RASHIN SO Complete Hausa Novel

Haliru ya kalli Basheer shima ya kallesa wani abu ne suka had’iye cikin zuciyarsu, Haliru ya kalleta yace”ayi hak’uri hakan bazai sake faruwa ba dama can farko sharrin shed’an ne”.
“hmm naji kada dai asake dukarmin ‘ya ana fakewa da sharrin shed’an”.Cewar Anna.
Basheer ya sunkuyar da kansa cikin ladabi yace”bazan sake ba ki gafarceni”.
Anna ta b’ata fuska tace”Allah ya gafarta mana zunubanmu”.
“Amin”.Suka had’a baki wurin fad’a.
Naja’atu dai jikinta duk ya mutu domin ta sadak’ar ayau saita koma gidan yah Basheer ko bataso, hawayen takaici da tausayin rayuwarta ne suka cigaba da shatata afuskarta tana gogewa afaikace.
Baffa Zakari ya kalleta yace cikin tsananin tausayinta yace”Naja’atu tashi ki shiga cikin d’aki ki d’auko akwatinki kibi mijinki”.
Cikin bak’in ciki da mutuwar jiki Naja’atu ta mik’e tsaye jiri na neman kwasheta ta fad’i k’asa! Saboda har duhu-duhu take gani cikin idanunta dak’yar ta tattaro dauriya ta shiga cikin d’akin alokacin ne hawayen bak’in ciki da rashin masoyi suka cigaba da gangarowa afuskarta wani irin d’aci da k’ololon bak’in ciki ke yawo cikin jini da sassan jikinta, jawo akwatin tayi ta fito da duk abinda tasan nata ne d’aga murya tayi sosai tace”Rufaida!Rufaida!! Zonan keda Suhail”.
Rufaida da Suhail dake wasanni suka shek’o da gudu suna tserar kawowa wurin Naja’atu dake tsaye tana jiransu, Rufaida ta fara isowa wurinta ta fad’a ajikinta sannan daga baya Suhail ya k’araso wurin mahaifiyarsu yana b’ata fuska kamar zaiyi kuka akan wai Rufaida ta rigashi, saida ta kallesa tayi masa gwalo tace”yeeeh na riga zuwa wurin Ummi”.
Suhail ya zumb’ura baki yace”kinga tana mini gwalo ko Ummi”.
Naja’atu tayi k’yafci cikin hasala tace”banason iskanci Rufaida ki daina tsokanarsa wannan ai salon ki jawa kanki raini ne”.
“na daina ayi hak’uri”.
Naja’atu taja hannunsu suka iso wurinsu yah Basheer da suka mik’e tsaye suna yiwa su Anna sai anjima, Baffa ya k’ara yi musu nasiha da wa’azi mai ratsa jini da tsoka sannan sukayi masa sallama suka fito daga cikin gidan, keke napep suka tarawa Naja’atu itada yaranta ta wuce dasu gida su kuma suka hau mashin d’in Basheer suka nufi hanyar zuwa gidan Haliru, saida ya fara kai Malam Haliru gidansa sannan ya tadda mashin d’insa ya nufi hanyar gidansa cikin tunane tunane……….
[11/27, 1:47 PM] Mugiratmusa66: ????????????????????????
*RASHIN SO*
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????
*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION*®✍????
(Onward together).
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sis Najer’art*
_Free page._
*PAGE 18*
Mai napep d’in ya ajesu Naja’atu agaban gidan mijinta tareda fitar mata akwatinta kud’i ta zaro cikin handbag d’inta ta biyasa, sannan ya shiga cikin keke napep d’insa yabar unguwar d’aukar akwatin tayi ta tisa k’eyarsu Rufaida agaba suka shiga cikin gidan kai tsaye suna shiga cikin tsakiyar gidan suka hango Haseena zaune saman kujerar katako tana gugar tafin k’afarta, jin motsin shigowar mutane yasa Haseena ta d’ago idanunta charab idanunsu suka fad’a cikin na juna, wani irin kallo Haseena tayi mata tareda sakin murmushin mugunta tace”‘yan yaji ne suka dawo lallai kunji dad’in zama gidan mai faskaren itace ji yadda fatarku ta chanza!”.
Maganarta ta soki k’ahon zuciyarta jaye idanunta tayi tace”kodai gidan mai saida kashi ne alhamdulillahi kwalliya ta biya kud’in sabulu, saboda ba rok’o mahaifina yakeyi ba”.
Haseena ta k’yalk’yale da dariyar k’eta tace”afff zancen banza na zata shi Zakarin sata yakeyi yana ciyar da uwarki, dallah gafara can! Inda ba’asan asalinki ba da kinfi nasara bak’ar isa”.
Naja’atu tayi tsaye ta kasa d’aga k’afafunta daga inda take tsaye yayinda su Rufaida suka isa k’ofar parlour suka zauna suna jiran tazo ta bud’e su shiga cikin d’akin..
Nuna kanta tayi cikin zafin kalamar da Haseena ta jefi mahaifinta dashi tace”mahaifina ne b’arawo mai ciyarda mahaifiyata da kayan sata!?”.
Haseena ta d’aga murya k’warai tace”nace Zakari b’arawo ne!Babu abinda zaki iyayi ko kinsan mijina ya bani labarin cewa ba shine yace yana sonki ba *AUREN HAD’I NE* iyayenku suka had’aku ba domin yana so ba!”.
