RASHIN SO Complete Hausa Novel

Gunjin kukan Naja’atu kawai ke tashi cikin d’akin girgiza kanta tayi tace”hak’urina ya k’are zuciyata zata iya fashewa idan ina cikin gidan Basheer farin cikina ya tarwatse asanadiyarsa, har zuwa wane irin lokaci kike tunanin zan iya riskar kaina cikin farin ciki da nishad’i babu rana babu lokaci!? “.
“ki daina fad’ar haka duk mai rai baya cire tsammanin samun rahamar ubangiji, kada k’unci da taskun rayuwa yasa kiyi sab’on Allah”.
Cigaba da shasshekar kukanta kawai takeyi cikin k’unci tace”bazaki fahimci yadda nakeji azuciyata ba sai yaushe zanyi farin ciki arayuwata sai yaushe zanji dad’in rayuwar aure, wannan wace irin *K’ADDARA CE* mai cikeda matuk’ar tashin hankali da tarwatsa zuciyar d’an Adam!?Allah gani gareka ina rok’onka idan laifi nayi maka kake jarabtata da wannan muguwar k’addarar ka yafemin”.”Ki daure ki cire komai azuciyarki Naja’atu ubangiji shi kad’ai yasan abinda yake b’oye”.Tana rufe bakinta ta fashe da wani irin rikitaccen kuka tana taya k’awarta Naja’atu kallo d’aya zakayi musu sai sun baka matuk’ar tausayi da ban takaici, saboda kukan da sukeyi kuka ne mai nuna tsagwaron damuwa da k’uncin rayuwa rungume juna sukayi sunata zubar da kwallar zallar takaici da haushin yadda rayuwa ke juyawa d’an Adam, cigaba da kukansu sukayi saida suka ci suka k’oshi sannan Saliha ta tattaro dauriya da hak’uri ta dinga lallashin Naja’atu tareda bata maganganu masu sanyaya zuciyar mai sauraro………
[11/27, 1:47 PM] Mugiratmusa66: ????????????????????????
*RASHIN SO*
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????
*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION*®✍????
(Onward together).
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sis Najer’art*
_Free page._
*PAGE 20*
Dak’yar da sud’in goshi Saliha ta samu Naja’atu ta daina kuka sannan ta k’ara bata hak’uri akan ta daure ta cigaba da zama agidansa, ko domin saboda tarbiyar ‘ya’yanta ganin ta sauko yasa ta k’ara yi mata nasiha akan hak’uri da rungumar k’addararta hannu bibbiyu sannan tayi mata sallama ta wuce gidan mijinta.
Tashi tsaye Naja’atu tayi idanunta duk sun kumbura tareda yin jajir alamar tasha kuka ta k’oshi kallon agogo tayi taga sallar azahar harta soma wucewa, da sauri ta fad’a bathroom tayi wanka tareda d’auro alwala sharp sharp ta fito daga cikin toilet d’in, shimfid’a sallaya tayi ta jawo hijabinta ta sanya tareda kabbarta sallah raka’a hud’u.
Bayan ta sallame sallah ta zauna saman sallaya qur’ani ta jawo ta fara karantawa cikin zazzak’ar muryarta kamar anbusa sarewa, ta jima tana karatun qur’ani mai girma sannan ta ajeshi gefe saman inda take ajiye littafan addini, zaunawa tayi ta fara kwararo addu’o’in neman sassauci azuciyarta tana addu’a hawaye sai sintiri sukeyi asaman fuskarta, kallo d’aya zakayi mata ka hango rashin kwanciyar hankali da bak’in ciki cikin a k’wayar idanunta, duk ta chanza yanayinta da kammaninta sun juye ta koma kamar ba ita ba akan tarin damuwa da k’angin rayuwa.
Ta dad’e tana kwararo addu’o’i sannan daga baya ta shafa addu’ar afuskarta tareda linke sallaya ta adanata asaman cushion, cire hijabinta tayi ta kwanta saman gado tana hango abubuwan da suke faruwa da ita marasa dad’i da tsantsar takaici arayuwarta, cikin ikon Allah batada masaniya barci b’arawo yayi awon gaba da ita..
____________________
*BAYAN WATA BIYAR*
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikin gidan yah Basheer babu wani sauyin rayuwa, kullum Naja’atu k’unshewa takeyi cikin d’akinta tasha kukanta babu mai lallashinta saboda yah Basheer ba k’aramin walak’anci da tozartata yakeyi ba, har lokacin baya bata ci, sha, sutura bale hak’k’inta na auratayya hantararta da tsangwamarta yakeyi akowane lokaci, wata rana har dukanta yakeyi yana zagin iyayenta saidai ya buga sai ya gaji babu mai bashi hak’uri.
