana kallonka sannan shi aure da kake ganinsa amana ne tsakanin mata da miji duk wanda ya cuci wani sai amana tacishi,ka kula da tarbiyar ‘ya’yanka tareda basu hak’k’insu domin suma sunada hak’k’i akanka kamar yadda kakeda hak’k’i akansu karka bari son zuciya da rud’in duniya ya kaika ga halaka!”.
Ya k’ara da cewa”Naja’atu mace ce mai rauni duk yadda take ka fita hankali da hangen nesa saboda haka na baka amanarta akaro na biyu, idan ka cutar da ita kaida Allah”.
Maida kallonsa yayi wurin Naja’atu yace”Naja’atu kiyi hak’uri kibi mijinki sauda k’afa tabbas wata rana zaki ci ribar hak’urinki,kuma ki daure ki cire komai azuciyarki tareda fawwalawa Allah ubangiji dukkan lamarinki”.
Kallon gefen Anna yayi yace”ko kinada maganar da zaki fad’a Balira?”.
Anna ta musk’uta tace cikin d’acin rai domin ba haka taso Baffa ya zartar da hukuci ba, taso ya koresu su koma inda suka fito amma tasan sam baxai tab’a iya aikata irin haka ba.
“kusan duk abinda nakeson in fad’a ka fad’a maigida amma inason in k’ara jawa Basheer kunne, ga Naja’atu nan zata koma gidanka duk laifin da tayi maka idan har kayi mata magana bataji ba kazo har gidan nan ka samemu ka gaya mana laifin da tayi maka, ka gani idan bamu ci mata mutunci ba sannan ka d’auki mataki amma bawai ka samu yarinya ba kana jibgarta kamar jaka!To daga rana ita yau karka sake yiwa ‘yata horon duka domin ba’a auren duka yanzu”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button