RASHIN SO Complete Hausa Novel
Can naga Suhail ya fito daga cikin toilet lullub’e da zane ajikinsa ya nufi cikin room d’inta, Naja’atu kuwa itama tana cikin toilet tana wankanta ta jima tana wanke dukkan b’angarori da sassan jikinta can sai gata ta fito d’aure da zane ajikinta itama ta shige cikin d’akinta, koda ta iso cikin d’akin har Rufaida ta wuce zuwa makarantar boko yayinda Suhail yake zaune cikin kayan da Rufaida ta sanya masa, murmushi ta sakar masa tace”Suhail Rufaida ta wuce ne?”.
Suhail yayi murmushi yace”eh mana Ummi ta tafi school saida ta shiryani sannan ta wuce”.
“Lallai ta k’yauta maka”.Tace tareda zama saman gado ta jawo kayan kwalliya ta fara gyara fuskarta.
Suhail sai kallonta yakeyi can yace”Ummi miyasa kika dawo gidan Abbanmu bayan kinsan acan gidan Baffa munfi sakewa da jin dad’i?Baffa yana matuk’ar sonmu da siyo mana biskit amma Abbanmu baya sonmu hantararmu da tsangwamarmu kawai yakeyi kuma baya siyo mana chocolates”.
Kallon mamaki da al’ajabi ne Naja’atu takeyiwa Suhail tayi shiru ta kasa k’wakk’waran motsi akan maganarsa, gashi dai k’aramin yaro ne amma ya fahimci Abbansa baya sonsu wani irin d’aci taji azuciyarta kwallar zallar takaici da k’ololon bak’in ciki ne ya zubo afuskar Naja’atu saboda Suhail ya sosa mata mikin dake cikin zuciyarta da rayuwarta, saka hannunta tayi ta share hawayenta tace”Suhail ka daina cewa Abbanka baya sonmu yana sonmu mana idan kaga bai siyo muku chocolates bayada kud’i kaji”.
Suhail ya zumb’ura baki tareda karkace kai yace”ai Rufaida ce ta gayamin baya siyo mana kayan dad’i mama Amarya kawai yake siyowa, wai kullum kullum sai ya shigo mata da leda ahannunsa ya shige cikin d’akin Amarya ya bata ita kad’ai”.
Naja’atu ta girgiza kanta cikin son kawar da zancen tace”k’arya take gaya maka babu abinda yake shigowa dashi ahannunsa, saboda haka karka k’ara d’aukar maganarta kaji”.
“na daina bazan k’ara d’aukar maganarta ba Ummi”.
Dad’i taji kad’an aranta ta rungumesa ajikinta tace”da k’yau yaron albarka ko kai fa”.
Tashi tsaye tayi ta ciro riga da sicket d’inta ta saka, tana gama shiryawa ta zauna saman gado tana lumshe idanunta masu haske tunanin rayuwarta na baya ya fad’o mata arai ta cigaba da tunane tunane alokacin ne hawaye masu d’auke da bak’in ciki suke zarya a kumatunta.
**********************
Naja’atu ta kwaso duka uban kayayyakinsu da sukayi daud’a ta nufi wurin famfo ta tulesu wuri d’aya, komawa cikin d’aki tayi ta d’auko roba, bokiti, sabulun wanki da klin ta zauna saman kujera ta fara wankinta cikin sanyin hali.
Tayi nisa cikin wankin kenan harta kusa kammala wankin saiga Haseena ta fito rik’e da k’unshin kaya ahannunta tana isowa wurinta Haseena tayi mata kallon sama da k’asa tace”ga wankin yah Basheer yace in kawo miki ki wanke”.
Naja’atu kuwa ko d’ago idanunta batayi ba bale ta kalleta tace”ki ajiyesu k’asa mana”.
Haseena duk’awa tayi kamar zata aje k’unshin tufafin amma tak’i ajiyewa tasowa tayi daga duk’e ta zazzagewa Naja’atu duka tufafin ajikinta cikin raini da walak’anci tace”banza ga tufafin nan dan ubanki ki wankesu fess idan basu wanku ba zakici gidanku saboda mijina zaiyi miki mugun walak’anci da tozarci iri iri daban daban”.
Naja’atu tashi shiru k’yam tana kallon walak’ancin da Haseena tayi mata, imani yayi mata yawa cikin d’acin rai tace”haba Haseena waike miyasa bak’ya son zaman lafiya!?”.
“eh banason zaman lafiya d’in na zazzaga miki tufafi ajiki zo kiyi abinda duk zakiyi!”.
Fara jaye tufafin tayi ajikinta tana ajewa gefe guda tana gama ajewa ta fara wankin kayansa kallon Haseena tayi tace”babu abinda zan iyayi miki dan Allah surutunki ya isheni ki tafi inda zaki! “.