Cikin wannan k’untacciyar rayuwa Naja’atu ke zaune agidansa ta rasa mi ke mata dad’i aduniya, farin ciki da kwanciyar hankali duk sun tarwatse mata asanadiyar rashin so da tsagwaron k’iyayyar mijinta, ji takeyi da wannan rayuwar bak’in cikin da take ciki gwamma ta mutu tabar duniya, domin ko gidansu taje ta sanarwa iyayenta babu abinda zasu ce mata illa kije kiyi hak’uri komai na duniya yanada k’arshe! Gashi har yanzu ta kasa ganin k’arshen abin yazo saboda yanzu ma abin na yah Basheer ya k’ara shahara domin ko ‘ya’yanta idan har ya fara dukansu sai yaga numfashinsu yana batun d’aukewa sannan yake daina dukansu, shiyasa yaran suka shiga tsoronsa sosai kamar mala’inkan d’ibar rai ko muryarsa sukaji yanzun suna shek’awa da gudu su b’oye domin kada idanunsa yayi tozali da fuskarsu.
Idan yana cikin gida basa fitowa har sai ya fita waje, idan suna wasa tsakiyar gidan sukaji kukan tsayuwar mashin d’insa zumbur suke tashi su shek’a da gudu d’akin mahaifiyarsu, ire-iren abubuwan ga ne ke k’ara k’onawa Naja’atu rai tareda haddasa k’iyayya mai zafi azuciyarta, shi kuma baya damuwa idan yaga yaransa suna gudunsa sai ma wani jin dad’i da tink’aho yakeyi akan iyalinsa suna matuk’ar tsoronsa kamar zaki.
Naja’atu dai ta k’ara jawo ‘ya’yanta ajiki tana basu kulawa da nuna musu tsagwaron soyayyar gaskiya, ta haka ne suke samun sauk’in damuwa aransu saboda alal hak’ik’a yah Basheer ba k’aramar takurawa da nuna musu k’iyayya yakeyi azahiri ba, saboda bayason mahaifiyarsu haka suma su Rufaida baya k’aunarsu ko kad’an azuciyarsa, haka suke zaune ak’untace cikin gidan ko bak’in kare ya fisu daraja suda Naja’atu.
____________________
*BAYAN SATI D’AYA*
Naja’atu ce kwance cikin blanket ta lullub’e jikinta saboda batada lafiya zazzab’i ne ke damunta, jikinta duk yayi mugun zafi sosai akan zazzab’i dak’yar take fitar da numfashin ciwo hawaye masu rad’ad’i sai zuba sukeyi daga idanunta saboda idan ta tuna da irin abubuwan da suke faruwa da ita sai taji d’aci da k’ololon bak’in ciki ya tokare mata a k’irji, yayinda Rufaida take zaune kusa gareta tana mata firfita da faifai tareda share hawayenta tace”sannu Ummi Allah ya baki lafiya”.Suhail yana kwance gefenta yana barci da minshari Naja’atu tayi hucin zafin zazzab’i tace”Rufaida ki d’aukomin panadol da ruwa cikin bak’ar leda in sha magani”.
“to Ummi sannu”.Tana rufe bakinta ta mik’e tsaye ta nufi wurin ledar magani da ruwa akofi ta kawowa Naja’atu maganin tasha tana yamutsar fuskarta kamar zata fashe da kuka.
Bayan ta had’iye maganin mak’wat ta mik’awa Rufaida ledar da kofin ruwan tace”ki mayarda ledar inda kika d’aukota”.
Rufaida ta amshi ledar da kofin taje ta maida a inda ta d’auko, sannan ta dawo ta cigaba da yiwa mahaifiyarta firfita cikeda tsantsar tausayi da damuwa, numfashin ciwo Naja’atu ta cigaba da fitarwa zufa sai tsattsafo yakeyi ajikinta.
Suna k’unshe cikin d’akin awaje hadari ya taso da iska mai saka sanyi nan da nan gari yayi duhu giragizzai suka bayyana acikin sararin samaniya, iska mai cikeda k’ura ta dinga kwasar hakukuwa da tsakuwa suna wulli dasu nan gari ya game bak’ik’irin hadarin ya kama tafiya har ya koma gabas, nan da nan aka fara tsuga ruwa kamarda bakin k’warya iska huhuhuhu sai shigowa takeyi cikin tagogin d’akinsu Naja’atu, rufe jikinta Naja’atu ta sakeyi tanata rawar sanyi da zafin zazzab’i Rufaida ta tashi tsaye ta kulle tagogin d’akin ta dawo ta zauna tana zama saiga yah Basheer shida Haseena sun shigo d’akin kai tsaye, suna shigowa tsakiyar d’akin Naja’atu da take lullub’e cikin bargo ta hangosu gabanta taji ya yanke ya fad’i dummm! Hankalinta yayi k’ololuwar tashi sosai zuciyarta ta girgiza ta k’ara lahewa tayi cikin bargon kamar mai yin barci, yah Basheer ya kalli Rufaida yace”keee tayarda mahaifiyarki daga barci!”.
Rufaida ta marairaice fuskarta tace”Abba batada lafiya fa”.
“keeee! Banason iskanci ki tayarda ita daga barci nace!”.Ya fad’a cikin tsawa da hargowa.
Jikin Rufaida yana makarkatar tsoro ta nufi wurin mahaifiyarta dake kwance,kafin ta iso gaban Naja’atu saita ta shi zaune cikin tururin zazzab’i dak’yar ta bud’a baki tace”lafiya mi nene yah Basheer!?”.