Wani irin fad’uwar gaba taji alokaci guda wani irin k’ololon bak’in ciki da tururin d’acin rai ya danne mata ak’irji ,duk yadda taso daurewa saida kwallar zallar takaici ya zubo mata afuskarta cikin tafasar zuciya tace”shida bakinsa ya gaya miki *AUREN HAD’I NE* mukayi ba auren soyayya ba!?Tabbas yah Basheer ya gama da rayuwata”.
Haseena tace”to zanyi miki k’arya ne ko kina shakka ne akan maganata?To bari idan yazo zansa ya maimaita agabanki ki jiya da kunnenki domin gani ya kori jii”.
Naja’atu ta kauda kanta gefe tace”naji idan yazo kisa ya maimaita d’in”.
Tana rufe bakinta saiga yah Basheer ya shigo cikin gidan d’auke da doya da kiret d’in k’wai ahannunsa direct ya isa wurin k’ofar Haseena ya aje kayayyakin, ya juyo yana kallonsu yace”lafiya baby na ganku tsaye cirko-cirko?”.
Haseena ta yamutsa fuska cikin kissa tace”dama gardama mukeyi da Naja’atu akan ka tab’a gayamin ba auren soyayya kukayi ba na had’i ne,shine nakeson yanzu ka gaya mata abinda ka sanardani agabanta”.
Yah Basheer ya bankawa Naja’atu muguwar harara wanda asanadiyar haka saida zuciyarta ta tsinke gabanta ya fad’i rasssss! Cikin d’aurewar fuska yace”eh nina gaya mata cewa auren had’i akayi mana nida ke ko k’arya na fad’a!?”.
Hawaye masu zafi suka wanke mata fuska girgiza kanta tayi cikin tsananin takaici da b’acin ran da yake kwance saman fuskarta tace”baka fad’i k’arya ba”.K’arasa maganarta keda wuya taja k’afafunta ta nufi bakin k’ofar d’akinta batare data tsaya sauraren irin kalmar da zata fito daga cikin bakinsu ba.
Ganin ta wuce yasa yah Basheer yaja hannun Haseena suka shige cikin d’akinta suna soyewa, Naja’atu ta sanya key ta bud’e k’ofar d’akin suka afka ciki itada ‘ya’yanta saida ta share bedroom da palournta ta gyara dukkan abubuwan dake cikin d’akin saboda yayi datti da k’ura sosai, domin kunsan wata uku ba kwana uku bane tana kammala tsabtace muhallinsu ta shiga cikin bathroom ta watsa ruwa ajikinta sannan ta fito ta d’aura zane da saka riga ajikinta, dayake ak’oshe suke shiyasa batayi dabarar yin girki ba, katangar gidansu tahau taba Saliha Aminiyarta kud’i domin Rayyanu ya siyo mata yoghurt gora biyu, Saliha tayi farin cikin dawowarta gidan Basheer duk yake tasan da wahala ya daina walak’antata tareda musgunawa rayuwarta.
Sun jima suna fira cikin shak’uwa da k’aunar juna sannan daga k’arshe Naja’atu ta sauko saman turmi kamar kada su daina yin firar akan so da yarda, tana sauka ta shige cikin d’akinta bada jimawa ba Rayyanu ya shigo da kansa har d’akinta ya bata sak’onta, duk da godiyar da takeyi masa bai tsaya saurara ba yayi sauri ya fice daga cikin gidan domin kada yah Basheer ya riskesa cikin gidansa.
____________________
Washegari da safe Naja’atu ta tashi ta share bedroom da palournta atsabtace duk inda yakeda k’ura tasa k’yalle ta goge sannan ta fad’a kitchen ta aza ruwan zafi, bayan sun tafasa ta juye cikin plask ta rufe sake zuba ruwa tayi cikin tukunya ta rufe da murfi, d’aukar plask d’in ta nufi d’aki dashi ahannunta tana shiga ta d’auko ledar madara da bournvita,sugar ta d’auko da babban kofi ta had’a tea mai kauri ta sanya sugar kallon Rufaida tayi tace”je kitchen ki d’auko kofuna guda uku”.
“to”.Cewar Rufaida bayan ta mik’e tsaye ta fice daga cikin room d’in.
Bata dad’e ba ta dawo rik’e da kofi uku ahannunta ta mik’awa Naja’atu, amsa tayi ta zuzzuba tea cikin kofunan taba kowa nasa ahannunshi ledar bread ta d’auko ta rabashi gida uku ta mik’awa kowa d’add’aya suka amsa suka fara breaskfast.
Shan tea kawai sukeyi sunyi shiru can Naja’atu ta tashi tsaye tace”tashi muje inyi miki wanka kada Rayyanu ya tafi ya barki kinsan shi bayason yin late aschool”.
K’arasa shanye tean tayi ta cire tufafinta Naja’atu taja hannunta suka nufi toilet, wanka tayi mata tasss sannan Rufaida ta fito daga cikin toilet d’in wurin Suhail ta nufa da yake zaune tace”Ummi tace ka isketa bakin toilet tayi maka wanka”.
Suhail ya kalleta yace”tayani cire tufafina”.
Saka hannu Rufaida tayi tana tayasa cire tufafinsa, ana gama cirewa ya fice daga cikin room d’in ya nufi hanyar bathroom yana isa ya iske Naja’atu tsaye tana jiransa, isa wurinta yayi ta kama hannunsa suka shige cikin toilet suna shiga ta fara yi masa wanka.