Haseena ta rik’e kwankwasonta tana girgiza jiki tace”afff iyayin banza na zata akwai abinda zaki iya min ne dana watsa miki tufafi ajikinki, amma sai naga akasin haka”.
“idan bazaki daina kiyi tayi idan bakinki yayi ciwo zakiyi shiru”.
“walak’antacciyar banza wadda miji baya sonta!”.Haseena tana saka mata wannan maganar taja k’afafunta tayi cikin room d’inta tana kad’a k’ugu da karkad’a jikinta cikin salo da yanga.
Tana wucewa hawaye masu rad’ad’i suka wanke fuskar Naja’atu wankin ta cigaba dayi cikin k’unar zuciya da tafasar rai, komai ya fice mata arai akan tsananin b’acin rai da bak’in cikin rayuwa ta rasa sukuni da walwala azuciyarta ta rasa waye zai wanke mata cuta da rad’ad’in dake mak’ale azuciyarta tabbas har abada baxata daina nadamar auren yah Basheer arayuwarta,wanke takeyi zuciyarta cunkushe da damuwa da bak’in ciki idan ta wanke ta sanya ruwa ta d’oraye saita shanya saman igiyar shanya, haka dai ta cigaba dayi harta kusa kammala wankin tana zaune saiga yah Basheer ya fito daga cikin d’akin Haseena, isowa wurinta yayi yana mata wani irin kallo mai cikeda matuk’ar tsana da tsangwama kallon tufafinsa data shanya saman igiyar shanya yakeyi domin ya gani ko sun wanku da k’yau…………
[11/27, 1:47 PM] Mugiratmusa66: ????????????????????????
*RASHIN SO*
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????
*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION*®✍????
(Onward together).
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sis Najer’art*
_Free page._
*PAGE 19*
Yana gama duba wankin ya juyo ahasale cikin suk’uwa yace”Naja’atu wannan tufafin fa basu wanku ba gaskiya ki sake wankesu”.Naja’atu tayi murmushi mai tattare da d’acin rai da bak’in ciki tace”to idan har basu wanku ba yah Basheer ka bari anjima in sake wanke maka kayan, saboda yanzu na gaji sosai jikina duk yayi tsami da ciwo”.Harara ya jefeta dashi alokacin ne yakejin wani irin sinadarin tsanarta da rashin so yana taso masa a k’irji cikin zafin rai da tafasar zuciya yace”keee munafukar Allah ba zanyi miki lamuni ba yanzu nakeson ki wanke mini tufafina!”. Fargaba da tsinkewar zuciya ya ziyarci Naja’atu ta kallesa cikin tattausan lafazi tace”kayi hak’uri naji zan sake wanke maka tufafinka”.
“shi yafi miki sauk’i”.Inji yah Basheer aharzuk’e.
Yana gama masifarsa yaja k’afafunsa yayi wucewarsa zuwa wurin Haseena.
Naja’atu cikin matuk’ar gajiya da galabaita ta jawo kayan data wanke ta k’ara wankesu tass, sannan ta shanya saman igiyar shanya tana kammala wankin ta wanke hannunta cikin ruwa masu tsabta, ta mik’e tsaye kenan zata shige cikin d’akinta saiga yah Basheer ya sake fitowa daga cikin d’akin Haseena, isowa wurinta yayi yana kallon kayan data gama sake wankesu d’aya bayan d’aya yana girgiza kansa.
Dubawa ya cigaba dayi har ya gama dube-duben tufafinsa juyowa yayi ahasale idanunsa sunyi jajir b’acin rai da tsantsar harzuk’a kwance cikin k’wayar idonsa dak’yar ya bud’i baki yace”Naja’atu yanzu keee haka uwarki ta koya miki wanki!?”.
Cikin tsananin tsoro da karaya Naja’atu ta dubesa tace”yah Basheer mi ya kawo zance uwata acikin wannan maganar?Inace wanki ka bani inyi maka kuma nayi to ba magana ta k’are ba! “.
Rikitacciyar tsawa ya daka mata wanda asanadiyar haka saida ta tashi zurawa da gudu cikin kakkausar murya yace”ke atunaninki wannan tufafin sun wanku kenan ke wace irin wawuyar mace ce wadda batasan yadda zata sace zuciyar mijinta ba?To bari kiji kowa yayi miki tsaye acikin gidan nan sai kin sake wankemin tufafina saboda dattinsu bai fita ba!”.
Cikin kad’uwa da rad’ad’in zafin kalamansa da suke iya tarwatsa zuciya zama guda tace”haba yah Basheer ka tausayamin wlh wannan wankin ya wanku na gaji sosai fa tun d’azu nakeyin abu d’aya!”.
“babu tausayi da so tsakanina dake! Domin haka dolenki ki sake wankemin tufafina”.