HAUSA NOVELRASHIN SO Complete Hausa Novel

RASHIN SO Complete Hausa Novel

Hawaye suka zuba a k’yakk’yawar fuskarta wani irin d’aci ke wanzuwa azuciyarta tabbas yah Basheer baiyi mata adalci arayuwa ba, ya tsangwameta da nuna mata tsantsar *RASHIN SO* azamantakewar rayuwar aurensu.
Jijjiga kanta takeyi tana rok’onsa gurfanawa tayi saman gwiwowinta hawaye masu rad’ad’i sai shatata sukeyi asaman fuskarta, rik’e k’afafunsa tayi tace”yah zan wanke maka amma kayimin hak’uri zuwa anjima kad’an dan girman Allah, zan wanke maka yanzu jikina duk rad’ad’in gajiya yakeyimin”.
Yah Basheer cikin tsananin tsana da tafasar zuciya yasa hannu ya tunkud’eta ta fad’i k’asa rikcham! Kanta ya bugi k’asa wani irin rikitaccen zafi da ciwo ya ziryaci k’wak’walwa da sassan jikinta cikin zafi ta saki gigitacciyar k’ara tace”ina lillahi wa inna ilaihirraji’un!Basheer so kake ka kasheni akan baka sona lallai ayau na tabbatar babu sauran imani acikin zuciyarka!”.
Basheer yace”nine mara imani yau zan nuna miki mahaukaci nake banida imani!”.
Dak’yar tace cikin rad’ad’in ciwo”duk abinda zakayi kaje kayi kafin kayi dubunka sunyi!”.Ta rufe bakinta ta mik’e tsaye dak’yar zata fice daga wurin yah Basheer ya fisgota da k’arfi tareda d’auketa da gigitattun maruka guda biyar wanda asanadiyar haka saida ta zabura da k’arfi! Ficewa tayi daga cikin hayyacinta da natsuwarta can ta sake wuntsila k’asa ta fad’o d’immmmm ta some! Jini ya cigaba da gangarowa daga cikin baki da hancinta.

Ganinta kwance a k’asa baisa yaji d’igon tausayinta azuciyarsa ba,saima nufar inda take yasshe cikin wani mayuwacin hali yayi gadan gadan kallo d’aya zakayi masa ka gano bai ji shakku ba bale ya razana yana isa inda take kwance ya shureta ko motsawa batayi ba, sa k’afafunsa yayi yahau saman jikinta da takalmi cikin k’ask’anci kamar wanda ya taka k’asa ko dutsi haka yayi mata, yana samanta tsaye saiga Haseena ta fito daga cikin room d’inta zata d’ibi ruwa akofi.

Tana isowa idanunta ya sauka akan Naja’atu dake kwance a k’asa zaune! Ganin yah Basheer yayi tsaye samanta yasa Haseena ta razana da kad’uwa alokaci guda tsoro da fargaba ne ya ziryaceta, cikin sassarfa ta k’araso wurinsa tace”yah Basheer lafiya mi kayi mata ne kardai kacemin ka kashe matarka da hannunka!?”.
Yah Basheer ya kalli cikin k’wayar idonta ya hango tsoro da fargaba ne kwance acikin idanunta murmushi ya sakar mata yace”a’a ban kasheta ba suma ne kawai tayi”.
Haseena ta dinga maimaita maganar azuciyarta tana cewa ji wannan sakarai suma yake kira da kawai baisan daga suman nan ba ana iya zarcewa har mutuwa! Ganin ta dulmiya cikin kogin tunani yasa yah Basheer ya jijjiga kafad’arta tayi firgigit ta dawo cikin hayyacinta, alokacin da natsuwarta ta dawo tayi sauri ta nufi famfo ta ciko kofi da ruwa, tana zuwa wurin Naja’atu bata tsaya b’ata lokaci ba ta juye mata duka ruwan ajikinta tayi sharkaf ta jik’e mata da kaya da ruwa.

Basheer ya kalleta yace”kee miye haka zaki wani zuba mata ruwa?”.
Harararsa tayi tace”ya bazan zuba mata ruwa ta farfad’o ba ko so kake ta mutu akamamu!”.

Basheer yayi shiru saboda yasan abinda ta fad’a gaskiya ne, can Naja’atu ta fara motsi da hannu numfashinta ya dawo dak’yar tana gama dawowa cikin hayyacinta ta tashi zaune tana cije baki alamar ciwo da zafi yana nuk’urk’usarta, duhu-duhu take gani jiri yana neman kwantar da ita lalube ta farayi da hannunta tace”dan Allah wanda yake kusa dani ya taimaka ya kaini d’akina”.

Alokaci guda Haseena taji wani irin tausayinta ya d’arsu azuciyarta da sauri ta isa wurinta ta taimaka ta mik’e tsaye tace”sannu kinji Allah ya baki lafiya”.

Jin murya kamar ta Haseena yasa Naja’atu ta k’ame wuri d’aya kamar gunki cikin al’ajabi tace”muryar wa nakeji kamar ta Haseena?”.

Haseena tace”nice ba kama bace”.

Basheer dai yana tsaye wuri d’aya yana kallon ikon Allah ,Naja’atu ta langwab’e kanta cikin marairaicewa kamar zatayi kuka tace”dan Allah ki taimaka ki kaini d’aki kada Abban Suhail ya kasheni!”.
“kwantar da hankalinki bazan tab’a bari ya cutar dake ba”.

“to.. to..nagode sosai”.Cewar Naja’atu.

Haseena taja hannunta ta kaita har cikin d’akinta tana kaita ta d’auko first aid box ta wanke mata ciwon kanta cikin tausayinta,sannan ta sanya mata bandage agoshi domin ya tsayar mata da jinin dake shatata afuskarta tana kammala taimaka mata, taja k’afafunta ta fice daga cikin d’akin da saurinta.

Koda ta iso tsakiyar filin gidan bataga kowa ba dole yasa ta nufi cikin d’akinta cikin sassarfa, azaune ta isko yah Basheer fuskar nan tasa amurtuk’e yace”yanzu abinda kikayi kin k’yauta kenan?taya ina dukan matata zakizo ki shiga tsakaninmu gaskiya banji dad’in wannan abin ba!”.

Kallon dake k’ara narkar da zuciyarsa ya fad’a cikin kogin soyayyarta tayi masa tace tana wani kashe idanu da yin k’asa k’asa da murya”haba mijina farin cikin rayuwata don kawai na hana ka kashe rai shine nayi laifi? Banaso ne kayi kisa amma bawai inada ikon in hana maka ka zartar da hukunci akan matarka ba, kayi hak’uri bazan sake shiga tsakaninku ba! “.
Juyar da kanta gefe tayi kamar tayi fushi asanadiyar haka jikin yah Basheer yayi sanyi saboda babu abinda ya tsana aduniya irin yaga Haseena tana fushi dashi, cikin sanyin jiki ya k’araso wurinta gab da gab suna jin numfashi juna yace”karkiyi fushi dani Hasee baby domin fushinki agareni zai iya tarwatsamin zuciya na fahimceki bak’ya laifi awurina, don haka kiyi hak’uri kinji masoyiyata”.Ya fad’a tareda rungumeta ajikinsa ita kuma sai langwab’ewa takeyi tana murmushin jin dad’i.

Cikin farin ciki tace”ba komai banyi fushi dakai ba mijina karka damu”.

Haseena ta had’e bakinsu wuri d’aya tareda fara aikawa junansu zazzafan sak’onni masu rikita k’wak’walwar d’an Adam, ganin suna shafe shafe da tsotse tsotsensu dole yasa naja k’afafuna saboda kada in gano abinda zaisa in makauce.

**********************Naja’atu tana kwance cikin rad’ad’i da zafin ciwo ta jawo k’aramar nokiar wayarta ta turawa Saliha sak’o akan tazo d’akinta, sak’on yana shiga ta cigaba da fitar da numfashin wahala da galabaita yayinda wani irin tururin d’acin rai da bak’in ciki yake nuk’urk’usar zuciyarta hawaye masu zafi suka samu muhalli afuskarta, bada jimawa ba saiga Saliha ta shigo arazane ta iso saman gado ta zauna tace”Subahanillah!Naja’atu mi zan gani haka waye yaji miki ciwo agoshi?”.

Hawaye suka cigaba da sintiri afuskarta babu k’ak’k’autawa cikin yanayin bak’in ciki tace”yah Basheer ne yake neman kasheni da sauran raina!”.

Cikin fargaba Saliha ta bugi k’irjinta tace”akan wane dalili yakeson ganin bayanki”.

Naja’atu taja numfashi mai tattare da damuwa da d’acin rai tace”saboda *RASHIN SO* Saliha kinsan idan mutum baya sonka zai iya yin komai don ganin ya kawar dakai adoron duniya! Ki taimaka ki kaini gidanmu wannan auren ya isheni idan har baso kikeyi awayi gari na zama gawa ba ki kaini gidanmu”.Tana kai k’arshen maganarta ta saki rikitaccen kuka mai cikeda bak’in ciki da tasku arayuwa.

Hawayen tausayinta suka cika idanun Saliha suna zuba afuskarta tana sharewa cikin matuk’ar tausayi da takaicin rayuwa tace”karkiyi haka Aminiyata idan kika sake komawa gida su Baffa baza suji dad’i ba kiyi hak’uri ubangiji yana tareda bayinsa masu hak’uri sannan komai zai wuce kamar amafarki”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button